Sawun Giwa

06

by @ammimalami99


~~~


A lokaci guda numfashinta ya katse a kirjinta lokacinda inuwar jikinsa ta mata rumfa a wajen daga kanta har kafafuwanta. El Yakoub ya dora hannunsa daya a kan jikin kan kujerarta yayinda dayan ya dorasa dai dai kan mouse dinta idanuwansa na bin screen din na'urar dan kallon aikin da takeyi a lokacin. Kamshin turarensa mai masifar kamshi ya bi ta hancinta yana nade kwakwalwarta gabaki daya. 


"Hello" 


Ta jiyo muryar Mu'azzam dinda ta sakata saurin sauke wayar daga kunnenta tana latsa duk wani button dinda ke jikin wayar wanda shi El Yakoub ma sam bai lura da hakan ba saboda yana tsaye ne ta gefen damanta yayinda wayar ke ta gefen hagunta. Ta cigaba da kallon screen din lokacin da yayi minimizing spreadsheet din da take hadawa ya shiga cikin emails dinta. Ya danno email dinsa dake sama gabaki daya kafin ya zaba wani file kwara daya yana bude sa. Zuciyar Aisha a lokacin tsabar yanda take rawar ganga a kirjinta ji take kamar ta kusa fallatsowa waje ne. 


File din yana budewa yayi scrolling kasa kafin ya kamo wani paragragh kwara daya yayi highlighting dinsa 


"Ki turawa Habeeb wannan paragragh din" 


Taushin muryarsa mai tasiri ga gangar jiki ta silalo daga bakinsa zuwa cikin kunnuwan Aisha da bata san sanda ta fara gyada kanta ba. 


"Kice masa nace akwai mistake a ciki ya duba da kyau ya turo mun asalin bayanin kayan" 


Ya karasa fada yana zagaye paragragh din da cursor din mouse din da take bi da ido kamar idan bata kalla da kyau ba bazata ji me yake fada ba. 


"Okay sir" ta furta da kyar kuma tun kafin ma ta rufe bakinta ya bace daga wajen ya nufi kofar office dinsa ya shige. 


Aisha ta sauke numfashin da batasan yaushe ta shake sa ba dan sai yanxu takejin kamar ta dawo office dinta dan dazu da yake kusa da ita sam ba duniyar data sani suke ciki ba . Tagan Mu'azzam yana sake kiranta sai kawai taji ta kasa dauka ta tura masa message cewar tanada aiki sosai. 

Tayi abunda ya umarceta kuma ba'a jima ba taga Habeeb din ya tura mata reply a yanda ta fahimta kamar an samu matsalar lissafin wasu carton din ceramic tiles ne na gini. Ta mike daga kan kujerarta tana gyara lullubin gyalenta kafin ta nufi office dinsa ta bude ta shiga. Yana zaune kan daya daga cikin kujerun dake tsakiyar office din kayakkinsa kan center table ya cire hular kansa tana ajiye can kan teburinsa.


Ta karaso garesa kuma har lokacin bai dago daga kallon iPad dinsa ba wadda yake rikeda pen dinta yana rubutu akai. 


"Sir" 


"Uhm" ya amsata


"Yace wai figures dinne ba daidai ba. Kuma yace 300 cartons ne ba 250 ba" 


Ya gyada kansa ahankali kafin yace "Kuma nawa ne total cost din 300 cartons din kenan?" 


"Around 5 point something million sir" 


Ta fada daga inda take tsaye tana kallon zanen rubutun da yakeyi jikin ipad din. Sai kawai ya dago ya kalleta, wani kallo da tsakaninta da Allah koh zasu wuni a nan ne su kwana bazata iya fassara ma'anarsa ba. Dan salon yadda ya dagon ma wani abun daure kai ne bare a kaiga tasirin kallon a kanta. 


"Exact amount din nakeso Aisha" 


Ya fada slowly, kamar idan bai fadi maganar ahankali ba bazata gane ba. 


Ta gyada kanta "Bari na dubo sir" 


Ta fice taje ta dubo ta dauki notepad dinda ke kan teburinta da pen ta ruboto dai dai adadin kudin dukda tana karantawa ta hadace amma bataso taje ya mata wani kallon da zai saka ma taji ta manta. Ta sake komawa ta karanto mai adadin kudin. 


"Zo" Muryarsa ta shiga kunenta bayan ta dago daga karanto mai adadin kudin dake rubuce akan notepad din da ke hannunta. 


Zuciyarta ta fara wannan abun. Wannan abun data lura a duk lokacinda yana waje sai ta jisa. 

El Yakoub ya dago ganin bata motsa daga inda take ba.


"Aisha" Ya kira sunanta yana nuna mata gefensa da pen dinda ke hannunsa. Sai kawai ta karaso din kuwa ta tsaya inda yake nuna mata kusa dashi a karo na biyu a wannan ranar. 


 "Idan 5.42 million zai siya mana carton dari uku, nawa ne carton daya kenan?" 


Ya aiko mata da tambayar yana rubuta adadin abubuwan da yake fada a jikin allon ipad din. Aisha bata samu damar amsa sa ba kuma Allah ya taimaketa yayi saurin amsa kansa dan koh lissafin bata fara ba duk kuwa da yanda ta kware a lissafi dan science tayi a makarantar sakandiri. 


"18.067k" ya furta yana rubuta adadin. 


Ta gyada kanta ahankali 


"Now, idan budget dinmu is 5million" muryarsa ta sake fitowa yana rubuta adadin. 


"Carton nawa zamu siya kenan?"


Shiru ya d'an wuce na sakanni kafin tace "Around 277 cartons sir" 


"Bingo" ya fada yana jinjina kansa cikin jin dadin amsar da ta basa ya rubuta adadin.


Ya juyo da kujerar zuwa saitinta wani abu da ya saka ba shiri ta dauke idanuwanta daga kan hannunsa dake rike da pen dinnan tana saukesu akan notepad dinta. 


"So, kice masa muna son carton 277 for a total cost of 5million naira" 


Ya gan sanda ta gyada kanta tana rubuta abunda ya fada a takardar data shigo da ita. Yayi shiru har zuwa sanda rubutun nata yazo karshe kafin ya cigaba


"Kuma ya gyara invoice din zuwa wannan sabon adadin sannan yayi confirming availability din kayan kafin lokacin tashi aiki sai ya turo miki copy din kuma ya turawa finance" 


Ya sake yin shiru har sanda ta karasa rubutunta ta dago ta kallesa tana jira taji idan akwai wani karin bayanin.


"Shikenan" ya fada yana kauce idanuwansa daga kanta ya juya kujerarsa ya cigaba da aikinsa. 


"Okay sir" ta basa amsa itama ta fice daga office din. 



~~


Kusan sati biyu suka wuce Aisha ta cigaba da aikinta kuma kullum sannu a hankali tana kara fahimtar aikin tana kuma iya kokarinta akansa dan koh daga yanda El Yakoub yake jinjina kansa duk lokacinda ta rubuto mai wani abun koh ta masa wani aikin tasan cewa bashida matsalar aiki da ita. El Yakoub din da har yanxu ba ta iya sakewa idan yana waje dan wannan kwarjinin da Allah ya zuba a halittarsa wani abu ne da ba kowa ne yake iya juresa ba har ya iya tunkararsa kai tsaye. 


Kullum zata shirya ne taje aiki bayan ta sauke Khausar makaranta. Tana zuwa zata sake review din schedule din El Yakoub kafin ta shiga office dinsa ta fada masa abubuwan da yake dasu ranar. Sha daya zata hada mai matcha dinsa da kuma fruit salad dinda ta lura yana tsananin sonsa barin mango. Daga nan kuma komai zai cigaba da tafiya ne akan wannan tsarin sai wasu karin ayyukan da takeyi da baza'a rasa ba dan tsabar typing din da takeyi hannayenta har sun saba yanxu ta kara kwarewa a computer. Inna data ganta lokacin tana shafa man zafi a hannun har tambayarta tayi wai halan aikin sakatarin rubutun na'ura kadai akeyi a cikinsa. 


Ita da Juwaira suka ringa dariya Inna na musu dakuwa kafin tayi mata bayanin ai ba abunda ba tayi dan har arranging meetings dinsa takeyi da kuma hada mai appointment da mutane daga kamfanoni da dama dake son ganinsa da dai sauransu. Inna ta jinjina kai jin aikin da yawa ashe shiyasa albashin yake da yawa. 

Matsalar kawai kwara daya ce, duk weekend yana turo mata wasu ayyukan da zata mai kafin Monday. Da farko ma Nurse Hadiza ce ta kirata tace tazo ta duba wayarta tagan an turo mata email dan har a lokacin bata gogesa daga wayarta ba. Taje ta duba ashe El Yakoub ya bata wani aiki da zata yi ne wanda ta rasa ya zatayi sa tunda ita ba na'urar nan gareta ba a gida sannan ba babbar waya ba bare tace zatayi amfani da ita tayi managing dan aikin nan dole sai a computer koh laptop zata iya yinsa da kyau batareda yaci lokaci ba. 


Ta rasa yanda zatayi kuma sosai ta shiga damuwar rashin samun damar yin aikin wanda sai da Inna ta fara masifar meye na dora wa kanta damuwa tunda dai batada shi suma suyi mata uzuri mana idan taje ba sai tayi bayani ba. Nurse Hadiza ce ta bata shawaran zuwa da sassafe ranar Monday ta fara aikin kafin yazo office din kuma hakan tayi. Karfe bakwai tayi mata a office din wanda kusan a lokaci daya suka zo da El Yakoub kuma yayi mamaki sosai da ganinta har sai da ta hango wannan mamakin a fuskarsa amma sai dai bai tambayeta dalilin zuwan nata da wuri ba kuma Allah ya taimaketa bai tambayeta aikin da ya bata ba sai bayan ta gama din. 

Hakan ta sakeyi wani satin tana jaddaddawa kanta dole ta siya babbar waya idan an bata albashi karshen wata ko da ita ai zata rage aikin kafin ta samu kuma ta siya laptop din dan bataso koh kadan wani abu da zai janyo mata matsalar da zata rasa aikin nan Allah ya gani. Duk kuwa da yanda aiki da El Yakoub ke zuwa da wani irin nauyin da bata san ainahin dalilinsa ba. Abunda kuma kawai ta fadawa kanta shine kwarjinin da Allah ya zuba masa ne da wani irin girma dayake dashi a idon duk wanda ya kallesa ya saka take jin duk wani abu da takeji idan suna wuri daya. 


Allah yagani waccan jumu'ar da tazo data gansa a cikin manyan kayan nan da suka sake fito da kyawunsa sai ta samu kanta da kirga kwanakin da suka biyo baya har izuwa wata jumu'ar din batareda tasan ma tayi ba. 

Dukda yanda suit din ke bala'in masa kyau manyan kayan kawai sun fita daban. Dan shekarunsa da suit din ke boyewa manyan kayan ne ke fito dasu, kuma ba wai shekarun kadai bane ita ta sani, kawai yanda suke kara masa wani irin natsattsen girma da cikakkiyar kamala irin wadda kuka san kayan Hausa na karawa kowane mutum saidai shi nashi ya fita daban dan kwarjinin da mutumin nan ke dashi wani abu ne da bata taba gani ba a tattare da kowa. 


Ga kuma wani irin kyawu dake zagaye da fuskarsa da ma kirarsa gabaki daya dan yadda y'an matan kamfanin nan ke kai mai harin kallo duk idan suka sauka wani aiki ita abun ma baya bata mamaki dan ya kai dinne kawai yanda wasu ke zuwa suna tambayarta idan dagaske itace secretarynsa ne abun ke takurata. Wani sa'in ma idan ta fito zata wuce gida koh idan ta shigo kamfanin tana lure da yanda wasu ke binta da kallon banza shiyasa har yau ba abunda ya taba hadata da kowa a ofishin bayan Ayo itama kuma dan suna aiki tare ne sai kuma Ameer secretary din Habeeb da yake yawan zuwa office dinta idan Habeeb ya aikosa da wasu takardun. 


~


Yau ta kama asabar ita da Juwaira da Khausar wadda ta saka rigimar dole sai ta bisu sun fita zuwa gidan wata kawar Juwairan da ta haihu sun je bikin barkar can cikin gari. Kuma a wajen bikin nan ne ta hadu da kanwar wadda ta haihun wadda itama kawarta ce dan dama duk Islamiyya daya sukayi. Sun dade basu hadu ba saboda yarinyar Lagos suka koma bayan anyi bikin auren yayarta shiyasa suka baje a parlon yayar Husnar suna hirar yaushe gamo kuma a hirar ne take fadawa Aisha ai an kusa bikinta har ta bata katin bikin dan ashe wai sun dawo daga Lagos bikin sunan ne da kuma nata bikin aure. 


Dama Inna sai da ta jaddada musu ana la'asar su juyo shiyasa suna yin la'asar din kuwa suka fito daga gidan Khausar na rike da ledar souvenir din bikin da aka basu har guda biyu zasu taka zuwa bakin titi su tara abin hawa. 

Juwaira sai santin anguwar takeyi saboda rashin hayaniyarta ga kuma gidajen da aka jera a anguwar cikin tsari abin sha'awa kai da gani kasan duk wanda ke zama anguwar ya d'an tara wani abin. Kuma suna tsaye ne lokacinda Juwaira ke tsokanar Aisha kan baza tace Mu'azzam ya gina musu gida a anguwar ba lokacinda wata dalleliyar bakar motar da ta fito daga anguwar zata hau titin ta tsaya a gefensu. 


~~


Yau ta kama asabar ne ranar hutu ga kowane ma'aikaci da magidanci har ma da yara dake zuwa makaranta. El Yakoub yana tsaye a harabar gidansa jingine da motarsa yana magana da wani magidanci dake nan makotansu yayinda gate din gidansa ke a bude wasu matasa guda biyu suna shigo da glass din windown da zasu chanja mai. Jiya ne ya dawo daga aiki yaga windown parlonsa a fashe ashe yaran makota ne dake buga ball suka bugota cikin gidansa ta fasa mai windon dan koh da ya dawo can ya hango ball din ta gangara gefen flowers dinda aka jera a wajen yasan watakila yaran sun bubbuga mai gate ba'a amsa ba suka hakura. 


Yau dinma bai fito da wuri ba sai azahar dan wani bacci yayi da safen nan bayan sallahr asuba da ya dade rabonsa da irinsa dan koh da ya tashi haka yaji sa sakwai duk wannan tarin gajiyar da ya kwasa ta aikin satin nan ta kau daga jikinsa shiyasa bayan ya dawo daga sallahr azahar ya shiga kitchen ya dafa abinci mai rai da lafiya ya zauna yaci abincinsa yana ci kuma yana sauraren dogayen voice notes dinda Mahmoud ya tura masa akan ayyukan da sukeyi a kamfaninsa dake chan Abuja wanda ragamar aikin ya barosa a hannun Mahmoud dinne yana turo masa duk bayanai ta waya shikuma zai yanke hukunci Mahmoud din ya aiwatar. 

Yana gama cin abincin ya kai plate din kitchen ya wankosa kafin ya tattaro abubuwan aikin nasa ya fara kuma ba shi ya tashi daga wajen ba sai dab da la'asar lokacinda yaron dake masa gyaran gida da aike mai suna Magaji ya shigo da yaran da yace Habeeb ya turo masa su chanja mai windownsa. 


Yaje masallaci yayi sallahr la'asar kuma ya dawo kenan ya baiwa Magaji makullin akan ya rufe mai idan yaran sun gama saka windown zai fita ne sai ga mahaifin yaran nan da suka fasa mai windown yazo basa hakuri tareda yaransa maza su biyu yaya da kanensa. Suka gaisa sosai dan dama basu taba haduwa ba dan mutumin wai ashe yayi tafiya ne. Yace yaran su basa hakuri El Yakoub ya shafa kansu yana ce musu ba komai su je su dakko ball dinsu dan Allah ya zuba masa son y'aya a zuciyarsa kuma wata kila dan an rabasa da nasa d'an ne duk inda yaga yaro sai yaji ya shiga ransa sosai. 


Saida suka tafi tukunna shima ya shiga motarsa ya fice daga gidan kuma har ya iso bakin titi lokacinda idanuwansa suka dakko masa fuskar Aisha. Aisha dai Aishar da ya sani tana sanye cikin wani lace dinkin riga da skirt mai ratsin ja da ya karbeta sosai yayi mata kyau ta yafa gyale ja saman kanta, wannan gyalen da ya ganta dashi a office dinsa. Tana tsaye tareda wata da kuma wata yarinya wadda bazata wuci kanwarta ce ba. Ya tsayar da motarsa batareda yayi shawara da kansa ba kafin ya sauke glass din gefen su idanuwansu suka hade cikin na juna daga inda take tsaye. Kuma bayan yaga asalin launin jan ne saboda motarsa nada tint ya saka ya yanke a ransa nan take cewa babu kalar datafi kowacce kyau a jikinta sai jar. Yaga sanda mamaki ya cika idanuwanta kafin ta yafa murmushi samansa, wani d'an karamin murmushi da ya karawa fuskarta kyau kafin tace 


"Sir Ina wuni"


Kuma wannan karamin murmushin nata ne ya saka nasa karamin murmushin hawa labbansa.


"Lafiya lau" 


Juwaira da Khausar kuma jin Aisha ta kiraye sa da Sir ne ya saka suma suka gaishe san ya amsa su. 


"Ina zakuje" Ya tambaya. 


"Gida zamuje sir" Ta bashi amsar tambayar tana riko gefen gyalenta wani abu da ya dauki hankalinsa har ya kalli wajen data rike kafin yace 


"Okay, kuzo na saukeku"


"A'a sir ba komai yanxu zamu samu abin hawa ai". 


Ta karasa tana daga hannun nan ta nuna masa hanya gefen jan gyalen nan da ta rike yana zamewa daga yatsunta. 


"I insist" ya sake fada yana kallonta. 

Sai kawai ta kalli Juwaira dake gefenta mamakin da take dannewa yana kokarin fallatsa kansa dan tun lokacinda El Yakoub ya zuge glass dinnan taga fuskarsa ta tsure dan tsakani da Allah ita bata taba ganin mutum mai zubin kwarjini, kyawu da kuma kamala kamarsa ba kuma lokacinda Aisha ta kirasa da Sir ne ta fahimci ta sansa kuma bazai wuce a wajen aiki ba. Juwaira ta d'an gyada mata kai kafin Aishar ta juyo tana ce masa 


"Okay toh shikenan sir, mun gode sosai". 


Ya kai hannunsa yana danna maballin bude motar. Juwaira da Khausar suka bude bayan motar suka shiga lokacinda itama ta bude gaban ta shiga kamshin mayen turarensa mai ratsa jiki yana gaishesu tareda sanyin A.Cn da ya kunna.Ya juya kan sitiyarin motar suna hawa kan titin nan kuma sai a lokacin ya lura ashe ta yafa wata karamar jaka a gefenta dazu da bai gani ba yanxu data shigo motar kuma ta dorata akan cinyarta. Kuma yanda ta nade yatsun ta akan hanun jakar kawai idanuwansa suka dakko masa abun ya masa kyau batareda yasan dalilin hakan ba. Ya maida kansa kan titin suka cigaba da tafiya shiru ahankali har zuwa sanda ya tambayeta ina ne gidan nasu ta fada masa. 


Suna tafiya kuwa ringing din wayarta ya fito daga cikin jakarta. Ta zuge zip din jakar ta fito da karamar wayarta kafin ta dauka tana dorawa a kunne. 


"Wa'alaikumus salaam"


Y'ar muryarta ta cika motar. Shiru kad'an kafin ta kara cewa 


"Inna muna hanya". Shiru ya koma ratsa motar 


"Ameen Inna" kafin ta sauke wayar ta maida cikin jaka tana sauke d'an karamin numfashi dan Allah yagani sai da tattaro dukkan wata natsuwa tata ta yabawa kanta kafin ta shigo motar nan. Tayi mamakin ganinsa a wajen, toh kenan shima gidansa na cikin anguwar da suka baro koh tunda ta hanyar ya fito. Ta juya kanta tana kallon waje inda suke wuce mashina da keke da wasu motocin ma da take ganinsu kasa kasa dan motar tasa babba ce kafin ta juyo lokacinda taga gudun motar yana ragewa taga ya karya sitiyarin ya shiga cikin wata babbar supermarket da aka bude kwanan nan dan ranar Nana har dawowa tayi da katuwar ledar wajen wai wani saurayinta ya kaita shopping. 


Sai da yayi parking motar tukunna ya kalli Khausar ta rearview din motar dan tana zaune a tsakiya ne gefen Juwaira dake zaune bayan kujerar Aisha. Sai ya sake juyowa ya kalli Aisha wacca daidai itama ta juyo ta kallesa ne itama.


"Ya sunanta" Ya tambaya


"Na'am" Ta tambaya itama dan bata gane wa yake nufi ba. 


"Kanwarki Aisha, ya sunanta?"


"Khausar" ta fada ahankali. 


"Zo ki rakani Khausar" ya fada bayan ya juya ya kalli Khausar ta rearview din. 


Yaga sanda Khausar ta juya ta kalli Juwaira da itama ita take kallo kafin ta kallo Aisha dukda ba kallonta takeyi ba dan ta sauke idanuwanta kasa kan jakar nan dake ajiye a kafarta. Sai ya bude murfin motar ya fita kuma sakanni uku kafin Khausar din ta bude murfin motar tana fitowa. Ya mata murmushi bayan ta fito kafin su fara takawa cikin wajen. Juwaira tayi saurin tabo Aisha ta gefen ta 


"Aisha waye wannan?"


"Boss dina ne shine mai kamfanin da nake aiki" Aisha ta fada bayan ta juyo gareta. 


Juwaira ta jinjina kai. 


A ciki kuwa suna shiga yacewa Khausar ta dauki duk abunda takeso. Yaga sanda idanuwanta suka haska da wani abu kamar walkiya na excitement kafin kuma yaga ta girgiza kanta tace 


"A'a nagode" 


Sai yayi murmushi kawai kafin yace ta biyosa. Ya dauki abubuwan bukatarsa kafin ya zaga wajen kayan kwalama. Duk abunda ya dakko kuwa sai ya nuna mata ya tambayeta idan tana so. Wani abin ma sakawa kawai yakeyi. Ba inda kuma yaga idanuwan Khausar sun haska da farin ciki harda guzurin murmushin da ya tuna masa da fuskar Aisha irin sanda suka nufi wajen freezer nan ya bude yana dauko robar ice cream. Sai kawai ya sake dauko wasu manyan robobin idanuwan Khausar na sake kara girma da hakan. 

Suka je wajen Cashier ya bada katinsa aka debi kudin kafin suka fito wani mai aikin wajen yana biyo su da ledar. Ya bude booth mutumin ya saka ledojin yana mai godiya kafin ya shige motar. Dama Khausar tuni ta shiga motar tana washewa Juwaira hakwaranta dan Allah ya gani ba karamin biyanta El Yakoub yayi ba saboda a duniya tana kaunar ice cream. Ya tada motar suka fice daga harabar wajen sanda wayarsa ta dauki karar shigowar kira. 


Ya kai hannunsa ya dauki wayar daga cikin console dinda ya ajiyeta yayi picking dan Habeeb ne ke kiran nasa. Muryarsa mai taushi ta cika motar sanda yake wayar da Habeeb dinda yake gayawa yana hanya. Kuma alokacinda suke wayar da Habeeb ne 

ya tuna da aikin da ya tura mata tayi mai dazun nan wanda zata mai submitting dinsu Monday. Yana sauke wayar kuwa yayi mata maganar 


"Kin duba emails din da na tura miki?"


Ya aikowa Aisha tambayar da batayi tsammaninta ba kuma tasan bazai wuci emals din aikin da zata mai ba da yake tura mata duk weekend. Kuma Allah yagani tsoron cewa eh takeyi kada ya tambayeta wani abu akansu da bazata iya basa amsa ba sai kawai tace 


"A'a ban duba ba"


Sai kawai kuma taji yayi shiru bai ce komai ba. Itama kuma tayi shirun batace komai ba har sanda suka iso anguwarsu. Ta juyo ta kallesa kafin ta daga hannunta tana nuna masa hanyar da zai bi.