GADAR TSAUTSAYI

GADAR TSAUTSAYI 15

by @nusybee143

Page 15




*ABUJA*

"Hajiya Hassy girman kujerarki!

Ga yaran na samo,ga su tsala-tsala,har sai sun fi Roxy garɗi ma"a cewar Amra a waya tana kallon su Azeema da ta saka suka cire after dress ɗinsu, kowacce ta zauna daga ita sai kayan banzan da ta saka 

Daga ɗaya ɓangaren Hajiya Hasana, wadda aka fi sani da Hassy ta ce"alright gani nan zuwa,kin san mai gidana yana gari,ga yaran miji da shegen sa ido,bana son a ɗago ni,dama gashi sun dame ni da tambayar ina na ji ciwo, matsiyatan yara kawai"

Amra ta ce"maganinsu za ki yi kamar yadda kika yi maganin ubansu,ki kai su sama su ma a rufe bakin su daina saka miki idanu, suna uzzura miki da tambayoyi na babu gaira babu dalili,kamar waɗanda suke aurenki"

Hassy ta ce"mhm!

Gani nan zuwa dai,idan na zo sai mu ƙarasa maganar ko?"Amra ta ce"okay sai kin zo"suka kashe wayar 

Abinci da abin sha Amra ta kawo musu,ta shimfiɗa ƙatuwar darduma ta ce"bismillah,mu zauna girls"babu musu suka sauko,ta yi serving ɗin kowa,itama ta yi serving kanta

Ba su juma da fara cin abincin ba kira ya shigo wayar Amra,wayar tana ɗakinta,don haka ta miƙe ta fice daga parlourn don ɗauko wayar 

Da sauri Azeema ta ciro ƴar ƙaramar ƙwayar da Roxy ta bata ta jefa a cikin kofin Amra,suka cigaba da cin abincin su a nutse 

Babu jumawa Amra ta shigo tana jan tsaki,don kiran da unknown number aka yi,kuma da ta ɗaga shiru ta ji,har ta gaji ta kashe wayar

Kallo su ta yi tana murmushi,ta zauna tana faɗin"sorry ko?

Na bar ku jira, kuma ƴar'uwar tawa tana hanya bata ƙaraso ba"suka kalle ta,sai da dariya ta kusa kama Azeema ganin yadda take magana tana wani karairaya kamar tana tare da namiji 

Ɗaya daga cikin ƙawayen Azeema, wadda ta fi ta iya bariki,ta yi fari da idanu ta ce"no babu komai baby,sai ta iso"Amra ta yi murmushi, Azeema da ɗaya ƙawar ta su suka kalle ta da mamaki jin ta kira ta da baby

Ai kuwa babu jumawa bacci ya fara fizgar Amra,suka cigaba da cin abincinsu a nutse suna kallonta suna murmushi 

Mintuna biyar kyawawa ya ishi Amra faɗawa bacci mai nauyi,suka kalli juna suka yi shewa, Azeema ta miƙe ta fara laluben kitchen,su kuma sauran ƴan matan suka fara tuɓe mata kaya

Babu jumawa Azeema ta dawo hannunta riƙe da tafasasshen ruwa, tana zuwa bata yi wata-wata ba ta sheƙawa Amra a daidai saitin gabanta,duk da nauyin baccin nan da ƙwayar ta saka ta sai da ta yi wani ihun azaba, ba tare da damuwar komai ba suka tattara komatsansu suka fice daga gidan 

Lokacin da za su fita daga layin a lokacin motar Hassy ta shigo layin,sai dai kasancewar babu wanda ya san wani a cikinsu ya sa suka wuce ba tare da sun tsaya ba ma,itama Hassy ta wuce gidan Amra zuciyarta cike da kwaɗayi da ɗokin haɗaɗɗun ƴan matan da ta gani Amra ta tura mata ta Whatsapp 






*MALIYA ESTATE, KANO STATE, NIGERIA*


"Muyassar menene yake faruwa ne?

A kwanaki biyun nan ƙararraki suna yin yawa akanka, mahaifiyarka ta kawo min ƙararka,haka zalika matarka,me yake faruwa ne?"

Kan Muyassar a ƙasa yana sauraren yayan mahaifiyar tashi ya ce"ban san akan me kake magana ba Abba"

Alhaji Yusuf ya ce"matarka ta tabbatar min da kana neman wata yarinya,har kana shiga lokacinta da sabgogin yarinyar , menene gaskiyar wannan maganar?"

Shiru ya ɗan yi, kafin ya girgiza kai ya ce"a'a Abba,Ni ban san da wannan maganar ba gaskiya"

"Abba wallahi ƙarya yake yi,har cewa ya yi wai ya fi sonta da ni,kuma akanta ni ba mace ba ce,ya rinƙa ci min mutunci saboda ita, tukunna ma,don ka ga ina rufa maka asiri, wallahi Abba tsohuwar budurwarsa ce,wato SHAHEEDA!!"

Cikin wani Irin ɓacin rai Abba ya kalli Muyassar wanda ya yi ƙasa da kanshi kawai yana saurarensu, muryarshi tana tsaitsayawa ya ce"menene gaskiyar maganar matarka?

Menene gaskiya game da halin da kake ciki na neman waccan yarinyar?"

Kai tsaye Muyassar ya ce"ka gafarce ni Abba,na san dai har yanzu ina sonta,amma...."marin da Abba ya saukewa Muyassar ne ya sa ya yi shiru, cikin tsananin ɓacin rai ya ce"ko babu komai ka nuna min ni ba mahaifinka bane,ko da na ɗauki shekaru kana riƙe a hannuna,ka tashi ka ba Ni waje kafin na fusata na yi maka abin da ba za ka taɓa mantawa ba,tashi ka ba ni waje!'ya daka masa tsawa

Babu musu Muyassar ya miƙe tsaye, fuskarsa babu alamun damuwa,duk da cewa shi kaɗai ya san yadda yake ji a ranshi,ya fice daga sashen Alhaji Yusuf 

Dubanshi ya mayar ga Hajiya Sa'adatu da ranta ya fi na Alhaji Yusuf ɓaci, cikin kakkausar murya ya ce"kina ina hakan take ta faruwa ne Sa'adatu?

Yaushe ɗanki zai yi lalacewar bijirewa umarnina?

Idan ban da shi wawa ne ko babu mata a duniya me zai yi da wannan fanɗararriyar yarinyar? wadda a yanzu ma babu tabbacin ko tana raye?

To ki ja masa kunne, wallahi tallahi, muddin magana makamanciyar wannan ta sake zuwa inda nake akan yaron nan to tabbas sai na shayar da shi mamaki,sai na ɗauki mummunan mataki akansa 

Ku bani waje zan huta"babu musu suka miƙe ɗaya bayan ɗaya suka fice, zuciyar Hajiya Ruƙayya da ta Arfa fes

Kai tsaye harabar gidan Hajiya Sa'adatu ta nufa,wajen parking space,anan ta iske Muyassar yana zaune,amma kallo ɗaya za'a yi masa ya bayyanar da damuwar da yake ciki, sai dai sam bata kula da hakan ba,tana zuwa ta sauke masa mari mai kyau, kafin ya ankarar ta sake sauke masa wani 

Dafe kuncinsa kawai ya yi ba tare da ya ɗago kanshi ba, Hajiya Sa'adatu ta cigaba da magana a fusace 

"Wallahi ba ka isa ba Muyassar! ba'a haifi yaron da zai bijire min haka ba, wallahi ko bayan raina ka auri yarinyar nan Allah ya isa ban yafe maka ba,kai ko labari na sake jin ka kalli hotonta sai na tsine maka!!

Kai in banda abin namiji me za ka yi da Shaheeda ga Arfa kana da ita?asalima ga mata nan birjik a gari ko da kana sha'awar ƙari,amma idan na sake jin batun Shaheeda to lallai sai ka gane kuskurenka,tabbas sai na ba ka mamaki,dalla shiga mu tafi"babu musu ya buɗe motar jiki babu ƙwari,itama ta shiga baya,ya tayar suka bar wajen 







*ROXY*

Yau kwana biyu kenan da tura Azeema gidan Amra da ta yi don rama abin da Amra ta yi mata,a ɗaya ɓangaren kuma tana samun sauƙi sosai,don zuwa yanzu hannun ya yi sauƙi sosai 

A yau ta shirya zuwa kano,amma kafin nan tana buƙatar ganawa da Amra tukunna,don haka ta shirya cikin wasu expensive track suit,irin wanda take yawan sakawa,ta sanya baƙin sketchers,ta ɗaura scarp akan dogon gashin ta sannan ta fice zuwa gidan Amra 

A hanya tana tuƙi tana kallon numbar David wadda tsawon kwanaki kenan yanzu idan ta kira ba ta shiga,ta rasa inda ya jefa wayar tashi 

A ƴan mintuna ta isa gidan Amra saboda gudun da take yi,ba tare da damuwar komai ba ta kutsa kai gidan tana gyara zaman baƙin spec da ta sanya ya rufe mata ƙwayar idanunta 

Murmushi ta yi ganin Amra a kwance an rufe mata ƙunar da wani yalolon mayani,tana sauke numfashi a hankali,ga wata ƴar'uwar cin mushenta da alamu ita ce take dawainiyar jinyarta,gefe kuma ga Hassy nan a zaune itama tana yin nata alhinin 

Da kallo suka bi Roxy gaba ɗayansu, ba tare da damuwa ba ta dubi Amra ta ce"ya jikin?"

Cikin Muryar kuka ta ce"ke ce kika turo su ko?

Dama wallahi ke nake zargi, tsinanniya kafira, Allah ya tsine miki albarka, shegiya arniya"

Ɗan murmushi mai sauti Roxy ta yi,ta samu waje ta zauna ta ce"ashe kin gane kenan

To ina fatan wannan jinyar ya zamar miki ishara ya hana ki aikata fasikanci har abada,dama na san ba za ki je asibiti ki zauna ba, saboda kin san me kika yi,ni lokacin bari na ƙasar ma ya yi,sai na ce Allah ya ƙara afuwa"

Miƙewa tsaye ta yi,ta yi taku biyu sannan ta waigo tana kallon Amra fuska babu yabo babu fallasa ta ce"Gobe ki sake yunƙurin aikata hakan, musamman da wayo da dabara kamar yadda kika yi min,amma kuma kar ki manta,a duk lokacin da kika yi yunƙurin aikata fasikanci Roxy zata zamo a tare da ke,ta tarwatsa mummunan nufinki,sai anjuma ko?"tana kai wa nan ta fice daga parlourn,babu wadda ta iya sake yi mata magana a cikinsu,har Roxy ta fice 






*KANO STATE, NIGERIA*

*HAISAM*



A hankali yake fitowa daga office ɗinsa,a yau ne ya shirya aikata aikinsa gaba ɗaya,a yi ta ta ƙare kawai,don haka daga nan ma gidan malam Tajo zai wuce kawai

Wayarshi ce ta yi ƙara, takaici ya kama shi ganin Nimra,ya ɗaga wayar ya kai kunne yana faɗin"I'm all ears Nimra "


Cikin shagwaɓa ta ce"I'm going back to Abuja, Please ka zo ka kai ni airport, Please Love!"

Cikin ƙosawa ya ce"Nimra meyasa kike son disturbing ɗina ne idan ina aiki?"

Cikin shagwaɓa Nimra ta ce"amma ai baka da lokacina,kai kullum kana tare da aiki, yanzu haka za ka rinƙa yi kenan ko nan gaba?"

"Okay wait, I'm coming "ya faɗa a gaggauce ya kashe wayar 

Yana ɓacin rai yana jan tsaki haka ya koma gida, lokacin Nimra ta gama shiryawa,tana ganinsa ta taso da farin ciki tana faɗin "Aunty Mariya sai mun yi waya,bye!"ta ja hannun Haisam suka yi waje yana bin ta da kallon mamaki, ita kuma Hajiya Mariya sai bin su da kallo take yi tana murmushi 

Har suka isa airport Nimra babu abin da take yi sai zuba surutu,shi dai jin ta kawai yake yi ba tare da yana gane abin da take cewa ba

Kafin su yi sallama sai da ta yi ta ɗaukarsu hotuna,shi dai ya biye mata don su rabu lafiya,bayan ta gama ya yi mata sallama, sannan ya shiga motarsa,ya tayar ya bar airport ɗin kai tsaye a unguwar da iyalan marigayi malam Tajo yake ya yi parking,a bakin ƙofar gidan ya yi parking motarshi yana ƙarewa gidan kallo,da tunanin ta inda ya kamata ya fara 

Ganin zai ɓata lokaci ya sa ya yakice tunani ya ƙwanƙwasa kofar gidan,babban ɗan gidan ya leƙo,yana ganinsa ya rissina yana gaishe shi 

Haisam ya amsa da sakin fuska, sannan ya ce"maman naku tana nan kuwa?"

Yaron ya ce"eh,bari na yi mata magana"

Haisam ya ce"okay to yi maza,ina jiran ka"yaron ya koma cikin gidan don sanarwa mahaifiyar tasu

Babu jumawa ta fito, Haisam ya rissina ya gaisheta yadda ya saba,ta amsa da sakin fuska sannan ta ce"bismillah!

Ashe kaine,yau dai don Allah ka taimaka ka shigo mu gaisa sosai"

Haisam yana murmushi ya ce"ai Mama yau maganar ma bata tsayuwa ba ce,mu shiga mu yi maganar,ina fatan dai yaran suna nan"Mama ta ce"eh duka suna nan, bismillah,shigo"babu musu Haisam ya bi bayanta,suka shiga cikin gidan 







*UNKNOWN LOCATION,KANO STATE, NIGERIA*


*ROXY*

Isowarta gidanta na sirri kenan ko minti biyar bata yi ba,ta shiga wanka,bayan ta fito sanye da bathrobe,kanta naɗe da ɗan ƙaramin towel ta ga wayarta da take ɓoye da number ɗinta ta sirri tana haske, kasancewar kowanne lokaci wayarta tana silent 

Bata kawo komai ba da farko, don ta ɗauka Oga boss ne,amma bayan ta shirya a cikin riga da wando hoodie tana duba wayar ta ga sabuwar number 

Tana kallo kiran ya katse wani ya shigo,ta dake ta ɗaga wayar ba tare da ta yi magana ba

"Barka da wannan lokaci Madam Roxy!"ta ji muryar mutumin da ba zata taɓa mantawa ba ta doki dodon kunnenta 

Da ƙyar ta dake,ta saita nutsuwarta saboda yadda gabanta ya yi masifar faɗuwa,ta dake ta ce "Barka!wanene kai?kuma daga ina?"

Ɗan murmushi ya yi mai sauti,sannan ya ce" na san ba za ki manta ni ba ai,amma kuma bari na sake yi miki tuni 

Sunana HAISAM ABDULMALIK MADAKA!kamar yadda kika sani, jami'in hukumar yan sanda na fararen kaya wato DSS, mai riƙe da muƙamin CSO 

Akwai rahotanni masu yawa akanki,na cewa ke ɗin ƴar safarar miyagun ƙwayoyi ce,kuma cikakkiyar ɓarauniyar yana,wato ƴar Yahoo,don haka hukumarmu tana nemanki,tana buƙatar ki kawo kanki,amma a shawarce kenan"

Wani murmushi ta yi ta ce"okay!

Kun gaji kenan?kun gaza da bibiyata ne?kun kasa?shine kuke nemana?

To ku cigaba da jarrabawa, wataƙila a dace,amma kuma ka sani......."

Ya cafke Maganar da faɗin "NO ONE CAN CATCH YOU ko?

Mhm!anya kuwa?ko da ace an kama tilon ɗanki MUBARAK?"

Cikin wani irin gigicewa da tashin hankali ta ce"what?what do you mean?

Ɗana?why?why?me Mubarak ya yi muku? don't try to make that mistake,zan iya kisa akan shi,kar ka taɓa min ɗana,shine kaɗai ya rage min, shine rayuwata,don Allah!!!"

"To malama FATIMA SHAHEEDA!

If you are ready then sai ki kawo kanki ga hukuma,Ni kuma sai na sakar miki ɗanki,akasin haka kuma?"ya yi ɗan murmushi ya kashe wayar






*To fa!dama Roxy ita ce SHAHEEDA?ita ce ƴar Ummeey wadda take kewa da bege a kowanne lokaci?wanne ɗa kuma ake magana akai?dama tana da ɗa?ya aka yi aka samu wannan kuskuren?to za mu ji dai,ku biyo Alkalamin Nusy bee a labarin GADAR TSAUTSAYI don jin yadda zata kaya*





#Nusy_bee