Zazzafan labari me cike da ilimin rayuwa
PAGE 2️⃣6️⃣🌹2️⃣7️⃣
بسم الله الرحمن الرحيم.
Sallama Mamy ta yi wa Hajiya Turai tare da fiddo damen kuɗi ta ajiye mata tayi gaba abinta.
Sosai Hajiya Turai ta ji daɗin kuɗin dan dama ta na ta neman yanda za ta samu kuɗin ta je waken sabon bokan da ta yi wanda zai mata aiki akan Mamy, tunda Hajiy Turai ta kyalla ido ta ga yanda Mamy ke facaka da kuɗi ta ji ta kwaɗaita da su shiyasa ta ke bin Mamy sau da ƙafa kamin wa,adin da ta ɗibar mata ya cika.
A ɓangaren Samhad kuwa bayan sun kammala cin abinci su kayi zaman shiru, remote Mubeen ya ɗauka ya kunna musu kallo, sosai Samhad ta nutsu ta na kallon Indian film ɗin da ake haskawa mai kyau, da yake film ɗin na soyayya ne idan akazo wajen da star zaiyi wa budurwashi kiss ko ya rungume ta sai Samhad ta runtse ido da ƙarfi tana kame jikinta saboda tsananin kunya, ta na son kallo sosai amma sam a gidansu ba ta da lokacin yinshi dan kullum cikin aiki ta ke kamar inji.
Duk abinda ta ke Mubeen na lura da ita sosai ta bashi nishadi a yanda ta ke nuna jin kunyar ta a filli.
Waƙa aka saka actor ɗin sai rungumar budurwa ya ke su na rawa a tare, Sallati Samhad ta saki a filli ta re da zamowa ƙasa ta saka kanta cikin gwuiwoyinta tana ɓoye fustarta.
Dariya Mubeen ya saki a zuciyarshi ya na saƙa wani tunani na daban, tashi yayi daga inda ya ke ya je gaban Samhad ya tsugunna ya na kallon yanda ta kame, lallausan hannunshi ya saka ya ɗago da fuskarta wacce manyan idanuwanta su ke a kulle gam sai ƙaramin murmushi ta ke saki.
Tsira mata ido yayi ya na kallon baiwar hallitar da Allah yayi mata sosai gashin girar idonta ya ɗauki hankalimshi yanda idon ke kyarma sai gashin ya dinga motsawa,
A fili ya furta, "Ma sha Allah ki na da kyau sosai Ustaza." a sukwa ne zuciyar Samhad ta doka kamar za ta ɓalle ƙashin da ke ƙirjinta ta fito wajen saboda yanda kalaman suka daki zuciyarta.
Gocewa ta yi daga riƙon da yayiwa fuskarta wata azababbiyar kunya na sa ke saukar mata.
Ɗaf ya ɗauke ta daga ƙasan ya nufi kan bed wanda ta gyarashi kamar kar a hau saboda yanda yayi kyau, ajeta yayi kan bed ɗin tare da matsawa jikinta sosai ya na ƙoƙarin janyo fuskarta da ta sake cusawa cikin jikinshi dan sam abinda yayi bazai bari ta iya kallon shi ba.
Wani irin nishaɗi da nutsuwa ke ratsa zuciyar Mubeen sam bai tsarawa kansa yin aure ba amma ƙaddara ta gifta da san zuciya irinta Mamy suka laƙaba mashi wannan kamilar yarinyar wace sam ba ta cancanci shiga cikin matsalolin da ke tunkarar rayuwarsa ba kullum.
Katse tunanin ya yi jin ta gantsarawa yatsarshi da ya tura tsakankanin hannunta cizo. "auch" ya furta ya na yarfe yannu tare da yamutse fuska kamar ƙaramin yaro, saurin tashi zaune ta yi tana kamo hannun tare da yin kwal-kwal da ido alamar za ta yi kuka.
Haƙoranta ne jere guda biyu a jikin fatar yatsar tashi da ta ciza, "na shiga uku! akwi zafi ko?" ta faɗi ta na fifita yatsar da iskar bakinta ga hawaye har sun fara zubar mata.
Lumshe ido yayi ya na jin wani yanayi na daban na kunno kai cikin rayuwarshi, saurin janye hannunshi yayi a fili ya furta "no ba yanzuba akwai sauran aiki".
Sakin baki ta yi tana kallonshi dan ba ta gane inda ya nufa ba sai ma tunanin da ke yawo a zuciyarta na bazai haƙura ba da cizon da tayi mashi.
Sake marairaicewa ta yi tana bashi haƙuri kamar wadda tagundile yatsar. Murmushi ne ya kufce mashi dan wani tunani yayi a zuciya bai san maganar ta fito fili ba.
Janyo ta yayi tare da faɗin. "ke fa ragguwace wallahi taya zanji zafin wannan cizon naki mai kama da susar kadangare Ustaza?".
Hummmm ta saki nannauyar ajiyar zuciya tare da lafewa a jikinsa kamar wata ƴar mage.
Gyaran murya yayi kamin yace "idan babu damuwa zuwa anjima ina so zamuyi wasu ƴan maganganu game da aurennan tunda kinga bansanki ba kamar yanda ke ma baki sanni ba, ina son sanin wacece ke ni ma kuma zan sanar da ke wanene ni, sam ba'ayiwa rayuwarki adalci ba da aka aura maki ni saboda kina da nutsuwa da kamewa.
KIBIYA NAIRA 200 DAN
KARANTA LABARIN RAYUWAR SAHMAD,
MASU JIRAN DOCUMENT NAIRA 400 KACAL.
9236291920
Maryam umar
Opay.
🌹RAYUWAR SAHMAD🌹(abar tausayi ce 😭)
DAGA ALKALAMIN✍️✍️ MARYAM STAR⭐⭐⭐