MATAR MAZA

Chapter 6

by @reza12

MATAR MAZA 6


Sosai Azima take ta tunani duk ta rikita ƙwaƙwalwarta, Idan ta saƙa wannan sai ta kwance. Idan ta tuno da alƙawarin da sukayi da Alhaji Audu sai gaba ɗaya ta sake firgicewa. Ana cikin wannan halin ne ma wani daga cikin samarin nata shima ya taso da gaske da nufin aure, shima da yake taci kuɗin sa sosai, harda alƙawarin aure yasa ta rasa yadda zatayi, kuma fa dole ta san yadda zatiyi da su wallahi.

 Zaune suke a cikin ɗaki su uku. Azima da Sadiya sai wata ƙawarta da suka haɗu a school da ta kawo mata ziyara mai suna Salma. Laptop din Azima ɗin ce a gabanta tana ta ƙoƙarin haɗa video call da saurayin ta ta cikin laptop din, dama abun da ya kawota gidan koken. Ta daɗe ba'a daga ba, sai daga baya ya daga suka fara hira irin ta masoya. Sadiya da Azima kuma suna gefe suna tattaunawa saboda gobe ne take son shiga Maroco saro kaya, suna magana akan yadda zata ƙara faɗaɗa kasuwancin nata. Kiran alhajinta ne ya shigo mata, hakan yasa ta waro ido tana kallon wayar domin bata yi zaton kiransa zai shigo a wannan lokacin ba. Ta na ɗagawa yace mata gashi a ƙofar gida ta fito yanzu. Ta sauke wayar tana kallon Sadiya da taji komai. Ta ce "Ashe yau a kwai kuɗi tunda ga ubansu yazo". Ta faɗa tana dariya. Ta harareta, sannan ta miƙe a ranta tana jin ya kamata dai tun kafin abu yayi nisa ta takawa wannan tsohon burki fa. Ta gyra jikinta sosai ta fesa turare, harda ɗan man baki, ta fito yar kuyat da ita, tasa gyale sannan ta ƙaraso gurin da salma ke waya ta sunkuyo a hankali ta ce mata "Ina dawowa Alhaji na ya zo". Tana faɗa tayi waje abunta. Salma tayi murmushi tana bin ta da kallo. A ranta dai tana so taga alhajin nan na Azima da ake bata balari kullum.

Saurayin nata ya ce "Wacece wannan?" 
Ta amsa da cewa "Ita ƙawar tawa da nake amfani da laptop ɗin ta na kira ka". Daga haka suka ci gaba da hira.

Tun daga nesa ya kafe ta da ido yana ƙara jin sonta na masa rami a zuciyar sa, tabbas yana son wannan yarinyar, kai dole ne ma yayi batun auransu cikin sauri. Da sallama ta ƙaraso tana sakar masa wannan murmushin nata na yaudara. Bayan sun gaisa ne ya tambaye ta karatu da kuma mutanen gida duk ta ce masa alhamdu lillih. Nan dai ya faɗa mata abun da ya kawo shi. Ya ce mata zaiyi tafiya ne na tsohon wata uku ko biyu, shi yasa yazo ya faɗa mata. Ai kuwa take taji wani sanyin dad'i na shigar ta. Yasa yaransa suka fito da kayan abinci masu yawa ya haɗa mata da kuɗi yace sai sunyi waya, ya sake tabbatar mata da cewar tafiyar gaggawa ce shi yasa ba zai tsaya har ayi aure ba, amma ta shirya yana dawowa za'ayi magana. Sosai wannan karan Hajiya ta ce to mai zai hana yazo ayi auran sai ki ƙarasa karatun a gidan sa, dan gaskiya ina tsoron irin wannan kashe kudin nasa, kar a samu matsala na san halinki. Azima ta ce "To ni dai ban tambayesa ba, kuma tunda kika ga yana kashewa ai yana da su ne ko, kawai Hajiya ki share, ai matar mutum ƙabarinsa ce ko?" Daga haka ta koma tana bawa Salma labarin, itama dai take ta mamaki ta ce "Kin san wannan gyan da muke wayar nan ɗan ina ne?" Azima ta girgiza kai tana kallonta. "Dan Maroco ne, ta Whasop muka haɗu, yau sati ɗaya, amma idan na faɗa miki irin kuɗin da ya kashe min sai kin ce karya ne". Azima ta ja tsaki ta ce "Shine kika kasa sayan ko laptop nan dan ubanta" "Mai kike ci na baka na zuba yarinya, shine yace zai kawo min wannan Monday din mai zuwa". Ta ce "Ita laptop ɗin ce har sai an kawo miki ba zai turo da kuɗi ki saya anan ba ko?" Salma ta ce "Baza'a saya anan ɗin ba, an faɗa miki irin wannan takun za'a saya min, to asalin mai kyau mai batir ba wannan shirmen banza ba wacce bata da wani kyau ba". Ta faɗa tana dungure laptop din. Azima tayi dariya ta na cigaba da cewa "Allah yasa dai ba irin samarin shahon nan kika samu masu karya ba". Ta faɗa tana dariya. Daga haka suka ci-gaba da tsokanar juna. Koda zata tafi sai da ta bata wani abu a cikin kuɗin da alhajinta ya bata. 

A ranar ta buɗe Whasop da laptop tana ɗan chatting da ƙawayen ta na school taga kira video call ta layin saurayin Salma. Sai bata daga ba tai masa sako akan bata nan. Sai ya dawo mata da sakon akan ya sani. Abun ya bata mamaki, to ya sani kuma yake kiranta har video call. Daga haka bata sake ce masa komai ba, kuma Kamar wani maye sai sake kira yake yi. Haka washegari ma ya sake kiranta lokacin ma tana duba kaya ne da aka ce mata an kawo. Ganin haka yasa ta masa dogon typing akan Salma fa ba gida ɗaya suke ba, dan haka ya daina kira idan tazo zata kira shi da kanta, dan Allah kar ya sake kiranta. Bayan kwana uku Salma ta sake zuwa nan ma sun dade suna hira da shi duk video call. Ashe wai tambayar ta sunan Azima yake yi, harda cewa ta kirata. Salma ta kirata tazo suka gaisa. Sai lokacin ma ta kula da shi ba laifi yana da kyau, gashi dai kamar dai yana da masu gidan rana, amma bata da tabbas, saboda samin yanzu sun iya fakejin. Bayan ta baro gurin taji Salma nata murna saboda yace ya saya mata laptop din, yanzu saura kawowa, harda nuna mata Ita, wata blue mai kyau da ita kuwa. A ranar ma ya sake kiran Azima video call bayan Salma ta tafi, sai ta ɗaga domin jin mai zai ce mata. Nan ya fara mata tambaya akan Salma, ganin haka yasa ta ɗan sake masa suna ta hira, tun daga lokacin kuma ya zama suna gaisawa, sai yai ta faɗa mata cewar yana son Salma sosai ta kula masa da ita. A wannan tsakanin taje Maroco ta dawo, wanda tayi kwana uku ne kawai. A hanyar dawowarta ne ta sake yin wani bazawari wanda suka haɗu a filin jirgi. Ita da kanta har mamakin yadda take da farin jinin mutane take, amma idan ta kalli tsarin halittar ta, sai kawai ta sake godewa Allah, lallai dole ne maza su nuna suna yinta. Tun a cikin jirgin ya dame ta, hakan yasa dole ta bashi number suka rabu. Shi ne fa tana zuwa gida ya kirata. 

A daren ranar saurayin Salma ya kirata ta daga yake tambayr ta kwana biyu bata hawa online. Nan ta sheda masa cewar ai tayi tafiya ne taje Maroco. Da mamaki ya ce mata shine bata neme shi ba, ai shima ɗan Maroco ne. Ta ce "Akan me zan neme ka?" Ta faɗa da mamaki ganin ya cika zaƙewa. Ya ce "Saboda a gaisa mana Azima". "No bana so, idan gaisawa ta wuce wannan to ba zan iya ba, sai anjima". Ta kashe laptop gaba ɗaya tana jin wani haushin sa. Tun daga lokacin kuma ya dage mata da kira, akan dan Allah idan zata dawo ta faɗa masa. Tun tana ki har dai tai masa alkawarin zasu haɗu idan tazo ɗin. Washegari kuwa mutuminta yazo har ƙofar gida, a lokacin kuma tana tsaye da wani, amma ko a jikinta, domin ita acikin samarinta alhajinta ne kawai bata so yazo ya samu wani, shima ba dan Komai ba saboda tsufansa ba zata iya masa rashin mutunci ba, kuma ko ba komai ya taka babbar rawa a rayuwarta a lokacin da bata da kowa. Sai da ta gama da wannan ya sallame ta kafin ta ƙaraso gurin sa. Ya buɗe Mota yace ta shigo. Tace masa bata hira a cikin mota.

Yayi dariya yana faɗin "Ashe har yanzu yarinya ce ke". 

Ta ce "Yar goye ma kuwa". 

"Naga alama, amma zan mayar dake wayyaya, kuma classic baby kinji". Ya faɗa yana basarwa. 

Azima ta sake kallonsa da kyau, ranta tana jin Lallai wannan bai santaba.

Daga yanayin magsnarsa ta gane yana da jiji da kai, ita kuma abun da ta tsana kenan a rayuwarta, sam bata son namiji ya nuna mata shi wani ne, daga lokacin zai fita mata a rai. Suna cikin maganar taga ya ɗaga waya yana tambayr guda nawa ake so. Bata ji nawa yace ba sai okay kawai taji yace. Bayan ya sauke wayar yace mata "Sana'ar sayar da macizai nakeyi, yanzu haka anyi odar guda goma sha biyar ne, zuwa gobe zasu iso ni kuma na kai masu". Ya karasa yana ɗan murmushi.

 Azima ta ce "Haba dai Macizan ake sayarwa kamar kaji?" 

"Kina mamaki ne?" 

Ta girgiza kai domin ita ko sunan majizan ma bata ko son gani. Sun dade suna hira dashi, kafin sukayi sallama tana ta mamaki yau da wani iri Allah ya haɗa ta. Shima dai bai barta haka ba sai da yayi nasa ihisanin. Tana shiga gida aka sake kiranta amma tace ba zata zo ba, bata ma ko san waye ba amma taki fita saboda ta gaji. Tana shiga ɗaki ta samu Sadiya da Yusra suna kallo a laptop ɗin ta. Ta anshe tana cewa, idan naje Maroco zan zo muku da taku ku daina taɓa min tawa. Nan kuwa suka fara murna. Daidai lokacin ta buɗe Whasop. Sai ga kiran saurayin Salma. Ta ɗaga video call tana mamakin irin nacin sa da kuma yadda koda yaushe yake son yin video. Suna cikin hira sai ga Salma ta shigo tana kiran sunan Azima. Tsayawa tayi tana kallon fuskar saurayin ta a cikin laptop ɗin ga Azima kuma ta sha kwalliya harda murmushi. Azima ita da bata ma kawo komai ba ta ce "Yauwa ga ta nan ma ta iso". Tana faɗa ta tashi a gurin. Salma da gabanta ya faɗi ta bi Azima da wani irin kallo. Dama suna yawan gulmarta cewar asiri takeyiwa samari, duk da tana da kyau amma yawanci duk masu kuɗi ne ke zuwa gurinta, kuma tana tsoron kar ta ci amanar ta. Sosai ta shiga tashin hankali har sai da Azima ɗin ta gane a fuskar ta. Sai kawai tayi dariya tana mamakin Salma, idan ma ba ita ba mai zatayi da wannan ɗan ƙaryar. Tun daga lokacin kuma Salma ta sauya mata, haka idan tazo za tai ta cin magani. Anan ne take sheda masa cewar ranar juma'a zata shigo Maroco, ai kuwa yayi murna sosai, ita kuwa bata kawo komai ba ta yarda zasu haɗu. Bangaren Alhajinta kuwa tun da ya tafi bata kara jin labarin sa ba. Haka sauran samarinta har gobe ƙaruwa suke, mai maciji shima ya dage da gaske aure yake son yi, domin shi faka-faka ma yake maganar ta bashi izini ya turo ayi a wuce gurin. A karon farko da taji Kamar zata iya sake yin wani auran, bata dai gama yarda ba tana tunani, amma dai tabbas ya dace tayi aure a cikin wannan samarin nata. Ana gobe zata tafi Maroco mai maciji yazo, bayan sun zauna ya gama faɗa mata cewar shifa da gaske yake dan haka idan ta shirya ta bashi izini. Nan ta shiga tunani, ta ko ina yayi amma yana da jiji da kai, kuma wannan majizan da yake ta batu ne bata gane ba, sai kawai ta ce masa zuwa gobe ya dawo zata faɗa masa idan tayi tunani. Ganin kamar sauri yake yi ne yasa ta ce "Wai ina zaka je haka?" Ya ce "Macizai ne a cikin mota zan kai su filin jirgi za'a tafi da su Amruka yau ɗin nan, idan na rasa wannan damar ba ƙananan kuɗaɗe zan rasa ba". Ya faɗa yana mikewa. Itafa ta na ce wasa yake yi da yace yana sana'ar macizai. Domin ta ƙure shi ta ce "Muje na gansu dai ganin ido yau". Ta faɗa tana dariya. "Ba zaki ji tsoro ba kin tabbatar?" Ta ɗaga masa kai suka Isa gurin motar. Ya buɗe bayan motar sai ga wasu akwatin ƙarfe biyu manya ɗaya a kan ɗaya. Ta kalleshi tana ƙoƙarin fara yarda da maganar sa tun ma kafin ta gani. Ya zaro wata maƙulli a aljihunsa ya buɗe a kwatin saman. Sai ga macizai kusan guda goma kowanne ya ɗago kai daga budewa. Ai take Azima ta sulale a gurin sumammiya zaɓar yadda ta kiɗime ta tsorata. Yayi murmushi kafin ya rufe su. Ya fara duba mutane yana kiran sunanta. Yana cikin haka sai ga Sadiya da Mansur sun dawo a mashin. Nan suka shiga da ita gida shi kuma ya ja motarsa yana ɗan sakin murmushi.

Tana buɗe ido ta sauke a kan Hajiya da take salla. Ga Ummi kuma tana cin abinci. Ihu ta saka domin tuno da Abun da ya faru. Sadiya ta shigo ɗakin da sauri tana kiran sunanta. Sosai ta rikice kamar dai abun take gani yanzu haka. Har Hajiya ta idar da Sallah tana ihu. Sai da ƙyar ta iya faɗa musu abun da ya faru, ai ba ma iya Sadiya ba, harda Hajiya sai da tayi dariya. Hajiya ta ce "A a wannan kwashe-kwashen naki har mai kura da zaki sai kin kwasho wallahi, to shine duk kika bi kika daga mana hankali". Haka suma su Sadiya suke tai mata dariya. Dalilin wannan abun ta ɗaga tafiyar tata, kuma ta goge number Mai majici, koda yazo taki fita sai ma tura sadiya da tayi akan kar ya ƙara zuwa bata sonsa. Da gaske dai ya rikice shi bai san laifin da yayi ba, ta zo ta faɗa masa da kanta. Ana gobe zata tafi ne, taje gidan su Anty domin ganin Fadila, amma ƙiri-ƙiri Anty ta hana ta, hakan yasa ta kira Musa, shi kuma baya ƙasr yace ta kira Anty idan har Fadila take son gani. Duk yadda tayi kewar yarta haka tana kuka tana roƙon Anty amma ina tace Wallahi ba zata ganta ba, haka kawai ta ɓatawa yarinya tarbiyyar da ake bata. Haka ta dawo duk jikinta babu kuzari, a ranta tana jin kenan shikenan an raba ta da yarta guda ɗaya. Hajiya ta ce "Idan kina so ki dinga ganinta aure zakiyi, Azima wannan tara samarin duk zubar miki da mutunci yake yi, dan Allah ki ƙira shi wannan mutumin da kuka yi alkawari yazo ayi abun nan ko zamu huta" ta ce Hajiya, ni da ƴata ace sai nayi aure zan ganta, a ina aka taɓa haka, wani irin zalunci ne wannan, to wallahi basu isa ba, duk abun da suke nema sun tara sun samu". A haka ta tafi Maroco zuciya ba dad'i. Kaman kuwa yadda suka tsara da saurayin Salma har filin jirgi yazo ya tarye ta. Sai dai abun da ya bata mamaki irin motocin da suka rako shi. Haka suka wuce da ita wani karamin gidan sa, tace masa ita fa a hotel take sauka yace mata banda yau. Sosai ya shiga yin hidima da Ita, har washegari da zata shiga kasuwa ya ce zai rakata, kusan gaba ɗaya kayan da ta sayo kuɗin sa ne, hakan yasa ta cika da mamaki, tayi sayayya mai yawa wanda bata taɓa yin irinsa ba, harda laptop ɗin da tai wa kannenta alƙawari. Kwananta uku a garin ta shirya dawowa. Tabbas ta sha mamakin irin kuɗin da yake dashi, shima ɗan asalin Nigeria ne aiki ya kawo mahaifinsa har aka haife shi a nan. Kalmar da ya furta mata ce tasa sai dai ta cire glass ɗin idonta tana kallonsa. Ya ce "Har ga Allah ba zan ɓoye miki ba Azima ina sonki, kuma auranki nake son yi idan har kin yarda?" Ya faɗa yana sake kallonta?" Ta ce "Aure fa, kana saurayin ƙawata, haba ai ko samari sun ƙare ba zan iya ba, sannan ma ni da kake ganin ba aure a tsarin rayuwata". Ya ce "Wa ya faɗa miki Salma budurwata ce, a'a kawai fa online freid ce ba komai ba, ban taɓa cewa ina sonta ba, itama kuma haka". Sosai fa ya dage mata, har da riƙe mata jaka. Amma tace sam ba zata iya auransa ba, dan Allah ma ya daina damunta. 

Haka ta dawo Nigeria da uban kaya. Sai dai ta dawo ta tarar da wani sabon tashin hankali. Salma ce tazo har gida tana zaginta wai ta ci amanar ta ta kwace mata saurayi, saboda ya kirata yana cewa ta shawo masa kan Azima. Duk yadda Azima ta so da ta tsaya ta fahimtar da ita amma taki. Hakan yasa itama yan zuciyar da yake suna kusa ta biye mata. Sosai faɗa Salma na faɗin ai dama kowa yasan ita asiri takeyiwa samari, kuma wallahi zata rama tana daidai da ita, kuma tace mata wallahi muddin tana raye ba zata aure shi ba. Wannan kalmar ce tasa Azima bata tsaya yin dogon tunanin abun da zai je ya dawo ba ta kira shi a waya ta sheda masa cewar ta amince zata aure shi muddin da gaske yake. Sosai ta sa a ranta zata aure shi ko dan ta kawo karshen wannan furucin na Salma, kuma ta sake tabbatar da cewar asirin takeyi, domin ba karamin wulaƙanci Salam tayi a gidan nasu ba, har Hajiya ta fadawa magana, gashi suka haɗu da sauran yan gidan ana ta kwashe musu albarka. Abu kamar wasa sai ga shi a Nigeria. Ta Kafa masa sharudan ta, akan sai dai ya saya mata gida a'nan Nigeria ko ya kama mata hanya, amma dai ba zata bishi Maroco ba. Ai kuwa take ya amince. A cikin ƙasa da sati ɗaya ta kawo shi gida matsayin shi take so, Hajiya ta cika da mamakin ina Alhaji Audu ɗin To da zata auri wani. Babu wata-wata aka daura mata aure da shi ko sunansa bata sani ba, kawai saboda baƙantawa wata.

A ranar da aka daura ta ɗauki Kafa har gidan su Salma, ana riƙe ta tana shiga cikin gidan gata da kwalliyar amare amma a fusace take, lokacin ita kuma tana gida cike da bakincikin abun da kawar tata tayi mata domin ta san da labarin auran ta yau. Ta shiga har ɗakin uwarta kamar yadda tai mata itama, ta faɗa mata magannun da ta tanada, sosai anan ma su kayi kacha-kacha Salma da alwashin ganin bayanta, kuma tace in sha Allah babu inda auren zai je, ba dai auran cin amana bane. Faɗa har cikin group ɗin makaranta, masu goyan bayan Azima nayi masu goyon bayan Salma na yi, amma yawanci anfi zagin Azima, saboda itace taci amana. A cikin ƙasa da sati ɗaya ya sama musu gida mai kyu kuma ta tare. Sai lokacin ne taji sunansa wai Kamal. Sai kuma a lokacin hankalin ta ya dawo jikinta, tunanin alhajinta ya faɗo Mata, sannan ga sauran samarinta. Ko kaɗan shima Kamal ɗin ba sonsa take ba, amma haka ta fara zaman aure da shi da zuciya ɗaya duk da auran nufi tayi da shi. Ashe duk kuɗin da take tunanin yana da shi wasa ne, sai yanzu da suka yi aure yake nuna mata asalin kuɗin sa. Sabuwar mota ya saya Mata mai kyau a cikin sati ɗaya da yin auren, ga kayan lefe da ya kawo mata a kwati goma sha biyu shaƙe....📝




Hahah Allah ya dawo da Alhaji lafiya