9
by @nanadiso10
PAGE 9.
Cikin zafin rai Rayyan ya isa gidan kakannin nasa, parking yai ya fito ya nufi cikin gidan yana ƙwala mata kira ba tare daya tsaya amsa gaisuwar da masu aikin Didi kakarsa ke yimasa ba “Zeynab.." ya faɗa da ƙarfi lokacin daya ƙarasa bangaren nasu, Mémé da fitowar ta kenan toilet tana bin bango tana ƙoƙarin fitowa daga ƙuryar ɗaki tace "Waye anan?” "Méme ina Zeynab take?" Rayyan ya faɗa cikin kaushin murya “Au! Wai dama Ummaru kaine? Har yaushe zaka dena kiran sunan Zainy haka a matsayinta na ƙanwar mahaifinka ka girmamata” har ya juya zai fita ba tare daya tankata ba sai kuma ya ja ya tsaya bakin ƙofa, second uku zuwa huɗu ya juyo ya kalli Mémé, ya saki wani miskilin murmushi “haka nike bana girmama wanda be girmama mahaifiyata ba”. Daga haka ya fice da falon ya nufi sashen Didi Mémé sai tsige masa take yi tana fadar Baida mutunci, Didi suna tare da Zeynab saboda tana dawowa sashenta tanufa tana faɗa mata karya da gaskiya akan zancen rashin lafiyar ta Rayyan da ita kanta bata san da ita ba, Didi na faman faɗa suka ga Rayyan bakin kofar dakin fuskar nan a murtuƙe tamkar anyi masa mutuwa. Gaban Aunty Zeynab ya fadi amma sai ta wayance, fuskarta ɗauke da murmushi “ɗan halak! Yanzu muke zancen ka da Didi Mike cewa an jima zamu je dubaka ashe har ma ka samu sauƙi...” kallon da yake yi mata yasa ta kasa ƙarasa zancen tare da yin ƙasa da kanta, Didi ce dake ta faman aika masa da harara itama tace “kayi tsaye ka tsare mu da idanuwa sai kace wuɗanda ake tuhuma ka kasa ƙarasowa daga ciki, ka shigo tunda Allah ya baka lafiya bai sa aka zo aka sanar damu zancen mutuwarka ba. Ace kayi ciwo har ka kwanta asibiti babu wanda ya zo ya sanar damu dan munafurci wannan ai rashin muhimmantamu ne a lamarinka” Ajiyar zuciya ya sauke yana ɗan danne ɓacin ransa da tsanar Aunty Zeynab da yake ji a zuciyarsa "Didi ba wannan ya kawo ni ba, nazo na jawa zeynab kunne ne a karo na ƙarshe akan mahaifiyata." Fizgo kai zainab tayi jin abinda ya faɗa cike da takaici, zuciyarta na wani zafi take kallonsa shima idanuwansa na akanta yace “Yes i mean it, stay away from my mother, enough is enough Wannan ya zamo na karshe da zaki sake faɗar munanan kalamai a kanta saboda bazan ci gaba da ɗaukar miki ba, wallahi ina da dama ruwan sama wannan bai isa ya dukar mun mahaifiya ba balle wani mutum domin ban haɗa darajarta data kowa ba, ki tsaya a matsayinki kafin nayi miki rashin mutuncin da bazaki taɓa mantawa dani ba.” Zaro idanuwa Zeynab tayi "Rayyan ni kake faɗawa haka? Ni kake cewa zaka yiwa rashin mutuncin ina matsayin kanwar ubanka, kenan bare ya fini a wajenka?" Didi da duk takaici ya ishe ta gane cewa da tayi duk wannan abun akan Fatima yake yinsa, tsaki ta ja, ta tashi cike da takaici zata bar ɗakin “Na ɗauka ganina kazo yi ashe rashin kunya kazo yi mana akan Fatima! Macen da zuciyarta babu Allah acikinta ta rabaka da kowa daga ita sai ɗiyanta, hmmm mu juri zuwa teku tulun zai fashe.” Zeynab ta taɓe baki “Ai na faɗa miki Didi makirar macece ta kwarai wallahi, ki ƙyaleshi yai abun duk da zai yi amma wlh Fatima sai ta wulaƙanta acikin family din nan indai ina da rayuwa..” Zeynab bata rufe baki ba taji saukar mari fauuu a fuskarta, cike da mamaki ta ɗago kai, idanuwanta dishi-dishi take gani amma ta tabbata basuyi mata karya ba wanda take gani a gabanta a matsayin ɗanta shine ya mareta, hannun Rayyan na rawa idanuwansa sun kaɗa sunyi jajir saboda tsananin ɓacin rai, kalaman da Zeynab ta faɗa akan Mom ɗinsa sun matukar koma masa rai tare da taɓa masa zuciya da har ya iya kai mata mari ba tare daya sani ba, abu guda ya sani a duniyar nan babu wanda ya isa ya taɓa mutuncin Mom agabansa ko shi waye ya ƙyalesa, Didi kuwa sai sallallami take yi ta riƙe Zeynab tana kallonsa da mamaki itama, nunata ya shiga yi da yatsa yana son yimata kashedi na ƙarshe sai dai zuciya ta kashesa ya kasa yin magana, dai-dai lokacin Dady da Rayyan na fita daga gida mom taje ta sanar dashi abinda ke faruwa ya shigo, sai daya shiga sashen Mémé bai isko Rayyan ɗin ba sannan ya nufo na Didi, saurin ƙarasa shigowa falon yai ya riƙe hannun Rayyan ɗin da atunaninsa ƙoƙarin sa ma Zeynab hannu yake yi, bai san mai gama har ta riga ta gama ba, kallon Didi yai ya kalli Rayyan haɗe da jan hannunsa “Ya kamata ku sani matsayin kowa daban acikin ku wajensa, bai kamata wasu abubuwan kuna yinsu agaban idanuwansa ba domin ita zuciya bata da ƙashi kuma an halicce ta da son wanda ke kyautata mata.” Yana gama fadar haka ya jasa suka fice, a kan hanya Dady tuki yake yana kallon Rayyan, bai taɓa ganinsa cikin irin wannan matsanancin fushi ba sai yau, murmushi ya ɗan saki yana maida hankalinsa akan titi, ya sani yadda yake son Mom ɗin tasa zai iya nuna fiye da wannnan ɓacin ran akan duk wanda ya taɓata, a haka suka isa gida da sauri Mom ta taso ta riko hannunsa ta zaunar dashi akan kujera, ruwa mai sanyi ta dauko ta bashi ya sha kafin ta fara yi masa faɗa tana haɗawa da lallashi akan ya dena kula duk abinda zasu yi mata ko zasu faɗa kanta, yan uwansa ne su da bazai taɓa samun kamarsu ba idan ya ɓata dasu, Rayyan ya kalli Mom, ya riko hannuwanta biyu “Mom ke kadai kin isheni a duniyata, na yarda narasa kowa narasa komai matukar ke, Dady da kuma ƙannena kuna tare dani.” "Duk da haka aryan ɗan uwa ɗan uwa ne, kaka, ƙanen uwa ko wan uwa da uba duka suna a gurbin iyayenka ne a Musulunci, zamani ne yake basu wannan sunan na kaka da kawunni da Gwaggo da sauransu, ka daure ka riƙa basu girmansu dan Allah kaji?” ya rungumeta yana jin wani sanyi a ransa, ya lumshe idanuwa, ya sauke wani lumfashi mai zafi haɗe da ajiyar zuciya "Mom kibar wannan zancen and on behalf of Zeynab Ina baki hakuri abinda tayi miki.” a jikinsa ta cirosa ta ɗan ɗaga hannu saiti a fuskarsa kamar zata maresa tace “Not Zeynab Aunty Zeynab ko kuma ka faɗa Gwaggo” Dariya ya saka shi da Dady dake zaune saman kujera yana kallon su cike da soyayya, yana kaunar Fatima bisa kyautatawa, soyayya da halaccin data yi masa yadda ta riƙe masa ɗan ɗan uwansa, haka kuma yana jin Rayyan a zuciyarsa tamkar ɗan daya haifa, tun tashinsa bai taɓa bata masa rai ba ko ya sashi abu yaki yi masa, haka kuma bai taɓa hanasa abuba yayi wannan dalilin yasa kullum yake ƙara jinsa a ransa. Hannun Mom data ɗaga Rayyan ya riƙo ya sumbata, Dady ya janyo pillow ya jefa masa yana cewa "Bar mun mata haka kazo naji yaushe ka shirya, kaima na tattaraka na miƙaka a hannun taka matarka kona huta da rigimarka." Kallon Mom yai “Mom da gaske?" “To me muke jira, ina dai kana son Hanan ɗin duk da baku san juna ba?" Kunya ce ta dan kama Rayyan, ya miƙe yana sosa kai ya nufi sama ɗakinsa “In dai kina sonta Mom shikenan ko ban santa ba ina sonta nima." Murmushi Mom ta saki tana ƙara jin kaunar yaron nata a ranta, ana cewa ƙaunar uwa da ɗa daban ce, amma har yau ita ta kasa banbance ƙaunar da take yiwa su Nayla da tasa.
"Zan so su fara ganin juna Alhaji kafin ayi zancen komai, na fara bincike kan tarbiyyar yarinyar data mahaifiyarta ban samu negative wani abu daga wajensu ba, amma duk da haka zan kara bincike sosai saboda bana son na aurowa yarona fulawa a juji ko kuma bara gurbi acikin mata." “Hakan ba laifi nima zan kara yin wani ta ɓangarena duk da nasan ko waye Alhaji Nuhu shattima, amma gudun tuhumar ki koda nan gaba, zan kara bincikawa saboda tsoronki nake yi Indai akan ɗan can naki ne tofa na sani ba kida sauƙi kuma bakya barin bashi.” Dariya duk suka sa a tare, nan take ya sanar da ita akwai wani taro da zasu yi na wani kasuwanci da zasu ƙulla da manyan yan kasuwa kuma har da alhaji shattima aciki, in sha Allah yana tunanin zai yi magana dashi Hanan tai representing nasa shima zai sa Rayyan ya wakilcesa a gun, Daga nan in suka haɗu sai a fara maganar ta yadda kowanensu zai faɗi ra'ayinsa tunda sun hadu da juna, sosai Mom taji daɗin wannan plan Saboda tafi so Rayyan yafara ganinta kafin aje ayi maganar haɗasu auren, dama weekend ne ranar Monday za’ayi taron, don haka zata tashi da daddare tayi masa addu'a Allah ya tabbatar masu da duk abinda yafi Zama alkhairi.
2026
***
***.