FARASHIN IZZAH

31

by @hauwajaywrites

Watanni suka shuɗe...

A hankali rayuwa ta fara dawowa Zahra yadda take a da. Ta gama iddarta lafiya.


Ta ci gaba da karatunta ba tare da wata matsala ba, yanzu ma kusan komai ya ƙare


External defense kaɗai ya rage mata, idan ta gama shi kuwa sai jiran sakamako.


Daga department ta fito, a hankali take tafiya, handbag ɗinta riƙe a hannu, gaba ɗaya a gajiye take


Tun safe take zirga-zirga tsakanin offices da supervisors, da ƙyar ta sauko matattakalar department ɗin.


A dai-dai lokacin wayarta sabuwa da Abbah ya siya mata ta yi ƙara, alamar shigowar sako, ta ciro ta daga jaka


Da farko ta yi tunanin wani ne daga classmates ɗinta, amma da ta duba sai ta ga alert ne na 1,500,000. Duba Wanda ya turo kudin tayi taga daga Abbah.


Murmushi ya suɓuce mata, ta girgiza kai.


"Wato saboda jiya na gama iddah kenan, Kai Abbah" Ta faɗa a hankali.


Ta san halin Abbah, duk lokacin da ya ji daɗin tayi wani abu mai kyau , sai ya nemo wata hanya da zai faranta mata rai. Ta saka wayar cikin jaka sannan ta ci gaba da tafiya.


Da ta isa parking lot, ta nufi wajen motarta sabuwa. Wadda Abbah ya canza mata bayan komai ya lafa


Ta shiga, tare da kunna shi

Ba tare da ta jira wasu ƙawayenta ba, dan gajiya ya mata yawa a jiki, gida take son ta koma ta huta.


A hanya kuwa wani Kira'a ne ke tashi a hankali. Ita kuma tana driving cikin nutsuwa


Karon farko cikin watanni da suka wuce, tana jin salama sosai a zuciyarta.


Da ta isa gida. Mai gadi ya buɗe mata gate ta shiga da motar, ta yi parking, sannan ta fito


Jakar hannunta a kafaɗa, kai tsaye parlorn ƙasa ta nufa

Tana shiga ta hango Mummy zaune

Batoul na gefenta.


"Assalamu alaikum." Ta faɗa.


Mummy ta amsa.

"Wa alaikumussalam."


Sai ta kalleta

"Ashe jiya kika gama iddah?"


Zahra ta yi murmushi.

"Eh Mummy."


Mummy ta gyada kai.

"Toh yayi."


Sai ta ɗan gyara zamanta.

"Yanzu kuma saura wani mijin ya fito."


Zahra ta yi shiru tana saurararta.


Mummy ta ci gaba.

"Amma Fatima ki tsaya ki yi zaɓe, kar ki sake aure ace ko wata biyu ba zaki cika ba a sake sako-ki, kinga yanzu ke yarinya ce, Karamar bazawara za a fara kiranki"


Zahra ta yi wani ɗan murmushi.


"Na sani mana Mummy." Ta ce.


"Amma ai kowa akan ƙaddararsa yake tafiya ba wanda ya isa ya tsallake abin da Allah ya rubuta masa."


Mummy ta gyada kai.

"Eh! Haka ne."


Sai Batoul ta yi wata yar dariya.


"Iyeee! Yau ke ce da wa'azi?" Ta faɗa tana kallon Zahra.


"Ina anan saboda za ki rigani aure kike yin abin da kika ga dama, Har a family ban tsira ba, ana cewa kanwata ta rigani aure. Yanzu kuma me amfanin auren wata biyu wanda ko cika bai yi ba?"


Nan take murmushin Zahra ya ɗan ɓace.


Ta kalleta.


"Whatever, Batoul" Ta faɗa a nutse


"Haka Allah ya ƙaddara min. Sannan ke ma ba ki fi ƙarfin haka ba. Mind you..... Kullum kina gaya min magana. Ina ɗauke kai ne kawai."


Nan take Mummy ta zaro ido tana kallonta da mamaki, kamar ba ita ba


Batoul ta miƙe tsaye.


"What?!" Ta faɗa.


"Batoul zaki kirani?"


Zahra ta ɗan ɗaga gira.


"Dama kin riƙe girman ne? Ai idan ba ki sani ba, yanzu na girme ki a yanayin rayuwa. Ask everyone saboda da kanki kin fada nayi aure kinga ko anan ai na dara miki"


Batoul ta matso kusa da ita

"Wallahi zan fasa bakin ki yar iska, shegiya!"


Zahra kuwa dariya kawai ta yi

"Dadin abin kin san ubana balle ki kirani da shegiya, sannan kuma gani a gabanki, ki fasa, wallahi kina taba ni zan Rama"


Batoul ta tsaya cak, ta kasa magana na wasu daƙiƙu. Domin ba ta taɓa jin Zahra ta mayar mata da magana haka ba.


Zahra kuwa ta juya tana dariya ta nufi staircase.


Mami da ke saukowa daga sama ta haɗu da ita.


"Zahra." Ta kira.


Zahra ta tsaya.


"Na'am Mami."


"Meyasa zaki biye musu?" Mami ta tambaya.


Zahra ta saki murmushi.

"Mami ki ƙyale su. Kullum sai sun gasa min bakar magana. Ina kyale su. Kuma Abbah yace Duk Wanda ya gaya min magana Akan aure na yana baya na dari bisa dari na mayar musu da bakar magana, hakan ne kawai zai sa su rabu da ni"


Mami ta girgiza kai tana murmushi. Ta lura Zahra ta canza fiye da yadda take tunani, ko kadan mutuwar aurenta bai dameta ba kuma ta cire damuwar komai dan har wani haske da kiba ta kara 


"Toh je ki cire kayan nan, ki watsa ruwa, sannan ki zo ki ci abinci"


Zahra ta gyada kai.


"Toh Mami."


Daga haka ta juya, ta wuce zuwa ɗakinta


Yayin da Mami ke kallonta tana murmushi a hankali.


A zuciyarta kuwa tana gode wa Allah.

Domin duk da abin da Zahra ta fuskanta... Ta sake tashi tsaye.


Mama na zaune a parlorn tayi tagumi, idanunta na kan Ibrahim da ke zaune a gabanta yana danna wayarsa ba tare da wani kuzari ba.


Tun bayan rabuwarsa da Zahra abubuwa suka sauya masa.


Mutanen da a da suke yabonsa a media kuma suke masoyansa, sun juya suna sukarsa. Followers ɗinsa sun ragu sosai.

Deals da yake samu ma sun fara raguwa.


Mama ta girgiza kai.


"Ai Ibrahim kai ne ka lalata komai."


Ya ɗago ya kalleta.


"Mama kamar ya kuma?"


Ta ɗan matso gaba.


"Baka iya buga wasan bane. Ni mace ce amma wallahi har na fi ka iya yadda zaka buga"


Ibrahim ya saki ajiyar zuciya.


"Haba Mama. Da na yi yadda kike so ma ai da yanzu wani maganar ake yi ba wannan ba."


Mama ta miƙe tsaye.


"Toh shikenan. Source of income ɗin ya kare ai kenan."


Ibrahim ya yi murmushi.


"Ba komai. Zan koma, zaki kuma sha mamaki"


Mama ta tsaya tana kallonsa sai kuma ta girgiza kai.


"Ai bana jin hakan me yuwa ne, kana tunanin ita ɗin da ka sani ce har yanzu?"


Shiru ya yi.


Mama ta juya ta wuce, ta bar shi da tunaninsa.


A ɓangaren Zahra kuwa... Weekend ne yau 


Ita da Ya Umar suna zaune a parlon sama suna hira


Ya Umar na ta ba ta labarin wani abin dariya da ya faru an office. Har dariya take yi tana rike cikinta


Can sai ya kalleta.


"By the way." 


Ta ɗago kai "Na'am?"


Yace,

"Yaushe kika fita solo date na ƙarshe?"


Ta yi dariya.

"Solo date kuma?"


"Eh mana. Kawai ki fita ki yi shopping, ki ci abin da kike so, ki more rayuwarki."


Ta ɗan yi tunani

"Gaskiya na daɗe."


Ya Umar ya ciro wayarsa.


"Good." Ya ce, sai kuma ya danyi danne danne 


Wayarta ta yi ƙara, ta buɗe, ta bude ido sosai tana kallon alert din

500,000


Ta ɗaga kai tana kallonsa "Yaya!"


Yana dariya yace,

"Go and enjoy yourself, ki tabbatar kin kashe dukka wannan umarni ne."


Murmushi ya cika fuskarta, ta tashi da sauri ta rungume shi


"Thank you Yaya naaa!"


Ya Umar ya yi dariya.

"Get lost."


Washegari da safe

Tun da wuri Zahra ta fara shiryawa


Bayan ta yi wanka

Ta shafa body mist mai sanyin ƙamshi, ta ɗauki wani elegant wine-colored abaya mai sauƙin ƙyalli, veil dinsa tayi rolling

Wani ƙaramin gold wristwatch a hannunta, da matching handbag.


Babu wani make-up mai yawa

Sai light gloss da powder kaɗan.


Amma kyau... Kamar an fito da ita daga magazine, ta koma ainahin Famous Zahratyyn ta


Da ta sauko ƙasa.

Mami har sai da ta tsaya tana kallonta


"Masha Allah Zahra" Ta faɗa.


Zahra ta yi dariya.