Episode 1
by @zahraroyal
GIDAN YAWA
By
Zahra Royal Star
Wannan Labari da gaske ya faru dan haka Komi Ka gani na b’acin rai ko kasin haka da gaske ne ya faru badaga ni bane, zanan k’addarar su ne yazo a hakan nayi ra’ayin sauya garuruwa da sunan mutane dan haka ina fatan za’a bini a hankali domin cimma gacin wannan labarin
Episode 1
Tsokaci
Rayuwa a gidan yawa ba koyaushe take kasancewa cikin farin ciki ba. Wasu lokuta, wurin ne ake fuskantar kalubale, tsana, hassada da gwagwarmayar rayuwa.
A cikin littafin GIDAN YAWA, za ku karanta labarin wata mata da mijinta da suka tsinci kansu cikin mawuyacin hali na talauci yayin da suke zaune tare da ‘yan’uwa a gida daya. Maimakon su samu tausayi da goyon baya, sai suka fuskanci tsangwama, cin zarafi da karan tsana daga na kusa da su.
Yayin da rayuwa ta yi musu tsauri, suka ci gaba da hakuri da juriya. Amma kaddara ta sauya alkiblar rayuwarsu lokacin da Allah Ya bude wa mijin kofar arziki. Sai dai arzikin da ya kamata ya zama mafita, ya zama sabon jarabawa. Sabbin sauye-sauye suka fara bayyana, zuciyoyi suka canza, alkawura suka fara dusashewa, kuma soyayyar da ta hada su ta fara fuskantar kalubale.
Shin arzikin zai hada kan iyalin ne ko kuwa zai raba su? Mene ne makomar matar da ta tsaya tare da mijinta a lokacin wahala? Kuma me zai faru lokacin da sabon aure ya shiga cikin rayuwarsu?.
Domin gano amsoshin wadannan tambayoyi masu cike da darasi, tausayi, soyayya, haushi da rudani, ku biyo mu cikin shafukan GIDAN YAWA.
TALLAH TALLAH TALLAH
RC: 8578922
RABEJI
TRAVELS AND GEN. CONTRACTS LTD.
Connecting worlds, Building futures.
IATA Accredited Agent
NANTA
QATAR AIRWAYS القطرية
aero taking you safely
AIR PEACE ...your peace, our goal
MaxAir
SAUDIA السعودية
TURKISH AIRLINES
Kenya Airways The Pride of Africa
EGYPTAIR
AWA AFRICA WORLD AIRLINES
TRAVEL & TOURS
- Visa Facilitation
- Ticketing/Reservation
- Hajj/Umrah Packages
- Packaged Tours/Cruise
- Hotel Booking
- Chartered Flight
- Honeymoon Planning
- Car Hired Services Home and Abroad
- International Universities Admission & Facilitation
- Consultancy Services
OTHER SERVICES
- Furniture Making
- General Farming
- Properties and Real Estate
- Import and Export
- General Registration
- General Contracts
- Clearing and Forwarding
- Food and beverages
Office Address:
Office No.6 Centro Plaza Buk Road Kano
Email:
***
Phone:
***
***
Unguwar Yammawa, Rimaye Kankia Local Government Katsina state Nigeria
Mafari……….. Gida ne babban gaske irin na talakawa sana ginin k’asa ne irin na zamanin da d’in nan. Akwai b’angare-b’angare a cikin gidan wasu sassa na gidan an zagayesu da ginin bulo da bulo wasu kuwa b’angaren an shafe da suminti hatta tsakar gidan k’asa ce kwance. Ak’alla sassa na gidan zasu kai shidda zuwa biyar kuma kowanne lungu da sak’o d’akuna ne reras a ciki.
Iska ce mai karfi ke tasowa, sakamakon hadarin da yayima sama kawanya. Garin yayi bak’ik’k’irin alamar koda Yaushe ruwa na iya sakkowa. Iska ce mai hade da k’ura ke tasowa tana bud’e ma mutane ido, da yawan jama’a gudu suke zuwa gidajensu, Saboda ita kanta iskar abar gudu ce yadda take tashi da karfin gaske.
A tsaye take kofar dakinta tana kallon yadda sararin samaniya ke sake rinewa, garin yayi duhu sosai Saboda gabatuwar mangaruba ya k’ara sama garin yin duhu sosai, iska mai karfe had’e da walkiya da rugugin hadari ne kawai kake ji. Sauke ajiyar zuciya tayi wacce tayi ta tafi a k’irga. Zuciyarta cike da tsoron sakkowar ruwan nan badan komai ba sai dan yadda dakin nasu ke zubar da ruwa, kwana suke a tsaye mudun dai ana ruwan sama.
Wani yaro ne yazo giftawa zai wuce naso dakin tayi saurin cewa.
“Usman ina Babawo yake?”
Wani kallo ya bita dashi kamar bazai amsa ba sai kuma yana tafiya ya ce.
“Yana can waje suna fada da wasu yara”
Bai tsaya jin mi zata ce ba yayi gaba abunsa ya shige lungunsu.
Girgiza kai tayi tana idasa shigewa cikin dakin nasu tana iya jiyo yadda rufin dakin ke wata irin kara ta iskar dake kad’ashi kamar zai cire daga saman d’akin.
Wani mayafi ta dauka tana sauke lumfashi a hankali take takawa Saboda k’aramin cikin dake jikinta daya fara girma. A hankali take tafiya Saboda iskar da akeyi mai k’arfi mai had’e da k’ura sosai.
“Ke kam Binta ina zaki je haka cikin hadari ga iska?”
Dan tsayawa tayi yana rufe idonta sakamakon iskar da ake tayi har lokacin ta ce.
“Wallahi Dije zanje waje ne na duba Babawo, kowanne yaro na tahowa gida amma shi banda shi?”
Tabe baki Dije tayi bata sake cewa komai ba sai binta da kallo da tayi harta fice daga cikin gidan.
“Kai kai kai miye haka Babawo kuke yi?”
Tashi yayi da sauri daga jikin yaron da suke fada dashi yana hakki kamar wadda yayi gudun tsere yana cewa.
“Mama ba shine ya fara jana ba”
“Daya fara janka saika kamashi da wannan dukan haka?. Kai Yanzu duk bakaga wannan hadarin ba hakan baisa ka taho gida ba kamar ko wanne yaro ko?’ Wato kai dai bazaka daina sani magana ba?, ace kai sai zuciya kawai Ka sani Wato ko?”
Babawon da bai wuce shekaru 13 a duniya ba, yana da jiki kadan ya dube ta da kayan jikinsa da duk sukai k’ura zaiyi magana ta kamo hannunsa tana cewa.
“Wuce gida na ce”
Sumi-sumi ya wuce ta yana jin yaron daya buga yana cewa.
“Kuma wallahi koba yau ba saina rama wallahi baka bigi banza ba, kuma Allah ya isa na”
Yadda kasan Babawon zai dawo ya rufesa da duka a yadda ya wani juyo yasa yaron faskawa da wani irin gudu yabar wajan.
Girgiza kai kawai Mama tayi ta bi bayansa zuwa cikin gidan nasu.
Kowa a gidan ya rufe k’ofarsa ba kowa a tsakar gidan.
“Mama ina Abba?”
“Bai dawo ba tunda suka tafi Katsina shida abokinsa amma nasan dai suna hanya”
“Mama yinwa nake ji”
Sauke lumfashi tayi tana fad’in
“Ko zaka je wajan Dije naga b’angaransu sunyi abinci d’azu idan anyi saura a sammaka”
“Mama yau ma ba abunda zakici ki kwanta a haka?”
Murmushin yak’e tayi tana shafa Kansa ta ce.
“Zanci mana d’an albarka kadai jeka Ka dawo”
Kamar zai tafi sai kuma ya tsaya yana sake dubanta ya ce.
“Amma Mama kinsan ko yayi saura bafa bamu zasuyi ba”
“Waya ce maka?”
“Hmm”
Kawai yaron ya fad’a yana yin hanyar waje.
Bayansa tabi da kallon tsananin tausayin kansu bare shi da yake yaro zata iya jure yinwa ita da Abbansa amma shifa?.
Babawo yana fita iskar Yanzu ta d’an lafa sai yayyafin da aka fara kad’an-kad’an, ya nufi wajan d’akin Inna Dije harsun turo k’ofa saboda iskar da akeyi.
Hannu yasa ya d’an buga kofar an dauki lokaci kamin Abu ya bud’e masa yana masa wani kallon tsana.
“Kai lafiya zaka zo ma mutane k’ofar d’aki?”
Babawo bai damu ba ya ce.
“Dama Mama ce ta ce idan kunyi sauran abinci dan Allah a bani”
Abu zaiyi magana Inna Dije ta fito tana cewa.
“Wai wannan wane irin abu ne haka an hana mutane su huta?, shi uban naka yana ina da bai kawo maku ba?, ance kuma kullum ni ce mai baku abinci dan rainin wayo?”
Wata irin zuciya ce tazo ma Babawo a wuya, amma baice komai ba ya juya zai tafi sai yaji Abu na cewa.
“Ga wani nan marassa zuciya saika d’auka”
Babawo bai juya bai kuma yi magana ba ya nufi d’akinsu, Inna Dije ta saki baki Tana cewa.
“Ahhh kai kuji min yaro da bak’ar zuciya?, kai idan banda abunka ina kai ina zuciya baka dashi baka ba wani ajiya ba?, yo aikin banza kai cinye abincinka zuciyar ma taci abunta”
Inna Dije ta kare maganar tana komawa d’akinta had’e da sakin tsaki mai k’arfi……….