A blurb for you
by @bintuuu
Bismillahir Rahmanir Rahim
MURADIN ZUCI📖📚
Bintu Musa ✍️
KADDARA....Itace sanadin da yasa ta tsinci kanta acikinsu. Daga lokacin da ta fara mallakar hankalinta ta fahimci banbancin ta da ahalin da ta daukesu jininta.
"Amma menene laifinta dan kaddararta tazo a hakan?"
"Shin me tayi da yasa take fuskantar kalubale daga garesu?"
Wannan sune tunanin FADWA a kullum. Amma kuma duk hakan tana daukansu da sauqi wani lokacin in aka hada da zafin da takeji na yadda kaddara ta hado ta cikin ahali daya da SHI.
Ta aminta da cewar har abada batada babban maqiyi kamarsa. Tana jin har abada zuciyarta bazata taba sauqowa akan abunda ya mata ba.
Saidai abunda bata sani ba shine kaddarar rayuwar ta tana manne da tashi. Ya zatayi Idan ya zamo shine qarshen bangon majinginar ta a lokacin da ta rasa madafa?
Labarin Muradin zuci zai tabo wani bangare ne na sabanin fahimta da ake samu a rayuwa. Kuma zamuga shin har tsawon wane lokaci zuciya take iya danne son wanda take matuqar so? Shin soyayyar da aka rayu da ita acikin zuciya takan iya boyuwa?
Har zuwa yaushe?
Ni Bintu Musa zan warware muku komai a sannu. Tafiya ce da nake fatan zata taba muku zuciya kamar yadda KUNCIN ZUCI yayi.
MURADIN ZUCI paid Book ne da zai fi karkata anan Arewapen, masu buqatar bi ta WhatsApp kuma zaku biya #500 ta wannan Account din: 8134692758 Opay
Fatima Musa Maina
Shaidar biya ta wannan layin. ***