Chapter 7
by @reza12
MATAR MAZA
(Life story)
7
Sosai take mamakin irin kuɗin da yake da shi, sannan kuma baya tsoron buɗe mata bakin aljihu a koda yaushe. Satinsa ɗaya a Nigeria ya koma Maroco gurin kasuwancinsa bayan ya angwance abunsa, ya bata ATN card dinsa akan duk abun da take so ta saya ta ciki. Murna a gurin Azima ba'a magana. Gashi ya tafi ya bar mata wata ƙatuwar Mota wacce ta fi tata da ya saya mata. Haka kawai zata ci uban gayu cikin kaya masu shegen tsada ta tafi unguwar su Salma dan su huɗu. Haka kuma yanzu yan gidan su gaba ɗaya babu wanda take shakka daga mazan har matan, dama dai ba tsoronsu take ba bare yanzu da ta zama babbar Mace ga kuɗi ga kuma miji ɗan gayu mai abun hannu. Ita kanta Hajiya ɗin yanzu ba komai nata take ji ba, idan abu bai mata ba, bata ɓoyewa zata ce ba zata yi ba, ko tace bata so, gaba ɗaya halinta na kafiya da taurin kai ne suka sake baiyana, sai dai abun hannunta baya rufe mata ido.
Yau Lahadi hakan yasa ta tashi da nufin zuwa gidan Anty domin ganin Fadila. Tun da tayi aure basu ƙara haɗuwa da yarinyar ba, wanda yanzu tana da shekaru shida kenan a duniya. Wasu shegun less ta ɗauko masu nauyin kuɗi, sai wacce da wacce kadai ke iya sakawa, ta rasa wanne zata saka daga cikinsu, domin dai so take yau ta tsone idon maƙiya. Hakan yasa ta kira Sadiya ta taya ta zaɓar wanda zaifi cizo. Ta ɗauki wani mai ruwan ƙwai har wani walƙiya yake yi. Ta shiga wanka, nan ma ta daɗe tana yi kafin ta fito, ko gurin shirya wa ma sai da ta ɗauki lokaci tana gyare-gyare. Lokacin da ta fito ita da kanta ta burge kanta, sai kawai ta saki wani murmushi domin tasan zata tashi kan yan gulma yau. Kai wallahi idan baka santa ba tsaf zaka ce matar shugaban kasa ce zaɓar yadda ta sha abun wuya da na hannu masu tsadar bala'i. Ta shiga ƙatuwar motar nan suka nufi gidan Mama.
Da ƙyar Mama ta amsa sallamar tana mata kallon banza. Ganin haka yasa kanta tsaye ta faɗa mata abun da ya kawo su domin dai ta san cewa bai wai tazo ganin wannan baƙar fuskar tata bane. Mama ta ce "Fadila bata nan gidan, kuma ko kin manta ne tana gidan ubanta ne?". Azima ta ce "Ba damuwa ta ko tana ina bane, ina son ganin ƴata ne". Ta faɗa itama babu ko girmamawa kaman yadda ta amsa mata. Mama ta cika da mamaki, dama tana jin labarin rashin kunyar Azima bata taɓa gani ba sai yau, to dai tana bata girma ko lokacin da take gidan musu. "Azima ni kike faɗawa magana haka"? "Ni ƴa ta nazo gani ba wani abu ba, kuma wallahi duk inda take sai na ganta na rantse miki da Allah". Ta ƙarasa tana ciro waya domin kiran Musa ɗin. Anan gidan ta kira Musa ya daga, ta ce "Ina aka kai Fadila ina so na ganta ne?" "Ya ce "Tana gidan Anty". Ya faɗa kanshi tsaye ba tare ma da yasan ko tana gidan su bane. Ya na faɗa ta kashe wayar ta nufi gidan Anty cikin shirin ta ba tare da ko ta yi sallama da Mama ɗin ba. Tana fita Mama ta kira Anty ta ce karta sake ta barta ta ga yarinyar duk rashin kunyar da zata yi, ko motsinta kar ta sake ta gani.
Lokacin da ta isa ta samu Anty ɗin a falo da alamu ita take jira. Babu ko sallama ta shiga, sai suka fara kallon kallo, tuni Azima ta fahimci an sanar da ita zuwanta. Sosai Anty ɗin ta bita da kallo ganin yadda ta sauya har wani Kyu ta ƙara, ga wani hutu da ya baiyana a jikinta, idan batayi karya ba har wani lafiya ta hango a jikin Azima da ya bata mamaki. Sadiya ce ta gaidata ta amsa ciki-ciki. "Fadila nazo gani". Ta faɗa tana daga tsaye, domin bata jin ko zama zata iya yi. "Wacece haka"? Aunty ta tambaye ta itama. Ganin kamar abun dai za'ayi yasa ta ce "Ban zo nan da nufin faɗa ko wani abu ba, ƴa ta nazo gani, ban san mai kuke nufi da ni ba, ɗan uwanku ya aure ni, kun sa ya sake ni to ba shikenan ba, mai yasa kuke son shiga tsakanina da ɗiyata mai nayi muku?" Ta ƙarasa da karfin ta domin dai har ga Allah bata kuma san mai tai musu ba, ina ce dai ta rabu da ɗan uwan nasu, ba sai su rabu da ita ba. Aunty ta ce "Kina son sanin dalilin da yasa ba zamu bari ki ga Fadila ba?" Azima ta ce "Bama gani ba, har ɗaukarta sai nayi ta dawo gare ni, ai yanzu ina da aure, ina da ikon da zan dauke ta, idan a baya kunce bani da ikon ɗaukarta". Tana rufe baki ta ce "Karya kike yar iska karuwa kawai, ke a tunaninki duk bamu san irin yawon ta zubar ɗin da kike yi bane, wato mu baki ƴarmu itama ki koya mata bariki irin naki, to wallahi baki isa ba, keda Fadila sai dai ko idan ta girma tayi aure lokacin tasan hankalin kanta, ba yanzu da tana yarinya ki cusa mata wannan banzar ɗabiyar da kika gado daga gurin taki uwar kike son gogawa tamu ƴar ba, wallahi tur da irin halinki". Anty ta ƙarasa tana barin falon. Azima da Sadiya suka bita da kallo har ta shige daki. Take hawaye suka zubowa Azima tana jin yadda kirjinta ke hawa da sauƙa. Karuwanci fa, kuma ita, sannan wai ita ce zata koyawa ƴarta, kuma wai ta gada a gurin tata uwar, innalillahi wa innalillahi raji'un kawai ta iya furtawa ta kasa ko bin bayan ta. Bata san lokacin da ta zauna a palon ba tana zubar da hawaye mai raɗaɗi ba. Sadiya ce ta riƙo ta har wajen mota itama tana kuka domin maganar ta taɓa su. Ta shiga ta tada motar suka koma gida babu wacce ta iya magana. Sosai ranar take ta kuka ta rasa mai ya dace tayi, kenan kallon da ake mata a gari kenan, kuma haka ake faɗawa Fadila a kanta cewar ita karuwa ce. Take wani tunani ya faɗo Mata. Bata san lokacin da ta miƙe tsaye ta nufi waje daga ita sai doguwar riga, kanta babu ko dankwali ta shiga mota. Bata tsaya a ko'ina ba sai gida. Har zata shiga sai kuma ta sake shawara, bai kamata Hajiya tasan abun da zata yi ba, duk da tasan ko da ta sani ma ko ta hana ta ba zata hannu ba wallahi. Haka ta koma gida ta dauki waya ta nemo number Kamal, wanda tunda ya tafi sau ɗaya sukayi waya. Har ta katse bai ɗaga ba, ta sake kira tana ji a ranta dole nema ta nuna musu cewar da da yanzu ba ɗaya bane. Sai da ta kusa katsewa Kafin ya daga da sallama. Sai kawai ta fashe masa da kuka mai jiniya. Take ha hankalinsa ya tashi, ya shiga tambayr abun da ya faru. Sosai take kuka ta ce masa kawai yazo Nigeria a cikin satin nan a kwai matsala. Duk da yana da aiki haka ya bar komai, kwana uku sai gashi a Nigeria da wata sabuwar motar irin tasa ta gida amma color daban. Acikin kwana ukun nan babu wanda yasan halin da take ciki, kuma babu inda ta fita, daga kuka sai kuka tana tauna abun da Anty tai mata.
Tarba mai kyau ya samu daga gareta, wanda yaji dad'i, ta bashi haɗin kai da kulawa domin tana so yayi mata aiki. Bayan Komai ya wakana ne ta zaiyana masa abun dake faruwa. Bayan ya gama ji yace to yanzu mai take so ayi. Ta ce "Ina so ne na shigar dasu ƙara domin ina so na dinga ganin ƴata a kusa dani, har ma tana zuwa yin wasu kwanaki tunda yanzu ina da aure, kuma ni ɗaya ce a gidan nan. Ai kuwa take ya kama mata, ta shigar da kara kuma ya daukar mata babban lauya. Musa baya gari amma sakon kotu ya riske shi haka dole ya dawo. A lokacin da labari ya isa cikin gida kuwa kowa ya shiga mamakin abun da Azima tayi, mai yasa ba zata kawo maganar gida ayi hukunci ba, shi kansa baba Mato bai ji daɗin abun da tayi ba, haka Hajiya ma sai da ciwonta ya tashi tsabar damuwa da tashin hankalin wannan abun, mai Azima take son zama ne, ta rasa wanda zata kai kotu sai dangin ubanta akan yarinya. Kowa yazo ita yake jefawa da magana akan cewar ta bar yarinya ta lalace tafi ƙarfin kowa, bayan ta gama yawon banza da sunan karatu, shine yanzu take son ɓata zumunci, to wallahi tayi kaɗan, kuma zasu ci ubanta a matsayin su na yayyanta. Har gida Maryam tazo a matsayin ta ta yayarta, akan ta janye ƙarar nan saboda zata bata zumunci. Azima ta kalleta sama da ƙasa, wannan ne karo na biyu da tazo gidan ta, zuwan farko lokacin sunan Fadila a gidan Musa, sai yau da tazo a matsayin yaya. Ta ce "Na janye kara inji wa?" Ta tambaye da rainin hankali. Maryam ta ce "Kin dai san baki fi karfin kowa ba ko? Kuma ki sani akan ki dai ke ɗin banza ba za'a raba zumunci ba, dan haka ki dai ki janye ko kisha mamaki". "To ba zan zanye ba, insha mamakin Maryam". karshe abun da faɗa aka rabu harda zage-zagen Iyaye, ita tana zagin Hajiya ita kuma Ammy,. Kaf family babu wanda ya isa Azima ta saurare shi, duk wanda yazo gida kuwa da faɗa suke rabuwa duk girman sa domin har ce musu takeyi wallahi ko Hajiya bata isa ta iya hana ta ba. Wallahi har wani tsoro tsoranta suka fara ji yadda take magana da ihu Kamar ba yayyanta ba.
Nan kuwa aka fara shari'a, zaman farko koto ta tabbatar da cewar tunda har tana da aure to shari'a ta bata dama tadinga zuwa gidanta, babu yadda za'ayi a raba ƴa da uwa koda kuwa meye dalili. Saboda haka kotu ta bawa Azima damar zuwa taga yarta a duk lokacin da taso, kuma ta bata damar ta ɗauketa tayi mata hutu na wani lokaci. Daga haka zaman kotu ya ƙare, ai kuwa a ranar taje har gidan ta dauko Fadila, wacce Itama take ta murna da ganin mamar tata, kowa ya sake ja baya da ita, yan uwa na tai mata tofin alatsine amma ko a jikinta, damuwarta kawai Hajiya ce, idan har ita ta saƙƙo to uban kowa ma kar ya hakura har gaba da abada.
A cikin satin ne kuma alhajinta ya dawo daga tafiya. Tashin hankali wanda ba'a saka masa rana, gashi kuma Kamal baya gida, domin ana gama shari'ar ya koma abunsa. Idan bata manta ba tayi blocking ɗin tsohon nan fa, amma shine ya kirata da wata number. Ta cikin wayar ya ce "Gamu a kofar gidan ki muda ƙawarki". Yana faɗa ya kashe wayar. Idan batayi karya ba cikin fushi yayi maganar wanda bai taɓa mata haka ba, to wacce kawa, ba dai Salma. Hankalinta ne ya ƙara tashi jin tare suke da kawa kenan dai yasan komai, ai kuwa ya zama dole ne taje koma mai yake takama da ita tana daidai da shi, aure ne dai ta riga tayi, idan kuma zai sake auranta ne tom ta zama matar Maza biyu to Bismillahi. Bayan tasa mai gadi ya buɗe musu ƙofa sun shigo ne ta tsaya a harabar fuskar nan tamau, jira kawai take taga da mai yazo kafin ta fara buɗe masa shafi-shafi na halinta wanda ta ɓoye masa. Sadiya ce ta fara fitowa sai drebansa ya fito ya buɗe masa. A hankali ta sauke ajiyar zuciya, ashe ƙanwa yace ba ƙawa ba, tayi tunanin ai Salma ce ta kawo shi. Suka ƙaraso har gabanta, a hankali ta gaida shi ya amsa yana kallonta fuskarsa a haɗe. Ya ce "Azima aure kikayi ban sani ba? Sannan kikayi blocking ɗina bayan alƙawarin dake tsakanin mu, a tunaninki idan kin yaudari wasu kin tsira ni zaki iya yaudara ta ne?" Ya faɗa da muryarsa mara hayaniya cike da sanyi. Zatayi magana ya daga mata hannu ya ɗora da faɗin "Kin bani mamaki, kuma na baki nan da sati ɗaya ki rabu da wannan mutumin zan aure ki, na faɗa miki, idan kuma kika ƙi na rantse miki da Allah sai kin auri maza biyu a lokaci guda, na faɗa miki, domin ni Alhaji Audu bana wasa, kuma bana saɓa alƙawari, yanzu haka daga gidan ku nake, itama Hajiya na tuna mata alkawarin da aka yi a gabanta, kuma wallahi sai an cika shi koda kuwa mutuwa kikayi sai an daure kin tafi da aure na cikin ƙabarin ki". Yana faɗa ya juya ya bar gurin ya shiga mota dreba ya jashi suka ƙara gaba. Duk yadda Azima ta kai da son yin magana wannan mutumin ya shayar da ita madarar mamaki, baki a buɗe har ya bar gidan kafin ta rufe bakin tana kallon Sadiya da itama bakin ta buɗe jin wata lukutar masifa daga sama. Sadiya tace "Kinga irin tashin hankalin da yaje yayi a gurin Hajiya, gashi dai ɗan banza maganar sa babu ihu amma ceke take da fushi da kaushi, tsaf zai aikata abun da yace wallahi, ni dai Allah na tsorata Anty". Azima ta sauke ajiyar zuciya ta juya ta koma cikin gidan ba tare da tace Komai ba. Guri ta samu ta zauna, sai kuma ta miƙe ta ɗan fara zagawa, sai ta sake zama, amma ta sake mikewa kamar ko mutuwa tayi sai an ɗaura auren ta tafi da auransa ƙabari. Da karfi tace "Amma dai wannan tsohon anyi Tsinnanne mara mutunci wallahi, sai kace ba musulmi ba, a ina aka taɓa yin aure biyu da har yake alfahari da hakan, kuma ni saboda bani da hankali sai na yarda na aure shi, kai wallahi bai isa ba, duk abun da zaiyi yazo yayi, ya dade bai aure ni da wani auran ba, bai san wacece Azima ba, ko dan ban taɓa nuna masa ɗaya bangaren bane ko". Sadiya ta ce "A'a fa Anty, wannan mutumin yana da gaskiya, ko kotu aka je yasin shi za'a bawa gaskiya, gara kawai kisan yadda zakiyi ki kashe wannan auran ba tare da shi Yay Kamal ɗin ya sani ba, idan yaso sai ki auri wannan ɗin kawai". Azima tai mata wani irin harara na baki da hankali. Ta ce "Shikenan kuma ni sai na zama sarkin aure-aure kamar wata lalacecciya ko". "To ai kamawa tayi, kuma nima mafita ce, ko so kike sai kowa yasan abun dake faruwa ne?....📝
Lamari fa ya sauyawa wa Azima, ko zata auri mata biyu ko kuma zata rabu da Kamal?
please comment da shering ɗin ku ke sa na fahimci kuna jin daɗin labarin.