ALWASHI 2

23

by @rufaidaumar

ALWASHI 

   48


***
KATSINA

Alh Sada Bilyaminu ji yake tamkar bai taɓa aurar da wani ɗa ba sai a kan Areef Sada Bakori. Gaba ɗaya gidan sai da aka yi masa sabon fenti mai sheƙi da ɗaukar idanu, kayan abinci kuwa tun ana saura sati biki aka soma jibge su a store ban da manyan tukwane da ƙarin ƙwararrun masu girki da aka ɗauko a gefe guda kuma har da ƙarin ƴan aiki don kula da baƙi. Yanayin yanda ya ɗaukaki abin ya yi wa Hajja Zayha daidai don ta sani duka wannan rawar ƙafar zai tashi a banza muddin shi da Mami suka san wace ce Laila. Zasu shiga razanin da ba su taɓa tsammani ba. 

Don haka wannan ke kwantarwa da Hajja hankali duk da cewa yaranta mata da suka zo domin bikin nasu ran a jagule. Faɗi suke yi ai wannan nuna fifiko ne ma Abban ke yi a zahiri. Ita dai murmushi kawai ta yi. 

A satin da ya kama na bikin sai ga  Areef ya iso. Shi kansa ya sauya, hutu ya ratsa shi sosai don wannan ne karon farko da ya taɓa zuwa ƙasar waje ba tare da guzurin wata damuwa ko ɓacin rai ba. Mami ta ji daɗin yanda ya saki fuska sosai cikin ƴan uwanta da suka zo daga Adamawa da mazauna Katsina. Wasunsu sai da suka furta, wai yaushe rabon da su ga haƙoran Areef haka? Wata Gwaggonsu faɗi take lallai dole ya washe baki tunda dai zai auri mata biyu lokaci guda. Haka ya fice ya na sunkuyar da kansa kawai. 

  Dukkan wasu shirye-shirye sun kammala a gidan, safiyar da ta kama can gidajen Amare zasu soma shagulgulansu na biki, nan ɗin ma zasu yi kamun Ango kamar yadda suka shirya, kwatsam sai Abba sai wayar Daddy Affan ya tsinta wai yana farfajiyar gidan sun zo tare da Momi Inayah. Abba ya ajiye wayar ya miƙe tsaye, Haj Nafisa ta dube shi. 

"Lafiya dai ko?" 

Kansa ya girgiza,

"Ina fa, kin ji wai Alh Affan ne ya zo da iyalinsa. Bari na ƙarasa na shigo da shi nan."

Ta kuwa saki baki don mamaki amma har ya fice ba ta iya furta uffan ba, kar dai ya zo a yi fito-na-fito tunda ba'a yi auren da ɗiyarsa ba? Jin alamun zasu shigo falon ne ya sa ta ɗaukar mayafinta da ke a gefe ta gyara lulluɓi. Abban ne a gaba sai Daddy Affan wanda fuskarsa ke a sake kai kace ba shi da wata damuwa da su, sai ko Momi Inayah a bayansa cikin shigar maroon abayarta. 

"Sannunku da zuwa." Haj Nafisa wato Anti Amarya ta furta itama da murmushi saman fuskar nata. 

Bayan zamansu Anti Amarya ta miƙe don haɗo musu abin motsa baki. Daddy Affan ya dubi Abba yana murmushin nan nasa da Momi Inayah ta tsani gani sanin da ta yi sam babu alheri cikinsa koda kuwa alherin ne zai fito daga bakin. 

"Congratulations Sada, ba ka gayyace ni ba, amma ni na samu labari na zo da kaina don a yi komai da ni. Ban da abinka, koda Areef bai auri Babyna ba, kana zaton cewa zan kasa zuwa aurensa ne? Kodayake ba ka ɗauke ni ɗan uwa ba ballantana shi ma ya yi min kallon Uba."

Abba ya yi ɗan yaƙe. 

"Sam ba haka bane, ka yi haƙuri. Ka san al'amarin ne..."

"No no no! Kar ka damu fa! Babu wani abu, everything is  written by Allah. Don haka koda ace Areef bai auri Nihla ba, our good relationship won't change. Ba su suka haɗa mu ba kuma ba za su raba ba."

Abba ya jinjina kai yana murmushin yaƙe.

"Gaskiya ne."

Ya yi niyyar ba su masauki sai dai Daddy Affan ya ce ai sun kama ɗaki a masauki gudun takura musu tunda akwai baƙi. Ya kira Hajja da Mami ta waya suka zo aka gaisa, Daddy Affan ya miƙawa Mami check na kuɗi har miliyan guda wai gudunmuwarsa ga Surukansa biyu. Mami ta karɓa a sanyaye ta yi godiya. Hajja kuwa kamar ta ɗora hannu a kai, sai dai da ta tuno kason Sameera dole ko ya je hannunta ta samu nata kason ko ma duka ranta ya yi mata sanyi. Ta san ai a yadda Sameera ta tsani Areef a yanzu babu wani abu nasa da za ta yarda ta ci shi sai a bisa dole. 

A waje suka yi karo da Areef bayan Abba ya tako mishi zasu wuce, wani murmushi Areef ya yi masa wanda tuni Daddy Affan ya ɗauki haske a murmushin, wato ya yi galaba a kansa. Matse leɓe kawai ya ɗan yi da haƙori a ransa shi kaɗai ya san me ya shiga kissimawa, a farko sam bai yi niyyar halartar bikin ba, ɓadda kama ce kawai ya sanya shi sauya shawara. Koda Areef ya ƙaraso, zai durƙusa domin gaida shi, ya yi saurin riƙo shi gami da ɗan rungume gefen jikinsa da hannu guda yana ɗan bubbuga bayansa. A hankali yace,

"Congratulations My Son."

Areef ya ɗago suka dubi juna bayan ya sake shi, murmushin yake har yanzu ya amsa da Thank you Daddy. 

"Ina ƙanwata? Ba da ita ku ka zo ba ne?"

Abba ya dubi Areef ganin yaron zai mishi kwaɓa, mene ne na tambayar yarinyar da ya ce ba zai aura ba to? 

Shi kuwa Daddy Affan wani miyau ya haɗiye yana ɗan murza yatsun hannunsa na dama duk a ƙoƙarin danne wani baƙin ciki da tsanar Areef din da ke taso mishi wanda yake jin kamar ya shaƙe wuyansa har lahira. Duk dauriyarsa sai ya ji ba zai iya amsa mishi wannan banzar tambayar mai cike da rainin hankali ba don haka ya juya ya miƙawa Abba hannu suka ƙara yin sallama bayan ya jaddada masa cewa jibin zai je Adamawar shi ma. Haka ya shige mota suka fice daga harabar gidan. Areef ya dubi Abba da ke mishi wani kallo ya shafi sumar kansa gami da sunkuyar da kai murmushi a saman fuskarsa. Abba kawai ya girgiza kansa. 

"Allah ya kyauta." 

***
KANO

Washegarin ranar da can Katsina suka fara nasu shagalin, aka sanya Laila a lalle. Gaba ɗaya jikinta a mugun sanyaye ba walwala, haka aka yi komai har da hotuna ta kasa sakin fuska. Zakiyya ta zo Kano biki, haka Maman Saif ta Miltara gidan da suka ƙaura inda a can ne Sameera ta raini cikinta, daga ita har yaranta mata sun shigo. 

Ana tsaka da taro a farfajiyar gidan kawai sai wata mota ta shigo gidan. Sau ɗaya ta kai duba ga motar ta gane na gidan ne don haka ta kauda kai, tasan bai wuce wasu baƙin aka ƙara samu ba. Sai dai matar da ta ga an buɗewa ƙofar baya ta fito ya sa ta miƙewa tsaye babu shiri har mayafinta na zamewa. Mama ce, riƙe da (crutches) da ke taimaka mata wajen tafiya. Ta sha doguwar rigarta na atamfa sai ko ɗan hijabin da ya sauka har bayanta ya rufe. Ba ta san sadda ta tafi a guje ta faɗa jikinta ba har Mama na ambaton Allah jin da ta yi tana neman kayar da ita. 

   "Ki bi a hankali mana Laila. Ba ki ganin  har yanzu da sauranta?"

Muryar Haj Sumayya amaryar Baba Barista ta katse ta. Ita dai Laila ta kasa sakin Mama sai kuka take yi. Mama kanta sai da ta yi hawaye ganin yadda ɗiyarta ta yi kyau ta yi kumari. 

Haka aka ɗunguma zuwa ciki, duk nacin Haseenah kan Laila ta fito su ƙarasa event dinnan sai haƙura ta yi don an yi an yi amma ta ce ita sam ba za ta ba. Dole suka cigaba da kula da baƙi hakanan. 

Ba su samu keɓewa da Mama ba sai dare, daga ita sai Mahaifiyarta a ɗakin. Haidar yana Maiduguri sai a goben zasu zo tare da sauran iyalan Baba Barista. 

  Laila sai shagwaɓa take yiwa Mama. Mama na ba ta labarin yanda cikin ikon Allah komai ya zo da sauƙi na ciwonta bayan an yi gwaje gwaje aka gane cewa akwai kyakkyawan zaton za ta miƙe don buguwar bai taɓa inda za ta nakashe ba. Wancan ma tashin da ba ta yi da wuri ba,  matsalarsa daban. 

Hira sosai har dai Mama ta jefowa Laila tambayar da ta jefa ta a razani. 

"Asalin mijin Areef can Katsina ko? Laila kim tabbata ba sunan ne kawai ya zo ɗaya da na baban Haidar ba? Wanda kika aura ba shi da haɗi da case ɗin Sameera?"

Ta yi ɗif ta kasa magana, ba ta iya yiwa Mama ƙarya ba. Mama tsoro ya dirar mata, ƙirjinta ya shiga bugu, ganin irin yanayin da ɗiyarta ta shiga ya ba ta tabbacin haka ɗin ne. Ta dafa kafaɗar Laila gami da karkato ta suna duban juna a zaune saman gadon. Laila ta dinga ambaton sunayen Allah da addu'o'i a ƙasan ranta, sun riga tuni sun shirya abinda za ta faɗawa Maman ita da Na'eem, hakanan Zakiyya ta aminta da shawarar, sai dai ji take kamar ba za ta taɓa nasara ba kan shawo kan Mama Kubra. 


 "Innalillahi wa inna ilaihir raaji'u! Laila ki ka auri wannan mutumin? Mutumin da iyayensa suka tozarta mu? Suka wulaƙanta mu? Mutanen da ba su san girma da darajar ɗan adam ba? Ya Allah!"

Laila cikin rawar murya ta ce

"Ma..ma, ina da hujja.."

Tas! Mama ta ɗauke ta da mari, kafin ta farfaɗo tuni ta ƙara mata wani a ɗaya gefen kuncin. Kawai kuma sai Mama Kubra ta fashe da kuka mai ƙarfi tana ambaton 'Kin cuce mu Laila!'

  A YI HAƘURI🙏🏾🤲🏽🤲🏽

©Rufaida Umar