PAGE 26
*RAGAYAR DUTSE.*
©️ *Nana Haleema.*
*Book 1*
*Page 026.*
Islaha bacci ta yi sosai sai lokacin sallar la'asar ta farka, ta miƙe jiki a sanyaye babu ƙarfi, ta sake yin wanka ta shirya ta rufe gidan ta shiga gidansu Safeera.
Allah ya taimaka Umma bata nan, daga ita sai ƙannenta ta. Islaha ta ce, "Bestie zan koma."
Safeera ta bita da kallo ta ce, "gabaɗaya kin canja, fuskarki ta ɗan kumbura kaɗan. Wannan abu yana baki wahala sosai."
Ta sauke numfashi ta ce, "bacci na yi, ban jima da tashi ba."
"Yanzu ya batun kuɗin?."
"Sai gobe in sha Allah."
"To ga wayarki, ɗazu ya aiko min da ita ya ce na kai miki."
Islaha ta karɓi wayar ta ga an canja mata screen ta dawo kamar dah. Ta yi murmushi ta ce, "na gode sosai, bara in yi masa waya na yi godiya, dan na san ya kashe kuɗi da yawa."
Safera ta yi murmushi tana ji suna waya tana yiwa Saleem godiya. Bayan sun gama Islaha ta ce, "Ya batun Umma, Kin yiwa mutanen KT ɗin magana?."
Ta yi ajiyar zuciya ta ce, "na yi magana da Yayan Umma, ya faɗa min zai yi mata magana in zara ta ji."
Islaha ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Allah kar ya bawa Umma ikon tafiyar nan, addu'a zamu dinga yi kawai" ta faɗa suna fara fitowa daga falon su Safeera.
Safeeea ta ce, "amin. Akwai abinci in za ki ci."
Ta kalle ta ta ce, "kin san in ina cikin wannan yanayin bana iya cin abinci sosai, na fi son abu mai ruwa da kayan zaƙi."
"Ai za ki sha gata, tunda wanda zaki aura duk ya san da wannan tsarabe-tsaraben naki, kin ga sai ki sake sangarcewa."
"Kamar kin sani kuwa, kafin ya tafi haka ya bani kayan zaƙi in ajjiye."
Safeera ta yi dariya, bata ce komai ba ta raka ta har ƙofar gida ta hau napep ta koma asibiti.
Lokacin da ta koma a nan ta tarar da akwai baƙi yan dubiya, wasu ta san su wasu kuma bata taɓa ganinsu ba.
Ta samu waje ta zauna, Sadik ya zo kusa da ita ya ce, "Islaha ya jikin? Mama ta ce bakya jin daɗi."
"na ji sauƙi sosai. Ya batun kuɗin?."
"Abu na farko, an samu mai bada ƙodar."
Islaha ta buɗe ido ta ce, "da gaske an samu?."
Sadik ya murmusa ya ce, "da gaske Islaha. Ƙanin Baffa ne, ya ce zai iya bayar da komai akan Baffa. Yanzu jira mu ke yi Dr yazo mu je dashi mu san abinda ya kamata mu yi. Fatan mu Allah ya sa komai ya yi daidai dana Baffa ɗin."
Islaha ta ce, "Alhamdu lillah! Kai amma na ji daɗi sosai."
Sadik ya ce, "nima na ji daɗi sosai Islaha, yanzu jira zamu yi ya zo sai a san abinda za a yi."
Ialaha ta ce, "mu je mu duba ko ya dawo." Bai musa ba suka nufi office ɗin Dr Isma'il. Suka yi sa a yana nan, suka sanar dashi abinda ya ke tafe dasu, ya ce su je azo donar ɗin.
Tare suka koma wajan likitan, aka shiga da ƙanin Baffa suka zauna.
Dr ya kalle sa ya ce, "Malam ya sunanka?."
Mutumin ya ce, "Sunana Yaƙub."
"Malam Yaƙub ya ku ke da Mutsatapa maddibo?."
"Yayana ne, uwa ɗaya mu ka haɗa."
"Shekarunka nawa?."
"Arba'in da uku."
"Kana da aure?."
"A'a, na taɓa yin auren dai amma maatar ta rasu."
Dr ya ce, "ka amince zaka bawa Mustapaha ƙoda ba tare da tilastawa ba?."
Ya gyaɗa kai ya ce, "na amince, domin ya wuce komai a gare ni."
Dr ya ce, "shikenan. Gobe in Allah ya kaimu litinin, ku zo da safe za a yi gwaje-gwaje dan mu san matakin lafiyar ka, zamu duba ka in komai ya yi daidai, zamu saka ka a tsarin abincin da ya kamata ka ci kafin ayi aikin."
Sadik ya ce, "mun gode likita."
Suka gaisa dashi ya ce, "babu komai, Allah ya ƙara lafiya" suka amsa da amin suka fito daga office ɗin suka koma suka zauna.
Suna zaune Hanan ta shigo ita da wani saurayi matashi mai ji da iyayi, suka ƙaraso inda suke zaune. Yana gaida Mama sai wani yatsina yake yi yana yauƙi kamar kuɓewa.
Ya ce, "Mama ya mai jiki?."
"Mai jiki da sauƙi."
"Allah ya ƙara sauƙi." Aka amsa da amin.
Ya saka hannu aljihu ya ɗauko dubu ɗari biyu ya bawa Mama ya ce, "Mama a siyi magani, sannan in akwai abinda ake buƙata a sanar dani zan bayar."
Ba tare da tunanin komai ba Mama ta karɓa tana ta zuba masa godiya, Hanna sai iyayi take yi saurayinta ya zo ya bada kyautar dubu ɗari biyu.
Labiba kuwa ta haɗe rai, kishi da baƙin ciki suka mamaye mata zuciya. Ba haka take so ba, bata so ta ga Hanan ta fita samo kuɗi, bata so ta ga Hanan da samari kala-kala ita kuma ba ko yaushe take samu ba. Hakan yana ƙona mata rai, bata so Hanan ta fita ko kaɗan.
Islaha dai tana zaune tana ganin ikon Allah, tana zaune tana ganin yadda ake kishi akan bin mazan kan titi. Tana kula dasu duka, ita Hanan da biyu take wani abun, tana yi tana kallon Labiba. Ita kuma Labiba ga kishin nan ya bayyana a tare da ita. Ta yi tsaki, a bayyane ta ce, "Allah ya kyauta."
*****
Rehaan da ya koma ɗaki kasa bacci ya yi, duk da baccin yake so ya yi amma ya kasa, so yake ya samu dama ya nunawa yarinyar can waye shi, so ya ke ya yi mata abinda bazata sake ganin wani ta ce masa waye kai ba. Gabaɗaya abin ya dame shi, ya rasa meyasa ta cushe masa zuciya har haka.
Ya yi shiru ba ya cewa komai, duk da ba hira ake yi ba, Mamy ce kawai a zaune sai Banisha.
A lokacin Jafar ya shigo da sallama suka amsa, ya ƙaraso ciki ya kalli Mamy ya ce, "Mamy in sha Allah da daddare zan koma Uk."
Mamy ta ce, "da wuri haka?."
"Eh Mamy, akwai aikin da zai mayar dani ne dole in koma."
"Allah ya kiyaye Jafar."
"Amin Mamy."
Rehaan sai a lokacin ya buɗe ido ya kalle sa ya ce, "baza ka bari mu tafi tare ba?."
Ya kalle sa cikin harara ya ce, "kai fa Jeddah zaka je daga nan, ni kuma kai tsaye can zan wuce."
"Ba sai ka raka ni Jedan ba."
"ko ina sai na raka ka? Kai kamar wani ɗan ƙaramin yaro komai sai an yi maka?. Ka ga Malam, ka ko yi yin abu kai kaɗai ba tare dani ba."
Rehaan bai ce komai ba ya ɗauke kai daga kallonsa, dan ya san tunda ya ce haka bazai tsaya ɗin ba.
Mamy kam murmushi take yi, ta san a duk duniya Rehaan ɗinta bashi da wani in ba Jafar ba. Shiyasa take son Jafar, bata jinsa a matsayin wanda zai auri Riyya, tana yi masa kallon ɗanta kamar Rehaan. Dan a duniya in kana so kaga farin cikin ta, ka so ɗanta.
Rehaan ya miƙe zaune ya ce, "zamu koma gida, amma ni bazan koma gida ba Mamy, zan je guest house akwai abinda zan yi."
Mamy ta kalle sa ta ce, "ba ka son komawa gidan ne kawai Rehaan."
"A'a Mamy, akwai abinda za a kawo min, in na gama zan dawo gidan in sha Allah."
Mamy ta ce, "shikenan ya yi. Yanzu zamu tafi?."
Ya ɗaga kai alamun eh ta ce, "to mu je."
Ma'aikatan asibitin da kansu suka shigo, hatta handbag ɗin Mamy riƙe mata aka yi, aka raka du har inda mota take, suka shiga suka tafi sannan kowa ya watse, ana murnar an rabu lafiya.
Islaha basu koma gida ba sai bayan sallar i'sha sannan Sadik ya tsaya a ƙofar gidan da mota. Ta kalle shi da murmushi ta ce, "na gode Hamma Sadik, Allah ya saka maka da alkhairi."
Ya yi murmushi ya ce, "Matar Hamma kenan. Ni da Saheer tare muka taso fa, Baffa babana ne kamar yadda babana yake babansa. Duk mun zama ƴan uwa, kar ki damu da wannan."
Ta yi murmushi ta ce, "gaskiya ne. In sha Allah da safe zan je bank saboda zancen loan ɗin nan, in na samu zan sanar da kai."
Ya yi murmushi ya ce, "Allah ya kaimu, ki kwantar da hankalinki, komai zai zo da sauƙi in sha Allah." Ta ɗaga kai daga nan ta fita ta shiga gida.
Ya bita da kallo yana murmushi, sai kuma ya girgiza kai ya ce, "Islaha ta Saheer. Tana da ƙoƙari, yadda ta damu da Baffa ko ƴaƴansa basu damu dashi ba. Shege Saheer, ba dai wayo da hange ba, ashe kaɗai ya san me yake shiryawa, shiyasa ya ƙwamuso ta daga gidan marayu. Ya yi zaɓe mai kyau" ya faɗa yana dariya ya ja motar ya tafi.
Islaha da ta shiga cikin gidan bata shiga harkar kowa ba, wanka kawai ta sake yi, ta sha black tea ta kwanta. In ta ce zata kula ƴan matan Mama faɗa zasu ja ayi, ita kuma ba wannan ne a gabanta ba. Da wuri ta yi bacci da niyar gobe ta tashi ta je banki.
Rehaan lokacin da suka koma gida tunda suka shiga yake jinsa wani iri, gabaɗaya rayuwar gidansu bata yi masa daɗi ko kaɗan, sai ya dinga jinsa daban kamar wani baƙo. A haka ya zauna a falon Mamy, ya yi shiru yana kallon waje ɗaya cike da tunani.
Abba ne ya shigo da sallama, Rehaan ya amsa yana tashi zaune sosai. Abba ya ce, "ashe kun dawo gida, yanzu nake shirin zuwa asibitin." Ya ɗan ɗaga kai ya ce, "mun dawo Abba."
Abba ya zaunaa kusa dashi sannan ya ce, "ya jikin?."
"na samu sauƙi."
"Allah ya ƙara sauƙi, ya kiyaye gaba."
"Amin Abba."
A lokacin Mamy ta dawo, ta miƙawa Rehaan tea ya karɓa ta zauna a gefensa. Ta kalli Abba ta ce, "ba mu jima da dawowa ba ai."
Abba ya girgiza kai ya ce, "Haka Rehaan ɗin ya ce min. Da fatan komai lafiya?."
"lafiya lau, ya ji sauƙi sosai."
"Ma sha Allah, haka ake so."
Rehaan ya ce, "Abba zan je guest house in yi kwana biyu, kar na tafi baka sani ba, akwai baƙin da zan yi a can."
Abba ya ce, "a nan baza ka sauki baƙin ba?." Ya yi shiru bai ce komai ba, dan baya son yiwa Abba musu.
Abba ganin ya yi shiru sai ya girgiza kai, ya yi murmushi yana jin daɗin halayensa. Gashi dai matsahin mai kuɗi ne, ana cewa matashin mai kuɗi baya shin maganar kowa, kuma baya jin shawara, sannan sun raina kowa, to babu Rehaan a cikinsu. Biyayya yake yiwa Abba sosai, ko a cikin gidan ba kowa yake tankawa ba, shiyasa ya yi mamaki da ya yi faɗa in faɗa shida Daada ranar da ya dawo.
Ya san an ƙure sa ne, kuma shi kansa ya san ba a kyauata masa ba. Babban mutum mai ji da ɗaukaka kamar Rehaan, ace wata yarinya da ba a san a ina take ba za a aura masa?. Shima dai ya ji ne, amma bazai amince ba.
Abba ya ce, "shikenan ka je Rehaan, amma kar ka dinga yawo kai kaɗai." Ya ɗaga kai sai a lokacin ya fara shan tea ɗin a hankali.
Abba ya ce, "Daada ta ce min ta ga yarinyar da ta yi maka, har sunan unguwarsu da sunan mahaifinta ta faɗa min. Da ina ɗaukar maganar wasa, amma naga da gaske ta ke Rehaan."
Ya yi shiru bai ce komai ba, dan sai dai ayi abinda za a yi amma bazai auri wacce zata basa ba.
Mamy ma ta yi shiru bata ce komai ba, ta lafiyar ɗanta take yi ba wannan surutan ba. Samun lafiyarsa ya fi mata komai mahimmaci, in mata dubu za a kawo masa daga ƙasar larabawa, indai baya so itana bata sonsu, in almajira aka kawo indai Rehaan yana so tana so ɗari bisa ɗari. Tana girmama abinda ɗanta yake so, tana son abinda ɗanta yake so.
Rehaan ya ce, "Abba this week zan je Jedda."
Abba ya kalle sa ya ce, "kwana nawa zaka yi?."
"Ban sani ba gaskiya, sun nemi aikina kuma na yi approving."
"Allah ya kaimu, Allah ya taimaka maka ya ciagaba da baka kariya."
"Amin Abba. Akwai sa