37
🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾
Mallakar
KHADIJA WRITES
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)
⸻
💖 Dedicated To My Mom 💖
⸻
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
🅿️-----37
Suhail bai ƙara cewa komai ba, ya nufi dining ya yi breakfast ɗin sa yana tsaka daci Iman ta fito har lokacin sanye take da hijab a jikin Kitchen ta koma ta zubo nata zata koma daki Suhail ya ce"Miyasa baki ci tare da mu"
"i need to be alone" shine abinda ta faɗa masa ta koma ciki
shi kadai yaci abincin bayan ya gama ya dawo palorn zeenah ta sauko zata fita amso sakon ta da mai delivery ya kawo mata
suhail ya ce"zeenah ina zaki je"
"zanje na amso abincin da ka kasa siyamin saboda nakin cin wanda matar ta girka"
"zeenah a hakan ko kin manta matar aure ce ke"
Rigar da ke jikinta ba ta da wani bambanci da fitowar wacce ba ta sa sutura ba, domin ta fito da duk wani shape na jikinta"
"idan ma mantawa nayi ai ba laifi nayi ba tunda mijin da nake aure ya kasa ciyar dani"
Iman ce ta sauko ƙasa hannun ta riƙe da plate da ta kammala ci abinci tun daga nesa take karewa Zeenah kallo a yanayin shigarta idan ka kalla zaka rantse bata da addini anyi mata kitson attachment daya sauka har gadon bayan ta ga wasu gogayen nails da aka mata fixing
iman ta bita da kallon mamaki a ranta tana cewa "Idan wannan ake kira da wayewa,Allah yayi mana tsari da ita wayewar da babu komai a cikin ta sai sabon Allah ta kuma gode wa malan da irin tarbiyar da yayi mata
ta gaban su ta wuce zeenah ta ɓalla mata harara dan gaba daya laifin kan iman ta ,ta ɗora sa dan da batayi abincin ai da duk hakan bata faru ba
haka zeenah ta fita amso ordern ta ta koma daki
gaba ranar haka Zeenah ta wuni tana siyan abinci a resturant Suhail
ya kyaleta tun tana bashi mamaki har ta dena dan a wunin gaba daya zeenah ta fito masa da mugayen halayen da bai san ta dasu a gidan baja Ibrahim ba a yanzu ya tabbatar da maganar hausawa da suke cewa baka sanin halin mutum har sai ka zauna dashi
tabbas da wani ya fada masa zeenah zatayi haka bazai taɓa yarda ba
a daren Iman ta girka Abinci dai-dai cikin ta ,fitowar daga wanka kenan tana zaune bakin mirror daure da towel
Suhail ya shigo ta daga ka ta kalle sa Suhail ya ce"Iman mi kika dafa yunwa nake ji"
yadda yayi maganar ya bata tausai ace namiji da gidan sa Amsa yana neman abinci ita kuma tayi alwashin baza ta kara yin girki ba har sai Ranar da Suhail ya dawo dakin ta amman a yanzu zata cigaba da girka iya nata kawai
"laaa!! yaya Suhail ka manta ba girki na bane na dazun ma da nayi naga kamar laifi nayi shiyasa na barka Amarya ta girka maku"
yasan sarai magana ta gaya masa haka ya juya ya fita ta cigaba da shirin kwanciya doguwar rigar bacci ta zura har ta hau gado sai kuma taji bazata iya barin mijinta ya kwana da yunwa ba haka ta sauko daga kan gadon hijab ta zura slippers ta fita Kitchen
suhail yana kwance kan four seater ya rufe ida nunsa amman ba bacci yake ba, bai ma lura da iman ba ta jima a Kitchen tana tunanin abinda zata girka masa daga karshen ta yanke yi masa jallof din cous-cous da coffee cikin mintuna Talatin ta kammala komai ta hada su kan tray ta fito falon ta ajiye a gaban suhail
A hankali ya buɗe idanunsa ya kalle ta
ta juya zata tafi suhail ya ce
"thank so much Iman"
"it's my pleasure"
shigar ta bedroom kenan kiran hafsat ya shigo wayar ta da sauri ta daga
Hafsat ta ce"Iman kedai baki kiran mutane sai dai a kira ki ko"
murmushi tayi ta ce"ba haka bane hafsat ina so na kiraki amman ba lokaci"
"hmmm haka ma zaki ce to yayi iman wani labari naji dazu Ammi ke fadawa Momy wai Suhail yayi aure,nayi mamaki wata biyu dayin aure ku har ya kara maki kishiya gaskiya yaya Suhail bai kyauta ba"
iman ta ce"Hafsat kenan nida ba kaina zata zauna ba"
"kefa haka kike, sai ki rinƙa nuna Kamar duniya bata dame ki ba kiyi wasa kina ji kina gani wata katuwa chan ta ƙwace maki miji kinga sai ki zama ƴar kallo tsakanin su Ranar da ya gaji da duhun kanki da uztazancin sai ya sako ki ,ki dawo gida sai su cigaba da shan soyayyar su Iman ki idan baki tashi kin tsaya akan mijinki idan ba zaki iya ba Wannan ya rage naki, Iman kina san mijinki from the first day nasan kina son suhail ,son da ke kanki bakin san kina mashi ba matukar kike ce haka zaki cigaba da ruyuwa a gidan kina ji kina gani zaman gidan zai gagare ki dole ki bashi kulawa domin ko sani namiji hankalinsa yafi karkarta wajen macen da tafi nuna masa soyyaya da kuma kula wa aure ba wai iya girka abinci bane ko wani abu daban ki tsaya ki lura da mijin mi ki rinƙa bashi shawara a fannin aikin miji ko baya sanki kina mai wannan abubuwan sai ya dawo ya fara sanki"
ajiyar zuciya Iman ta sauke tana jin
magangunan hafsat kawai take nazari kuma dk Abinda ta fada game da Suhail Gaskiya amman miyasa Hafsat ta gano ta da wuri haka
tana son Suhail,san da bata taba yi wa namiji wani irin saba bayan yaya Mubarak da Malan son da Allah ne ya saka mata shi ba tare data shirya ba ita kanta batason tayi nisa a son shi sai da yayi aure ta jin zuciyatar kamar zata buga
hafsat ta bata shawara kuma ta yadda zatayi aiki da duk Abinda ta fada mata
iman ta ce"yaushe zakizo"
"soon in sha Allah kin San ban samu addimission a makarantar da na nema ba "
iman ta ce"Allah yamaki chanji da mafi Alkairi a gaidamin aunty Zaituna"
ajiye wayar tayi
zeenah ce sanye da kayan bacci ta nufo inda Suhail ke zaune ganin yana cin abinci ta kallesa "babe ina ka sami abinci"
suhail ya cigaba da cin abincin ba tare daya kulata ba ganin haka ta janye plate din daga gaban sa ta nufi dakin iman tqna kwance taji an turo kofar dakin da karfi
tashi tayi ganin zeenah ce ajiye mata farantin tayi ta ce"hey villager wannan ya zama na ƙarshen da zaki dafa abinci a ranar girki ki ba suhail,ki sani idan ma wani abu iyayenki suka baki ki zuba mishi dan ki mallakesa ki sani ni zeenah Asiri baya tasiri akaina banda ma shegen shishigi miji baya ta taka amman ka rinƙa shige masa banda ma ƙaddara ina suhail ina ke kwata-kwata baku dace ba ki dube ki sai kace mai tallar Abinci ki sani bazanyi kishi dake ba dan ko yan aikin gidan mu sun fiki daraja a ido banza yar matsiyata kawai"
ta juya zata fita suka hada ido da Suhail da tun shigowar ya biyo ta bai mata magana ta fita ta bar dakin
duk cikin maganganun zeenah babu wanda ya mata ciwo kamar kiranta da tayi da yar matsiyata da abin iya kannta ya tsaya ko damuwa bazatayi amman ta taɓa mutanen da suka fi komai mahimmanci a rayuwar ta
hawayen da ta jima tana adanawa suka fara saukowa daga idanun ta Suhail ya kara cikin dakin
"iman kiyi haƙuri da zeenah ta maki"
hannu ta daga masa alamun yayi mata shiru
"iman please"
"yaya Suhail dan Allah ka fita duk maganar da zaka faɗamin yanzu sai tafi min ciwo fiye da wanda matar ka ta gama fadamin akan idanunka matar ta shigo har dakina ta zage ni ka kasa mata magana you have nothing to tell me dan Allah ka fitar mi daƙina bana san ganinka"
rufe ido tayi ta rinka fadawa Suhail duk maganar da tazo ranta
“Dan Allah ka fita daga ɗakina bana son ganinka"
Ta juya masa baya tana kuka kamar ranta
Suhail ya tsaya cak kamar wanda aka dasa a wajen yana kallon ta ya rasa mi yasa ya ƙasa tsawatar zeenah ba
Bai taɓa ganin Iman cikin irin wannan yanayin ba.
dan allah ku daure ku rinka comment da likes yafi sa mutun yayi posting da yawa