RAYUWAR SAMHAD

RAYUWAR SAMHAD

by @maryamstar248


PAGE 7️⃣ TO8️⃣



_______________________________
بسم الله الرحمن الرحيم.



Tura ƙofar ɗakin da Samhad ke ciki Salma tayi tare da yin sallama ta shiga. 

Zaune take akan gado idanunta a lumshe tana karatun Alkur'anin, jin sallamar Salma ya sanya  ta buɗe manya fararen idanunta wanda suka ɗan faɗa saboda damuwa da kuma rashin lafiya. 

Amsa sallamar tayi tana sakarwa Salma  ƙaramin murmushi, Tunda ta zo gidan daji Salma ta kwanta mata arai sosai. 

"Antyah barka da safiya fatan kintashi lafiya? " Saukowa Samhad tayi tana sake mamakin halayar Salma, Sam bata da girman kai, agirma zata bawa Samhad kusan shekara 2 zuwa 3.

Katse tunanin tayi ta cewa 

"Ai kece Anty ba ni ba" Samhad tayi maganar cikin  yanayinta na sanyi. 

"A,a naƙi wayon gaskiya da gani kin girmeni nesa ba kusa ba kuma ko babu komai aike Antyna  ce tunda kina matsayin matar Yaya MUBEEN dole nabaki girmanki"

Cak numfashin Samhad ya tsaya na wucin gadi, maganar Salma tashiga yamutsawa cikin kwanyarta ta, so take mayi magana amma ta kasa. 

Ganin haka yasa Salma jan hannunta ta zaunar da ita kan gado tare da bude water bottle dake ajiye kan bedside ta bata. 

Amsar ruwan Samhad tayi tashiga sha babu ƙaƙautawa, Saida ta shanye tas sannan ta ajiye robar tana dauke ajiyar zuciya. 

"Salma intambaye ki? "

"Ki tanbayeni Anty Samha zan baki amsa". 

"Da gaske ni matar aure ce? "

Numfashi Salma ta sauke kafin cikin sanyi murya tace

"Da gaske ke matar aurece SAMHAD, ke matar Yaya Mubeen ce da aka ɗaura muku aure Shekaran Jiya  ranar juma'a bayan an sauko daga sallah". 

Salma wai ni miyasa rayuwa take garani kamar kwallon kafa, miyasa kullum rayuwa take sauyamin? Bana farin ciki kamar kowa, bana walwala kamar kowa, bansan miye farin ciki ba sede inga wasu Sunayi bade ni inyiba, dan Allah Salma ki gayamin idan akwai wani abu wanda nike yi ba daidai ba wallahi zan gyara, ina so inyi rayuwa kamar kowa, ina so inyi farin ciki kamar yanda kowa yakeyi. 

Matsanancin kukane ya sarke ta ya hanata ƙarasa maganar da takeyi. 


Kwantar da ita Salma tayi akan kafadar ta tana rarashin ta, itama zuciyarta a karye take jin irin maganganun da Samhad ke faɗi. 

Banko ƙifar yayi da k'arfi yana danne abinda ke yunƙuro mishi, 
Direct inda kinda Salma take ya nufa cikin tsawa yace bar nan ke. 

Rikicewa Salma tayi ta ajiye Samhad dake kwance a kafadar ta ta fice tare da janyo musu ƙofar. 


Cak ya dauki Samhad da ta tashi cikin yanayin firgici zata fice itama. 
ɗif numfashinta ya dauke kamin ta dawo daidai yayi mata masauki a faffaɗan ƙirjinsa. 

Wani yanayine wanda bata taɓa kasancewa cikin saba ta riski kanta, ji take zuciyarta na faɗa mata ta samu bango abin jingina ta samu mafaka ta samu inuwar da zata kare mata rana me tsananin zafi. 

Flash back. 


Tunda ya baro wajen da yaje neman Saniga ya bashi kwaya be samuba ya dawo gidan babu wanda yasan da shigowar dan bada mota ya shigo unguwar ba. 

Yanzu ya shigo cikin gidan ya tarar duk an hallara za'ayi break fast, Alla-Alla yake ya wuce yayi abinda zaiyi batare da kowa ya fahimci zuwanshi ba, Amma wannan munafukar Mammy ta riga data ganshi shine ta kirashi wai yazo ayi break fast dashi. 

Daddy ne yayi mishi garejen kallo tare da maida hankali ga tea da Mammy ta hada mishi. 

Tsaki Muneeb yaja tare da wucewa dan ɗaukar abinda ya kawoshi sashen. 

Karab kunnuwanshi suka jiyo mishi abinda Samhad ke faɗi shine ya tsaya jikin ƙofar yana saurarensu. 

Zuciyarshi ce ta hau tsuma jin kalaman  dake fitowa daga bakin yariyar. 
Dafe kanshi dake sarawa yayi yana Ambaton sunan ALLAH. Wato bada Amincewarta suka aura mishi itaba hasalima batasan da auren ba tunda gashi tana tambayar Salma da gaske anyi mata aure, 

Miyasa Daddy kullum yake goyon bayan waccan munafukar matar me fuska biyu, miyasa zata shigo da yarinyar da bataji bata gani ba cikin rayuwarsa, wannan game ɗin ita dashi suka fara bugashi miyasa zata dinga sako wanda basusan farkon yanda aka fara buga wasan ba??? 

Jin kukan Yarinyar yake har cin kasan zuciyarsa shiyasa yakasa daurewa ya shigo. 



Numfashi yaja tare da sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya tana shafa bayan ta don tasamu nutsuwa. 

Luf tayi a jikinsa tana shaƙar sanyaye ƙamshi tsadadden turarensa. 



Daga alkalamin maryam star⭐✍✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨