ALIYU HAYDAR

Chapter 10

by @nieemartullah

Kamar yadda ya fada ma aunty zai dawo ya dauketa yana idar da sallar isha'i ya wuce gidan su,bayan yayi sallama ya tsaya har saida aka bashi izinin shiga kafin ya shiga,yanxu kam gidan yafi cika da mutane akan daxu da safe saida ya shigo ne ma ya fara danasanin shigowar da yayi da ya kira aunty kawai a waya ta fito,cikin ladabi ya tsugunna ya gaida manyan da ke zaune a parkour amsa mashi suka yi cikin sakin fuska suna tambayar shi aiki yace masu alhamadulillah,yaran ma hada baki suka yi suka gaishe da shi Sa'adah ce ta kafe shi da ido tun shigowar shi kuma yana lure da hakan yarinyar qanwar aunty ce tana bala'in son shi kuma yasan da hakan amma bai taba nuna yasan tana yi ba,Nafeesah ya kalla yace ta ce ma aunty yazo tace tohm ta miqe don isar da saqon shi,bayan dan lokaci sai gata ta fito tare da aunty a bayan ta sallama yayi ma mutanen parlour ya fita ba tare da ya kula irin kallon qurillar da sa'adah ke mashi ba.............................................

Adan firgice ta juyo har abinda ke hannunta yana faduwa,bata ji shigowar ta ba bare sallamar da tayi ajiyar zuciya ta sauke ganin wadda ta shigo din,ba tare da tace komai ba ta sa hannu ta dauki hoton da ya fadi sai ta zauna gefen mom ta daura kanta a kafadar ta,sun dauki kusan mintuna uku kafin JAY tayi breaking silence da fadin shin sai yaushe ne mom zaki fada man damuwar ki ?damuwar da tun daga lokacin da na fara wayo na fahimci kina cikin ta ko ban cancanci sanin damuwarki ba,ina jin babu dadi aduk lokacin da na ganki cikin damuwa kuma na kasa saka ki farin ciki,kamo hannun Jaiyana tayi ta saka cikin nata sannan tace bawai na qi na sanar maki da damuwata bane saboda wani abu ina son kullum ki kasance cikin farin ciki shiyasa bana son na fada maki abunda zai saka ki damuwa kamar yadda ni damuwa ta zama rayuwata amma yanxu dole zan fada maki.

45 years ago

Kallo daya zaka yi ma wannan ahali ka tabbatar da irin farin cikin da suke ciki,wata kyakyawar yarinya ce da aqalla baza ta wuce shekaru goma ba a duniya da da bakinta ya kasa rufuwa saboda murna ta juya ta kalli magidanci da yake zaune akan kujerar asibiti da aka tanada don masu zuwa dubiya tace Baffah munyi kama ko tana nuna masa babyn da ke hannun ta wanda ta kira da Baffah ya kalleta shima fuskar shi na bayyanar da farin cikin da yake ciki yace eh mamana kunyi kama,matar dake kwance kan gadon mara sa lafiya ce ta juyo ta kalli yayan nata tana murmushi sannan ta juya da akalar kallon nata kan mijin ta martanin murmushin ya mayar mata sannan yace Allah yayi maki albarka kin gama yi man komai a duniya har ban san da wani baki zan yi maki godiya ba tunda ya fara magana take ta murmushi tace ai ni zanyi maka godiya sannan na yima ubangiji na godiya saboda yayi man ni'imar da ba kowa yayi ma ba tabbas nasan nayiwa mata zarrah da na same ka a matsayin miji ka zame man bango abin jingina acikin rayuwa ta ka zame man inuwa a lokacin zafin rana a kullum ina ma Allah godiya da ka kasance miji na kuma uban ya ya na ko iya haka kadai Allah ya barni ya gama yiman komai ballantana kuma irin soyayyar da dangin ka suke nuna man nida yarana,Allah ya saka maku da mafificin alkhairi likita ne ya shigo ya qara duba ta,ganin babu wata matsala yasa ya basu sallama dama bai sanar da kowa tana asibiti ba sai da aka sallame su suka koma gida sannan yaje gida ya sanar ma iyayen shi Jaiyana ta sauka,sunyi murna matuqa basuyi qasa a gwiwa ba suka biyo shi zuwa gidan nashi ko wannen su bakin shi ya kasa rufuwa,kafin kace me gida ya cika da yan uwa na kusa da na nesa a wannan rana Ammah ta ga tarairaya wurin dangin Baffah kowa burin shi yayi abinda zai faranta mata haka kwanaki suka shude har yau ya kama suna yarinya ta ci sunan mahaifiyar Ammah wato Khadijah gidan ya cika da yan uwa da abokan arziqi ana ta kai kawo,a duk lokacin da Ammah ta bude idonta taga yadda yan uwan Baffah ke tarairayarta sai ta qara ganin qima da dararjar su ta kasance marainiya da bata da kowa sai su dalilin zuwan su Nigeria ma shine lokacin da masifar yunwa da talauci ta rinqa kashe yan uwansu a somalia shiyasa ita da iyayenta suka dawo Nigeria har zuwa lokacin da itayen ta suka rasu ta dawo hannun iyayen Baffah da zama har soyayya mai qarfi ta shiga tsakanin su,ita kam bata da bakin da Zata godema wannan ahali,a haka sakanni suka rikide suka koma mintuna,mintuna suka koma awoyi,awoyi suka koma ranaku,ranaku suka koma satittika,satittika suka koma watanni,watanni suka koma shekaru,yau Khadijah ta cika shekaru biyar a duniya ni kuma ina da shekara goma sha biyar a duniya kuma a lokacin ne na kammala junior secondary school alokacin aka ringa qananan maganganu akan naqi nayi aure saboda a lokacin duk sa'anni na duk sunyi aure ni kadai ce na rage banyi ba Baffah yace sai nayi karatu zai aurar dani yace musu kuma shi aure ai lokaci ne da lokacin yayi za'a yi hakan yayi man dadi so sai saboda dama ni hakan nake so,a ranar wata lahadi da bazan taba mantawa ba arayuwata ranar da har abada bazan daina ganin laifi na ba don badan saboda ni ba da Ina tunanin abinda ya faru ranar wataqila da bai faru ba nace ma Baffah sai ya kaimu mu wurin wasa Baffah yace haba mamana abarni na huta mana haka na dage sai ya kaimu,toh da yake Baffah yana da son yaranshi sai yace toh muje mu shirya har Ammah zamuje muna ta tsallen murna muka je dakin Ammah muka ce mata Baffah yace ta shirya zamu fita hannun Khadijah ta kama don ta shirya ta ni kuma na wuce dakina don na shirya ba'a dau lokaci ba muka fito gaba dayan mu cikin shirin fita Ammah na riqe da hannun Khadijah ni kuma Baffah na riqe da nawa hannun idan har ganmu a lokacin sai mun burge ka saboda ba qaramin kyau muka yi ba,na bude back seat na zauna Ammah ta bude dayan side din ta saka Khadijah a cikin kafin ta bude front seat ita ma ta shiga,tunda Baffah ya dauki hanya ya lura Ammah wasn't in a good mood sai ya tambaye ta meke damunta?tace mashi babu komai kawai gabanta ta ne ke ta faduwa dariya yayi yace da alama yau baki azkhar ba kika fito dan murmushin qarfin hali tayi tace ranka ya dade tunda ba muyi nisa ba da mun koma gida Baffah yace ai tunda mun fito kuma babu maganar komawa tun daga nan ta ja bakinta tayi shiru bata qara cewa komai ba har suka qarasa minjibir park,sunyi wasa sosai har gab da maghrib Ammah ta kalli Baffah tace ranka ya dade ya kamata mu tafi gida kar muyi dare sosai,eh yakamata gaskiya ku tashi mu tafi sosai taji dadi ganin zasu tafi don har yanxu hankalin ta yaqi kwanciya so take kawai ta gansu a gida,bayan sun dauki hanya ya tsaya ya siya masu gasasshiyar kaza da yogurt sannan suka ci gaba da tafiya gab da zamu shigo cikin kwaryar garin kano sai ga wata trailer tayo kan motar mu Baffah yayi iya qoqarin shi na ganin ya kaucewa wannan motar amma ina ganin hakan yasa Baffah ce mana mu saka seatbelt din mu na gama saka nawa ina qoqarin na juya na saka ma Khadijah sai qara muka ji gbam motar ta daki tamu motar ban qara sanin abunda ya faru ba sai kawai tashi nayi na ganni kwance akan gadon asibiti ashe suma muka yi gaba dayan mu wani bawan Allah ne yaxo wucewa ya ganmu shine ya taimaka aka kawo mu aibiti,ni da Ammah ba muji ko rauni ba amma shi kuma Baffah ya sami rauni a goshin shi da kuma qafar shi,babban abinda ya qara daga mana hankali shine cewa da akayi ba'a ga Khadijah ba,mun shiga cikin matsanan cin tashin hankali an bada cigiyar ta amma ko mai kama da ita ba'a gani ba,bamu sani ba ko tana raye ko kuwa ta rasu Allah kadai ya barma kanshi sani na shiga cikin tashin hankali mara misaltuwa saboda har gobe ina ganin ni ce silar batan Khadijah,da ban ta kurawa Baffah sai mun fita ba da wata qila ina tare da yar uwa ta,wasu hawaye suke sakko kan fuskar mom da sauri JAY ta saka hannu ta shiga goge mata hawayen da yaqi tsayawa wani na korar wani,rungume ta tayi itama tana hawaye sai bayan dan wani lokaci JAY tace ina ji a jiki na nan ba da dadewa ba zaku qara haduwa ganin dai har yanxu bata dena hawaye ba yasa JAY tace dama ni bani da qawaye Tasneem ce kawai,ina ji a jikina zata zo da yaranta guda talatin ta fada tana nuna talatin din da hannun ta sosai abin ya bawa mom dariya har bata san lokacin da ta fara dariya ba ganin tayi nasarar saka ta dariya yasa ita ma tayi murmushi tace mom bari naje daki akwai ayyukan da zanyi kafin na kwanta gyada mata kai kawai tayi ita kuma ta fita daga dakin har tayi hanyar dakin ta sai kuma ta fasa ta nufi dakin hajiya mama,sallama tayi ba'a amsa sa ba hakan yasa ta tura qofar kawai ta shiga a zaune ta tarar da ita ga carbi a hannu a sai uban gyangyadi take,wata dariya JAY at kyalkyale da ita hakan yasa hajiya mama bude ido amma taqi kallon JAY ta ci gabada da jan carbin ta,su hajjaju ana ta zikiri ko kallon ta bata yi ba ta cigaba da abinda take ganin taqi kulata yasa ta tace Allah ya baki haquri hajjaju ni shigowa nayi nace maki sai da safe ko kallonta bata yi ba har ta fita daga dakin,dardumar da take kai ta linke ta cire hijabin binta ta kwanta.............................
Bayan fitar faruq dakin billy ta wuce,tarar da ita tayi kan abin sallah hakan yasa ta wuce dakinta kawai ba tare da tace komai ba,alwala itama tayi ta shimfida abin sallah ta fara sallah bayan ta idar da sallah ta dade a sujuda tana addu'ar samun nasara even though she lacks nothing from her husband and his family but she still misses her family too,she wants to be in the midst of her own family,bayan ta gama duk addu'o'in ta,ta wuce toilet tayi wanka bayan ta fito ta saka wata silky doguwar rigar bacci ta feshe jikinta da turare ta dauki hijib ta saka kafin ta wuce dakin billy ganin bata dakin baki daya amma tana iya jiyo qarar ruwa yasa ta fahimtar tana toilet,fita tayi ta rufe mata qofar ta tafi part din mijinta AVM Adnan.................................
Bayan ya ajiye aunty ko part din mama bai shiga ba ya wuce part din shi,bayan yayi wanka ya Kayan bacci marasa nauyi ya dauka ya saka kafin ya kwanta wayar sa dake ajiye kan bedside drawer ya dauko ya shiga kiran number JAY sai da ta kusa katsewa ta daga  tace Assalamu Alaika sai da yayi ajiyar zuciya sannan ya amsa mata cikin muryar ta mai sanyi ta gaishe shi amsa mata yayi sannan ya tambayeta mom tana nan lafiya qlau,bai san meyasa a yan kwana kin nan yake jin fargaba a tsakanin tarayyar shi da JAY,sai da ya gama shawara da zuciyar shi akan abinda zai fada kafin yayi gyaran murya yace babe dama ina son muyi wata magana ne daga can bangaren Jaiyana tace ina jin ka,akan maganar da mukayi dake ne kwanaki kika ce zaki yi ma dad magana toh jiya ne Abbah ha qara man magana akan suna son suji ya mukayi dake,na fada mashi yanda muka yi dake sai yace man zuwa gobe na same shi na fada mashi yanda muka yi dake,a bangaren JAY sosai hankalinta ta tashi jin maganar da sadeeq yake yi saboda ita har ta manta ma sunyi maganar amma da ta tuna maganar da sukayi da hajiya mama sai hankalin ta ya kwanta,sai da ta saita muryar ta sannan tace mashi nayi ma mom magana tace man zata yi ma dad magana amma bata kai ga yin maganar ba wata tafiya ta taso mashi cikin gaggawa hakan yasa tace a bari ya dawo sai ayi mashi magana jiya kuma nayi waya dashi yace man idan har ya gama abinda ya kaishi da wuri ba zai wuce kwana goma ba zai dawo,sosai yaji hankalin shi ya dan kwanta da jin wannan bayanin nata hakan yasa yayi murmushi yace yace babu komai ai Allah ya dawo mana dashi lafiya tace ameen,sai kuma ta qara cewa sadeeq please can we talk later ina dan duba wasu files ne bai so jin hakan ba amma sai yace no problem dear talk to you later take care of yourself love,dan murmushin yaqe tayi tace ok thanks tare da kashe wayar,bayan ta kashe wayar shima aje wayar yayi ya janyo system din shi don akwai wasu sauran ayyukan da bai gama ba gashi gobe Monday,bai tashi akan system din ba har wuraren qarfe biyun dare kafin ta kashe system din yayi addu'a ya kwanta....................................
A bangaren Laylah kuwa kamar yadda suka tsara ita da Hafsat washe gari da sassafe suka dauki hanya sunyi tafiya mai nisa a motar Laylah kafin suka iso wani dan qamin qauye wanda mota bata shiga hakan yasa suka bar motar su a bakin garin suka hau mashin,shima tafiya ce mai nisa suka yi akan mashin din kafin suka sauka,bayan sun sauka suka rinqa ratsa bishiyu da ciyawu suna wuce har suka qaraso bakin wata bukka Hafsa ce ta riqo hannu Laylah sannan tace da qafar hagu zaki shiga tana fadin gafaran ku dai daga cikin bukkan kuwa wani dan gajeran mutum ne baqiqqirin abin tsoro sai uban layu a jikin shi gefen shi kuma wata qasa ce sai kuma kwarya da wani abu acikin ta kamar ruwa gurin zama Hafsat ta nunawa Laylah kafin itama ta zauna tana masa wani irin kirari wata mahaukaciyar dariya mutumin ya fashe dake ita Hafsat na taya shi sai kuma ya Tsuke fuska kamar ba shike dariya ba barkan ku da zuwa wannan fadar yaku wanda suka kwashe kayan su daga gaban Manzo,muna muku lale marhaban ya ku watsatstsu tun kafin zuwan ku aljanu sun sanar dani zuwan ku da kuma abinda zai kawu ku,don haka ku matso nan ku gani kwaryar dake gaban shi yayi wasu yan tsubbace tsubbacen shi sai ga fuskar Jaiyana ta fito tana kwance akan gadon ta tana bacci peacefully hannun shi ya miqa sama sannan ya qara fadar wasu maganganu sai ga wani qullin magani akan tafin hannun shi miqa ma Laylah yayi ta saka hannun dama zata karba ya daka mata wata mahaukaciyar tsawa yace don baki da hankali zaki sa hannun dama anan gurin,toh tabbas idan har kika qara yin irin wannan kuskuren a gaba sai na saka aljanu sun kashe shi sannan na sadaukar da jinin ki wurin dodo Hafsat jikin ta har yana tsuma ta shiga bashi haquri tare da yi mashi kirari hakan yasa ya qara miqa mata maganin wannan karon hannun hagu ta saka ta amsa yace idan har kika je gida kinga wannan qullin maganin zaki bari sai qarfe biyun dare zaki tashi kiyi wanka dashi,ruwan maganin da kika yi wanka dashi zaki diba ki dafa mashi abinci da shi daga nan ko uwarshi ce yarinyar kallon namiji zai rinqa yi mata har abada bama ita kadai ba har ma da sauran mata baki daya,godiya ta shiga kwarara mashi kamar me sannan tace a temaka man a bani wanda zai sa ya manta da ita har abada dariya ya qara kecewa da ita wadda har taso tsorata Laylah sai ya qara miqa hannun shi sama sai ga wani qullin maganin ya qara fitowa ya miqa mata yace wannan kuma a cikin ruwan wankan shi zaki zuba mashi idan har yayi amfani da ruwan toh kamar yadda ake ruwa ya dauke ya manta da ita har abada,handbag dinta ta bude ta zaro nera million biyar ta bashi tace idan har naga aiki yayi yadda ya dave zan bawa Hafsat tukwici ta kawo maka suka miqe suka fita wani farin qyalle ya dora akan kudin sai bat suka bace....................................
Tana zuwa part din ta tar dashi yana ta packing kaya cikin trolley bag qarasawa tayi tana taya shi kafin tace yallabai tafiya kuma babu sanarwa yana cigaba da abinda yake yace yanxu muka yi waya da AM yace lallai yana buqatar gani na a gobe shiyasa kika ga ina  hada kaya na dan bata fuska tayi irin bata ji dadi ba sai yace chill ai bazan dade ba da munje zamu dawo wani dan aiki ne bamu qarasa ba zamu qarasa sai mu dawo bata qara cewa komai ba ta cigaba da hada mashi kayan shi har ta gama tayi zipping trolley din ta aje ta gefe,bayan ya gama shiryawa ya ja trolley din suka fito babu wanda suka fada ma a cikin yaran suka wuce airport bayan ta raka shi ita kuma ta dawo gida dakinta ta wuce ta kwanta da kewar mijinta har tayi bacci....................................
Bayan sun gama waya da sadeeq sai taji duk hankalin ta yaqi kwanciya ta kasa yin komai hakan yasa kawai ta kwanta tayi bacci,duk da ta dade kafin bacci ya dauke ta hakan bai hana ta tashi a qarahen dare kamar yadda ta saba ba,bayan tayi alwala ta fito ta shimfida prayer mat ta dakko well folded hijab dinta ta warware ta saka tare da tada sallah cikin nutsuwa take yin komai har ta idar,bayan ta idar da sallar ta zauna nan inda tayi sallah tana addu'a har bata san lokacin da hawaye suka fara fita daga idon ta ba sai da taji damshi akan fuskar ta kafin ta fahimci kuka take,tayi addu'a sosai har sai da taji an fara kiraye kirayen sallar farko na asuba,ta dan samu nutsuwa a zuciyar ta fiye da dazu hakan yasa ta miqe tare da fara yin raka'atanul fijr ta zaune har taji an shiga sallah,miqewa tayi ta tada sallah shima bayan ta idar sai da ta qara wasu addu'o'in kafin ta dauki wayarta ta shiga kiran dad don tana da tabbacin ya tashi yanxu don kuwa a can Moscow tasan yanxu qarfe bakwai na safiya ne,yana fara ringing daga can bangaren dad ya daga tare da yin sallama cikin muryar shi mai cike da dattaku,itama daga nata bangaren ta amsa kafin  ta shiga gaishe da shi da tambayar lafiyar shi yana amsa mata da lafiya qlau,hira suka danyi mai cike da qauna ta tsakanin uba da yar shi kafin suka yi sallama,ganin har yanxu tana da sauran lokaci yasa ta kwanta ta qara yin bacci kafin ta shirya zuwa office..................................
Daren jiya tayi duk yanda bokan su ya umarceta da tayi safiya na yi ko gari bai gama yin haske ba ta tafi kitchen don hada breakfast,tana yi tana kallon lokaci tana ganin lokacin tashin shi yayi ta dauki dayan qullin da aka ce ta saka mashi cikin ruwan wanka ta wuce hanyar dakin shi,tana shiga ta tarar ya farka amma bai sauka akan gadon ba dan murmushi tayi mashi tace sweetheart har ka tashi good morning,shi dai sai kallon ta yake yi saboda yana ganin hakan matsayin sabon abu ganin kallon da yake yi mata yasa tayi yaqe tace bari na hada maka ruwan wanka ta shige toilet din bata jira jin mai zai ce ba bayan ta hada ruwan ta zuba maganin kafin ta fito ta same shi inda ta barshi hakan yasa ta qaraso inda yake tace oya tashi kaje kayi wanka bari naje na qarasa hada maka breakfast Taya fita a dakin shi dai yana tsaye saboda zuciyar shi taqi yadda da sabon al'amarin nan,tunanin ya fara yi kodan yace mata aure babu fashi shiyasa take yin abinda take,tunanin hakan da yayi yasa shi yin murmushi yace su Laylah manya da duk baki san yadda ake kula da miji ba sai da yace zai qara aure Hmmmmmm had it been tana yi man irin abubuwan nan mema zai sa ni tunanin qara aure da wannan tunanin ya rage kayan jikin shi ya wuce don yin wanka.......................................
Qarfe takwas da minti goma ta tashi daga baccin da ta koma toilet ta wuce don yin wanka,bayan kaman minti goma sha biyar ta fito daure da farar bathrobe a jikinta gaban gadon ayaanah ta karasa ta tasheta riqe hannun ta tayi ta wuce da ita toilet don yi mata wanka bayan tayi mata wanka ta shiryata cikin wasu pink din riga da farin wando tayi mata styling din gashin kanta kafin ta dora mata band a kai bayan ta gama shiryata ta wuce gaban madubi ta zauna tana goge jikinta da dan qaramin towel,bayan ta gama ta dan yi yan shafe shafen ta kafin ta dauki oil perfumes dinta na Haramain million da surrati ta shafa ajikin ta kafin ta wuce closet dinta ta dauko wata simple black abaya anyi mata adon stones daga gaban rigar veil din abayar tayi rolling kafin ta qara daukar turaren ta na channel coco mademoiselle da Dior miss Dior ta fesa kadan ba da yawa ba saboda zata fita,qaramar handbag ta dauka ta saka wayar ta aciki ta riqe makullin mota ta fito zuwa dakin mom,a bakin kofa ta tsaya tayi knocking kafin ta shiga dakin da sallama hannunta riqe da na ayaanah a bakin gado ta tarar da mom a zaune cikin shiga ta alfarma tana duba wasu kaya da tayi order dan duqawa tayi ta gaishe ita ayaanah ta gaisheta kafin ita ma ta zauna bayan ta amsa gaisuwar su tace JAY har kin shirya kenan eh mom zan fita tace toh Allah ya tsare ki kula sosai kinji tace in shaa Allah mom hannu ta miqa ma ayaanah ta na mata alamar taxo,kan cinyar ta ta dora ta tace mu baby yau sai school ko tace mata eh yawwa idan kika je school banda rashin ji kin ji tace toh yawwa maxa tashi kiji kar ku qara yin latti tashi tayi ta bi bayan JAY bayan sun fita daga dakin mom dakin hajiya mama suka wuce shima knocking tayi kafin suka shiga,da sallama a bakinta a kan stool din dake gaban mirror ta zauna ta gaishe da ita ita kuma ayaanah ta zauna akan gadoJAY tace lafiya naga kina hada kaya kamar wadda zata yi bulaguro?toh me zan zauna inyi tunda abinda ya kawo ni anyi an gama kinga kuwa ai sai na koma inda na fito,toh ai kuwa baki ga ta tafiya don kuwa su dad next week zasu dawo kuma akwai taron da za'ayi idan su dawo qara ma ki rufawa kanki asiri ki maida kayan ki,ni dama zuwa nayi na miki sallama zan tafi aiki,hajiya mama tace toh a dawo lafiya Allah ya tsare tace ameen har ta juya zata fita taji hajiya mama na fadin kinga tashi ki bita kin wani zauna man akan gado baki ko gaishe ni ba,murmushi JAY tayi tace ayaanah tell her good morning,da yake yarinyar nada wayo sosai yasa tace good morning old woman baki sake hajiya mama ke kallon ayaanah can kuma tace uwarki ce old woman bani ba kinga waccan da ke tsaye tana nuna JAY tace itace old woman bani ba,dan girgiza kai kawai JAY tayi ba tare da ta qara cewa komai ba ta ja hannun ayaanah suka fita suka bar hajiya mama nata sababi ita daya...................................
Bayan yayi wanka ya shirya cikin wasu qananan kaya ya fito parlour ya tarar Laylah har ta gama shirya masa breakfast akan dining,bayan ya zauna tayi serving din shi ya fara ci abincin jin yayi masa dadi yasa shi zagewa yaci da yawa har yana santi itadai sai dariya take yi mai,bayan ya gama cin abinci ta raka shi har bakin motar shi kafin ta koma cikin gida,a yau yasa wa ranshi zai koma gidan su JAY don jin feedback dinta,office dinshi ya wuce direct da tunanin idan ya dawo daga office zaije wurinta............................