FreeArewaPen original
RAYUWAR SAMHAD
- 1views
- 65chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
HAUSA NOVELS WRITER
Sample · Zazzafan labari me ƙunshe da darasin rayuwa
𝑷𝑨𝑮𝑬1️⃣_________________________________بسم الله الرحمن الرحيم.Tsaye suke a kanta suna ta sheƙa dariya, ɗayar budurwar wadda take kusa da ita ta fara magana cikin dariya. "Ke yanzu baki da sauran amfani, a haka za ki ka ƙare rayuwarki a auren dan daba wanda ya addabi kowa, waya sani ma ko can wajen yawon iskancin da kika saba kuka hadu har ya biyo ki gida, mu de wallahi an cucemu ambata wa gidan mu suna, Allah kaɗai ya san in da abun kunyar da kika aikata yaje"" Nifa ba ma wannan ba Zee waifa Abba har wani fankama da tunkaho yake ya aurar da wannan borar. " Haka su ka saka ta a gaba suna ta ci mata mutunci, Duƙar da kanta ta yi ta na zubda hawaye masu zafi, A zuciyarta take cewa wannan wace kalar rayuwa ce? bata jin daɗi a wajen kowa ba ta da me sonta, babu wanda ya damu da ita, mai yasa Mahaifinta ze zama cikin masu yiwa rayuwarta illa, ta gaji da wannan rayuwar wadda babu komai acikinta sai bakin ciki da mutane masu son zuciya. Ɗago da kanta tayi jin abin da zee ke faɗa. "Samhad ke da jin daɗin duniya har abada, sai dai ki gani awajen wasu ki dauki wannan aure a matsayin 'kaddarar da za ta sadaki da mutuwa, gidan da za ki shiga ki 'dauƙe shi kamar kabari, don wallahi ina tabbatar miki daga yau ko in ce daga yanzu Kin yi bankwana da farin ciki sai dai kiga wasu nayi ba dai ke ba."Ta 'karashe maganar tana jefawa Samhad kallon tsana. Girgiza kai Samhad tayi cikin sheshshekar kuka tace "Nayi imani da ubangijina babu me kashewa ko rayawa sai shi, kuma dukan wani abu da zai sameni nayi imani daga shi ne, Anty Zee na riga na miƙa al,amarina a wajen Allah na san Allah yana sona tun da har yayoni mace kuma musulma, bari in tuna miki wani abu shi aure nufin Allah ne idan Allah ya nufeka da yin shi babu makawa sai kayi, wannan misali ne da ke, batun yanzu na san kina son kiyi aure ba na san ki na da buk'atar aure tun shekarun baya amma Allah be nufa kin yi ba, kin sha gorantamin cewa babu wanda ze aureni ahaka zan k'are rayuwata, kimmanta Allah shine ya ke tsara al,amurransa. Alhamdulillahi ko a haka aka tsaya naci riba dan na san na riga nayi gaba na barki a baya 'yar gata diyar so" ta karashe maganar tana sakarwa Zee murmurshi wanda ya sanya zuciyar Zee bugawa da k'arfin gaske. Kallon Zee Haneefa tayi tare da jan hanninta su kai waje, fitarsu babu jimawa Samhad ta fashe da matsanancin kuka wanda jikinta har girgiza yake tsabar kukan, A hankali takai hannunta wajen wani photo tana shafa kuskar wacce ke cikin photon tana murmurshi kamar za,a kirata ta amsa. "Ummanah farin cikina Ina kaunarki dan Allah ki dawo gareni ba zan iya jure rashin ki ba, rayuwar ta isheni haka nan wai kin san mai Abbu ya yi min? Auren dole Tatum in kuma auren cuta, Abbu ya cutar da rayuwata ba zan iya jure wannan...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.