RAYUWAR SAMHAD

Zazzafan labari

by @maryamstar248

BOOK 2️⃣PAGE4️⃣
____________________________________________________________________________________________________

بسم الله الرحمن الرحيم.


Kai kayan Mubeen ya yi wajen accounter sannan ya jawo wani basket ɗin ya miƙawa Samhad tare da jan hannunta su ka bar wajen zuwa sasahen  kayan mata, kaya ne na gani na faɗa a wajen tun daga abayoyi dogayen riguna da riga da wando kala-kala na mata, jidar kayan Mubeen ya ke kamar ba da kuɗi zai biya ba sai da yayi basket biyu manya sannan ya nufi sashen iners, bra da pant ya nunawa Samha tare da faɗin "Samhadidi bisimilla nan ɓangarenki ne."


Humm Yah Mubeen ni fa kunya nikeki please mu tafi hakanan." ta faɗa tare da sunne kai ƙasa.

Aiko babu inda zamuje sai mun gama siyayyar kaf, kinga malama banason gulma idan za ki shiga ki zaɓa to idan kuma ni in zaɓo miki fine." ya faɗa ya na tsare ta da idanuwansa.

Cikin siririyar sassanyar muryarta ta ce "Ok ka zaɓo min kawai babu damuw ai." ta yi maganar ta na ƙoƙarin ja da baya, riƙo ta yayi tare da yin magana ƙasa-ƙasa yanda ita kaɗai za taji abinda ya ke faɗi.

"Idan kin yarda zan zaɓo miki ammafa da sharaɗi idan kin yarda."

Kai Yah Mubeen sharaɗin mi kuma؟."

Sharaɗin shine za ki bari ingwada miki da kaina..."

Ba ta bari ya ƙarashe ba tayi gaba da mugun sauri kamar za ta tashi sama, murmushi Mubeen ya yi tare da bin bayanta ya taya ta zaba dan sai wani kakkauda kai ta ke.

Sai da su ka gama da ɓangaren kaya sannan ya nufi ɓangaren kayan girki, anankam Samha ya bari da aikin zaɓa, aiko ta dage ta dinga jida dan Samha akwai son girki ko a gida Ita Hajiya Adama ke bama kuɗi ta yo siyayyar kayan girki idan sun ƙare.

Sai da suka gama sanan  suka je wajen lissafi, aiko Mubeen ya kashi ƙudin dan lissafin da aka yi sai da Samha ta shiga shock saboda jin maƙudan kuɗaɗen da aka salwantar.


Manya-manyan ledoji ne aka shiga jida ana kaiwa cikin motar da suka zo da ita, sai da aka gama kai kayan ya kulle motar ya ja hannun Samha zuwa wajen da aka ake sai da snacks da Ice cream ya yi musu tak away su ka dawo mota ya ja suka nufo gida.


Lokacin da su ka iso har an fara sallar azahar a gaggauce Mubeen ya yi parcking ya ba ma Samha key idan ta fitar da kayan sai ta kulle motar ya wuce masallaci.


Duk da kayan sumfi ƙarfinta ha ka ta shiga jidar su ta na kaiwa ciki, sai da tayi sawu biyar sannan ta gama ta kulle motar tare da shiga ciki ta ajiye kayan ta nufi yin sallah. 




Bayan an taso da ga sallah Mubeen ya nufi part ɗin Daddy dan ansa kiran da ya yi masa, bayan sun gaisa Daddy ya ɗauko wasu takardu ya miƙawa Mubeen tare da faɗin " Son ina son ka yi bincike akan takardunan nan da zuwa dare ka maido min."

To Daddy in sha Allah."

Allah ya yi muku albarka, tashi ka je dama shine kiran, idan ka fita ta turomin Auta Salma duk yau ban ganta ba tun safe."

"To Daddy, a huta lafiya." ya faɗa tare da miƙewa ya fice daga sashen, waya ya ɗauko ya kira layin Salma....🖊️


ANAN ZAN DAKATA SAI KU BIYONI A PAGE NA GABA DAN JIN YANDA ZA TA KAYA.


RAYUWAR SAMHAD LITTAFIN KUƊI NE PAGES 200 DOCUMENT 400 KACAL KI MALLAKI NAKI CIKIN SAUƘI.


9136291920
MARYAM UMAR
OPAY.

DAGA ALƘALAMIN✍️🖊️ MARYAM STAR ⭐⭐⭐
(ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU💪🌹)
🌹RAYUWAR SAMHAD 🌹(Abar tausayi ce😭)