Muradin zuci
by @bintuuu
Papa daskarewa yayi anan tsaye a falon ya gagara zama yana bin matar tasa da kallo, ya sani wannan din ba sabon abu bane sanin masifa da fitinar matar tasa da yake fama dashi tun fil azal wanda kowa ya shaida a kaf danginsa cewa Fatiman fitinanniya ce kuma in bataso zaman lafiya ba toh ba wanda zai zauna lafiya a can gidansu dake Nigeria. Sai ya koma ya zauna kan kujerar a hankali ya duqar da kansa yana kallon Babyn wadda kamar hadin baki itama ta bude idanunta a hankali, dan stiff yayi yana kallon kwayar idanunta da suka kasance grey color, duk da kasancewar ta jinjira hakan bai hana manyan idanunta fitowa fili ba a lokacin da take kallonsa. Duk yanda yake jin nauyin tashin hankalin dake tunkarosa hakan bai hanasa samun kansa da yi mata murmushi ba, sai ya kwantar da murya ahankali yace mata "Assalamualaiki" nan twins suka matso suna kallonta, Imran yace "Papa please let's keep it" sai ya dago kai yace "She's a girl Imran". Imam kuwa sai kallonta yake baice komai ba shima, sai Papa ya sake duqawa ya kalleta yanajin tausayinta na shiga kowane sashi na zuciyarsa, tayaya wannan innocent being din zata zamo masifa bayan in za'a bata zabi itama bazata so abunda ya faru da ita ba ko kadan, har sannan bata dauke idanunta daga kan Papan ba sai can kuma ta fara motsi tana dan bata fuska alamun zatayi kuka nan ya hau jijjigata yana kallon kayan sanyin dake jikinta, mamakinsa daya a wannan lokacin shine ta yanda kayan jikin jinjirar yake fes da kyau ga wani tashin qamshi da takeyi, sai ya dan dago ta yana sake duba kayan dan ko daga texture din mutum zai fahimci ba daga cikin wahala ta fito ba. Idonsa ne yakai kan wani rubutu ajikin farin towel din nata sai ya kai hannu ya yaye kadan yana ganin sunan da akayi engraving kamar saqa ajiki da harafin larabci "FADWA" ya maimaita sunan a fili, sai lokacin Imam yace "Papa sunanta ne?" ya gyada kai "Sunanta Fadwa" Imran yayi murmushi ya duqa kansa gareta yace "Hi Fadwa" sai Papa ya shafa kansa bai bar murmushin qarfin halin ba, yace "Yes.. Her name is Fadwa" ya qarasa fadi yana danne duk wani tashin hankalin da ke kokarin taso masa a zuciya.
Rai a bace Momma ta shiga dakinta Habiba na biye a bayanta, cikin kwantar da hankali tace "Ranki shi dade kiyi hakuri kar hakan ya ja miki matsala ga lafiyarki" ta juyo a fusace tace "Sai an fitar da yarinyar nan daga gidan nan, ke yanzu yarinyar nan bata miki kama da aljana ba?" Habiba ta dan duqar da kanta tace "Ki gafarceni ranki shi dade, amma yarinyar ba lallai ta kasance aljana ba sai dai asalinta ne zai iya zama da tangarda" Momma tayi saurin cewa "Dama batun shegiya kam shegiya ce, kuma wallahi ba zan raini 'yar cikin shege tareda 'ya'yana ba" kafin Habiba tayi magana suka jiyo tashin kukan yarinyar Momman 'yar kimanin shekara biyar dake kwance akan gadon tana bacci, sai Momman ta juya gareta da sauri tace "Jidda na kin tashi" yarinyar ta gyada kai tana murza idanunta sai uwar ta miqa mata hannu da nufin ta iso gareta. Tana shafa bayan Jiddan ta juya zata fadi magana a Habiban aka turo kofan dakin Imran ya shigo a daddare, qin qarasowa yayi cikin dakin yayi sai ya tsaya anan bakin kofar yace "Mama Habiba kije Papa na kiranki" da sauri tace da Momma "Ranki shi dade bari naje" gyada kai kawai Momma tayi batace komai ba tana kallon Imran din dake tsaye a bakin kofan yaqi shigowa, dan hararansa tayi sannan tace "Meye na tsayawa a bakin kofan toh?" sai yayi murmushi ya juya while Habiba na biye dashi suke fice tana kallonsu, sai can kuma tayi tsuka ta cigaba da shafa bayan Jidda dake shirin komawa wani baccin.
Fitan Habiba falon ta samu Papa na tsaye yana jijjiga Fadwa dake kuka a hannunsa, cikin ladabi ta duqar da kanta tace "Ranka shi dade akwai abunda kake buqata ayi ne?" sai ya juyo yace "Kuka take bansan me takeso ba ko zaki gwada lallabata" nan ta miqa hannu ya bata ita ta cigaba da lallabatan, amma har zuwa karfe goma na dare Fadwa bata bar kukan ba duk da ruwan dumin da Habiba ta bata tasha, har zuwa sannan kuma Momma bata sake fitowa daga dakinta ba duk da kukan jinjirar da take jiyowa ya karade gidan. Hankalin Papa in yayi dubu ya tashi a wannan lokacin ya rasa me ke masa dadi. Sai bayan Habiba ta danyi dabarunta ta gano ciwon ciki ne ke damunta sannan ta fada masa, aikuwa nan da nan ya dauki car key twins na biye dashi zasu fice siyo mata maganin sai Habiba ta sake tuna masa yarinyar na buqatan madara da kayan sakawa har dasu pampers ya gyada kai tareda ficewan. A daren Papa suka fita zuwa super market don nemo madaran nata, yana tafe a motan yana tunani har sai da Imam dake seat din gefensa ya ankarar da shi isowarsu gurin ganin zasu wuce sannan ya dakata, daga nan kuma suka biya boutique na saida kayan yara amma kuma sai suka samu a kulle, haka ya hakura ya biya dasu pharmacy ya siyo maganin ciwon ciki na daidai jinjiri sabon haihuwa sannan suka koma gida.
Bayan Habiba ta bata maganin cikin sa'a suka samu ta fara bacci sannan Papa ya sake dubasu kasancewan suna cikin daya daga cikin dakunan dake nan downstairs, ganin Fadwan tayi bacci yasa shi ficewa sannan ya nufi dakin matarsa, anutse ya bude kofan sai ya sameta a zaune a bakin gado sanye cikin kayan bacci tana dan dafa cikin ta dake dan mata ciwo kadan, da sauri ya qarasa yana mata sannu amma bata ko dago kanta ba sai ya zauna kusa da ita ya sake cewa "Sannu, ko in taimaka miki ki kwanta?" nan ma ta girgiza kai bata ce komai, shiru sukayi sai can yayi qasa da murya yace "Fatima, yarinyar nan itama batada zabi akan abunda ya faru da ita" sai sannan ta dago kai tana kallonsa tace "Ni bance laifinta bane daman, kawai bazan riqe yarinyar da bansan asalinta bane, ya kawai daga ganin yarinya a yashe zaka dauko ka qaqabamin nima inaji da kaina" sai yayi murmushi tareda kamo hannunta yace "Haba mana Binta na, ai ba lallai sai ke zaki raine ta ba, ga hadimanki dayawa da duk abunda kikace shi zasuyi, Ina laifi in kin taimaki yarinyar da batada gata ayanzu sai na Allah da namu, ki tuna fa muma ba dabarar mu bane ya bar mana namu 'ya'yan cikin gata kuma a gaban mu" sai ta kwace hannunta tana hade fuska tace "Ni ka daina dangantamin yarana da irin wannan maganganun, kuma ai ba mu kadai bane mutanen da zamu iya riqeta, akwai orphanages dayawa ai" Papa na kallonta yace "Then..Menene makomar yarinyar kenan? what if.." kafin ya qarasa ta fara qoqarin gyara kwanciya tace "Ni kawai banaso, nace banaso ana dole ne? naji yau ta kwana a gidan amma zuwa gobe bazan lamunci zamanta a gidan nan ba" da haka ta kwanta ta juya masa baya yana kallonta, can ya sauqe numfashi ya miqe ya fice. Dakin twins ya tafi a upstairs dan tabbatar da ko sunyi bacci sai ya samu Imran nata munsharin bacci abunsa while Imam na zane a takarda anan zaune kan upper bunk dinsa dake saman na Imran din, murmushi Papa yayi yace "Imam bazaka bar zanen nan haka ba kayi bacci?" sai ya dago kansa, ahankali yace "Saura kadan" yace "No son, it's late..ka kwanta haka nan sai gobe ka qarasa" da haka ya qaraso bakin gadon ya fara tattare masa takardun, sai ya dago takarda guda daya yana gani a zuciyarsa yana mamakin baiwar yaron a kullum in yaga abubuwan da yake zanawa kala kala. Sai da ya tabbatar ya kwanta sannan ya nufi switch din dakin zai kashe wutan yaji Imam din yace "Papa, cikin ya daina mata ciwon?" sai ya juyo yace "You mean Fadwa?" ya gyada kai ahankali, sai Papa yayi murmushi yace "Eh ya daina har tayi bacci, now sleep....saida safe" da haka ya kashe wutan sannan ya fice tareda rufo musu kofan..
Tunda ya koma dakin kwanansu Momma bata juyo ta kallesa ba duk da idonta biyu har sannan, har ya gama shirin baccinsa yazo ya zauna a gefen gadon bata motsa ba kuma idanunta a bude tana kallon wall din dakin ta bashi baya, sai ya juyo yana kallonta yace "Kinyi bacci?" shiru tayi bata amsa ba, qasa qasa ya sake cewa "Ya cikin naki?" nan ma tayi shiru, ganin halin nata ne ya motsa yasashi kwanciya shima ya juya bayansa yana jin zafin hali irin na matar aurensa.
Free page
Bintu Musa ✍️ 📚