BARRISTER SUHAIL

38

by @officialkhadeey

🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾

Mallakar

KHADIJA WRITES

YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)


💖 Dedicated To My Mom 💖


بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

🅿️-----38


yana barin dakin iman ya koma part din Zeenah zaune take a falo tana danna waya kamar ba ita bace ta aikata abinda ya faru yanzu ba 

kan kujera ya zauna 

"zeenah miya kai ki dakin iman"

"babe naje mata gargadi akan kar sa ke maka girki in ba ranar kwanan taba"

"but why the insult" 

kallon mamaki take masa ganin kamar ya damu akan abinda yayi "babe ko ka fara san tane?" shine tambayar da ta masa 

"zeenah ba wai maganar ina son ta ba ko bana son ta you are all my wives kuma Dukkanin kuna da haƙƙi a kaina infact idan da kin dafa min da kanki ai banje wajen ta ta bani ba ko"


"kayi hakuri bazan kara ba"
hannun sa ta kama kamar wani karamin yaro "babe mu shiga ciki bacci nake ji"

haka ya bita Tamkar wani raƙumi da akala washe gari bai samu fita sallar Asubah a daki ya jasu tare da zeenah wanda sai da yayi mata jan ido kafin ta yarda ta bisa sallan 

suna ganawa ta koma kan gado tana hamma alamun bacci bai isheta suhail ya ce"zeenah bazaki je ki hada breakfast ba ,na faɗa maki yau zan koma office"

baki ta turo ta ce"babe ni gaskiya bazan shiga Kitchen ba ko na shiga ma ban san mai zan girka ba ko tafasa ruwan zafi ban iya ba idan kuma so kake na kone sai na dafa maka"

"amman zeenah haka zamu cigaba da zama ace duk ranar girkin ki sai dai muci Abincin resturant"

Zeenah ta ce"kar ka damu babe anjima za kira mummy ta samo mana mai aiki sai ta rinƙa girkawa shikenan ko"

kai ya jinjina a ransa ya ce"zeenah wata irin mata ce ita ba abinda ta sani a harkar auratayya banda kullum taji sa a jikin ta ita da ko gajiya ma batayi"

ransa a bace ya fita ya koma part dinsa wanka yai ya shirya kansa cikin wata farar suit mai gajeran hannu yayi kyau sossai ko ya fito daga ɗakin ya kalli kofar dakin Iman yana so ya shiga amman ya ƙasa haka kawai yaji baya san hada ido da ita 

bai kara bi ta Dakin zeenah ba yayi wucewar sa sai da ya biya ta wani gidan Abinci dake kan hanyar sa yayi breakfast daga bisani ya wuce office.

iman na kwance akan gado taji alamun kamar ana bude gate bata sake tabbatarwa ba sai da ta leka taga Suhail ne ke bita da mota tana tsaye bakin taga har ya gama  fita da motan.

koma wa tayi baƙin gado ta zauna hawaye taji ya fara sauko mata wanda ita kanta basan na  minene ba karin Farko tun bayan auren su da Suhail ya fita ba tare da ya duba lafiyar taba 

ji tayi gaba zaman gidan ya ishe ta kamar ta tari Suhail ta ce ya sake ta ta koma gidan su 

"Ta san cewa Musulunci bai so mace ta nemi saki ba tare da dalili ba, amma zuciyarta ta kai wani matsayi da take jin zaman gidan yana ƙara mata ciwo a zuciyar ta" 

Alqur'ani ta dauko ta fara karantawa cike da natsuwa a hankali ta fara jin damuwar ta na ragewa bayan ta gama ta ajiye Alqur'anin kallon agogon dakin tayi ganin karfe goma ta fita zuwa Kitchen dan samawa kanta abinda zataji 

tea da egg kawai ta iya haɗawa ta koma daki 

a haka har aka shafe sati guda ba tare da iman ta saka suhail a idon ta ba tun abin na damunta har ta fara hakura idan yana gidan haka  ta ke kulle kanta a daki har sai ya fita kafin ta ke  fita ta daura girki duk da ma abincin baci take ba tasha kwana da yunwa madara da milo ta dauko ta kawo bedroom din ta take sha idan zata kwanta 

tun a shekaran jiya ya kamata ta amshi girki amman gaba daya ya tare dakin zeenah sai da ta jiyo Maganar su daga daki

kullum cikin sallah da karatun Alkur'ani take ba dare ba rana tana rokon Allah ya kawo mata maganin damuwar ta  kamar yadda har zuciyar da ranta,take yafe wa suhail  tana jin tsoron Allah ya tambayi Suhail a ranar gobe kiyama kan haƙƙin da bai cika mata ba"


a haka sai da akayi sati ukku  gam Suhail bai ya leƙa dakin iman ba duk da lokaci zuwa lokaci  take fado masa a rai da ya nufi hanyar dakin sai yaji kamar an ce ya koma 

washe garin ranar suhail na fita office zeenah ta kira yusrah 

yusrah ta ce"Zeenah ya magungunan ina fata suna aiki yadda ya kamata"

murmushin mugunta tayi ta ce"yusrah ai ba Abinda zai hana na kara ma malamin nan kudi aiki kamar yanka wuƙa yanzu ko Maganar ta ma Suhail bayayi  har na manta rabon da ƙafarsa ta taka dakin ta"

dariya yusrah tayi ta ce"ai na faɗa maki,ki kwantar da hankali yanzu sai ki turo abinda za'a kai masa amso wasu sabbi kuma"

"okay zan tura naki dubu dari biyar sai ki basa"

yusrah na ajiye wayar ta harari gefen ta  hmmm zeenah kenan a tunanin ki zan kai mishi kudin nan ku cigaba da cutar yarinya bata ji bata gani ba nima zan cigaba da kwasar rabona har zuwa Ranar da zaki gane babu wani boko ko malam da zai maka abinda Allah bai maka ba.

Ammi ce zaune dakin malan tana yi masa bayanin mafarkin Iman da take yawan yi duk cikin kwanakin nan 

Ammi ta ce"Malan na roke ka ka barni naje naga halin da ƴata take cikin"

ajiyar zuciya malan ya sauke ya ce"Maryama ba wai na hanaki kije wajen khadija bane ki tuna yanzu ba ita kadai bace ina ganin zuwanki ba bazai zama maslaha ba kamar yadda nake fada maki zan cigaba da addu'a komi zaizo da sauki in sha Allah"

Ammi ta goge kwallar dake fitowa daga idanun ta ce"To shikenan Malan”

Tun ranar Malan ya mai da hankali sosai wajen yiwa iman addu'a Ammi Mutanen da Allah ke haskaka masu abinda ke faruwa ta hanyar mafarki hakan yasa bai dauki maganar da wasa ba 

yau sati hudu kenan rabon da Iman ta ga Suhail har ta hakura dashi harkan gaban kawai take yi 

daren ranar tana kwance akan gado tana game wanda a Yanzu shi kadai ke debe mata kewa da mamaki taji an turo dakin har ta manta rabon da taga wani ya shigo dakin 

daga kan da zatayi taga suhail ne sanye da wata brown din jallabiya yana tahowa a iya kwanakin da tayi bata gansa taga duk ya chanza yayi sanyi 

da kyar ya karaso cikin dakin wani irin kunya da nauyin iman ya cika idanun sa ya rasa ta indai bai bata haƙuri ya kuma roke ta yafiyar kwananta daya dauka ya ba Zeenah 

zama yayi bakin gadon Iman bata fasa abinda take ba kusan minti goma ganin baida niyyar fita kuma ba magana zai ba iman ta tashi ta dauki hijabin zata koma falo

da sauri ya rike hannun juyowa tayi ta fige hannun ta daga kansa zata fita ya riga kaiwa bakin kofar ya kulle ya saka key din jikin aljihun sa 

a fusace ta ce"Suhail ka bude min kofa"

kafe ta yayi da ido 

tsawa tayi masa ta ce"Suhail nace ka buɗe min daki"

"iman bazan bude maki har sai kin sauraren ni"

Yana tsaye bakin ƙofar yana kalon ta zuciyarsa na bugawa karin farko a Rayuwar da ya ji yana kunyar hada ido da wata mace wani irin nauyi yake ji 

tabbas yanzu ya gane babu wata soyayya tsakanin shi  da iman girmamawa ce da kuma mutuntawa  kawai a matsayin ta na matar da mahaifinsa ya aura masa