GADAR TSAUTSAYI 14
by @nusybee143
Page 14
Shiru Oga boss da Azeema suka yi suna kallonta, Roxy bata damu ba,ta koma ta kwanta saboda nauyin da ta ji kanta yana yi mata,a hankali ta ce"Azeema ki nemi masu taya ki ɗin,zan tsara muku yadda za kuyi"Azeema ta rissina tana faɗin "noted ma'am!"
Roxy ba ta sake magana ba ta koma ta kwanta,su kuma suka fice daga ɗakin
Hannun Azeema Oga boss ya riƙo yana faɗin "ke wai ba ki da hankali ne?
Ya za ki biye mata don tana cikin ɓacin rai da ciwo?
Kin san girman kasadar da kika ɗauko kuwa?
Ko ba ki yi tunanin abin da kan iya kai wa ya dawo ba bayan aiwatar da wannan ɗanyen aikin?"
Azeema ta yi murmushi tana girgiza kai ta ce"sanin kanka ne Roxy bata yin abu ya kwaɓe mata,bayan haka ka san bata juyawa baya akan ra'ayinta, sannan kuma abin da ta yi mana ba zai ba ni dama na juya mata baya ba,tabbas sai na cika mata burinta,sai na hukunta mata wannan azzalumar matar da ta yaudare ta ta cuce ta, karuwar banza kawai"
Oga boss ya jinina kai yana kallonta yana murmushi, kafin ya ce "to Allah ya bada Sa'a"Azeema ta shige ɗakin da Roxy take kwance tana faɗin "Ameen"
*ROCKY ESTATE, KANO STATE*
"Barka da dawowa Alhaji!"juyawa ya yi yana kallon mai aikin Hajiya Mariya da take gyara dinning area,ya ce"Barka dai,ina Amna?
Ko ta koma wajen Nanny ɗinta?"
Ta ce"Amna tana wajen Hajiya Nimra,suna sashenka"Haisam ya ji kamar ya ɗora hannu aka ya ƙwala ihu, ba tare da ya yi magana ba ya juya ya fice daga sashen
A parlourn shi ya samu Nimra da Amna a zaune suna kallo,kallo ɗaya ya yiwa Nimra da ta tsuke cikin kayan bacci,ta saki gashin kanta gadon bayanta,ya ɗauke kanshi,ta miƙe tana kwantar da Amna da take bacci,ta nufi inda take tana taku ɗaiɗai tana girgiza jikinta, cikin karairaya ta ce"welcome sweetheart!
Tun ɗazu ina ta jiranka "
Kallonta ya yi ya ɗauke kai,ta ƙaraso tana daf da rungume shi ya kauce,ta tsaya tana kwaɓe fuska kamar zata yi kuka
Bai sake kula ta ba ya ɗauki Amna ya wuce da ita wajen Nanny ɗinta, Nimra bata yi zuciya ba ta bi shi,har ya ƙarasa wajen Nanny ɗin Amna,tana fitowa Nimra ta sake biyo shi
Tsayawa ya yi fuska a ɗaure ya ce"ya dai?
I hope everything is fine"
"So nake mu yi magana"ta faɗa a shagwaɓe
"Sai da safe ma yi maganar"yana faɗa ya wuce don komawa sashenshi
"But you promise me za mu yi magana idan ka dawo"ta faɗa tana biyo shi da sauri
"Sai da safe" ya faɗa ba tare da ya kalle ta ba"
"Ai gobe ma fita za kayi ba tare da na sani ba"bai saurare ta ba ya shige sashen shi, amma kafin ya shiga parlourn ta biyo shi
Cikin ƙosawa ya kalle ta ya ce "ina haɗa ki da Allah ki yi haƙuri gobe za mu tattauna, yanzu kin ga akwai aikin da zan yi,idan kika zo kika yi interrupting ɗina za ki iya janyo min matsala,na yi Miki alƙawarin zan saurare ki mu yi maganar"
Ba a son ranta ba ta juya ta fice daga sashen,ya shige parlourn shi ya rufe ƙofa yana jan tsaki
Ya tsani naci,ita kuma wannan akwai ta da nacin tsiya
Yana zama ya fara kiran Saleem,babu jumawa Saleem ya ɗaga kiran
"I'm sorry Saleem!
Ɗazu na ga kiranka,bana cikin yanayin da zan iya ɗagawa ne"
Murmushi Saleem ya yi,ya ce"ba yawa yallaɓai,ai na san yanayin aikin
Na samo address ɗin iyalan marigayi Malam tajo,dama shine abin da na kira na gaya maka kenan"
"Good job Saleem!tura min"
"Okay Sir "daga nan suka yi sallama
Ko da Saleem ya tura address ɗin Haisam ya daɗe yana mamakin inda ta luluƙa ta kai su,ya yi murmushi yana girgiza kai,a hankali ya ce"Allah sarki yarinya!
Ƙarshenki kuma ya zo kenan,sai dai na ce mu haɗu kawai nan gaba kaɗan "
*MALIYA ESTATE*
"Zan fita "ɗaga kai ya yi yana kallon Arfa da take a shirye tsaf, rungume da Zuhra, cikin kwanciyar hankali tana sanar masa zata fita"
A fusace ya ce"a gidanku haka aka koya miki tarbiyyar tambayar miji idan za ki fita?sai da kika shirya kika gama komai sannan za ki wani tambaye ni za ki fita?"
"Wanne mentality ɗin naka ne ya gaya maka tambayarka nake yi Muyassar?
Ai ba Ni kaɗai ba ce aka yi missing koya min abubuwa da yawa a gidanmu,kai ma kamar ka samu lack of home training,tunda na ga baka san darajar aure ba,baka san darajar mace ba,asalima kai babu abin da ka sani sai tunanin karuwa da son kanka, don haka nima a bar ni na yi abin da na ga dama"
Muyassar ya girgiza kai, yanzu ya daina mamaki idan Arfa tana yi masa rashin arziƙi, saboda yadda ta samu cikakken goyon baya daga wajen wadda take faɗawa maganganu duk sanda suka samu matsala,wato mahaifiyarsa Hajiya Sa'adatu
Bai sake yi mata magana ba,yana kallo ta fice daga gidan,yana zaune bai tashi ba sai da ya ji ƙarar motarta, sannan ya miƙe jiki a mace ya ƙarasa jikin window yana leƙen waje
Shi mutum ne mai son hutu da kwanciyar hankali,yana son soyayya da kulawa,amma babu wadda yake samu daga wajen Arfa zai tsabar kishi da zargi,bayan haka bata iya komai ba
Ya rasa menene dalilin da ya sa mahaifiyarsa take matuƙar son su Arfa,don akan Arfa ba ƙaramin ci masa mutunci ta yi ba,sai da ya ji komai ya fice masa a rayuwa
Ga masifar soyayyar Shaheeda da take taso masa tana hana shi sukuni,ko a yau da zai ganta da wallahi sai ya aure ta,sai dai duk abin da zai faru ya faru,ba damuwarsa ba ce
Ya daɗe a wajen yana karanta wasiƙar jaki game da rayuwarshi da shaheedansa, kafin ya fice daga parlourn don barin gidan,a ranshi yana jin da yana da wani wajen da zai rinƙa zuwa yana yin zamansa ko ma ya kwana da ya je,ya huta da ganin Arfa, wadda har yanzu daidai da second ɗaya bai taɓa sonta ba
*ROXY*
Yau kwana biyu kenan da samun tsautsayin da ta yi, jikinta ya yi kyau sosai,har ma ta cigaba da yin kananan ayyukanta da system ɗin Oga boss
Da kanta ta shiryawa Azeema yadda zata yi da zarar ta je gidan Amra,don tuni sun biya ta ƙungiyar su Amra ɗin,da ta tara manyan mata da yan mata,duk wadda kake so a kai maka,to an yi matuƙar Sa'a Amra ta buƙaci a kawo mata Azeema, wadda ta sauya suna zuwa star girl,dama tuni Roxy ta san irin matan da Amra take kwaɗayi irin su Azeema ne,don haka abin ya yi mata daidai ba tare da wata matsala ba
Cikin wasu tsinannun kaya Azeema ta shirya, Roxy tana daga zaune tana kallonta tana ɗan murmushi, kafin ta ce"Good!
Haka nake son gani!na tabbata idan ta ganki zata yi burin aiwatar da mummunan ƙudurinta"sai kuma ta yatsina fuska ta ce"na kasa gane abin da mata suke buƙata a jikin ƴan'uwansu mata,da har suke jin za su iya illata wani akan wannan mummunar ɗabi'ar tasu
Daga yau ina buƙatar a cire mata sha'awar ya mace a rayuwarta har abada,ina buƙatar ta ji a duk duniya babu abin da ta tsana sama da wannan dabbancin,in other hand kuma ina buƙatar ta ji tabbas Roxy ta wuce tunaninta,tafi"babu musu Azeema ta ɗauki abayarta ta ɗagawa Roxy hannu,ta fice daga dakin tana ƙoƙarin saka abayar
Itama Roxy miƙewa ta yi ta fice daga ɗakin, a ranta ita kaɗai ta san wutar fansar da take ruruwa a cikin zuciyarta
*KANO STATE*
*HAISAM*
Da sauri-sauri yake fitowa daga sashensa,don a rayuwarsa ba ya son ɓata lokaci ko kaɗan, musamman a irin abin da ya shafi aiki
Nimra ya gani a raɓe a jikin bangon parlourn,ta narke idanu ta langwaɓar da kanta,a cikin zuciyarsa ya furta
"Kai!inna lillahi wa inna ilayhi rajiun!
Wannan wacce iriyar masifa ce?"
Katse masa tunani ta yi, cikin yauƙi take faɗin
"Good morning sweetheart!"
A taƙaice ya amsa da"morning!"
Lumshe kyawawan idanunta ta fara yi tana buɗewa cikin sigar jan hankali, Haisam ya ɗauke kanshi, zuciyarsa tana zafi
"Can we go now?
Za mu iya magana?"
Ba shi da zaɓin da ya wuce cewa"okay! bismillah "duk da cewa yana da abu mai muhimmanci da zai yi,ya juya ya koma cikin parlourn, ta biyo bayansa
Yana zaune ya zuba mata idanu ganin bata da niyyar yi masa magana,gashi shi kuma yana da abu mai muhimmanci da zai yi, cikin ƙosawa ya dube ta ya ce
"Nimra kin san yadda aikina yake, kuma a kowanne lokaci kusan na ce miki ina bakin aiki ne,idan kina da magana mai muhimmanci then let's talk,is not proper ki zuba min idanu kina kallona bayan kin ce min kina da magana,nima kuma ina da inda zan je, don akwai aikin da zan yi"
Shagwaɓe fuska ta yi,ta ce"kenan yanzu baka da lokacin iyalinka sai na aikinka kenan?"
Kanshi tsaye ya ce"kusan haka!"
Ya faɗa ne don ta ƙyale shi, amma a maimakon haka sai ta kama murmushi tana faɗin "You must be joking my friend!
Whatever,ko ma dai haka ne ni nan zan sauya yanayin aikin nan da yake cinye haƙƙin mutane,ka ba ni time, shima aikin ka ba shi,for now dai,a yi maganar a yanzu,anan, yaushe za ka tura magabatanka gidanmu?idan ba za ka iya magana ba ni zan yi wa daddynka magana,idan ya so sai su je can wajen abbana "
Shi abin ma dariya ya ba shi,amma ya ɗaure fuska ya ce"ba sai kin gaya masa ba,idan na samu time zan yi masa magana, yanzu dai kina gani na da shiri aiki zan fita "juya ƙwayar idanunta ta yi ta ce"alright babu matsala,sai na ji ka,amma kar na ji shiru Please "ya jinjina kai kawai yana miƙewa,ta miƙe itama ta rufa masa baya suka fito har wajen motarshi
Sunkuyar da kanta ta yi daidai windon motar tana kallonsa tana narkar da idanu yadda ta saba idan tana son ta ja hankali, ɗauke kanshi ya yi daga kallonta yana yunƙurin tayar da motar,da wata iriyar sexy voice ta ce"safe trip sweetheart!
Allah ya dawo min da kai lafiya "ya jinjina kai sannan ya tayar ya fice daga gidan
Kai tsaye address ɗin da Saleem ya tura masa ya nufa,sai gashi ya ya tsinci kanshi a gaban wani katafaren gida
Bin gidan ya yi da kallo yana sake duba address ɗin da mamaki,amma da ya tuna wacece Roxy sai ya yi murmushi kawai,yana sake duba hotunan da aka tura masa
Ya kai wajen mintuna talatin a ƙofar gidan kafin ya samu yaron da zai aika gidan ya yi masa sallama da matar gidan,babu jumawa sai gashi ta leƙo,sanye da hijabi har ƙasa,autanta Habu yana riƙe da hannunta
Har ƙasa ya durƙusa yana gaishe ta,ta amsa da sakin fuska sannan ta ce"ka shigo ciki mana,sannu da zuwa"ya yi ɗan murmushi ya ce"a'a dama ba shiga zan yi ba, tallafin marayu ne aka ce na kawo muku"ya ciro kuɗi ɗaurin 100k guda biyu ya ce "gashi, Allah ya ji ƙan mahaifinsu ya albarkaci rayuwarsu"hannunta yana rawa ta karɓa tana faɗin "oh Allah!
To an gode an gode sosai, Allah ya saka da alkhairi, yadda kuke faranta mana Allah ya faranta muku, Allah ya kula da ahalinku kuma"ɗan murmushi Haisam ya yi,ya ce"babu komai Mama, in sha Allah ina nan dawowa nan kusa,hi boy!"yaron ya ɗaga kai a sanyaye yana kallonsa, tsananin kamar da suke yi da mahaifiyarshi ya sake tabbatar masa da zarginsa,kamar har ta yi yawa ma,ya kama hannun yaron yana yi masa wasa,duk da yadda ya nuna masa ba zai saki jiki da shi ba,amma saboda kayan biscuits da sweets ɗin da ya kawo masa ya saki jiki da shi,har ya ɗaga masa hannu da zai shiga motarshi
Sai da suka shiga gida ya ɗaga waya ya kira Saleem, Saleem yana ɗagawa ya ce"komai ya yi daidai Saleem, thanks very much for your effort "
Saleem ya rissina kamar yana gabansa ya ce"ka cancanci fiye da haka daga gare ni Oga, Allah ya ba da sa'a, Allah ya ba ku nasara akan maƙiya"Haisam ya kashe wayar yana murmushi
#Nusy_bee