Chapter 3
*_The Amazing Pen_ ✍️..........*
*_NACINA YA JAWO MINI..._*
*003🔥*
Karatu yayi nisa sun fara shirin exams na kammala SS1 zuwa SS2. Sa'eeda ta shiryawa exams ɗin tsaf kuma takan koyawa Maryam inda bata fahimta ba kasancewar Maryam slow learner ce, duk da mahaifin Maryam ya kawo wa Maryam lesson teacher wanda zai dinga koyar da ita, hakan bai saka ta cimma Sa'eeda Koda da taku ɗaya a karatu ba, a gaskiya hakan nama Maryam ciwo a zuci, gata ƴar masu kuɗi,ƴar gata gurin iyayenta amma ace ƴar talakawa tafita komai, ga kyau, ga ilimi, ga natsuwa, ga, ga, haba abin yayi yawa.
Duk wannan zancen a zuci ta ke yinsa,bayan Sa'eeda ta kammala koya mata wasu calculations a Economics kasancewar su ƴan Art students ne,itama tana da burin zamowa ƴar kasuwa daga jin Sa'eeda lokacin da suka kammala exams na ƙarshe tana faɗin ita Art class zata shiga saboda tana son harkar kasuwanci carab ta ce itama shi zata karanta saboda yanda ta ji Sa'eeda na kururuta course ɗin Business Administration, don haka tana zuwa gida ta sanar ma Mom ɗinta, da farko taso yin jayayya don ita tafi son ƴarta ta karanci bangaran likitanci(saikace tanada kwakwalwar ne😂😂😂),don ace ƴarta ta tanada ilimi amma jin ta ce ita Business Administration zata karanta kuma Dad ɗinta ya goya mata baya yasa ta haƙura.
Mafi ƙololuwan ɓacin ranta shi ne ashe saboda Sa'eeda zata karanci Business Administration yasa ita ma ta ce za ta yi, amma babu yadda ta iya tunda mijinta ya ba da go ahead. Cikin ikon Ubangiji su Sa'eeda sun kammala exams ɗinsu,makaranta ta ba su hutun wata ɗaya da kwana huɗu saboda gab da azumi suka kammala exams kuma a ƙa'idan makarantar basa karatu cikin azumi shiyasa su ka yi hutu.
@@@@@@@@@@@@@
"Ummina anga wata, anga wata, yiriri!!! ", Sa'eeda da murnarta ta ke sanar ma Ummanta, da yake kusa dasu akwai masallaci wanda ladanin masallacin ne yayi shelar ganin watan, Umma dake zaune kusa da ƙofar ɗakinta tana shan iska ta ce " ALLAH ya sadar da mu albarkarsa, ya kuma amsa mana addu'oin mun gabadaya," da "Ameen ", Sa'eeda ta faɗa wacca ke cike da zumuɗin ganin wata, don tun tana ƴar shekara 12 ta dena shan azumi, complete ta ke yi wanda har mamaki Ummanta ta ke yi ganin ko Nusaiba da ta ke budurwa da ƙyar ta ke yin azumi 15 Duk da tana shan na haila wanda wajibi ne ga duk wacca ta balaga saidai mai ciki, ko mai jinin biƙi, ko mara lafiya,wacca ta ke bi mata ma Zaliha ita ma duk kwanwar ja ce, balle Ilkima wacca ta ke sa'ar ƴarta sa'eeda.
"Yawwa Idi shigo da kayan ciki" Nusaiba ce ke bama wani almajiri wanda ke karatu a wata makarantar Allo ta kusa da gidansu, kwalin indomie ne da kret ɗin Kwai, carton ɗin madarar peak, Bournvita, da dai sauransu. Sai wani ɗadɗaga kai ta ke ita ga saurayi mai kud'i ya kawo mata Ramadan basket.
Umma Kande da futowarta kenan daga bayi ta cillara uban guda haɗe da faɗin"Arziki kashi, yau gashi ƴata ta tako mana ", har da wani rungume da murna.
Nusaiba dai sai murmushi ta ke kawai, don ita kadai ta san yadda ta samu ramadan basket ɗin, abinda Umma Kande bata sani ba shi ne, Nusaiba ta daɗe da zubar da mutincinta awaje, hasalima tun tana ƴar kimanin shekara 17 ta fara zubar da mutincinta,a lokacin Umma Kande na saida gyaɗa da aya soyayya, haka zata ɗora mata tallar tare da mata gargaɗin ta tabbatar ta sayar sannan ta dawo gida, Umma Kande irin matan nan ne masu son abin duniya, da wannan gardaɗi da Umma Kande ta ke ma Nusaiba a kullum ya sa ta fara bin maza, har daga ƙarshe ta zama gwana bata wannan hotel ɗin bata wancan, tana yi ne duk don faranta ran mahaifiyarta.
Yanzu ma wani sugar daddy ne ALLAH ya haɗata dashi, yana kashe mata kuɗi sosai kuma a lokaci guda yana amfanuwa da albarkatun jikinta.
**Ƴan Uwana iyaye mata, a rage son abin duniya da dogon buri, baki da gashin wance ba lallai sai kinyi kitson wanca ba, haƙiƙa iyaye mata wani lokacin mukan tafka kuskuran da a ƙarshe zamuyi dana sani mara amfani,ba dole saikin tsawatarwa ƴarki akan lallai saita saida ta kawo miki kuɗi ba, duk abinda ALLAH ya ƙaddara takawo miki sai ki godewa masa,ki roƙeshi yasa Albarkha,amma tirsasa yara musamman ƴaƴa mata akan sai an saida talla na ɗaya daga cikin abinda ke fara sasu bin maza wanda a ƙarshe siyo abin kunya,Allah ya tsare mana imani**
Sa'eeda dai da Ummanta kallon ikon ALLAH su ke yi kawai, don duk habaicin da Umma Kande take yi da Umma Sa'eeda ne, amma ko ihhmmm ba ta ce ba hasalima da ta ga abun nasu ba gaɓa, ta ce ma Sa'eeda su wuce ɗaki, haka suka tattara tabarmarsu suka shige ciki abinsu.
Haka suka fara azumi abinsu, kuma ba laifi suna yinsa ciki kwanciyar hankali.
@@@@@@@@@@@@@
Azumi dai wasa wasa ya soma yin bankwana, don yanzu in sunkai sunkai na 25,har an soma shirye shiryen sallah, masu 'ya'ya tuni an siyawa yara kayan sallah, wasu ma har kala shida shida, kamar yanda hakan ta faru a gidansu Sa'eeda.
Abban Sa'eeda ya ma Nusaiba,Zaliha da Iklima ɗinkin sallah har kala biyu -biyu,sannan kowacce da takalmi baya wanda suka samu daga samarinsu , haka Umma Kande ta fito da kaya niƙi-niƙi waje daman saida ta fakaici Umman Sa'eeda na waje sannan tafito da kayan, da gayya take fito da kayan ɗaya bayan ɗaya tana faɗin "Kai! Kai!! kai!!!, daɗi kashe ni, wannan gata haka, 'ya'ya masu ƙashin arziki bayan wanda babanku ya yi kala biyu-biyu har da wanda mazajenku sukayi(wai fa mazajenku😂😂😂su Umma Kande ba dai ilimi da sanin ya kamata ba).
Tana wannan surutan ne duk don ta ƙunsa ma Umman Sa'eeda baƙin ciki saboda ta san ba'a ma Sa'eeda kayan sallah ba hasalima ita ta hana shi yi mata, dan tsoranta yake sosai dalilin mugun asirin da take mishi akai-akai tare da rufe bakin danginsa akan 'yar dukiyarsa wanda daga ita sai yaranta suke ci. Ko ƙala Umman Sa'eeda ba ta ce mata ba, sai dai murmushi kawai tayi da girgiza kai,ita ba baƙuwar zafi ba ce hakan da Abbansu Sa'eeda yayi bai dameta don ta san watarana sai labari.Haka dai Umma Kande ta gama iyayinta da kayan ta koma ɗaki.
@@@@@@@@@@@@@
KEBBI
"Oyoyo oyoyo mutan India, ashe dai da gaske kuke za kuzo sallah", Mum ce mai faɗin haka tana rungumar wata ƴar kyakkyawar yarinya mai kimanin shekara 3 a duniya da murmushi ita kuma yarinyar sai ciccijewa ta ke ita ala dole mai ƙyuya duk da sukan yi video call da ita hakan bai hanata nuna halin nata ba (ƙyuya) .
Wata kyakkyawar mata nagani ƴar wanka, fara tas kamar balarabiya ta ƙarasowa cikin falon tana samun guri kusa da Mum da faɗin "Washhhhh wallahi duk na gaji", cire veil ɗinta tayi wanda yayi daidai da kalan jallabiyarta marun,mai adon stones haɗe da veil ɗin, sannan ta russuna ta gaida Mum.
"Mum mun sameku lafiya? ", Mum da ta ke fama da Fanan ta amsa mata cike da kulawa tana faɗin "lafiya lau , ya mijin naki, ya aiki ", da "Duk lafiya lau" ta amsa mata
kai da Mum taga Fanan taƙi zama wurinta ta saketa da faɗin "Ja'irar yarinya zaki zo hannuna ne" da gudu da haye saman cinyar mamata tana dariya sai duk suka fashe da dariya.
Mum tace " Sameera zo ki ɗauki kayan Sadiya da tazo dasu kiwuce mata dashi ɗakinta", haka wata mai kimanin shekara 46 ta fito zuwa wurin Sadiya ta gaishe ta,Mum ce ta bada umarnin a dafa ma Fanan noodles taci.
@@@@@@@@@@@@@
Bayan sunyi wanka ita da 'yarta a lokacin an kusa kiran sallar magrib da yake saukan yamma su ka yi, masallacin gidansu suka ji an kira sallah, sai suka fara haraman shan ruwa, sannan suka gabatar da sallah.
Bayan isha'i Sadiya ta wuce ɗakin Mum don yin hirar yaushe gamo,da sallama ta shiga, ganin Mum na lazimi yasata zaunawa a sofa tare da ɗaukar Fanan bisa cinya.
Sanda Mum ta kammala lazuminta har sarauniyar ƴan ƙyuya tayi bacci,Mum ce ta dawo itama kan sofar bayan ta cire mayafin sallarta,ƙara gaisawa sukayi sannan aka shiga hirar ƴa da uwa anan ne take sannar ma Sadiya dramar da tasha kafin Sadam ya yarda zuwa UK karatu.
Dariya Sadiya ta saki tana cewa "Mum ai duk ke kika sangartashi, in yana tare dake ji kike kamar ki komar dashi ciki, ba dole yaƙi yarda ba duk da most friends ɗinshi a nan KEBBI University suka samu admissions hakan bazai mai daɗi ba"
"Amma yasan ƙa'idar gidan ai, ke da Sakinah a can UK kuka yi Karatunku", dariya Sadiya ta sukeyi tana fad'in "Auta ne fa", tsaki ta ja Mum sannan ta ce " wallahi ranar Auta ya ɓata min rai, da ƙyar na shawo kansa ya yarda da tafiyan" hamma Sadiya tayi tana faɗin "yanzu dai su Auta ana can ana boko, duk da nasan Auta da ƙoƙari Saidai sangarta in yana gabanki", Mum tace " Na ji ina ruwanki idan ma yayi sangartar", wannan karon dariya Sadiya takeyi har da riƙe ciki "Ni!!! na isa shiga tsakaninku", Mum tace "kya dai ji da shi", sallama sukayi don har 10:25pm yayi ta ɗauki Fanan suka nufi ɗakinta wanda tun tana budurwa ta ke ciki, ta shimfiɗar da Fanan sannan tabi lafiyar gado.
Washi gari kuwa har gidan ƴar uwarta Sakinah saida taje, nanma sukayi hira sannan ta dawo gida.
@@@@@@@@@@@@@
Yau dai ake sa ran ganin wata, Alhamdulillah da ƙarfe 11:45pm na dare Sarkin musulmi ya sanar da ganin wata,kowa sai murna yake, da addu'ar ALLAH ya karɓa ibadun da a kayi a watan.
Bayan an fito Idi Aunty Sakinarh da familinta suka iso gidan Mum, kasancewar mijinta tafiyar gaggawa ta samesa zuwa Germany. Maa shaa Allah🥰 Tabarakallah kawai na iya furtawa ganin wata hamshaƙiyar mata wacca baza tawuce shekara 28 a duniya ba, ta sha peach colour lace da ratsin gold wanda ko makaho ya taba yasan lace ɗin na ɗaruruwan kuɗine, ga gwala gwalai ya cika mata wuya kasancewar ta ƴar duma duma, bayan awarwaraye da zobba a hannunta, ta yafa yalwataccan gyale mai adon stones da takalmi tu match, ga twins ɗinta Maa shaa Allah Tabarakallah, suma sun sha kyau.
Haka dai wannan family suka sha shagulgulan sallah, sai bayan sallah da sati ɗaya Sadiya ta koma India cike da kewar ƴar uwarta da mum ɗinta.
Bayan tafiyarta da kwana biyu Daddyn Sadam ya dawo Nigeria da yake yayi tafiya zuwa China akan wani harkar kasuwancinsa bayan ya gama ne ya wuce Saudia aikin Umra.
@@@@@@@@@@@@@
KADUNA
Bagaren su Sa'eeda sunyi shagalin sallah dai dai malisa, kaza ɗaya Umma Sa'eeda ta siyo musu suka yanka, suka soya suka ci, ita kuma Hajiya Umma Kande kaji ɗai ɗai har goma suka yanka haɗe da ginsamin naman shanu da Abbansu Sa'eeda yakawo taƙi rabawa taba Umman Sa'eeda, haka su Zaliha da iklima sukai ta suya tsabaragyan rashin mutunci a ƙofar ɗakin su Sa'eeda suka sa kaskon tuyar(Kai jama'a in kana duniyar nan ka sha kallo😂😇), so suke Umman Sa'eeda ta tanka amma taƙi hasalima jawo ƙofarta tayi kasancewar akwai wutar nepa sai suka kunna fanka abinsu, duk wannan soye soyan da ake Nusaiba bata gida, tadai cema mamanta zataje tasha amsar saƙo wanda bata sanar da ita wani kala ne saƙon ba tun safe ta fita.
Ashe Nusaiba tama sugar daddynta Alhaji Sagir alƙawarin goron sallah ne, yace su haɗu a hotel, sai da ta fito daga layinsu ta tari ɗan keke napep a lokacin tasa niƙaf da yake duk sanda za ta hotel yin harka da niƙaf ta ke zuwa, tana isa hotel ɗin ta kira number sa, sai ya sanar da ita number ɗakin, sai da ta cire niƙaf ɗin sannan ta wuce direct ɗakin, isarta keda wuya ta ƙwanƙwasa, kamar jira Alhaji Sagir yake ya buɗe mata ta shige,ce mata yayi ta zauna yana son suyi wata muhimmiyar magana, ba musu ta zauna tana wani lanƙwasa da lashen lebe irin na tsoffin karuwan nan, (sai Kace mayya😀, Fans ai ita ta cancanta da zamowa mayyar ba Sa'eeda ba🙃).
@@@@@@@@@@@@@@
Alhaji Sagir zama yayi kusa da ita haɗe da rumgumota sannan ya ce"My sweet honey kinsan wani irin goron sallah nakeso kibani kuwa?
Nusaiba tace " Wanda nasa ba baka mana ko akwai wani goron na daban ne?
Ɗan murmushi yayi sannan yace" Sosai ma kuwa my sweet honey"
cikin zaƙuwa Nusaiba tace "To sanar min na ji sugar na"
Gyara kwanciyar Nusaiba yayi a ƙirjinsa sannan yace " Nusaiba ina so in ɗaga darajarki a duniya,zaki samu kuɗi kamar ba gobe,in har kika bani haɗin kai"
Ɗagon kanta Nusaiba tayi daga ji yace zai ɗaga darajarta a duniya sannan zatayi kuɗi, har ta fara harsaso yanda zata fantama da kuɗi ita da familinta wayyo daɗi
"Na yarda sugar na kuma zan baka haɗin kai"
murmushi yayi a zuci yake faɗin 'ai nasan zaki yarda mayyar kuɗi '
Ɗan lunfasawa yayi sannan ya cigaba da cewa "Inason in biya buƙatata dake ta baya ma'ana ba yanda na saba kasancewa dake ba kamar yanda kika sani, ta duburarki nakeson biyan buƙatana dake,sannan zan turamiki dubu ɗari biyar #500,000 in kin yarda kuma zan haɗaki da abokaina suma masu irin wannan harkar, wallahi Nusaiba kin gama kuɗancewa in kin yarda amma"
Shiru Nusaiba tayi tana tunani ta yarda ko ko A'a, can da ta tuna mamanta zataji daɗi kuma sun kuɗance, kawai saita amince(Ya Salam, Allah ka tsaremu daga faɗawa halaka da kuma zugar shayɗan).
Jin ta amince yasashi sakin wani munafikin murmushi, don haƙarshi ta cimma ruwa.
Haka suka fada halaka ita dashi duk da tasha baƙar wuya saboda farkon yinta kenan, bayan sun kammala masha'arsu sukayi wanka, ita Nusaiba har da gashi tayi don taji maza(kwaɗayi ma muɗin wahala🙃🙃🙃), sai huɗu na yamma ta iso gida duk da yanayin tafiyarta ya sauya amma Umma Kande bata gane wani abu game da Nusaiba ba, hasalima murna ta ke tayi saboda Nusaiba ta siyo kayan abinci haɗe da wasu kajin duk acikin kuɗin da Alhaji Sagir ya saka mata a account, murna iya murna Umma Kande tayi harda yima Umman Sa'eeda gori ƴarta batada mashinshini. (Umma Kande anyi bagidajiyar Uwa🤔).
@@@@@@@@@@@
Tunda daga wannan ranar Nusaiba ta zama ƴar hannu don Alhaji Sagir ya haɗata da abokanansa suna sharholiyarsu da ita.
Duk fantamawar da Nusaiba ta ke da kuɗi ko ajikin Umma Kande hasalima gadara ta ke ƴarta nada farin jinin samari, haka suma ƴan uwan nata duk da basa sharholiya irin nata amma suna ɗan matse matse da taɓe taɓe a zauran gidansu su da samarinsu.
Sa'eeda dai hutunsu ya ƙare sun koma makaranta,yanxu tashiga SS2, samari sun fara kai mata hari kasancewar ta kyakkyawa ga sexy eyes farare tas, gashi tanada ɗan girman jiki, don duk halittar ƴa mace ta gama bayyana a jikinta duk da ƙarancin shekarunta don yanxu take cikin shekara na 16,amma Maa shaa Allah.
Sa'eeda ta ɗaukar ma kanta alƙawarin sai ta kammala secondary kafin ta fara soyayya saboda soyyaya bata cikin tsarinta kwata kwata.
@@@@@@@@@@@@@
ABUJA
Ɗaki ne mai duhu sai ɗan wani haske kaɗan da nake ɗan iya hangowa wanda bai wadaci ɗakin ba, ga tururin hayaƙi daya turniƙe ɗakin, ni kaina da kyar na iya shiga ɗakin haɗe da addu'a dan ɗauko muku rahoto, wasu surutai kamar suddabaru naji muryar wata tana faɗi wanda nakasa gane mai ta ke cewa, kwatsam naga wani haske kamar walƙiyar ya ɓullo ta cikin bangon ɗakin ya haska ko'ina, wani halitta nagani kamar mutum amma wada, kansa a ƙasa yake, shi baiyi ƙasa ba kuma bayi sama ba, yana a tsakatsaki, tsawansa bai wuce tsawan hannu ba, sai rangwajejan kai kamar ƙwarya,yanada idanuwa kamar na mage, da sharɓa sharɓan kafakuwa kamar na babban mutum, kai in taƙaice muku, halittar nan batada kyawun gani hasalima mai ciki zaka iyayin ɓari ganin wannan muguwar hallitta.
Matar da naji na surutai sanda babu haske a ɗakin na sake kai dubana gareta tsohuwace amma ba can can ba, zata kai kimanin shekara 78 a duniya saidai a idanuwa kaɗaine zaka iya ganewa amma jikinta mai kyaune kamar ƴar shekara 40 a duniya. Sujjada naga tama wannan halittar, (wa'iyazubillah)..............................
*Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️*
***