Chapter 2
*_The Amazing Pen_ ✍️..........*
*_NACINA YA JAWO MINI..._*
*002🔥*
Tashi ya yi ya wuce ɗakinsa, haɗadɗan ɗaki ne wanda dan ko amarya sai haka, in fact ko amaryar ma sai wacca ta cika amarya,ɗaki ne mai kyau da tsari, gashi babu wani tarkace dayawa,fentin ɗin ɗakin fari ne tas, bed ɗin ma fari ne haɗe da ratsin gold,a can ta gefe kuma akwai sofa da centre table mai kyau, gaskiya ɗakin ya kai ƙarshan haɗuwa.
Wanka ya yi kana ya fito, a gurguje ya shirye saboda jin an kusa tayar da sallah, ash color jallabiya ya sa mai taushi haɗe da sheƙi, sannan ya daddala kalolin turaruka masu ƙamshi da tsada sannan ya fito,wayarsa da take aaljihu ya ciro jin tana vibrating, ya kalla na ɗan wasu seconds sannan ya yi picking.
A can aka ce
"Hello Sadam, yane kana gida ne"
Sadam ɗan jimmm kaɗan ya yi kafin ya ce
"Eh, yanzu zan shiga masallaci"
A can ya ce "OK, gani nan zuwa, in shaa ALLAH ", da OK ya ce tare da katse kiran.
@@@@@@@@@@@
Massallaci ya nufa don sallar Asr, bayan an kammala ya dawo cikin gida da yake a cikin gidan masallacin yake,kafin ya shiga ciki ya tsaya, ganin mai gadi ya buɗe tanƙameman gate, wata rantsatstsan motar ta danno cikin gidan, kana ta nufa inda ake parking tayi parking, wani guy ne wanda bai wuce sa'ar Sadam ba ya fito d'an kimanin shekara 20 da haihuwa, Kamal kenan na hannun daman Sadam, abotarsu ba ta yanzu ba ne, sun yi makaranta tare tun daga primary har secondary sai dai abinda kowa yake son zama a rayuwarsa ya banbanta, Sadam nason ya gaji mahaifinsa kasancewar shi kadai ne ɗa namiji a gidansu wato cikakkyan ɗan kasu shiyasa yake son karantar Business Administration a Oxford University, UK.
Sa'annan Kamal nason zamowa ɗan Jarida, shiyasa yake da sha'awan karantar Mass communication.
Rungume juna suka yi sannan suka nufa ciki a tare, hannunsu na sarƙafe da na juna, da sallama suka shiga, Mum da ke falon ta amsa musu tare da faɗin "Kamal kazo yin sallama da ɗan uwan naka ne? Kamal wanda yake a russune ya amsa mata da" Eh Mum ya faɗa min jibi ne tafiyar kuma jirgin safe zai bi ", Mum ta ce" Toh maa shaa ALLAH ,Auta ya faɗa min kaima ka samu admission", Kamal yace"Eh Mum"
"Toh ALLAH yasa Albarkha, ya sa Ku gama lafiya", da Ameen suka amsa sannan suka nufi sama ɗakin Sadam .
Nan suka fara hira kamar karsu rabu kasancewar Kamal akwai zuba kamar famfo, sai ƙarfe 8:00pm Kamal ya wuce gida.
Haka dai Sadam yayi shirye shiryen sa, sannan ya ziyarci sister ɗinsa ɗaya wacca ta ke aure a nan KEBBI, tana auran wani ƙusan gwamnati, ita ɗayar sister ɗinshi tana aure a Pakistan da ƴarta mace, sannan washa gari jirginsu ya cilla sararin samaniya zuwa UK.
@@@@@@@@@@@@@@
KADUNA
Wasa wasa lokacin sauka ya ƙarato, Alhamdulillah Umman Sa'eeda tayi bakin ƙoƙarinta wurin ganin ta ma Sa'eeda kayan sawa na fitan sauka daidai gwargwado wanda da adashen kuɗin kayan wankin mutane da ta ke yi ne ALLAH yasa ta samu kwasan farko.
"Abban Sa'eeda don ALLAH ka taimaka koda na pure water ne mu samu tun da ka ga ranar asabar ne saukan, gashi yau ne kasuwa ta ke ci",
Duk wannan zancan da Umman Sa'eeda ta ke yi yana jinta a kishingiɗe a ɗan gadonta yaƙi kulata, ta ƙara da faɗin" ka yi shiru Abban Sa'eeda "
Buɗar bakinsa ya ce" Toh me kike so na ce, ni na sakata makarantar da zan ba da wata gudunmmawa na ehhh! , tun farkon karatunta ai na ce miki ban da halin biyata mata kuɗin makaranta amma ke gaki ƴar iyayi ke don a ce ɗiyar tana makaranta kikayi cuku-cuku har ta fara, kina wahalar da kanki da wankin dauɗar mutane!''
sai da ya lumfasa duk tana jinsa bata ce komai sannan ya ɗora da faɗin"Don haka karki sakemin maganar karatun Sa'eeda kuma wannan kashedi ne na miki, ban hanaki ba ko dako za ki yi don ƴar gold ɗinki tayi karatu bai shafe ni ba, ki ƙarata can da gulmarki"
Zumbur ya miƙe ya kakkaɓa babbar rigarsa zai ƙara gaba, Umman Sa'eeda ta tashi da sauri tana dubansa sannan ta ce"Duk naji bayananka, kamar yanda ka ce karatun Sa'eeda bai shafeka ba,toh in shaa ALLAH daga yau bazaka sake jina na maka batun karatun Sa'eeda ba, wannan alƙawari ne, kuma sai Sa'eeda ta zamo fila mai haske wannan gidan wanda yake cike da duhu, in shaa ALLAH "
Taɓe baki yayi kana yace" Wannan ke ta shafa, ni kin ga tafiya ta"
da sauri ya ƙara gaba, Sa'eeda da ta ke bakin ƙofa ta yi saurin matsawa, ALLAH yas a bai ganta ba,da tasha ranƙwashi, ita wallahi ta rasa mai ta.yi wa mahaifinta yake kyararta baya sonta, sai dai ƴan ɗakin Umma Kande wanda ba su da aiki sai tsagwaran talla titi-titi da garagin motoci, duk sun sha bleaching, har da sa'arta Iklima ta fara bleaching da taɗi a zauransu.
Duk fa wannan zancan acikin zuci Sa'eeda ta ke yi,zumbur kamar wacca aka tsikara ta dawo hayyacinta ta shige d'akin.
@@@@@@@@@@@@@@
"Ummina mai ya sameki kike kuka, kinaso in fara kuka ne, Abbana ne koh, toh kiyi haƙuri wataran sai labari,bana son zubar hawayanki Ummina"
tana maganar muryarta na rawa saboda zuciyarta na mata suya akan maganganun da mahaifinta ya faɗama Ummanta kamar bashi ya haifeta ba.
Hawaye suka fara sulalowa bisa kuncinta, ganin haka Ummanta tsagaita kukanta tana dubanta, don a rayuwarta ta tsana jin kukan ƴarta ta,haka ta tallafo kuncinta tana dubanta da murmushi ta ce " Haba sanyin idaniyata, ban sanki da saurin karaya ba, da juriya da jarumta na sanki, don haka bar kukan nan, shsre tsadaddun hawayanki kin ji, abar kaunata"
da wannan kalaman Sa'eeda ta tsagaita da kukanta ta ɗago sannan ta kalli Ummanta tace "Toh ke ma ki daina kukan kin ji Ummina"
Cike da shagwaba ta ke maganar har ta so ba Ummanta dariya, tace "Toh na bari tawan", a tare suka murmusa,sannan suka cigaba da sabgar su.
@@@@@@@@@@@@@@
Umma Kande ce da ƴaƴanta mata uku da namiji ɗaya wanda ya kasance babba a gidan ɗan kimanin shekara 25,suna zaune a ɗaki suna ƴar hirarsu cike da annashuwa har da shewa.
Nusaiba wacca ta ke bima Musa tace" Wai ni ya waccan Allazi bokon da mamanta suka ƙare da baba ne, ya basu gudunmuwan ne, na ji biki bamu chapter mun sha ba"
Umma Kande ta sheƙe da wata bazawarar dariya har da buga cinya,"Yo kema kinsan maganar gizo bata wuce ta koɗi,zan bari babanku ya bama wannan mai kama da mayun tallafi ne, haba ina badai ni jikan sarkin ruwa ba sai dai wata"
Sai suka ƙara sheƙewa da dariya sannan da ɗora ta faɗin"Ai ku sha kurumunku, in har kun ga kuɗi sun fita daga aljihun Babanku saidai ku za'a ma hidimar, don wlh ko zan yi yawo tsirara sai na ga ƙarshen wa'incan mayun"
Alamar jinjina ƴaƴan suka mata tare da wasata kamar ƙaura. Haka suka cigaba da hirarsu har aka kira sallah amma babu wanda a cikinsu ya iya miƙewa don yin sallar(Wa iyazubillah🤔🤔🤔) .
@@@@@@@@@@@@@@
Yaune ranar sauka, fili ne babba wanda yake cike da kanopils, ƙananun kujeru da na alfarma, filin ya cika maƙil da mutane har babu masaka tsinke, a bangare guda ƴan sauka jere suna shigowa filin don fara karatu, haka suka kammala karatun cikin tsari da burgewa.
Manyan baƙi tun daga kan wakilin sarki da na hakimi,ƴan siyasa da masu hannu da shuni duk sun hallarta . Alhamdulillah haka karatuttuka sukaita wakana da wa'azuzzuka da dai sauransu har aka fara shirin bada kyaututtuka ga wa'inda suka cancanta.
Mc mai magana ya fara da faɗin "Toh yanzu-yanzu ba da jimawa ba za mu fara bayaf da kyaututtuka ga ɗaliban da suka cancanta sannan sukayi zarra"
Kowa a filin ya natsu don sauraron zakarun shekaran, Umman Sa'eeda na hango can a zaune tasa wata atampa roba taji jiki sosai, sai murmushi ta ke ganin yau ƴarta tilo ta kammala haddan Al Qur'ani mai girma cikin nasara da aminci duk da ta samu ƙalubale a baya sannan yanzu ma dai bata gama fuskan ƙalubalan ba hasalima wasan yanzu aka soma(wasa farin girki).
Mc ne ya fara da cewa " Wacca tafi kowa hak'uri da natsuwa itace Sa'eeda Sulaiman", haka ta taso tana murmushi tazo filin inda za'a bata kyautar wanda wakilin mai girma sarki zai bada, haka a kai ta bada kyatuttuka wanda kusan Sa'eeda tai ta tasamu.
Daga ƙarshe Mc ya fara wasa gwarzon/gwarzuwan shekaran, nan da nan fili da rincaɓe da hayaniya don jin zakara/zakariyan shekaran, Mc yace"Gwarzo ko gwarzuwan shekaran nan shi ne ko ita ce", sannan ya tsagaita, mutune sai tsuma suke da ƙosawa don jin overall best student, Mc ya ƙara da faɗin "ita ce Sa'eeda Sulaiman", filin ya ɗauka da kabbara"Allahu Akhbar!!!
haka taje ta amsa kyautarta had'e zunzurutun kuɗi har #100,000,wanda kyauta ne daga wakilin sarki a ba ma wanda yayi Zarra.
@@@@@@@@@@@@@@@
Haka suka dawo gida ita da Sa'eeda da maƙotan da suke mutunci dasu, wa'inda kwata-kwata ba su fi mata uku ba, don Umma kande woman leader ɗin unguwar ne . Daidai gwargwado Sa'eeda da gudanar da walimar saukanta wanda 'yar walimar ba su da yawa daga Maryam aminiyarta ta boko sai wasu sa'oninta ƴan layi.
Bayan sallar Isha'i, Sa'eeda ta dubi Ummanta tace"Ummina ya za'a yi da wannan kuɗin da na samu ", Umma Sa'eeda tace" Zan buɗe account a sa kuɗin gobe in shaa ALLAH don tun yanzu zan fara tarin kuɗin karatunki na jami'ah, tunda na san bazan samu daga Abbanki ba kuma Koda na fara sana'a ba karɓuwa zatayi ba, saboda Kande, ko ya kike gani ke"
Sa'eeda saida ta lunfasa sannan tace"Toh ummina duk yanda kika tsara banda jayayya, ALLAH yayi mana jagora ", da" Aameen ", umminta ta bita dashi, sai suke yi shirin bacci don garin ya soma yin shiru.
@@@@@@@@@@@@@@@
Haka dai rayuwa ta cigaba da tafiya yau da daɗi gobe babu daɗi, a bangaren Sa'eeda sai a hankali, hutun boko ya ƙare sun koma makaranta ka'in da na'in babu kama hannun yaro.
Ta shiga SS1 Art class saboda tun tana ƙarama ta ke da sha'awan kasuwanci kuma Ummanta tanason haka, shiyasa ta ke son karantar Business Administration,saboda fannin kasuwancine, haka ta fara SS1 cikin nasara da aminci.
Sa'eeda karatu tareke ba dare ba rana tunda yanzu ba islamiya ta ke zuwa ba sai dai tilawan Al Qur'ani mai girma da litattafai,karatu yayi nisa sun fara shirin exams na kammala SS1 zuwa SS2.........................
*Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️*
***