FARASHIN IZZAH

Chapter 30

by @hauwajaywrites

Bayan sun idar da sallar Magrib... Zahra da Ya Umar suna zaune a parlorn sama. A karo na farko cikin kwanaki masu yawa, ana iya ganin ɗan walwala a fuskar Zahra thought ba sosai ba, amma ya fi na baya


Ya Umar kuwa yana zaune a kujera kusa da ita, yana bata labarin abin da ya faru da lawyers ɗin da suka haɗu da Abbah


"Da farko ma suna mamakin yadda case ɗin ya yi ƙarfi, dan sunci sai ya yarda tukun court zasu raba auren" Ya faɗa


"Da suka ga medical reports da sauran evidence ɗin da aka tattara sai suka ce komai zai yi sauƙi."


Zahra ta yi shiru tana saurarensa ta ce 

"Ai yanzu kam Ya Umar ko bai yarda ba idan kotu ta sake ni ai shikenan, sai ya cigaba da halinsa"


Kai Ya Umar ya gyada sai kuma ya ci gaba


"Abbah ma ya jikasu da kudi sosai, ya ce baya son wani kuskure ko kaɗan."


A hankali Zahra ta ce,


"Allah ya saka masa da alheri, Kai ma Ya Umar Allah biya ka, thank you"


"Amin, Zahratyy" Ya Umar ya amsa


Har zai sake magana ne wayarsa ta fara ringing, ya duba screen ɗin, sai ya miƙe tsaye


"Bari na ɗauki wannan call ɗin."


"Okay." Zahra ta amsa


Daga haka ya fita zuwa balcony, Ita kuma ta janyo wayarta.


Ta shiga wani game tana bugawa a hankali, gaba daya hankalinka yana kai kawai, kawai taji an bude kofar parlon


Batoul ce ta shigo, da ganin Zahra sai ta tsaya, sannan ta saki wata dariya


"Toh..." Ta faɗa tana girgiza kai.


"Ashe ƙarshen alewa ƙasa ne fah"


Zahra ta ɗan ɗago kai

Sai kuma ta mayar da hankalinta kan wayarta tamkar ma ba ta ji abin da Batoul ta ce ba.


Batoul ta sake dariya.

Amma da ta ga Zahra ko kallonta ba ta yi ba, sai ta zauna tana latsa wayarta ita ma


A daidai lokacin Ya Umar ya dawo ciki, da ya ga Batoul sai ya haɗe gira, amma bai ce komai ba.


Zahra ce ta miƙe

"Yaya bari na koma sama" Ta faɗa


Ya Umar ya kalleta "Kin fasa hirar kenan?"


Zahra ta yi dariya

"Ai mun gama magana Yaya"


Ta kalli Batoul,


"Hira kuma sai anjima ko gobe Yaya"


Ya Umar ya gyada kai.

"Alright, Baby"


Daga haka Zahra ta wuce sama, shima Ya Umar ya sake fita bayan ɗan lokaci.


Ba tare da ya ƙara kallon inda Batoul take ba


Can bayan isha'i 

Lokacin dinner ya yi, kowa ya taru a dining area


Abbah, Mami, Mummy, Ya Umar, Batoul, da kuma Zahra


Da suka iso dining ɗin duk kusan lokaci guda suka iso, Abbah ya lura Zahra tana neman kujerar da zata zauna


Kai tsaye ya miƙe, ya janyo mata kujera da kansa


"Zauna nan Baby" Ya faɗa cikin kulawa


Zahra ta yi murmushi

"Thank you Abbah naa" Ta zauna


Abbah kuma ya ɗauki serving spoon, da kansa ya fara zuba mata abinci


"Kici sosai fah" Ya faɗa

"Likita ya ce kina buƙatar ƙarfi."


Mummy ta yi wata yar ƙaramar tsaki, ta kau da kai


Abbah ya ji amma bai nuna ba


Batoul kuwa... Ko kallon inda suke ba ta yi ,tamkar babu wanda ya dame ta a wajen, ta ci gaba da cin abincinta 


Mami dai tana kallon Zahra lokaci zuwa lokaci, tana son tabbatar da cewa tana ci.


Ya Umar kuma lokaci-lokaci sai yana saka mata ruwa ko yana tambayarta ko tana buƙatar wani abu, Mummy sai wani kallo take masa Duk lokacin daya hakan,


Zahra na jin wani abu da ta daɗe bata ji ba, jin cewa tana cikin mutanen da suke ƙaunarta...


Yau ya Kama ranar zaman kotu na farko...

Tun da sassafe gidan Abbah suka fara shiri


Zahra gaba daya jikinta ya gama sanyiz, kana ganinta kasan tana cikin tension,

Mami ce ta shiga ɗakinta, ta same ta zaune gaban mirror tana kallon kanta


Ba kwalliya sosai ta yi ba, wani simple black abaya ne a jikinta da veil dinsa tayi rolling kanta


Mami ta ƙaraso ta tsaya bayanta.


"Kina lafiya?" Ta tambaya


Zahra ta gyada kai.

"Alhamdulillah, Mami"


Mami ta gyara mata gefen veil din ta ce


"Ki kwantar da hankalinki Baby, komai zai zo ya wuce, ko yaki ko yaso dole ya baki takardanki Yau"


Zahra ta yi murmushi, amma a zuciyarta wani irin bugun zuciya take ji, ba ta taɓa shiga kotu ba a rayuwarta


A parlorn kuwa

Abbah, Ya Umar da lawyers suna ta ƙare wasu bayanai na ƙarshe.


Ɗaya daga cikin lawyers ɗin ya riƙe file, cike da documents, medical reports, Hospital records, Photographs, da sauran takardun da za a gabatar


Da Zahra ta sauko, kowa ya tsaya yana kallonta, ba karamin kyau tayi ba


Abbah ya miƙe, ya ƙarasa kusa da ita


"Ready?"Ya tambaya


Ta gyada kai "In sha Allah."


Sai ya dafa kafaɗarta.


"Karki ji tsoro, muna tare da ke...."


Karfe tara da rabi suka isa harabar Kaduna High Court


Tun daga parking area ana ganin mutane na kai-komo


Lauyoyi sanye da bakaken suits, wasu sanye da wigs


Ga masu kallo, da iyalan waɗanda suke da ƙara


Zahra ta fito daga motar a hankali, ta kalli ginin kotun


Wani irin yanayi ne ya rufe mata zuciya


Ya Umar ne ta kamo hannunta


"Hey." Ya faɗa.


"Don't panic."


Zahra ta yi murmushi kaɗan, sai suka shiga


A gefe guda kuma.

Ibrahim ya iso tare da Mama.


Tun daga parking area Mama take ta magana.


"Karka yarda da komai, ka tsaya da ƙafafunka, wannan ai matsalar gida ce, ba ta kai ace na kotu bane, zaku sasanta kan ku"


Ibrahim bai ce komai ba, fuskarsa babu walwala


Da suka shiga corridor ɗin kotu, Idanunsu suka haɗu da na Zahra


Zahra ta kau da kai da sauri


Ibrahim kuma ya tsaya yana kallonta da mamaki, ido ya zuba mata na wasu dakiku


Sai Mama ta ja hannunsa.

"Mu wuce ciki"


Da misalin goma na safe.... Aka kira shari'ar


Kowa ya shiga. Zahra na zaune a layin gaba tare da lawyers ɗinta.


A bayanta Abbah, Mami, Ya Umar da da Anty Jiddah.


A ɗaya ɓangaren kuma Ibrahim da Mama.


Alkali ya shigo, kowa ya miƙe, sai da ya zauna sannan aka zauna


Bayan an gabatar da bayanan shari'ar.

Lawyer ɗin Zahra ya miƙe.


"My Lord..." Ya fara.


Sannan ya gabatar da buƙatar warware auren.


Ya bayyana cewa wanda ake ƙara ya aikata abubuwan da suka haddasa mummunan rauni ga matar nasa.


Da farko Ibrahim ya zauna cikin kwanciyar hankali, sai dai lokacin da aka fara gabatar da hujjoji, hankalinsa ya fara tashi sosai


Likitan da ya kula da Zahra ya bayyana sakamakon binciken da aka yi

Shi kuwa ya bayyana irin raunin da aka samu a jikinta, da yadda aka kaita asibiti cikin matsanancin hali


Lawyer ya miƙa takardun ga kotu.


Alkali ya duba, sannan ya yi wasu tambayoyi


Likitan ya amsa.

Bayan haka aka gabatar da wani report, aa biyu.


A wannan karon, dukan daya mata tana da cikin , gaba ɗayan kotun ta yi shiru


Mama ta kalli Ibrahim da sauri. Ibrahim kuma ya ɗago kai, kamar wanda bai gama fahimta ba, Likitan ya ci gaba da bayani


"The patient suffered a..." Zahra ta runtse idanuwanta.


Mami ta kamo hannunta

Lawyer ɗin Zahra ya ci gaba.


Ya bayyana yadda aka kai ta asibiti., yadda aka yi mata treating din internal injuries, da yadda rayuwarta ta shiga haɗari, sai ya juya ya nuna Ibrahim.


"My Lord."


"Muna da hujjoji da shaidu da ke nuna cewa abin da ya jawo wannan kwanciyarta a asibiti shi ne harin da wanda ake ƙara ya kai mata."


Nan kotun ta sake yin shiru.


Mama ta kasa haƙuri, ta miƙe tsaye


"My Lord!" Ta faɗa


"Duk ma'aurata suna samun matsala! Ba wai dan sun yi faɗa ba sai ace za'a raba su...."


Alkali ya dakatar da ita.


"Madam" Ya faɗa cikin tsauri


"Zauna."