MURADIN ZUCI

Muradin zuci

by @bintuuu

Ina miqa godiyata ga qunguyar mu ta Wow (women of words) Association.

Da kuma godiya ta musamman ga:

Ramlat (Mai Dambu)
Sayyid (Legends pen)
Nusaiba Rimi (Nusy Bee)

Thank you so much for been there for me when i need you, Allah ya bar zumunci.

Fatima Dahiru
Hajara Usaini

Ina matuqar godiya agareku for your support, My sisters from another mother, Allah ya saka da alkhairi da dukkan qwarin gwiwan da kuke bani a koda yaushe.


Wannan qirqirarren labari ne in yayi kamanceceniya da wani ko wata ayi min afuwa bisa kusukure ne.








MURADIN ZUCI📖📚
  
  Bintu Musa ✍️ 



Bismillahir Rahmanir Rahim 


Houston, United States. 

25th October.

Daren Talata, 9:00 pm.



Hankali a tashe matashiyar balarabiyar take tuqin motarta qirar Honda prelude, wadda ta kasance daya daga cikin motocin da suke tashe a wannan lokacin. Tafiya take ba tareda itama ta san inda ta nufa ba, idanunta na kan titi tunda ta fara tuqin taqi juyawa ta kalli seat din dake gefenta. Hannunta da suke riqe da steering wheel din ta kalla ganin yanda suke rawa sai ta sake damqe sitayarin tana mai qara gudun motan a yayin da zuciyarta ke kadawa da wani irin yanayi da yasa idonta kawo kwalla. Tafi awa daya tana yawo acikin garin kuma har sannan bata tsaida inda ta nufa ba sai zagaye take acikin wata makekiyar unguwa ta rasa a wane taqamaiman gida zata tsaya, gashi har sannan jikinta sai rawa yake, can kawai ta samu kanta da tsaida motan a gefen hanya ta kifa kanta akan sitiyarin da hannunta duka biyu ke riqe dashi har sannan. Hawaye masu zafi taji suna zuwa mata idanunta ba tareda ta sharesu ba ta dago kanta tana bin gurin da ta faka motan nata da kallo, ganinta tayi gaban wani babban gida mai cike da alatun rayuwa ga haske a ko'ina tar, samun kanta tayi da qurawa compound din gidan ido ganinsa dauke da gajeran gate irin wanda yawancin 'yan qasar suke amafani dashi a gidajensu, nan kuma idonta yakai kan shukokin compound din da take hangowa daga inda take zaune cikin motan. Sai kuma ta kai hannu ta fara share hawayen da ya sauqa a fuskanta, ahankali ta juya ta kalli seat din dake gafenta ganin har sannan babu wani motsi da basket din dake ajiye a gurin yayi, sai ta kai hannunta ahankali ta yaye farin towel din dake lullube akai tana kallon kyakkyawar jinjirar dake baccinta hankali kwance sai tashin qamshin turaren babies take mai dadi, kuka ne yazo wa matashiyar da sauri ta kai hannunta ta rufe bakinta gudin kar ta tada Babyn. Aqalla ta kai minti biyar tana kallonta sannan cike da jarumta ta maida towel din ta rufe yarinyar, da haka ta jawo baqin gyalen kanta ta rufe fuskanta sannan ta juya ta duban street din unguwar, kasancewar kebababbiyar unguwa ce ta masu hannu shuni sosai sai ya zamtoh babu kowa a daidai street din da take, ganin haka yasa ta bude motan ta fice tareda zagayawa daya bangaren domin daukan jinjirar. Ahankali ta dauko basket din ta juya tana waige waige ganin ko ana kallonta sannan ta fara tafiya a sannu ta tura qaramin gate din and to her luck kuma ba'a datse yake ba, da sauri ta nufi gefen shukokin ta duqa ta ajiye basket din hawayenta na diga kan towel din amma haka ta miqe ta fice da gudu gudu tana sake waigawa ko da wani ya ganta har ta qarasa ga motarta ta shige da wuri ta tayar. Sai da ta kai qarshen layin sannan ta faka motan ta juya tana kallon gidan ta madubi sai kuma kuka mai qarfi ya kwace mata, wani irin zafi takeji a zuciyarta kamar wuta a wannan lokacin tana kukan ahankali take ambaton sunan jinjirar. Can kuma ta kasa daurewa tayi saurin bude motan da nufin ta koma ta dauko yarinyar dan ji take duk wani jarumtar da ta fito dashi kuma ya watse, bazata iya ba...bazata iya ba. 
Fitan ta ke da wuya ta hango fitowan wani magidancin mutum daga gidan tareda wasu yara guda biyu suna tafe a jere dashi zasu fita daga compound din gidan, da sauri ta sake komawa cikin motan ta tayar tareda figanta ta bar arean da gudunta.
Tasani..Lokaci ya qure mata..Ya qure mata har abada kuma..


A yayin da magidancin ya fito daga gidansa tareda yaransa maza da suka kasance 'yan biyu kuma 'yan kimanin shekaru sha biyu, hankalinsa naga fita kwata kwata bai lura da abunda aka ajiye masa a compound din gidansa ba sai daya daga cikin yaran ne ya riqe masa gefen riga domin jawo hankalinsa yace "Papa look..A basket" sai ya juya shida dayan yaron nasa suka kalli gurin da IMRAN ke nunawa da yatsansa ya sake cewa "Papa menene?" a sannu shi Papan ya fara nufan gurin cikin kaffa kaffa yaran na biye dashi a baya, kafin ya qarasa kawai dayan yaron nasa dake bayansa ya tafi kansa tsaye ya tsugunna zai bude, da sauri Papa yace "Kash. IMAM meyasa bak.." kafin ma ya qarasa maganan Imam ya bude towel din suka kalli cikin basket din a tare, Imran dake boye a bayan mahaifin nasu shima ya leqo kansa, dago kai Imam yayi yace "Papa it's a Baby" daskarewa Baban nasu yayi yana kallon kyakkyawar Babyn dake bacci hankali kwance ga kuma kayan sanyi na yara mata mai kalan ruwan hoda a jikinta dauke da zanen flowers wanda hakan ke nuni da kasancewar babyn 'ya mace, hannu Imam ya kai zai dauketa sai Papa ya janye hannun nasa still yana kallon jinjirar da kana ganinta kasan farinta ba na 'ya'yan mu hausawa bane, Imran ya duqa kusa da dan'uwansa shima yana kallon yarinyar sai ya dago kai yana murmushi yace "Papa let's keep it" shidai Papa har sannan baice komai ba gashi alamun tashin hankali ya bayyana qarara a fuskarsa sai kuma ya miqe ya fara bin arean wajen gidan nasu da kallo ko da zai hango wanda ya musu wannan ajiyar a daren nan, can kuma ya juyo yace "Ku tashi mu koma ciki akwai sanyi" sai Imran yace "Papa anan zamu bar Babyn?" Imam dai yanata kallonta har sannan bai sake cewa komai ba, sai Papa yace "No, we're taking her with us" da haka ya sunkuya ya dauki jinjirar tareda furta duk addu'an da tazo bakinsa, sai twins suka miqe suma Imam ya dauki empty basket din suka fara tafiya a gaba while mahaifin nasu yana biye dasu a baya riqe da babyn a qirjinsa suka koma cikin gidan nasu.

A lokacin da suka shiga babban falon gidan nasu suka samu Momma zaune a inda suka barta ga jakadiyarta mai suna Habiba na matsa mata kafafunta da suka kumbura dalilin tsohon cikin dake jikinta, dago kai tayi tace "Ha'a, har kun dawo?. Da mota kuka fita ne?" sai Imran ya qaraso gurin ta da saurinsa yace "Momma we found a Baby" sai ta dan hade gira ta juya tana bin mijin nata da kallo ganin yana riqe da nannadadden towel a qirjinsa, qarasowa Papa yayi tareda zama a gefenta atake kuma Habiba ta miqe kanta a duqe cikin ladabi ta matsa gefe, sai ya duqo ya bude wa Matar tasa towel din tana ganin yarinyar kamar idanunta zasu fado, sai ta dago kai tana kallonsa tace "Menene wannan din?" yana kallonta shima yace "Jinjirace Fatima, anan cikin compound dinmu aka ajiyeta" sai ta dafa cikinta ta fara qoqarin miqewa yana kallonta, da sauri Habiba ta matso zata taimaka mata amma ta daga mata hannu da nufin ta barta sannan ta qarasa miqewan da kyar duk suna kallonta ta kalli Imam dake riqe da basket din har sannan, fuska a hade tace "Bani abun nan" sai ya matso ahankali ya bata ta karba tana kallon mijin nata tace "Kawo ta mu fitar da ita daga gidan nan tun kafin ta jawo mana masifa muna zaman zaman mu" da mamaki Papa yake kallonta yace "Meye haka kike cewa ne Fatima, clearly dai kina gani jinjirace alamun bata sha iskan duniya sosai ba, meye nata kuma?" Momma tayi qanqan da ido tace "Shiyasa zamu mayar da ita inda muka ganta sannan mu kira police da social services, we are not keeping a stranger's Baby in this house wallahi" da mamaki Papa yace "Haba Fatima, ki nutsu da Allah. Ta yaya zamu maida baiwar Allahn nan out there in this cold weather kawai dan kina tsoron abunda hukuma zasuyi, kin manta akwai CCTV a street din ne? Anan zasu gani su kuma shaida ajiye mana ita akayi ai" a fusace tace "Ni ba hukuma nake gudu ba, qananun maganan da hakan zai jawo mana acan gida nake gudu, ya muna zaune qalau zaka jawo mana masifa har cikin gida" sai ya dan girgiza kai ya miqe tareda miqa mata yarinyar yace "Dan Allah ki riqeta, ki kula da ita kafin insan ta inda zan bullowa al'amarin, the mother might come back, bakisan yanda nake burin hakan a raina ba, it's too cruel for the baby, social services will just be passing her from one home to another in the name of adoption, she's innocent" tsayawa Momma tayi tana kallon yarinyar yayin da duk wani annurin fuskanta ya gushe, idonsa a kanta ya sake miqo hannunsa "Riqeta mana Fatima" sai lokacin Imam ya matso tareda dan miqa hannu zai karbeta ai da sauri Momma ta tureshi har sai da ya fadi, rai a bace take kallonsa tace "Uban 'yan karfin zuciya, inna gaura ma mari ba" kafin Papa ya dagosa ya riga ya miqe yana kallon mahaifiyar tasa dake harararsa, sai Papan ya juyo gareta yace "Wai me yake damunki ne Fatima, Lafiyan ki kuwa?" tace "Ba lafiya nake ba, ta yaya muna zaune lafiya zaka shigomin gida da jinjira sabon haihuwa har kana fadin in riqeta, wallahi ka koma da ita duk inda ka daukota tun wuri" da haka ta juya tana riqe da cikinta da yayi nauyi sosai ta wuce dakinta dake nan downstairs wanda tun zuwansu gidan take zama acikinsa dalilin bata iya hawa stairs taje asalin dakinta dake can sama, sai duk suka bita da kallo yayin da Habiba tabi bayanta da hanzari gudun kar ta mata masifan da ta saba.