RAGAYAR DUTSE

PAGE 27

by @nanahaleema11

 *RAGAYAR DUTSE.*


             ©️ *Nana Haleema.*


*Book 1*

*Page 027.*



Safiyar Monday da rashin ƙarfi Islaha ta tashi, yawan lokaci in tana cikin yanayi menstruation haka take kasancewa cikin mutuwar jiki da rashin karsashi. Ga yawan ɓacin rai, zazzaɓi da kasala.


Tana tashi wanka ta fara yi, ta shirya ta fito falo ta sha tea kamar ko yaushe, iya shi kawai ta sha ta ɗauki handbag ta fita ta tafi bank dan neman loan. Ta jima a can, sai sha biyu na rana sannan ta samu dama ta tafi asibitin duk ranta a ɓace yake. 


Kai tsaye wajan Mama ta nufa, ta same ta a zaune ita da Adda da Labiba. 


Ta zauna sannan suka gaisa, Islaha ta ce, "Hamma Sadik bai zo ba?." 


Adda ta ce, "ya zo, suna can ana yiwa Kawu gwaje-gwajen da ya kamata." 


Ta ɗan girgiza kai sannan ta miƙe tsaye ta ce, "bara in je wajansa" ta faɗa tana barin wajan tana takawa a hankali kamar bata so.


Adda ta kalli Mama bayan Islaha ta ɓace daga wajen ta ce, "Mama har yanzu kina da ja akan halayen yarinyar nan? Har yanzu kina kan bakar ki na bakya so ɗan ki ya aure ta?." 


Mama ta ɗan taɓe baki ta ce, "to ai dolen ta ta kula da Baffan ku, dole ta kula dashi dan shine silar zamanta a gidansa. Ya ciyar da ita, ya shayar da ita, har suttura ya yi mata, dan ita butulu ce sai ta kasa tsayawa akan cutarsa?."


Adda ta kalli Mama da mamaki ta ce, "Labiba da Hanan meyasa basa tsayawa akan kula dashi? Naga ai su haifarsu ya yi, ita kuma Islaha bai haife ta ba." 


"Ai ya fi sonta a kansu, sau nawa yana yi nata abu ya share su?."


"Haba Mama, ki yi adalci ko sau ɗaya ne akan Islaha don Allah." Mama ta ɗauke kai daga kallon ta bata ce komai ba. 


Islaha kuwa Sadik ta kira a waya, ya ɗauka ya ce ta same sa a office ɗin Dr Isma'il. A nutse take tafiya har ta je office ɗin, ta yi knocking aka bata dama sannan ta buɗe ta shiga. 


A zaune ta same su, itama ta ƙarasa ta zauna, Dr ya ce, "Alhamdu lillah komai da ake buƙata an samu. Ƙodarsa lafiya lau take, sannan blood group ɗinsa ya yi daidai dana mahaifinku. A taƙaice za a iya sakawa mahaifinku ƙodarsa."


_(In aka yiwa donar gwaji, yana ɗaukar kwanaki bai fito ba, mu bamu da lokacin jira ne, shiyasa muka ce har an yi kuma result ya fito dan labari ya tafi yadda ake so)._


A tare suka yi murmushi tare da furta, "Alhamdu lillah!."


Dr ya murmusa ya ce, "yanzu zamu ɗora sa akan tsarin abinci...." 


Ya juya ya kalli Kawu ya ce, "Baba akwai abincin da ya kamata a dinga ci saboda ƙarin jini da gina jiki. Za a dinga cin kayan lambu, iriinsu salad, zogale, alayyahu da sauransu. Sannan Baba za a dinga cin tuwon alkama da miya wacce bata da maiƙo. Sannan a tabbatar da ana shan ruwa yadda ya kamata, ya zama ana shan ruwa wadatacce a kullum."


Kawu ya ɗaga kai ya ce, "in sha Allah likita."


"Sannan Baba a gujewa cin gishiri, abinci wanda yake da maiƙo sosai. Saboda ana so a ci abinda zai yi saurin narkewa, ba a son cin abincin da bazai narke da wuri ba. A ƙauracewa shaye-shayen magani wanda ba likita ne ya bayar ba, sannan ko da rashin lafiya zata faru kafin lokacin aikin, in ka je asibiti zaka sanar dasu tsarin da ka ke kai. Sannan a gujewa shan maganin gargajiya."


Baba ya ce, "to likita. 


Islaha ta ce, "Dr zuwa yaushe za a yi aikin?." 


Dr ya ce, "ranar monday kamar yau in sha Allah. Ranar in ta zo, daga awa takawas zuwa awa sha biyu kafin aikin Baba ko ruwa kar a sha, ayi haƙuri a jure har sai an yi an gama." 


Baba ya ce, "Allah ya sa a yi a sa'a." Aka amsa da amin. 


Dr ya miƙa musu takarda ya ce, "Za a je ayi payment na kuɗin, ƙarfe takwas na safiyar ranar littinin za a yi aikin in Allah ya amince. Za a iya biyan kuɗin a yanzu, za a iya bari sai lokacin ya gabato. Za a iya ba da half, in an gama a ba da half."


Islaha ta karɓa tana ganin kuɗin da yake rubuce, sai da ta goge ido dan lissafin ya tsaya mata cak. Ta kasa gane yadda zata karanta zero a rubuce, ƙwaƙwalwarta ta je hutu. Ta ɗan goge ido ta sake kallo, ta ga miliyoyi ne a rubuce a kai. Ta ɗan danne ruɗaninta sannan ta ce, "mun gode Dr." Ya yi murmushi suka tashi suka fita. 


Wajan su Mama suka koma suka sanar dasu abinda yake faruwa, aka yi fatan alkhairi da fatan Allah ya sa a yi a sa'a. 


Islaha ta koma kusa da Sadik da yake cikin irin yanayinta, ya kalle ta ya ce, "Matar Hamma ya mu ke ciki?." 


Ta sauke numfashi cikin takaici ta ce, "wai na je bank a bani loan na naira miliyan biyar, wai account ɗina kuɗi masu yawa basa shiga, dan haka sai dai a bani miliyan ɗaya. Mtsww! Ko me zan yi da miliyan ɗaya oho." 


Ya ɗan sauke numfashi ya ce, "haka za ki yi haƙuri ki karɓi naira miliyan ɗayan, ko na magani sai ayi dashi. In sha Allah zamu yi magana da Saheer, ko filinsa da ya siya bayan wanda yake ginawa ne sai a siyar."


"Ko a siyar da gidan da yake ginawa ba, neman lafiya mu ke yi ai."


"A a, gwara dai a siyar da filin za a samu wani 

abun in Allah ya yarda."


"Allah ya amince. Nima zan san duk yadda zan yi wajan ganin na samo kuɗin da za a yi aikin."


"Allah ya taimaka mana, Allah ya basa lafiya, ya sa ayi a sa'a."


"Amin Hamma Sadik. Tunda an gama komai bara na wuce wajan aiki kawai, zuwa anjima sai in dawo." Ya amsa ta yi masa sallama ta bar wajansa zuwa wajan su Mama.


         *****


Suna zaune a babban falon Daada gabaɗayansu, kowa sai ɗaure fuska yake yi, ba sa son wannan taron na Daada, take haɗa taron babu gaira babu dalili, da abu yayi mata daɗi ko akasinsa zata ce kowa ya zo, kuma dole kazo ɗin babu yadda zaka yi.


Kowa yana zaune har Abba, amma Rehaan bai shigo ba, kuma shi kaɗai ake jira, dan saboda shi aka tashi taron gabaɗaya.


Mama taja tsaki ta ce, "kowa ya hallara a wajan nan amma ban da shi, da yake shi ɗan gwal ne. babu wanda zai ce bai kyauta ba. Inda wani ne ya kai yanzu bai zo ba, ana nan ana ƙananun maganganu."


"Assalamu alaikum" ya furta a hankali yana shigowa falon a hankali kamar ba ya so, aka amsa gabaɗaya ana kallonsa.  


Daada ta kalle ta ta ce, "gashi nan dai ya shigo...." Ta sake kallon Rehaan ta ce, "Shugaban masu sanyin jiki da rashin ƙwarin jiki kamar mace, wata macen ma ta fika karsashi, kai ta abu kamar mara laka. Mtsw! Allah ya sauwaƙe maka wallahi, gabaɗayan ka rago ne. Sai ka samu waje zo ka zauna. Kai kenan kullum babu kuzari, kana tafiya kana yauƙi kamar mace?." 


Bai ce komai ba, a hankali ya ƙarasa kusa da Juwairiyya ya zauna kamar ko da yaushe bai ce komai ba.


Daada ta ce, "yauwa akan bikin Juwairiyya da Jafar, da kuma Muhammad da Ishlaya." 


Rehaan ya ɗaga kai ya kalle ta suka haɗa ido,  ta gyaɗa kai tana buɗe idanunta ta ce, "kalle ni da kyau, wallahi sai ka auri yarinyar nan ko bani da rai." 


Rehaan yana lumshe ido cikin soft voice, da yaren da ta fi so ayi magana dashi ya ce, "ni ina da wacce zan aura Daada."


"Allah ya tsine mata ko wacece, baza ka aure ta ba, sai ka fara auren zaɓina. Daga nan ka auro matan duniya ma, ni bai dame ni ba."


"Ni kaɗai zaki yiwa zaɓi? Kowa a gidan nan choice ɗinsa yake aure, meyasa ni za a ce na auri zaɓin ki?."


Daada ta ce, "saboda na isa, na isa nayi zaɓin abi ko ba a so." 


Ya ɗan ɗauke kai daga kallon ta bai ce komai ba, yana ɗan gyaɗa kai dan wannan zaƙewar da take yi shine zai saka bazai amince ba, sai ya gani in ita ta haife sa.


Daada ta ce, "mara kunya fitsararre, dan baka da kunya baka da mutunci, ina faɗa kana mayar min da amsa kamar wata sa'ar wasan ka. Ni na haifi ubanka, amma ina faɗa kana faɗa kamar wata ƙanwarka." Bai ce komai ba, sai ma rufe ido da ya yi yana ji kamar ya yi tsuntsuwa ya gudu daga parlour.


Daada ta ce, "saura kwana nawa bikin Jafar ne?." 


Abba ya ce, "da ɗan saura Daada, kin ga an ɗaga bikin saboda Riyya tace tafi so sai ta gama karatu, kuma karatun nata bai wuce wata biyu ta gama ba. Ina tunanin zai kai wata uku yanzu,  ko sama da haka nan gaba."


"To a haɗa da Rehaan, a je gidan da na faɗa maka a tabbatar an nema masa auren yarinyar." 


Abba da mamaki ya ce, "da wuri haka?."


"Eh haka nake so."


Hamma Zayyad da ya kasance babba a gidan ya ce, "to me zai hana baza a ƙara lokacin ba, saboda gidansu yarinyar da ki ke magana su shirya ko?. Haka kawai za a je musu da maganar biki nan da wata uku ko biyu? Kamar ya yi kusa ko?."


Daada ta kalle sa sheƙeƙe ta ce, "baza a ƙara lokaci ba, hakan za a yi babu wanda ya isa ya canja min. Shugaban masu iyayi, kai ga babban ko?." Zayyad bai ce komai ba ya yi mata shiru.


Ta kalli Rehaan da ba ita yake kallo ba ta ce, "sai ka je gidan su yarinyar ku daidaita kanku." 


Bai ce mata komai ba dan ko kallon ta ma bai yi ba, in ya kalle ta sai ya tanka mata, shi kuma baya so ya ce mata komai akan tatsuniyarta.


Daada ta ce, "dan haka a fara shiri, a tabbatar da anyi komai yadda ya kamata." 


Rehaan ya ji kamar an kawo ƙarshen zaman sai ya miƙe zai fita daga parlour bai kalli kowa ba Abba ya bisa da kallon mamaki ya ce, "ina zaka je ana magana?." 


Ya ɗan yatsine fuska ya ce, "na yi tunanin an gama, na gaji ne" ya faɗa yana komawa ya zauna. 


Daada ta harare sa ta ce, "sai ya nuna min ban isa dashi ba, sai ya nuna min shi jinin indiyawa ne ba cikakken bafulatani bane. Dan jin fulani bazai yi wannan ɗibar albarka ba, indai nonon bafulatana ka sha babu kai babu ɗabi'ar banza"


"Wai meye da indiyawan nan, su ɗin kafirai ne?" Ya tambaya yana kallon ta dan ya gaji da zagin Mamy da take yi a fakaice. 


Daada ta ce, "akwai inda ya kai india kafirci, Meye basa bautawa? Kai ɗin nan in ka yi musu kyau sai su fara bauta maka. Har sai an buɗe baki an ce musu kafirai? Faɗa ma ɓata baki ne."


Rehaan ya lumshe ido ya buɗe ya ce, "ko ina akwai kafirai, ko a cikin fulani akwai waɗanda basu da addini. Gwara india, da wahala a samu wanda bashi da addini, fulanin fa?" ya faɗa yana kallon ta.


Daada ta zuba masa ido kawai tana kallonsa, sai kawai ta fashe da kuka tana faɗin, "ni ka zaga ko? Kai tsaye dani ka ke tunda ni bafulatana ce. Dani ka ke kawai, ka fito kai tsaye ka zage uwata da ubana. Na shiga uku, yau jikana ne yake zagina, ko a gidan nan shine auta a maza, amma ni yake kallo yana zagi."


Ya ɗauke kai daga kallon ta yana jin takaici a ransa, ya juya yana kallon Mamy da ta ɗan yi murmushi kawai bata ce komai ba. 


Abba ya ce, "ki yi haƙuri Daada."


"Kana jin ɗanka yana zagina baka hana shi ba,

sai ni zaka hana kuka?." 


Abba ya kalli Rehaan ya ce, "Ka bata haƙuri."


Rehaan ya kalle ta yana ɗan taɓe baki ya ce, "miyoɗi jam" ya furta yana kallom Mamy da take kallonsa. 


Daada ta goge ido, kukan nata yana tsayawa alamun daman na rigima ta ce, "duk bala'in ka fulani sun fi indiyawa, babu ta yadda zaka haɗa fulani da india wallahi. Indiyawan banza da wofi." Bai kulata ba ya ɗauke kai daga kallonta yana ɗan lumshe ido.


Daada ta ce, "ishlaya ce sai kuma sai ka aura wallahi." 


Ƙasa-ƙasa ya ce, "sai ki saka na aura ai." 


Juwariyya ce kawai ta ji me ya ce, ta yi murmushi dan ta san an ƙure sa ne, ba dan haka ba har a tashi ba zai ce komai ba. 


Daada ta ce, "sai batun Janan, ɗan uwanta ɗan wajan babban ku Abiy yana son aurenta amma taƙi amincewa, kuma ni ina son haɗin. Ya ku ke gani?." 


Janan ta yi rau-rau da ido tana kallon Daada, bata son auren zumuncin nan, amma Daada ta dage sai an haɗa. Ta san kuma Hamma Zayyad da Mama amincewa zasu yi, haka kawai za a yi mata auren dole bayan kowa ya san bata ƙaunar auren. 


Hamma Zayyad ya ce, "a ganina zata amimce, duk muna son haɗin mu ma sosai, ai ƙarfafa zumunci ne." 


Kowa ya amince da maganar Hamma har da Mamanta. Daada ta washe baki ta ce, "Haka nake so na ji, auren zumunci ai akwai daɗi, musamman na uwa ɗaya uba ɗaya. Ba irin na Jafar da Juwairiyya ba, da suka ɗauko ƴan uba."


Abba ya kalli Rehaan da bai ce komai akan maganar ba ya ce, "Rehaan baka ce komai ba, meye ra'ayin ka a kai?."


"A bata dama ta zaɓi wanda zata aura. Aure ba abinda za a yiwa mutum dole bane, ita zata zauna dashi ba wani ba....." 


ya ɗan ja numfashi saboda ciwon cikinsa ya ce, "In tana so sai ayi, in bata so a bata dama ta kawo wanda take so. Dan Jazy zai auri Riyya ba hakan yana nufin itama lallai sai ta auri wani daga family ba. Riyya tana son Jazy, ba Jazy ne kaɗai yake sonta ba. Amma Janan bata son Khalil, shine yake sonta......"


"Don Allah kar a yi forcing ɗinta, a bata dama ta auri wanda take so kamar ƴan uwanta."."


Abba daman ya san shi kaɗai ne zai faɗi gaskiya, shi kaɗai ne bazai hangi kuɗi ba. Dan ya san Maman ta kuɗin Khalil take gani, dan yaron yana da abin hannu shima. Shi kuwa Rehaan babu kamar sa, kuɗin Khalil bazai buɗe masa ido ba, a wajen Rehan Khalil bai wuce ma'aikaci ba, shiyasa ya saka shi ya yi magana dan ya ɗora a kan tasa.


Abba ya ce, "maganar Rehaan gaskiya ce Daada, kar a tilasta mata." 


Kowa ya zubawa Daada ido ana jira a ji me zata ce, dan kowa ya san yadda take son Khalil, a cikin jikokin ta yana daga cikin wanda take mutuwar so. 


Daada ta ce, "zan yi shawara akan hakan." 


Kowa ya saki baki da hanci yana kallon Daada, yadda ta amsa maganar kai tsaye an san maganar da Rehaan ya yi ne ya dakatar da ita. Lokaci ɗaya hassada da baƙin cikin Rehaan ya sake ninkuwa a zuciyarsu.


Mama ta kalli Daada tana ƙwafa a ranta, sannan ta kalli Abba da Rehaan tana girgiza kai cikin mamaki da al'ajabi. A haka taron ya watse kowa ya kama gabansa.


      Mama da yaranta da suka koma apartment, suka saka ta a tsakiya kowa yana kawo mata suka akan maganar ta ko ina. 


Sameer ya ce, "yanzu Mama Rehaan ya zama kamar shine babba a gidan nan? Hamma ya yi magana, maimakon a karɓi maganar sa sai aka karɓi ta