MURADIN ZUCI

Muradin zuci

by @bintuuu

Washegari tun da lokacin sallahn asuba yayi Papa ya kwankwasa dakin su Habiban dan jin lafiyan yanda suka kwana. Bayan ta bude sai ta sunkuya ta fara gaisheshi cikin ladabi sannan ta fito daga dakin domin bashi guri, da ya amsa mata sai ya shiga cikin dakin direct ya nufi gadon inda Babyn ke kwance tareda Jidda, bacci ya samu tanayi kamar ba ita ta tada musu hankali jiya da kuka ba, sai ya maida towel din ya rufe tareda gyarawa Jidda duvet dinda take lullube itama sannan ya juya ya fice daga dakin. A falon ya tadda Habiban tana jiran fitowansa sai yace "Ya cikin nata?" kai a duqe tace "Da sauki, bata sake wani kukan ba ranka shi dade" ya gyada kai sannan ya nufi upstairs gurin 'yan samarin yaran nasu. Tare da twins din yayi sallah anan falon suna biye dashi ya jagoranci sallahn dalilin rashin yawaitan masallatai a kasar a wannan shekarun. Har Habiba ta gama hada breakfast Momma bata fito ba, da Papan ya leqata ya mata magana ma bata kulasa ba sai ya dawo dinning area din suka cigaba da cin abincin da yaransa wanda suma a daddare suka gaisa da mahaifiyar tasu a wannan safiyar. 

Habiba dai ita take tsaka mai wuya, fushin Momma uwargijiyar tata take tsoro matuqa gashi tasan ko giyar wake tasha bazata tsallake maganar Papa ba. To wa ya isa ya tsallake magana ko umarnin Yarima mai jiran gado bayan sarki Abdulfatah, sahun giwa ne ya taka na raqumi shiyasa babu yanda ta iya ta amshi kulawan jinjirar ta hada da aikinta na kula da uwargijiyar ta da tazo yi takanas a qasar.

Da Papa ya shirya fita gurin aiki ne Habiban ta sake tuna masa batun tufafin Babyn sannan ya sake shiga dakin dan dubota, nan ma ya samu ta koma wani baccin bayan Habiba ta bata madaran tasha kadan. Duqawa yayi idonsa akanta zuciyarsa na qara karyewa, sai ya kai hannu ya kama qananun fingers dinta duk bata motsa ba, wani irin nauyi yaji zuciyarsa nayi akanta, what a cruel world! This beautiful innocent child didn't deserve this, wane mara imanin ne zai yasar da wannan yarinya?.. Da wannan maganganun zucin ya miqe cikin sanyin jiki sai twins suka shigo dakin Imran na gaba suka qaraso bakin gadon suna kallonta. Sai Imran ya hau gadon ya kai hannu yana taba fuskanta yace "Papa bacci take har yanzu?" ya gyada kai yanajin nauyin yin maganan kar suga gazawarsa, sai ya juya yana kallon Imam ganin ya tsaya dan nesa da gadon idonsa quri akan babyn baice komai ba, dan murmushi Papan yayi sannan yace "Daga nan zaka gaisa da ita kuma Imam?" sai ya girgiza kai ya qaraso bakin gadon amma bai hau ba, cikin nutsuwarsa da ta zame masa jiki dukda yarintarsa yace "Papa ya cikin nata?" sai Papan ya amsa da "Ta samu sauqin, gashi har baccin ta takeyi ma" ya gyada kai bai sake cewa komai ba sai Imran dinne yake wasa da hannunta suna magana da Papan, sai da suka dauki lokaci a dakin sannan suka fice while Papan yayi kiran Habiba dake wajen Momma, bayan ta fito a hanzarce yace mata "Kayan sakawa ne kadai ya saura acikin abubuwan da take da buqatan ko?" tace "Eh ranka shi dade, da dai mayukan yara irin wanda kuka siyo kwanaki da Gimbiya" ya gyada kai sannan ya dauki qaramar jakansa dake dauke da takardun da zai buqata a wajen aikin nasa sannan ya sake leqawa dakin matar tasa suyi sallama. Tana hakimce a bakin gadon hannunta riqe da plate Habiban ta kawo mata nata breakfast din, ganinsa yasa jidda baro gurin mahaifiyarta ta qaraso garesa tana maqalqale kafansa, sai yayi murmushi tareda shafa kanta yace "Where is my little pumpkin?" tana dariya tace "Mee Papa" da haka suka qarasa gurin Momman da idanunta ke kan plate din bata dago ba har sannan, saida ya zauna a kusa da ita ya umarci jidda da taje gurin yayunta sannan ya sake maida hankali gareta yace "How are you feeling?" a nutse tace "Na dauka samun 'yar tsintuwar yasa ka mantawa dani da kuma jininka dake jikina" madadin ya nuna haushin kalaman nata sai ya danne tareda dan yin murmushi yace "Jiya kadai dan ban bi abunda kikeso ba yaci ki zamo me fahimta ta Fatima, i thought ko bance ki kula da ita ba ke me jin tausayin tane, cikin sanyin nan akayi dumping dinta batareda tausayi ba, menene nata aciki, sannan menene laifi na dan na nemi kulawa da ita, ke kanki kin sani babu yanda za'ayi in fitar da yarinyar nan waje a jiya, in kaita Ina? Haba Fatima, Ina imaninki ya tafi?" sai lokacin ta dago kai tana kallonsa, nan hawaye suka fara taruwa mata a Idanu sannan tace "Wato dan na nemi kare mutuncin ka shine rashin imani, yarinyar da kana gani kasan 'yar qazanta ce, wane irin maganganu kake son jawo mana da mutuncin ka, daraja da kuma kimarka?" nan kuma ransa ya fara baci yace "Kina gurin ne da aka sameta ta hanyar qazantar, wai me yake damunki ne Fatima, da kike maganar kima da daraja kina tsammanin mahaifan nawa zasuyi alfahari da cewar na yardar da yarinyar ba tareda na bata shelter bane?" Tayi shiru bata basa amsa ba sai ya sake cewa  "Zan zamo jagora bisa mulkin iyayena da kakanni da zan karbi ragama kuma ace tun yanzu bazan iya kwatanta jinqai ba me na zamo kenan? will you be proud of that man?" nan ma tayi shiru batace komai ba, sauqe numfashi yayi sai ya nutsar da muryarsa wannan karon cikin lallashi ya kuma fadin "Ki tayani mu samu ladanta koda na qanqanin lokaci ne Fatima, tunda baki amince da mu riqetan ba zan samo mafita tunda wannan ba qaramin case bane a qasar nan. But before that, please ki ban hadin kai mu kula da baiwar Allahn nan, gidaje dayawa acikin estate dinnan amma sai Allah ya kawota garemu, bamu san me ya boye a cikin lamarin nan ba" ta gyada kai nan ma bata amsa ba sannan ta cigaba da cin abincinta, ganin tayi shiru yasa shi yi mata sallama tareda miqewa ya nufi kofa ta bisa da kallo sannan ta dan tabe baki tana qara hade fuska.

Papa bai dawo gidan ba sai karfe sha daya na safen ya shigo gidan hannunsa niqi niqi da kaya. A dan gigice ya shigo falon sanadin jiyo kukan Fadwa da yayi tun kafin ya bude kofan, sai ya samu su Imam da Imran din tsaye a dan nesa da dakin da Fadwan ke kwance tana ta tsala ihu sun kasa shiga ciki. Da sauri ya ajiye kayan akan table sannan ya nufi dakin ya shiga nan ya sameta har fuskar nan tata tayi jaa abunka da farin fata, cikin hanzari ya dauketa dalilin wani irin tausayi da ta basa ya dorata a kafadansa ya hau jijjaga ta, baiwar Allah sai ta tsaida kukan ta fara ajiyan zuciya jin ta ajikin mutum, sai ya juyo yana kallon twins da suke kallonsa a bakin kofan, idon Imran tsuru tsuru dayake yafi dan'uwansa Imam din tsoro a tarin lokuta, da sauri yayi magana ganin yanda baban nasu ke kallonsu "Momma tace kar mu shiga" ya sake cewa "Imam ya shiga ta dakeshi" sai Papan ya kalli Imam din da ya sunkuyar da kai baice komai ba, da haka ya fito ya wucesu yana kiran Habiban, da saurinta ta fito daga dakin Momman tana sunkuyar da kai jikinta na dan rawa na sanin me tayi, amma kuma ba laifinta bane tunda itama uwar dakin nata ce ta umarceta da tayi mata wasu ayyukan tabar yarinyar, ganin yanda take a tsoracen sai Papa ya fahimci wani abu, ya fara kokarin danne bacin ran nasa yace "Ya kika barta tana kuka, bayan na bar miki kulawanta" da sauri tace "Ka gafarceni yallabai, hakan bazai sake faruwa ba" sai ya gyada kai tareda sauqo da Fadwan daga kafansa yana kallon yanda ta fara kokarin komawa bacci, ya miqota ga Habiban yace "Ki mata wanka, ga kayanta can na kawo, ki tabbatar ta qoshi sosai kafin ta koma baccin, banason abunda ya faru yau ya sake maimaituwa" jiki na bari Habiba ta amsa da "Kayi hakuri yallabai ka gafarceni, bazai sake faruwa ba" sannan ta miqe tareda karban Fadwan ta nufi dakin kwanan su da ita, da dan hanzari Imam ya dauki kayan da Papan ya siyo wa Fadwan yabi bayan Habiban Imran na biye dashi da wasu a hannu suka shige dakin dukansu. Sauke numfashi Papa yayi yanajin bacin ran abunda matar tasa ta aikata bayan ko awanni uku masu kyau ba'ayi ba ya gama neman alfarman tallafinta gurin kula da marainiyar Allah, sai ya girgiza kai kawai ya nufi dakin nata aransa yana tunanin yanda halinta ke sake banbanta a kullum sabanin yanda ya santa baya. 
Sai 12 ya shirya tafiya wajen aikinsa bayan ya tabbatar da Fadwan ta samu kulawan da take buqata sannan yayi sallama da iyalinsa ya fice, bayan ya gamo ayyukansa wajen 4 o'clock bai koma gida ba ya nufi gidan Abokinsa me suna Ladan dake living anan Houston din shima da familynsa, dan zuwa sannan duk tunanin da zeyi yayi akan lamarin nan and it's all leading him to one option, shine dole ya bada jinjira nan ga child services, dole yayi reporting ga police, duk yanda yake son yarinyar da kuma son samun ladanta dole haka zai hakura saboda jalala irinta matar da Allah ya hadasa da ita.


Free page 

Bayin Allah mun dawo wata tafiya banjiku a lounge section domin comments ba, Kunsan Bintun taku haka ne ke bata qwarin gwiwan rubutun 😍. Inason jin ra'ayinku akan wannan tafiya sosai.

Ayi Like, Follow da kuma comments fisabilillah, I lob u all 😍