GADAR TSAUTSAYI 16
by @nusybee143
Page 16
Tashin hankali ba'a saka maka rana! faɗar irin halin da Roxy ta shiga ɓata baki ne,a haukace ta sake ɗaukar wayarta ta aikawa Haisam kira
Sai dai ya ƙi ɗagawa,bata sare ba, cikin ficewar hayyaci ta cigaba da yunƙurin kira,sai da ta yi kira goma,a na sha ɗayan ya ɗaga
Cikin tashin hankali ta ce"to ai ba ka gaya min inda zan same ka ba,ina zan kawo kaina ɗin?"
Kai tsaye ya ce "ki yi tracking number na mana,ke ba software engineer ba ce?kuma a good tracker?try it mana"
Cikin tsananin rauni ta ce"ba zan iya ba,don Allah ka taimaka min,ka gaya min address ɗinka na yi maka alƙawarin zan kawo kaina,amma ina roƙonka kar ka taɓa min ɗana,shi kaɗai ne farin cikin da ya rage min a duniya,idan ka cutar min da shi ban san yadda zan yi ba"
Kai tsaye Haisam ya ce"to da kyau!
Zan tura miki address yanzu,ina buƙatar na ganki a wajen nan da thirty minutes,ko kuma wannan yaron ba za ki sake ganinsa ba har abada"
"Na yarda "ta yi saurin amsawa jikinta yana rawa
Kashe wayar ya yi,babu jumawa message na address ɗin ya shigo ,tana gani ta miƙe tsaye,ko ganin gabanta bata yi sosai ta ɗauki hanya,a wannan lokaci ko ita ba zata iya misalta irin tashin hankalin da ta tsinci kanta a ciki ba
Bata juma ba ta samu kanta a wani ƙaton fili da ba shi da nisa da gidanta, Haisam ta hango a kan motarshi a zaune yana murmushi game da tafa hannayensa,ta ƙarasa gabansa, cikin rawar murya ta ce"ina ɗana yake?"
Yana murmushi ya ce"mu gaisa mana, Roxy zan ce ne ko Fatima Shaheeda?the most smartest girl I have ever seen in my life?"
"I said where is my son Haisam?
Kar ka yi min wasa da rayuwar yaro!i can't tolerate it anymore!"ta faɗa cikin fusata da tashin hankali
Murmushi ya yi,ya nuna motar gabansu,ya ce"Men!"babu musu sai ga zaratan jami'ansu sun fito su biyar,hannun ɗaya riƙe yake da Habu,ɗan autan maman Fauziyya,matar marigayi malam Tajo
Tana ganin Habu ta hau ihu ta nufi inda yake da gudu tana faɗin "ɗana!ku ba ni ɗana,shi kaɗai ne da Ni,don Allah ku ba ni,ku yi min duk abin da za ku yi min amma ku ƙyale min ɗana,shine rayuwata....."
Sam bata ankara ba har suka buga mata ankwa suka ja ta zuwa motar Haisam,tana ihu tana fizge-fizge,tana ji tana gani aka tafi da Mubarak, wanda bata san inda za'a kai shi ba, tsabar tashin hankalin da ta riski kanta a ciki kafin a je station ɗin ma numfashinta ya ɗauke
*BAYAN KWANAKI UKU*
*MALIYA ESTATE*
Izuwa yanzu gaba ɗaya ahalin Maliya sun samu labarin abin da yake faruwa a gari,wato dai yan jarida sun baza cewa wannan matashiyar yarinyar da ta addabi jami'an tsaro ta hana su saƙat take aikata abin da ta ga dama,ba kowa ba ce face ɗaya daga cikin ahalin a baya kafin ta hau GADAR TSAUTSAYI wadda ta kai ta halin da take ciki,wato Fatima Shaheeda,babbar ya a wajen uban wannan ahali wato Maliya family
Yan jarida sun nemi Alhaji Yusuf Maliya don jin ta bakinsa akan bayyanar sunan ƴarshi a matsayin mai aikata babban laifi a ƙasa,duk da yadda ya kasance mutum mai mutunci da ƙima a idanun mutane
Kai tsaye ya amsa da cewa tun kafin a zo wannan gaɓar ya daɗe da mantawa da ita a cikin ƴaƴanshi,ita ba ƴarshi ba ce, shiyasa ma ta daina amfani da sunan da ya saka mata,ta sakawa kanta wani
A ɓangaren Hajiya Zainab kuwa yau kwananta biyu a asibiti,tun da ta samu labarin nan ta shiga tashin hankali sosai,amma hakan bai yi wa abokan zamanta ba,suka yi ta yaɗa maganar suna yar mata da habaici,hakan ne ya hauhawar da jininta,wanda ya tilasta mata kwanciya jinya
Babbar yar Alhaji Ishaq, Maryam ce take kula da ita a asibitin,bayan ta samu sauƙi ta matsa a sallame ta,kai tsaye ta wuce gidan Hajiya Saudat
Hajiya Saudat da bata juma da komawa ba don ta huta ta bi ta da kallo, ganin lokacin d aka shirya sallamarta bai yi ba, ba tare da tunanin komai ba Hajiya Zainab ta zube a gaban Hajiya Saudat tana kuka mai tsuma zuciya
Kama hannunta ta yi, suka wuce zuwa bedroom ɗin Hajiya Saudat, Hajiya Saudat ta zaunar da ita a gefen gado tana kallonta, cikin kwantar da murya ta ce"a yi haƙuri,komai mai wucewa ne,komai idan aka koma ga Allah mai sauƙi ne, Zainab babu wanda ya isa ya ja da ƙaddara,idan kin yarda Allah ne mai yin komai ki gaya masa cikin dare da rana,yana kusa da ke,kuma yana ji kuma zai amsa kokenki
Ke ɗin mai haƙuri ce, Allahn da ya jarabce ki shine zai kawo miki mafita, ba'a fushi da yi da iyawar Ubangiji
Ki yi haƙuri Zainab,ki mayar da al'amuranki ga Allah"
Zainab ta share hawayenta ta ce"Hajiya ni ba wannan ne yake damuna ba,sai yadda kishiyoyi suka saka ni a gaba, kowacce da kalar maganar da take yi saboda abin da ya faru,wasu a cikinsu ma faɗa suke yi wa ya sani ko abin da Shaheeda ta yi tarbiyyar gidanmu ne?
Akwai ciwo sosai,duk wani haushin Alhaji da suka ji a baya a yanzu suna hucewa a kaina,ga maganar da ya je ya yi da yan jaridu, Hajiya,ba zan ɓoye miki ba,na ji ciwon wannan maganar,ya nunawa duniya ko babu Shaheeda zai rayu, Hajiya ba ni na ce akai Shaheeda makaranta ba, asalima wallahi ban goyi bayan hakan ba,ya zan yi?
Hajiya ki ba ni shawara, zuciyata kamar zata fashe "
"Haƙuri autar Hajiya, haƙuri, addu'a,istigfari,sallar dare,miƙa lamura kacokan ga Allah, sanyawa a zuciya cewa Allah ne mai yi,kuma shine mai jarabtar bawa, kazalika shine mai warware matsaloli,za ki ji zuciyarki fes zainabu
Ki duba cewa,ban taɓa haihuwa ba,amma a yanzu ko wata mai ƴaƴa goman ba zata gwada min farin ciki da cin moriyar yara ba, akwai wadda ta haihun,amma kuma bata ci moriyar yaran ba,duk wanene mai yi? Allah
Don haka yanzu ki tuna,akwai Allah,idan kika miƙa komai ga Allah,hakan ya isa"
Hajiya Zainab ta goge hawayenta, cikin sanyin murya ta ce"in sha Allah Hajiya, Allah ya yi mana jagora "
Hajiya Saudat ta dafa kanta ta ce"Ameen autar Hajiya!
Allah ya albarkaci rayuwarki! Allah ya share miki hawaye, Allah ya zama gatanki auta "
"Ameen hajiyata, Ameen, Hajiya yunwa nake ji"
Hajiya ta yi murmushi ta ce"mu je ki ci ɗanwaken da na saka a yi min"babu musu suka miƙe suka fice zuwa dinning area
Da kanta ta bawa Zainab abincin,tana ba ta tana janta da hira, wadda ta sa ta manta da damuwar da take ciki,suka sha hirarsu abin su
Hajiya Zainab bata tafi gida ba sai da Alhaji Yusuf ya zo ya ɗauke ta da kanshi, Hajiya Saudat bata nuna masa damuwar komai ba,a mota ma suna tafiya yana ta kwantar mata da hankali cikin dabaru da hikima
*MUYASSAR*
Ɗaga kai ya yi yana kallon Arfa da take ta waƙa cikin farin ciki, cikin ƙosawa ya ce"Arfa na gaya miki kina damuna,ba ki bar ni na yi abin da yake gabana ba kin wani sako ni a gaba da waƙe-waƙen banza da na wofi,bana son sakarci fa!"
"Sakarci?"ta faɗa tana fashewa da dariyar rainin hankali, ta ce "oh Allah!
Wato sakarya ce ni,to ita kuma yar safarar cocain mecece ita?jan wuya?"
Shiru ya yi bai ba ta amsa ba,ta ɗaure fuska gami da jan tsaki,ta ce"Allah wadaran naka ya lalace!
Na godewa Allah da ya sa uwata ta gari ce da ta ba ni tarbiyya,gani nan a ɗakin aure ba a gari ina gantali kowa yana tsine min ba, lalacewar tawa bata kai jami'an tsaro su rinƙa bi na muna tsere da su ba, saboda ina yaɗa baɗala a bayan ƙasa,wa ya sani ma ko iya nan ɓarnar ta tsaya ko ta wuce haka?mu dai Allah ya tsare mu daga aikata irin wannan mugun aiki "
Miƙewa Muyassar ya yi don ficewa daga ɗakin,don ya fara gajiya da irin wannan surutan na Arfa,don shi har yanzu bai ji soyayyar Shaheeda ta yi rawa a cikin zuciyarshi ba,ji yake yi waɗannan zantuttukan da Arfa take yi tamkar ana zuba masa ruwan dalma a cikin zuciyarsa,amma sai Arfa ta tare masa hanya
Calmly ya dube ta ya ce"Arfa ba ni hanya,zan wuce "
"Ba za ka wuce ba, saboda ina zargin waccan tsinanniyar tunda aka kama ta ka gigice,wa ya sani ma ko kana zagawa kuna haɗuwa? wataƙila ma ɗan da aka ce an yi mata tarko da shi naka ne,wanda kuka samu a rariya!"
"Arfa!ko ki ba ni hanya na wuce ko na sauke miki mari!"
"Idan ka fasa marina ba ka haifu cikin Umar da Sa'adatu ba!"bata rufe baki ba Muyassar ya sauke mata mari,bata gama gane kanta ba ya sake sauke mata wani sannan ya hankaɗe ta gefe ya nufi hanyar fita
"Kan uban can kayyasa!ni ka mara?
Muyassar Allah ya isa na,mugu azzalumi macuci,matsiyacin namiji, wallahi na yi nadamar aurenka,kuma kai ma na yi alƙawarin sai ka yi nadamar sanina,kuma ...."
"Yadda kika yi nadamar aurena haka nima na yi nadamar aurenki, kin ga babu amfanin zaman nadama,don haka ki je na sake ki Arfa!!!"yana kai wa nan ya fice daga gidan da sauri,yana jin kururuwa da ihu da fizge-fizgen Arfa amma ko kallon hanyar bai yi ba,ya faɗa mota ya fice daga gidan
*HAISAM*
"Daddy yaushe za ka dawo?"
Kallonta ya yi yana murmushi ya ce"ba zan juma ba in sha Allah,ki yi min addu'a sweetheart!"
"Allah ya dawo da kai lafiya, Allah ya ba da Sa'a daddyna!"
"Ameen mummyna!
Much love"ta yi kissing ɗin shi a kumatu,shima ya yi kissing ɗinta ya ja mota ya fice daga gidan
A bakin jail ɗin ya tsaya,ya nuna ID card ɗinsa,ba tare da ɓata lokaci ba aka ba shi hanya ya wuce da wayarsa a hannunsa
Yana zuwa ya bayar da sunan criminal ɗin da yake son gani,babu ɓata lokaci ma'aikatan suka tafi don kiranta,shi kuma ya zauna a inda aka tanadar masa
Babu jumawa aka gabato da Roxy,kanta a ƙasa, idanunta sun canja da alamun ta sha kuka sosai,sai dai babu alamun karaya a tare da ita,ta samu waje ta zauna,amma still kanta a ƙasa, idanunta a kan hannayenta da suke ɗaure da handcuff
Murmushi ya yi sosai,ya ce"Barka dai!
Sunana CSO Haisam Abdulmalik Madaka,Ni jami'in tsaro ne na farin kaya,wato DSS
Tsarina ne muddin na saka abu a gaba tabbas sai na cimma shi, musamman idan ya zamana an wulaƙanta ni
To!yau ga ni ga Roxy, wannan fitacciyar wanted ɗin, wadda take rayuwa cikin kwanciyar hankali tana gwara kan jami'an tsaro,amma sai ga ta a hannun waɗanda take rainawa hankali,malama Roxy Barka da zuwa komar Haisam!!"
Kamar ba zata yi magana ba,sai kuma ƙasa-ƙasa ta ce"ina ɗana?"
"Ban ji ba sosai, maimaita"ya faɗa yana aika mata wani kallon rainin hankali
Ɗaga kai ta yi ta kalle shi,a hankali ta ce "cewa na yi ina ɗana mubarak?
Wanne laifi ya yi maka ka kama shi?"
Wata ƴar dariya ya yi ya ce "laifin da Amna ta yi kika saka aka yi musu barazana,ko ba ki san kukan ƴata yana tayar da bala'i bane?kuma muddin ta yi kuka sai na rama mata?"
Hawaye suka zubo mata ta ce"to ba gani ba?ka rama akaina mana!
Menene dalilin da ya sa zaka rama akan wanda bai takawa kowa komai ba?"
Haisam ya ce"ita Amna me ta yi miki kika razana ta?"
Tana goge hawayenta ta ce"ban yi da zummar na cutar da ita ba, ko da ban haihu ba na san zafin ɗa, ballantana ɗan da iyayensa da suke nuna masa soyayya ba sa raye"
"Ban ga alamun kin san zafin ɗa ba Shaheeda,da ace kin san zafin ɗa da ba ki jefar da naki don wani ya tsinta ba,ba ki ji tsoron abin da zai same shi ba?
Allah ya taimaka ya faɗa hannun na gari, alhamdulillah uwar riƙon nashi sai da ƙyar ta yarda da ni tunda na ambaci ɗaukar yaron na zo yi, sai da na yi mata bayanin wacece ke,da manufar da ta sa kika jefar da yaron ba ta kirki ba ce, sannan ta ba ni shi,a yanzu kuwa ba za ki sake ganinsa ba,zan ɗauke shi na mayar da shi inda zai yi rayuwa irin wadda kike yi,ko kina ganin za ki yiwa Allah wayo, shiyasa kika ɗauke ɗanki kika kai shi matsera wajen tarbiyya,ke kike lalata na wani?kina son shi har haka kika kasa tsayawa ki yi masa tarbiyya?a maimakon haka ma sai kika canja suna,kika canja addini don ki fi jin daɗin aikata ɓarnar da kike so?
Ina jiran ba'asi Shaheeda!!"ya ƙarashe a ɗan tsawace, ranshi a ɓace, saboda ya ji zafin yadda ta wulaƙanta rayuwar yaronta fiye da komai
#Nusy_bee