NACINA YA JAWO MINI..

Chapter 1

by @narrnarhhbukar00

*_The Amazing Pen_ ✍️..........*








*_NACINA YA JAWO MINI..._*




*001🔥*

*KADUNA*

Zaune suke ɗaliban shiru a aji kasancewar malamin Maths ne kuma gashi mugu, hakan yasa ɗaliban maida hankulansu gaba ɗaya gun allon,calculations yake yana bayani amma babu mai ganewa, yana kai karshe yace "Do you all understand" ɗaliban sukace "yes" saboda tsoransa da sukeyi.
 Uncle Musa yace"Good, now let me give class work ". 
Nanfa ɗaliban suka ruɗe,Uncle Musa ya rubuta calculations guda biyu a board, sannan yace su fara. 
Kwasam saiga wata  yarinya wacca bata wuce shekara 15 a duniya tashigo da gudu tana haki, saboda gudun da tasha, kawai ɗaliban sukeyi Uncle Musa yace," Stop there!!!",  cike da tsawa, haka yarinya ta tsaya jikinta na ɓari, kafafunta suna rawa.  

Uncle Musa yace" why are you late in my class".  Cikin rawar murya yarinyar tace"I'm sorry Sir". Kawai sai tafashe da kuka, suko ɗalibai daɗi suke taji, harda dariya ƙasa ƙasa kar malamin yaji su,Uncle Musa yace "kneel down and give me your hand, next time you won't there come late to my class". 

 Haka yarinyar ta miƙa hannunta tana kuka, yako zaneta babu sassauci, tashi tayi daga kneel down ɗin ta wuce seat ɗinta wanda yake gaba ta zauna, kuma yace saita yi class work ɗin.
 Baiwar ALLAH haka ta ciro littafinta tafara rubutu,cikin wasu mintuna sai gata tagama class work ɗin taje yin submitting, cike da mamaki Uncle Musa ya bita da kallo, ɗaliban ma sai haushinta sukeyi saboda tafisu nacin karatu da hazaƙa, haka ɗaliban suka kasance har lokacin tashi break yayi suka fita. 

Bayan sun fita suna wasa naji ance Sa'eeda, ashe yarinyar nan ce wacca Uncle Musa ya duka a aji ce, waiwayowa tayi tana kalonta tare da  cewa "Maryam ya akayi ne"  wacca aka Kira da Maryam ta ce "Sa'eeda meyasa kikayi latti, bayan kinsa yau Uncle Musa muke dashi" cike da damuwa Sa'eeda tace"Hmmmm Umma kande ce ta aikeni kuma wurin da nisa, shiyasa nayi latti" Maryam tana kallonta da mamaki ta ce"Amma tasan zaki makaranta ai, shi ne ta aikeki alhalin tanada mayyan Yara 'yan mata ",   murmushi mai ciwo Sa'eeda tayi sannan tace" Bakomai ai lokacine, watarana sai labari ". 

 Haka suka cigaba da hiransu har aka koma aji, darussa  aka cigaba dayi har 2:00pm tayi aka tashi gida.
           
                @@@@@@@@@

A natse suke tafiya ita da Maryam  suna hiransu, har kowa ya bi hanyar gidansu. Tana shanyo kwanar gidansu gabanta ya fara dukan uku-uku saboda tasan aikin gida na jiranta,haka ta isa har zauran gidansu tana ɗauke da sallama, amma babu amsa duk da akwai mutane a gidan, shiga tayi ɗakin mahaifiyarta tare da sallama, cike da so da ƙaunar ƴarta ta tilo ta amsa tana fara'a, gaisheta ta yi sannan ta ajiye jakarta.

Zama tayi tana" Washhhhhh ALLAH na", Ummanta dake linke wankin kayan mutanen da tayi ta ce"ALLAH yasa dai ba'a miki dukan latti ba" marairaice fuska ta yi kamar za ta yi kuka sannan ta ce"ALLAH Umma sai da Uncle Musa ya duke ni hada saka ni kneel down"cike da tausayin ƴarta ta ta ce"Karki damu ƴar albarkha wata rana sai labari kin ji, ki ci gaba da haƙuri, in shaa ALLAH baza mu dawwama a haka ba, Ubangiji zai taimake mu".

 Sa'eeda tace "Umma bara na yi sallah sai inje in yi aikina" da kallo tabi ƴarta dashi tana tausayin halinda suke ciki. 

Tuno kyara da tsangwamar da suke fuskanta ita da ƴarta wurin kishiyarta da mijinta yasa ta zubar da hawaye. Fitowar Sa'eeda daga ɗaki ke da wuya tabji Umma Kande na kwalla mata kira har da ɗura mata ashariya  da ce wa "Ubannwa kika ajiye da zai miki aikin gidan! " a daburce Sa'eeda ta ce"Uhm... Uhmm sallah dama nakenso nanyi sai nanfito  aikin ". 

Tsaki mai karfi tanja tana cewa" Aikin banza, Ke ga ustaziya koh, maza kinyi sallar nanbaki minti 10 kinzo ki yi aikin! ". A tsorace tace" To". 

Haka taje tayi sallah Ummanta na kallonta cike da tausayi ko abinci bata ci ba, taje ta gama aikin kafin ta dawo ɗakinsu tashi abinci.

             @@@@@@@@@@

Wurin karfe 4:00pm na yamma ta shirya zuwa islamiya wacca take bayan layinsu, tana tafiya tana karatunta cikin murya mai zaqi ga ƙira'ah mai daɗin gaske,har ta isa makarantar.

Faslul Imam Shafi'i naga ta shiga wato ajin ƴan sauka,zama tayi a bencin farko, duk da akwai ɗalibai amma bansuda yawa, saboda yanzu ake shigowa, jakarta ta bude ta fito da Hadisi tana dubawa,a haka aka cika ajin har malaminsu ya. shigo tare da sallama, duka ɗaliban suka amsa , sannan ya zauna yana fuskantar ƴan aji.

Malam Yusuf ya ce "Alhamdulillah tunda kun sauke har sau biyar, kuma wasunku ma sun kammala haddar alqur'ani mai girma, toh don haka time table na jarabawan sauka zai fito gobe, ku shirya sosai, sannan za mu fara Karatuttukan sauka cikin satin nan".
 Farin ciki ne ya mamaye 'yan ajin ban da Sa'eeda wacca tasan ba suda halin biyan kuɗin saukar duk da tafi kowa hazaƙa a ajin gabadaya. 
Malam Yusuf ya katse musu surutu da cewa"Sannan k ufada wa iyayenka maganar kuɗin sauka a kan an yanke naira dubu ashirin ga kowani ɗalibi (#25,000) ".
Haka ya bar ajin, su kuma sai murna suke yi ban da Sa'eeda wacca ko ƙawa bata da ita a ajin sai dai a boko, haka suka fara maraji'ah har lokacin tashi ya yi aka tashe su, suna fitowa Sa'eeda ta nufi office ɗin shugaban makarantarsu, don ita gaskiya ta fasa saukar don Ummanta bat ada halin biyan kudin saukar, gashi mahaifinta yana dashi babu laifi yana noma amma bazai biya mata ba, koda ma ya yi niyyar biya, kishiyar Ummanta zata hana saboda ta ga yaranta basa karatu sai talla,da wannan zancen zucin ta shiga office ɗin shugaban makarantar da sallama.
Malam Harun ya amsa cikeda fara'ah yace"Sa'eeda kace haka ". Tana murmushi ta ce" Eh malam, daman na zo ne wurinka".
 Sai ya ce "To to inajinki Sa'eeda". Sai data lumfasa kafin ta ce "Malam dama game da maganar saukan'r mu ne, shi ne nazo ince ma ko za a iya cire ni daga cikin 'yan saukan saboda a gaskiya iyayena basu da halin biya mini kuɗin sauka, shi ne na ce ko za'a cireni sai wani lokacin". 
Shiru ya yi yana kallonta tare da yin nazari, don gaskiya ya san ba suda halin biya hasalima a scholarship Sa'eeda take tun daga aji daya har zuwa aji shida  saboda hazaƙar ta,haƙiƙa bai dace ya dakatar da Sa'eeda ba kodan ƙoƙarinta da natsuwarta.
Kawai ya ce "Sa'eeda ", cikin taushin murya ya ƙara da cewa" Na ji bayananki, kuma na fahimta, in shaa ALLAH hukumar makaranta zat a duba don baza mu ji daɗi ace mai hazaƙar aji bata yi sauka ba saboda rashin kuɗin sauka ba, ki kwanatar da hankalinki in shaa ALLAH, ALLAH zai rufa asiri".
Haka sukayi sallama cike da farin ciki tawuce gida. 

                    @@@@@@@@@

Isarta gida keda wuya aka fara Kiran sallah, jakarta ta ajiye taje alwala sannan tayi sallah, sai taci abincin dare kana  ta dauko assignment ɗinta na makaranta tayi, sai ta yi karatun littattafanta na boko da islamiya, sannan ta sanar ma Ummanta yanda sukayi batun sauka da shuganban makarantar su, cike da farin ciki ta ke jin ƴarta na mata bayanin yanda sukayi da shuganban makarantarsu.
 Sa'eeda na kammala bayininta sai mahaifiyarta ta ce"ALLAH kai ne abin Godiya, ka ƙara rufa mana asiri duniya da lahira". Ameen Sa'eeda ta bita dashi.
Washa gari ta tashi da wuri kasancewar tasan aiyukanta na gida, ta soma yi don tsoron yin latti a zaneta, haka ta kammala tayi shirinta tsaf, sannan ta karya kumallo,ɗaukar jakarta tayi ta fito tsakar gida tana shirin wucewa ta ji an ƙwalla mata kira, a tsorace ta waiwayo sannan ta amsa saboda jin wacca tai mata Kiran, "Ke dan uwarki zo nan". 
Kanta aƙasa ta nufo inda take, kafin ta ƙaraso wurin ta ji an hankaɗeta, ji ka yi timmmmm a ƙasa gashi gidan nasu ko siminti babu, haka uniform ɗinta yayi buju-buju ,a rauna ne ta ɗago idanunta cike da ƙwalla tana kallon budurwar wacce ta riƙe ƙugu tana girgiza kai alamun masifa.
Sa'eeda da ƙyar ta iya miƙewa tana dubanta  ta ce "Haba Nusaiba, mai na miki kika ture ni alhalin akwai filin da zaki iya wucewa ba tare da kin tabani ba" tana maganar hawaye na zuba a idanunta, ita ko wacca aka kira da Nusaiba mai zatayi inba shekewa da wata bazawarar dariya ba tana tafiya left and right tana girgiza jiki kamar wata karuwa.
 Buɗan bakin Nusaiba ta ce "Hmmmm Sa'eeda kenan, to ke a tunaninki zan bi wata hanyar don ina jin tsoranki, to wallahi kinyi kaɗan, ke bama ke ba harta wannan Uwartaki bata isa ba, eheh! Irin wai ita Allazi bokon nan, ana dai yawan tazubar ne kawai aka ɓige da boko!!!". 
Duk wannan abinda yake faruwa a idanun ƴan gida banda mahaifiyar Sa'eeda da take ɗaki tana jinsu, saidai tayi murmushi da girgiza kai alamar ALLAH ya kyauta.
 Sa'eeda ba mai hayaniya bace, haƙuri ta bata ta wuce wurin Umma kande,a ƙasƙance ta ke duban Sa'eeda, ta ce "Jeki wurin Maman Dije Kice nace tabani saƙon", da,  "To" ta bita dashi ta wuce don tasan idan tayi musu ma ɓata lokacinta zata yi gashi gidan Maman Dije akwai ɗan nisa kaɗan.
Haka ta wuce tana sassarfa taje ta amso saƙon ta kawo mata ba tare da ta shiga ɗakinsu ba ta wuce school. 

              @@@@@@@@@@

A class kuwa, principal na gani ya shigo Jss3, ashe ajinsu Sa'eeda ne, a tare ƴan aji suka miƙe suna gaisheshi, ya amsa musu cike da kulawa kana ya ce cikin harshen turanci "Dan gane da Junior waec ɗinku, kowanne a cikinku zai biya #2500 sannan za'a zana exams ɗin 3rd na watan da zai shigo, don haka kowa ya mayar da hankalinsa sosai a karatu banda wasa". Principal ya ɗau tsawan lokaci yana jawabi kana ya fita daga ajin.
Ɗalibai sai murna sukeyi sun kusa zama seniors, haka darussa sukaita wakana har lokacin tashi yayi suka wuce gida .
BRIGHT STARS INTERNATIONAL SCHOOL shi ne sunan makarantar su Sa'eeda, makaranta ce mai kyau da tsari, ga koyarwa sosai,babbace sosai don tana da field ɗin football da handball duk a ciki, tana ɗaya daga cikin makarantun da ake ji dasu a garin.
Kasancewa Sa'eeda ƴar talakawa ce kuma a cikin wannan makaranta ya samo asali ne a dalilin wani malamin primary dinsu wato Uncle Saleem wanda yake koyarwa a matsayin corper a government school ɗinsu, ganin Sa'eeda da ƙoƙari ya yi cuku-cuku har  ALLAH ya ƙaddara tasamu scholarship a makarantar,wannan kenan. 

            @@@@@@@@@@@@

Bayan dawowarta makaranta ta sanar ma Ummanta batun Junior waec.
"lallai akwai karatu gabanki Sa'eeda, ga shi islamiya kun kusa fara exams" cewar Umma.
Murmushi Sa'eeda tayi tana fadin"Ai Umma yanzu zan fara karatu in shaa ALLAH ".
 Umma ta murmusa da faɗin" ALLAH ya miki Albarkha, ya ci gaba da tsare gabanki da bayani, yasa ku fara a sa'a ku gama a sa'a"
  "Allah humma Aameen Ummina". 
Haka dai Sa'eeda ta cigaba da zuwa islamiya da boko, ga kuma karatun da tasa gaba tanayi, ba kama hannun yaro, a wannan week ɗin time table ɗin exams ɗinsu na boko da islamiya ya fito, aka fara shirye shiryen exams. 
Alhamdulillah sun gama exams ɗin islamiya sannan sukayi na boko wanda ya ɗaukesu har tsawan wata daya.
 
         @@@@@@@@@@@@@@

KEBBI

"Mum, don ALLAH ki roƙa mini Abba ya janye tafiyana UK karatu,duka abokaina Federal University, Birnin KEBBI sukayi applying , amma ace ni sai ƙasar waje"
 A shagwabe yake magana kamar zaiyi kuka.
Mum tace " Haba Sadam, sai kace yaro, bayan kasan ƙa'idar gidannan, duka 'yan uwanka a can Oxford University suka yi, sai avkanka kake so a canja tsari, haƙuri kawai zakayi katafi, kar Dad ɗinka ya ɓatama rai ba ruwana"
Kamar zai yi kuka yace, "shikenan Mum", murmushi mum tayi sannan tace, "Yawwa Autana, kaga tafiyarka jibi ne sai ka fara shirye-shirye ko",  " Toh Allah ya kaimu" kawai Sadam ya iya cewa................







*Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️*
 ***