ƘWAI BIYU

Chapter Twenty Four

by @thehealerspen654

Da gudu ta isa cikin bedroom ɗinta, cikin sauri ta fara dube-dube. Cike da zafin nama ta ɗakko abun gwajin ciki ta shiga banɗaki domin ta gwada fitsarinta.


Wasu zafafan hawaye ne suka fara gangarowa daga idonta, a daidai lokacin da abun gwajin ya tabbatar mata da cewar tana ɗauke da juna biyu.


Waje ta nema a banɗakin ta zauna daɓar, ta fara rusa kukan da ita kanta bata san dalilin zuwan sa ba a wannan lokacin. Amma tafi alaƙanta shi da kukan farinciki.


A hankali ta miƙe tayi wanka zuciyarta fal da farinciki, da kuma raɗaɗin ƙalubalen da zasu fuskanta a nan gaba ita da ɗan da yake cikinta. 


Duk da tana tantama a zuciyarta, amma ta tabbatarwa da kanta cewar, wannan magwajin cikin bai cika yin ƙarya ba.


Hakan ya saka ta fara shiryawa a gaggauce, sannan ta nufi ɓangaren Sultan.


A kwance ta tarar dashi kamar yadda ta barshi yana bacci. Wasu sababbin hawayen ne suka sake gangaro mata, saboda ta fara tunanin ko yaya Sultan zai ji idan hakan ya tabbata?


Matsawa tayi dab dashi ta fara taɓa shi a hankali:


"Sultan..."


Firgit ya farka, tare da motsawa, idonsa a rufe sannan yace:


"Ya akayi?" Acikin sigar bacci.


Sunkuyar da kanta tayi, saboda wata matsananciyar kunya da ta baibayeta ta fara wasa da abun gwajin da yake hannunta.


Jin shurun da tayi ne ya tilasta masa buɗe idonsa. Yadda yaga yanayinta ya saka ya miƙe zaune, musamman yadda yaga hawaye suna bin kuncinta.


"Why are you crying?"


Ɗagowa tayi ta kalle shi ta sake sunkuyar da kanta, sannan tace:


"Amai ne ya tashe ni daga bacci...shine nayi gwajin ciki...amma ya nuna min kamar akwai...mu tafi asibiti. Please!"


Da sauri ya ƙarɓi magwajin da yake hannunta tare da ƙare masa kallo. Sam bai fahimci komai ba. Hakan ya saka cikin zafin nama ya ɗakko wayarsa ya kira Dr. Cara yace mata ga su nan zasu zo asibiti.


Miƙewa yayi da sauri ya shiga banɗaki yayi brush, bai iya tsayawa yayi wanka ba ya zira jallabiya kawai. 


Sannan ya kama hannunta suka nufi wajen ajiye motoci.


A hanya suna tafe zuciyoyinsu banda bugawa da son samun tabbaci babu abinda suke yi. A zahiri Radiya tafi kowa damuwa da son samun tabbaci, amma a baɗini...Sultan shine sarki a fagen.


Duk da ranar Lahadi ce bai hana Dr. Cara fitowa ba, duk da bata san ainahin me yake faruwa ba, amma ta tabbatar da cewar al'amari ne mai mahimmanci.


Suna isa office ɗinta Sultan ya nuna mata magwajin cikin, da sauri ta karɓa fuskarta cike da mamaki, sannan ta kama hannun Radiya suka nufi ɗakin gwaje-gwaje.


Shigar su ke da wuya Sultan ya gaza samun nutsuwa, sai kai kawo yake yi. Wayarsa ya zaro ya fara kiran layin Sauban, saboda ya sani sarai shine kaɗai wanda zai samar masa da nutsuwa a halin yanzu.


Bayan kammala ɗaukar jinin Radiya Dr Cara ta kwantar da ita a wani gado domin ta huta, saboda ta lura da yadda yanayinta ya sauya sosai.


Ba sai an faɗa ba, tabbas alamu sun nuna Radiya tana da juna biyu, amma don ta sake tabbatarwa suka bi hanyar gwajin jini, wanda shine kankat.


Allurai ta fara yi mata, tare da saka mata ƙaramin ruwa domin ta samu kuzari sosai a jikinta. Sannan ta miƙe ta sake komawa ɗakin gwajin.


Da hanzari ta fito ta nufi ɗakin da Radiya take, ta zauna a gefen gadon, sannan ta kalle ta cike da tsananin farinciki tace:


"Finally...congratulations!"


Tare da rungume ta.


Wata sanyayyiyar ajiyar zuciya Radiya tayi, wannan karon kuwa farinciki da murna ne suka mamaye fuskarta tare da annushuwa. Sannan taji wani babban nauyi ya sauka daga ƙirjinta. 


Cike da farin ciki ta kalli Dr Cara tace:


"For how many weeks?"


"Nine."


Abinda Dr. Cara ta furta kenan tare da ficewa cikin gaggawa daga ɗakin, ta bar Radiya tana dariya tare da ɗora hannunta a ƙasan mararta ta furta:


"Hello little."


Da gudu-gudu ta nufo in da Sultan da Sauban suke a tsaye, da sauri Sauban ya nufo in da take. Ganin yanayin annurin da yake fuskarta da kuma takardu a hannun ta ya saka Sauban yace:


"Alhamdulillah ya rabbi."


Sannan gabaɗayansu suka zube ƙasa sukayi sujjada ga sarki Azza Wajallah.


Murmushi kawai Dr. Cara tabi su dashi musamman a daidai lokacin da suka rungume junansu suna kukan farin ciki. Ita kanta sai da tayi hawayen murna sannan ta miƙa musu sakamakon ta basu waje su sarara.


Waje suka nema suka zauna, suka yi shuru kowa yana saƙe-saƙe acikin ransa, suna tuna irin gwagwarmayar da suka sha da wahalhalu domin samun wannan cikin.


Sauban ne ya juya ya kalli Sultan yace:


"Just like dream."


Jinjina kansa kawai Sultan yayi a daidai lokacin da yake ƙoƙarin goge wasu siraran hawaye da suka zubo masa, sannan ya miƙe ba tare da yace komai ba ya nufi ɗakin da Radiya take kwance, Sauban yabi bayansa.


A kwance suka tarar da ita hannunta ɗaure da ƙarin ruwa tana bacci, sakamakon alluran da akayi mata domin ta huta.


A sanyaye ya ƙaraso gefen gadon, ya zauna tare da ƙarewa fuskarta kallo, sai yanzu yaga alamar canji a tare da ita, saboda ya lura tayi haske sosai. 


Wani ƙayataccen murmushi ya saki. Sannan ya miƙe ya koma in da Sauban yake tsaye, ya kalli Radiya yace:


"Radiya rigima."


Dariya suka saka gabaɗayansu, sannan suka fice.


A hanya suka haɗu da Dr. Cara sai murmushi take musu ta kalle su tare da sake yi musu murna. 


Sannan suka tambaye ta nan da yaushe Radiya zata iya tashi, tace musu nan da awa ɗaya zuwa biyu.


Jinjina kansu suka yi, sannan suka nufi wajen parking cike da annushuwa domin su je gida su sanarwa da Ammey.


A zaune suka iske ta ta idar da sallar walha, tana lazimi. 


Suna dab da ƙarasawa Sauban ya tsaya cak. Da sauri Sultan ya juyo ya kalle shi. Da mamakinsa sai yaga Sauban yayi masa alama da ido akan ya shiga shi kaɗai.


Nan fa kunya ta kama Sultan, amma a hakan ya daure ya ƙarasa.


Durƙushewa yayi kusa da ita, sai da ya jira ta kammala addu'o'inta, sannan ta juyo ta kalle shi. 


Yanayin da taga fuskarsa ya saka cikin damuwa ta mayar da hankalinta kan Sauban da yake gefe fuskarta cike da alamar tambaya.


Saboda ta tabbatarwa da kanta cewar, tabbas akwai wani babban al'amarin da yake faruwa.


"Me ya faru?"


Abinda ta furta kenan tana kallon Sauban, ba tare da ta amsa gaisuwar da Sultan yayi mata ba.


Shurun da Sauban yayi ya saka ta mayar da hankalinta kan Sultan da yake durƙushe a gabanta, tare da sake maimaita masa tambayar.


Sunkuyar da kansa yayi ƙasa hawaye suka fara gangarowa a fuskarsa sannan yace:


"Radiya ce..."


"Me ya same ta?"


Ta katse shi cike da tashin hankali.


"Tana da...juna biyu."


Zumbur tayi ta miƙe tsaye, tare da rufe bakinta da hannu biyu alamar matsanancin mamaki.


A daidai lokacin Sauban ya ƙaraso ya kamata ya zaunar da ita a gefen gado.


Wasu hawayen farinciki ne itama suka fara zarya a kuncinta tare da dara ambaton: "Alhamdulillah ya Rabbi."


Gabaɗayansu kukan suka ci gaba da yi, musamman Sultan da har yanzu yake a durƙushe kansa a sunkuye. 


Hannunta ta saka ta jawo Sauban jikinta ta fara shafa kansa tana sake maimaita: "Alhamdulillah!"


A hankali shima Sultan ya miƙe ya zauna kusa da ita, shima ta rungume shi cike da farin ciki.


Haka suka kasance na tsawon lokaci a jikinta kamar yadda ta saba, ajiyar zuciya kawai take yi, saboda ita kaɗai tasan farincikin da take shiga a duk lokacin da ta haɗa waɗannan duniyoyin nata guda biyu a jikinta.


Sannan daɗindaɗawa, ga wannan babban abun farin cikin.


Sultan ne ya fara miƙewa yayi musu sallama, sannan ya nufi asibiti wajen Radiya saboda ya tabbatar da ta kusa farkawa.


Fitar sa ke da wuya suka sake buɗe wani sabon shafin kukan ita da Sauban. Sannan daga bisani ta miƙe ta fita, tare da fara shirye-shiryen kyaututtuka na nuna godiyarta ga Ubangiji.


Ranar ma'aikatan gidan, da mabuƙata sun sha goma ta arziƙi.


Haka shima Sultan, kai tsaye gidan marayunsa ya fara nufa, ya dinga wadaƙa da dukiya, ba ga yaran ba, ba ga ma'aikatan ba, kai duk wanda ya haɗu dashi a wannan rana sai da yayi katarin arziƙi.


Sannan daga bisani, ya nufi asibitin.


Yana shiga ya iske ta farka, wata nurse tana ƙoƙarin cire mata ruwan da yake hannunta. 


A sanyaye ya ƙarasa in da take, kallo ɗaya tayi masa ta sunkuyar da kanta saboda wata matsananciyar kunyarsa da take ji, gashi ya ƙura mata ido yana murmushi.


Sai da ta tabbatar nurse ɗin ta fita, sannan ta juyo a sanyaye ta kalle shi tace:


"Congratulations!"


"Congratulations once again."


Ya furta yana murmushi. 


Sunkuyar da kanta tayi, sannan ta fara ƙoƙarin gyra mayafinta, sannan ta miƙe ya kama hannunta suka nufi waje.


Sai da suka yi sallama da Dr. Cara, sannan suka nufi wajen ajiye motoci.


Cikin zafin nama ya buɗe mata motar, bayan ta shiga ya mayar ya rufe, sannan shima ya zagayo ya shiga.


Kwantar da kanta tayi ajikin kujerar motar, saboda sam jikinta babu ƙwari tunda ta yi wannan aman. Don ma ta ɗan huta yanzu.


Hakan ya saka ya juyo ya kalle ta yace:


"Kina son wani abun ne mu tsaya a hanya?"


Mirgino da kanta tayi ta kalle shi tare da girgiza masa kai alamar "a'a."


"OK."


Ya furta tare da tayar da motar.


Suna isa gida ya saka aka shirya mata abun karin kumallo, haka ya zauna ya saka ta a gaba sai da taci ta ƙoshi, sannan ya rakata ɓangarenta ta kwanta domin ta ƙara samun hutu.


Haka Sultan ya ci gaba da kula da ita tsawon sati guda baya gajiya. Duk da Zainab tana yawan zuwa ta taya ta zama, saboda ya hana ta zuwa aiki.


Sai dai babban abinda yake damunta shine, wata matsananciyar kunyarsa da take ji, sannan ta lura yayi baya-baya da ita, gashi kuma ta rida da ta gama sabawa dashi.


Duk iya ƙoƙarin da take yi na guje masa saboda ta sani zama da Sultan na ɗan lokaci ne, idan bata sabawa kanta nisantarsa a yanzu ba sai yaushe?


Sai da iya soyayya da kuma kulawa ta Sultan ta saka tana jin kamar bazata iya jurewa ba, hakan ya saka dole ta fara tunanin mafita yadda zata ɗan ja hankalinsa ya dawo gareta.


Miƙewa tayi ta nufi kitchen ta fara ƙoƙarin shirya masa abincin rana, duk da masu aikin sunyi ƙoƙarin dakatar da ita saboda jan kunnen da yayi musu, amma ta ƙi. 


A hankali ta shirya masa girki, ta jera komai a wani kwando mai matuƙar ɗaukar hankali, sannan ta shiga tayi wanka tayi sallah, sannan ta fito sanye da wata doguwar rigar atamfa ta karɓi jikinta sosai ta ɗauko mayafi ta yafa.


Sannan ɗaya daga cikin masu aikin ta ɗauki kwandon tayi mata rakiya zuwa wajen ajiye motoci.


Driver ta nema kai tsaye, saboda ta tabbata idan ta