🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾
Mallakar
KHADIJA WRITES
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)
⸻
💖 Dedicated To My Mom 💖
⸻
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
🅿️-----36
kowa ya watse ya rage saura Zeenah kadai a cikin dakin
cire mayafin jikin tayi dan gaba daya ya tukura mata bata saba saka manyan mayafai irin haka
ta karewa dakin kallo tsab taɓe baki tayi ta ce"not bad"
wayar ta,ta dauko ta kira yusrah dan tayi mata bayanin magungunan matan da ta sa ta karbo mata wata jaka ta bude ta fito dasu tili guda ta ware wanda zata yi amfani dasu a daren ta maida sauran jaka ta boye
suhail bai dawo gida ba sai wajen karfe tara na dare sai da ya biya ta resturant ya masu takeaway na abinci kafin ya koma gida
dakin Zeenah ya fara shiga kamshi sabulin da ya mamaye dakin da kuma karar ruwan da yaji a bathroom ya tabbatar masa da wanka
ajiye ledojin yayi akan gado ya nufi dakin Iman tana kwance kan gado tana chart da yaya Mubarak yana shigowa ta ajiye wayar
miƙa mata ledar yayi ta amsa ya zauna gefen gado
ya jima yana nazarin abinda zai ce mata
"Iman" ya kira sunanta
"kamar yadda sha'ira ta kawo zanyi kwanakin bakwai a dakin zeenah daga nan kuma sai kowa ce ta rinƙa girkin kwana bibiyu"
"kina ganin haka yayi"
"yayi"
ta faɗa ba tare da ko kallan saba a ranta kuma ta ce"idan ma zakayi kwanakin da yafi haka ban damu ba"
tana kallon sa ya fita yaja kofar dakin
Iman ta daɗe tana kallon ƙofar da ya bi Ba ta san dalilin da yasa zuciyarta ta yi nauyi Tun farko ai ta san zai yi kwana a ɗakin Zeenah Amma jin ya faɗa mata dai-dai yake da cin fuska a wajen ta
ta dauki wayar ta cigaba da abinda take labari yaya Mubarak yake bata akan sabuwar budurwa da yayi yau a wajen Aiki
yana tambayar ta yadda zai fara gaya mata yana sonta
dariya ta kwace mata
ganin ta jima bata masa reply ba yasa ya kira ta a waya ta "iman shine zaki ƙi maidomin da sako na"
har yanzu bata daina dariyar ba ta ce"yaya kawai dai nayi mamakin yadda ta sace zuciyar yayana cikin sauki haka"
"iman an faɗa miki nidin na wasa ne yanzu ki fada min me zance mata Har yanzu ban faɗa mata ba"
Iman ta ce "yaya mai kake jira"
"ina tsoron kar ta ce bata sona "
iman ta ce"haba yaya ai ba wata mace da zata fada mata kana son ta taƙi yarda kyakkyawan saurayi kamar ka but yaya duk kyanka baka kama ƙafar yaya suhail ya fika babban hanci kawai zaka gwada masa"
Mubarak ya ce"oho haka ma zaki ce to kije gaki ga Suhail din nan da gangan ma na kiraki neman Shawara da Hafsat ma na kira dan tafiki wayewa da Ƙwarewa a wannan fanin"
tasan sarai ramawa yayi katse wayar yayi
"lalle ma yaya shine ya katse min waya"
ajiye wayar tayi
ta dauko ledar takeaway din da suhail ya kawo mata fried rice with chicken sai salad plate ta dauko a Kitchen ta juye ta ci sossai dan rabon ta da abinci tun da safe
Suhail na fita dakin sa ya koma yayi wanka ya saka jallabiya ya koma dakin zeenah
Zaune take bakin gado tana gyara gashinta a gaban mirror Da jin ƙarar ƙofar ɗakin, ta miƙe da sauri ta gyara gashin kanta
Sanye take da wata sleeping dress ta net mai kyau da ta ƙara fito da kyawunta yayin da ƙamshin turarenta ya mamaye ɗakin
bakin gado ta zauna ta ce"babe sai yanzu"
"na shigo kina wanka"
ga abincin chan na kawo maki nasan kina jin yunwa
da kansan ya dauko plate ya juye masu abinci tana cin tana serving din sa abinda Iman bata taba yi masa ba kenan idan ta girka ta kawo masa shikenan
rabon da yaci abinci cikin kulawa irin haka bama zai iya tunawa ba
tana ci tana basa labarai masu dad'i bayan sun gama ya kwashe plate ya kai Kitchen
“A daren ranar Suhail ya kwana tare da Zeenah. Hakan ya sa ya yi tunanin cewa Zeenah mace ce mai kulawa"
kiran sallar Asuba ta farka dashi daga dogon bacci daya sauke sa dakin sa ya koma yayi wanka ya ya fita Masallaci har da gari ya soma wayewa kafin da yado
a Kitchen ya tarad da iman ta ɗora doguwar hijabi kan kayan baccin dake jikin tana ferar doya ,kamshin turaren Suhail kadai ya tabbatar mata yana wajen tsaye yayi yana kalon ya saka hannayen jikin Aljihu
"yaya Suhail ina kwana"
"lafiya qlau iman"
hannu ya ka zai taya ta aikin ta ce"a'a ya bar shi ta kusa kammalawa"
Ganin taƙi basa ta taya shi ya koma Dakin zeenah da mamaki ya ganta vkwance yadda ya barta sai bacci take a fusace ya kai mata duka a ƙafa
"zeenah zeenah"
jin kiran da yake mata yayi yawa ta fara buɗe ido a hankali
ranta a bace ganin yadda yake kiran sunan ta
sai da ta gama bude idanun ta ya ce"Zeenah bakiyi sallah ba har gari ya waye"
tsaki taja "Haba babe, saboda sallah kawai zaka tashe ni daga baccin"
"zeenah sallar ce kawai kin kalli rana kuwa"
Suhail ya yi shiru yana kallonta damuwa ya ratsa zuciyarsa Bai taɓa tunanin Zeenah tana da rauni a bangaren addini har haka ba
"kaga babe nifa kar karfe sha biyu nake kaiwa banyi sallah dan haka kawai ka rabu dani kawai nayi bacci na"
janye duvet din yayi ya ce"Wallahi baki isaba badai a gidana ba ,ki tashi ki yi sallah idan ba haka bazaki koma baccin nan ba"
ganin da gaske yake ta tashi ta sauko daga ka gadon tana ta jan tsaki alwala kawai tayi ta fito har zai tambaye ta ko tayi wanka tsarki amman ya kyaleta
bai kara shiga mamaki ba sainda yaga yadda tayi sallar cikin minti ɗaya ta kammala suhail ya kalle ta ya ce"Zeenah duk tsawon lokacin haka kike sallah zeenah wai ni kin ma yi karatun isilamiya kuwa"
gaba daya sallah nan batayi kama da wanda ya je isilamiya ba "
hawaye ya kawo a idanunta taji haushi Abinda Suhail yace
“I never expected this from you Kwana ɗaya kacal da aurenmu, ka fara daga min murya
"Zeenah ba daga maki murya nake ba but ya zama dole ki tsaya Addini yadda ya kamata"
tashi tayi ta dauki dauke Prayer mat din ta koma bakin gado ta zauna
suhail ya tashi ya fita koda ya fito yaga iman ta kammala gaba daya aikin ta jera kulolin abincin kan dinning
wanka yayi ya shirya kansa cikin wata farar gezner an mishi dinkin Captain
yana barin Dakin ta shiga wankavta shafe biye avwa wajen wanka wanda haka ya zame mata dabi'a duk sanda ta shiga wanka zaka rantse zata chanza fatar jikin tane
haka wajen kwaliyar ma ta bata wasu mintocin tayi hakan ne duk fsn ta birge suhail
atamfa ta saka staright gown duk ta kame mata jiki da kyar take kiya kwakwaran motsi tana tana tsaka da saurin dankwali Suhail ya shigo
bakin mirror din ya ƙasara yana kallon turo baki tayi babe"baka ke nayi kyau ba"
"zeenah kinyi kyau"
murmushi tayi ta ce"thank You babe"
suhail ya ce"ki fito muyi breakfast tun dazu iman ke jiran mu a dining"
ido ta zaro "god forbid, wanchan abar wallahi kaga kawai kaje kayi mana takeaway ni yunwa nake ji"
Suhail ya ce"kinsan wahalar da tasha wajen haɗa mana breakfast din chan kuwa"
"i don't care ni dai nace bazan ciba idan kaga bazaka iya sayomin Abinda zanci sai nayi order online thank god i have my own money da ba sai na jira wani ba"
ya rasa gaba daya Wannan dalilin chanjin zeenah gaba ɗaya ta chanza ba kamar zeenah da ya sani bayan bace sabbin rashin mutunci kullum take fitowa dasu wanda a baya bai santa dasu ba