07
~~~
"Aisha" ya kiraye ta.
Aisha ta juyo sanda Juwaira ta ja hannun Khausar suka shige cikin gida yayinda itakuma tayi taku biyu da suka dawo da ita gabansa inda yake tsaye gefen motarsa.
"Mesa baki duba emails din ba"
Ya kalli sanda ta kalli yatsun hanunta da suka riko gefen gyalen nan kamar dazu kafin ta sake dagowa ta kallesa. Yasan meyasa bata duba ba dan yana sane da ita sanda take zuwa da wuri wuri duk Monday tayi aikin kafin ta tura masa. Kawai dalilin da yasa ba ta yin aikin a gidan yakeso ya sani. Ya cigaba da kallon yadda take wasa da jan gyalen nan kafin tace
"Bani da laptop a gida shiyasa"
Kuma sai bayan ta fada din ya fahimta. Ya fahimce dalilin da ya saka bata yin aikin a gidan sai kawai ya nade hannayensa a kirjinsa.
"Aisha"
Ta dago ta kallesa
"Lokacinda Habeeb yace zaki iya tambaya na duk abunda kike bukata na aiki dagaske yakeyi"
Ta kalli gefensa dan da kyar take iya jure kallonsa Allah ya gani.
"Mesa baki fada mun ba?"
"Sir ban sani ba?"
"Baki san me ba?" Tayi shiru bata amsa ba.
"Baki san cewa dagaske yakeyi ba?" Ya sake tambaya.
Ta kallesa. A'a fa. Ita ba abunda take nufi ba kenan. Tana nufin bata san cewa ya kamata ta gaya masa cewan batada na'urar yin aikin ba. Koh kuma ta fada masa tana bukatar na'urar yin aikin. Ganin tayi shiru ya saka yace
"Okay toh shikenan, zan aiko miki dashi anjima in sha Allah kinji".
Ta gyada kanta tana cigaba da murza gyalen nan dan shi kadai ne wani abin da yake dauke mata hankali daga wannan kwarjinin nasa daya cika iskar wajen gabaki daya.
"Nagode sosai" ta fada masa.
Sai ya rasa sau nawa a wannan ranar kadai ta furta mai kalmar nan.
~~
"Shi ogan naki ne ya siyo duk wa'ennan kayan Aisha"
Inna ke fada bayan ta shigo cikin gidan ta cire gyalenta ta ajiye a kan gadon Inna inda Juwaira ke zaune tana tauna meat pie dinda sukayi take away dinsa daga wajen bikin nan.
Khausar kuwa na zaune kasan carpet din dakin gefen kafar Inna tana jira Aishar ta shigo kamar yadda Inna tace kafin ta taba kayan duk kuwa da yanda ta ringa rantse rantsen ai ita ya siyowa tunda da ita aka shiga wajen.
"Eh Inna, shine mai kamfanin da nake aiki"
"Haka Juwaira tace mun, toh wai saboda me ya siyo duka wa'ennan abubuwan?"
Ta aiko mata tambayar da ita kanta bata san amsarta ba. Dan lokacinda suka tsaya supermarket dinnan duk wani tunani barin kanta yayi sanda yace Khausar tazo ta rakasa ciki. Inna ta jinjina kai ganin Aishar bata amsata ba.
"Kyautatawa kawai Inna" Juwaira ta fada bayan ta hadiye gutsirin meat pie dinda ke bakinta.
"Toh angode, Allah ya saka da alkhairi"
Inna ta fada tana turawa Khausar ledar. Aikwa dama kamar jira take tuni ta bude ta tana fitoda robobin ice cream dinnan da Aisha ta tsaya tana kallo cikin mamaki dan dama tasan dole kayan suyi yawa ganin yadda ledar take babba. Sai kawai tayi baya tana kwantawa saman gadon Inna ta lumshe idanuwanta. Kuma acikin hotunan da kwakwalwarta ta rike sai kyakkyawar fuskarsa ta baje kanta a allon ganinta.
Kaman yanda ya fada zai aiko a kawo mata din hakanne ya farun dan tana zaune wani Khalifa jikan Hajiya Zulai dake nan makotansu ya shigo ciki wai ana sallama da Aisha. Dama sallahr isha'i ta sallame shiyasa bata koh cire hijabin datayi sallahr ba ta fito waje.
Ta iske Magaji tsaye a bakin kofar gidansu ta fito suka gaisa kafin ya miko mata wata kakkaurar leda yace y'allabai ne yace ya kawo mata. Ta karba da godiya kafin ta juya ciki.
Tana shiga kuwa a tsakiyar dakin Inna aka bude ledar nan kafin ta fito da kwalin ipad pro dinda ke ciki. Khausar tayi wani tsalle ta diro daga inda take zaune jan hasken kwan fitilar dakin Inna yana haska ipad dinnan sanda Aisha ta bude kwalin nan tana fito da ita.
"Wooow" Khausar ta furta tana kallon katuwar ipad din dan har keyboard gareta da pen. Aisha ta sake bude ledar ta fito da case dinta da aka sako cikin ledar shima tana yaba tsananin kyawun ipad din dan irinta take gani a hannunsa a office yana amfani da ita.
"Wannan itace laptop din" Inna ke tambaya tana jujjuya katuwar wayar da Aisha ta miko mata.
"A'a wannan fa ipad ce"
Khausar ta fada tana kokarin danna button din jikin wayar da zai saka ta kawo a cikin hannun Innar. Inna ta bige mata hannu sanda wayar ta kawo kafin ta mikawa Aisha wayar
"Ungo ta kunna miki ita"
"Yaaya dan Allah mugani"
Khausar ke fada. Aisha kuwa ta mika mata wayar ta karba tana jira ta bude.
"Wannan ne abun rubutun kenan"
Inna ke fada bayan ta fito da keyboard din mai kyau dashi d'an karami .
"Eh da wannan dinma" Aisha ta fada duk tana mika mata su tagani tareda pen din. Inna ta tabe baki kafin tace
"Toh yanxu meye amfanin zaman gida a karshen satin idan har nan dinma aikin zaki ringa yi"
Ta mika mata kayan ta karba. Kafin ta fitoda case dinma ta karbi wayar daga hannun Khausar dake danne danne ta sakata a ciki.
"Inna aikin weekend din kamar ina ragewa kaina aikin da zanyi idan satin ya fara ne ai".
"Toh Allah ya taimaka" Inna ta fada.
"Yaaya wannan fa" Khausar ke tambayarta bayan ta fito da kwalin d'an karamin mifi dinda ke cikin ledar shima. Aisha ta karba tana dubasa dan itama daga farko bata gane meye din ba sai daga baya. Kuma Allah yagani duk cikin wa'ennan abubuwan da ya aiko mi fi dinne kadai abunda ya faranta mata rai dan tana ta tunanin yadda zata saka data a cikin ipad din har tayi amfani da ita tunda ba babbar waya gareta ba bare ta jona hotspot. Kuma sai bayan ta kunna mifi din tukunna ta lura da cewar har datar ma duka ya loda mata a cikinsa. Suna zaune a nan sanda Juwaira ta dawo daga dakin Maman Naanan dataje taga bidirin da akeyi itama ta jona su. Maman Naana da aka kaiwa tagani koh karbar wayar batayi ba ca tayi kawai Allah taimaka dan ita yanxu idan ba dole ba ma koh wulgawar Aisha ba son gani takeyi ba Allah yagani.
Ita kanta Nana sai bayan kwanaki biyu ranar ta kama litinin da daddare tukunna taga wayar sanda Aisha ta dakkota zuwa daki saboda wasu takardu da El Yakoub yace ta hada mai kafin gobe. Dan dama can dakin Inna take ajiyeta sai yanxu da yake dare ne wajen karfe goma da wani abu saboda bai turo mata aikin ba sai wani karfe tara da rabi sanda suke sauraren littafin su. Inna nata fadan aikin meye kuma zata yi a cikin daren nan. Ta tattaro komai tazo dakinsu toh sai a lokacin Nana taga wayar ai kuwa ta dankaro wani zagi ta dire.
"Kam*** Aisha ubanwa ya baki abar nan"
"Wajen aiki aka bani ita"
Aisha ta bata amsa tana cigaba da danne dannenta daga inda take zaune saman katifarta ta jingina jikin pillown. Juwaira dake kwance kan katifarsu ita da Nana ta laka karamar wayarta a kunne tana sauraren labarin wani littafi da akeyi karfe goma ta juyo tana kallon Nanar datayi tsaye bakin kofa dan dama ta shigo dakin kenan ne taga wayar. Nana ta sake fado wani zagin
"Wai uban me kike a aikin nan da hardasu ipad ake baki"
Nana ta sake tambayarta kuma haka kawai sai tayi shiru ta shareta dan bata san ma yadda zata amsa wannan tambayar tata ba kuma addu'a take a ranta Allah ubangiji yasa kar Juwaira ta tanka ta kuma sai Allah ya karbi addu'ar dan Juwaira bata amsata ba suka barta tsaye a wajen. Nana ta saki wani katon tsakin da ya gauraye dakin kafin ta daga labulen ta fice daga dakin ta wuce zuwa dakin uwarta cikeda kunar zuciyar da ya ziyarceta lokaci daya dan har wani baki baki take gani. Juwaira itama ta maida martanin tsakin da Nana tayi ta juya tana cigaba da sauraren littafinta. Aisha ma ta cigaba da abunda takeyi sanda taga alamar shigowar wani email dinsa ta saman wayar. Taga cikakken sunansa a email dinnan dan dama tun asali da email dinsa na YK ventures yake tura mata komai amma da ta fara amfani da ipad dinnan sai tagan yana tura mata daga personal email dinsa kuma sai a lokacin taga asalin sunansa, El Yakoub. Taji sunan yamata nauyi a lokacin data fito dashi daga ranta zuwa fatar bakinta,
"El Yakoub".
Ta shiga email din tana kallon dogon layin rubutun da ya mata akan wani file data hada ta tura masa kuma abubuwan da yace ta chanja din a cikinsa ita duk bata gane ba. Kuma bata sani ba koh bacci baccin data fara ji ne koh kuwa yanda yayi dogon rubutu amma kuma bayanin is not detailed. Ta juya ta kalli Juwaira da tayi bacci dan har wutar dakin ma a kashe take hasken ipad dinnan dake ajiye a gabanta kadai ne. Ta tura mai reply cewan bata gane bayanin nasa ba. Kuma mintina biyar, shida, bakwai har ta cire rai da ganin reply dinsa sanda taga karamar wayarta dake ajiye a gefenta tana haske.
Ta kalli wayar da tsammanin ganin kiran Mu'azzam dukda sunyi sai da safe dashi tun dazu amma sai tagan wata number da bata sani ba. Ta cigaba da kallon wayar har ta katse tana mamakin wanda zai kira number wayarta a cikin daren nan. Toh koh dai mistake ne. Sai ga wani kiran ya sake shigowa ta dauki wayar tana kallon number sanda taga reply din El Yakoub ya shigo cikin ipad dinnan layi kwara daya.
'Pick your phone Aisha'.
Zuciyarta tayi wani irin dummmm. Tace "Na'am?" ga kanta ita kadai dan babu wani dake dakin da zai jita tunda Juwaira dai bacci takeyi. Ta sake kallon wayar ta kalli email din kafin tayi shahadar daukar wayar zuciyarta na harbawar da har cikin kunnuwanta tana jiyo bugun nan. Toh ina ya samu numberta?
"Aisha, it's me"
Wannan muryar ta El Yakoub ta malalo daga cikin wayar nan tana wanke Aisha daga kai har kafa dan har saida ta motsa yatsun kafarta dake tankwashe.
"Sir barka da dare"
Muryar Aisha ta fito a cikin dakin nan nasu da take zaune wanda karar gudun fankar dake aiki kadai kakeji.
"Yauwwa" El Yakoub ya bata amsa ta dayan bangaren inda yake zaune a parlonsa saman pillown kujerar daya dora a kasa ya zauna akai ya jingina bayansa a kujerar. Yana sanye cikin vest fara kal da wandon baccinsa na flannel launin ja da baki. Launin da duk ya kallesa yake tuna mai da gyalen Aisha da karamin hannunta datake kama gyalen dashi. Wani karamin table ne a gabansa da ya dora laptop dinsa akai yana aiki sai kofin shayi mai zafi da yake kurba akai akai.
Ya jingina da kujerar nan yana shafa sumar kansa da dayan hannunsa kafin yace
"Kin bude file din?" Ya tambayeta
Ta danno file din kafin tace "Eh"
El Yakoub ya gyada kansa "Wannan introduction din da kika rubuta ki gogesa"
Tayi abunda yace din sannan tace "Na goge"
"Good, yanxu start a new one" ya fada yana maida wayar kunnensa na hagu kafin ya dauki shayin ya kurba.
"Okay sir me zan rubuta"
Ta tambayesa dan bata san me zata rubuta ba bayan wanda ta rubuta din da yace mata ta goge. Shiru ya biyo baya na sakanni kafin ya fara fada mata abunda zata rubuta sai kawai ta chusa wayar cikin hulanta daidai kunnenta tana rubutun da hannyenta biyu tana sauraren yadda muryarsa mai taushi ke shiga kunnenta. Yana yi yana tsayawa har sai ta karasa rubutun kafin ya cigaba da magana dan yana jin karar typing din nata daga cikin wayar.
"Yanxu ki duba page two"ya cigaba da fada bayan ta gama rubutun.
"Sunan client dinda kika rubuta is wrong" ya fada.
Aisha ta duba wajen tana tabbatarda maganarsa. Ta rasa yanda akayi tayi mistake dinnan ya rabb. Ta goge yana karanto mata ainahin sunan.
"Na chanja sir" ta fada bayan ta gama jin yayi shiru.
"Okay turamun nagani" Ya fada ahankali bayan tayi maganar.
"Toh" Ta amsa sa itama.
Y'ar karamar kalma amma yadda muryarta ta fito ahankali ya sakashi lumshe idanuwansa daga kallon screen dinnan kafin ya sake budesu gashin idonsa da suka hade da juna suna raba kansu. Ta tura mai ya duba kafin ya sake turo mata wani file din shima yana karanto mata wajajen da zata gyara da inda zata sake rubutawa. Kuma Aisha bata sani ba watakila yadda bacci yaci idanuwanta ne koh kuma yanda muryarsa ke fita ahankali ne yana mata wani bayanin bayan ta tura masa file dinnan na biyu, yayi shiru bayan ya gama bayanin yana ce mata bari ya dubo wani file din bacci ya rinjaye idanuwanta.
"Kin gan file din?" El Yakoub ya tambaya.
Shiru ya biyo baya.
"Aisha"
Shiru.
"Aisha"
Ya sake kiran sunanta amma still shirun ne ya sake biyowa baya sai shima yayi shirun kuma can cikin wayar kunnuwansa suka jiyo masa sautin fitar numfashinta ahankali alamar dake nuna tayi bacci.
~~
"Mama, kudin wayar nan tawa za'a ninka sau uku a siya ipad dinnan"
Nana ke fada tana daga ihone 11 dinta a hannu kamar ta rike takarda daga inda take zaune a kasan carpet din mamarta ta lankwashe kafa daya yayinda dayar take a mike.
Maman Naana dake zaune gefen gadonta ta jinjina kai cikin mamaki da takaicin wannan zancen.
"Toh wai ni abunda ma nakeso na sani, har wani kamfani ne wannan takewa aiki"
"Hm mama kenan" Nana ke fada bayan ta ajiye wayarta saman kafarta
"Mama mutumin da take aiki karkashinsa fa ba kananan kudi garesa ba, katon kamfani yake da a Abuja. Kudinne suka masa yawa shine yazo nan dinma ya buda wani"
"Kuma da yake bai san ciwon kudin ba shine ya dauki waya mai makudan kudade ya bata?"
Maman Nanan ke fada bayan ta gama jin abunda Nana ta fada. Nana ta girgiza kai irin kamar Maman Nanan bata gane zancenta ba
"Mamaaa, nace miki fa kudin ne dashi shiyasa yake b'arinsu kuma wallahi idan aka cigaba a haka wata rana kila sai Aisha ta dawo da mota"
"Kamar yaya mota" Maman Nana ke fada tana rike haba.
"Ah toh mama, irin wa'ennan manyan manyan mutanen fa kyauta garesu, bare ita da take aiki matsayin sakatarinsa ai tsab zai dauki mota ya bata yace ta ringa zuwa kamfani da ita kar kiyi mamaki ma kila hadda direba"
"A aikin sakatarin kadai???"
Maman Nana ta fada tana dukowa gaba tsabar yadda maganar ta daketa.
Nana tayi wani murmushin takaici wani zafin bakin ciki yana zagaye kirjinta dan lokacinda taga wayar Aisha har hajijiya sai da taji ta dauketa. Ya za'ayi ace wai Aisha na neman take ta? Ya za'ayi ace Aisha, Aisha dai data sani wai tana neman kai wani matsayi a rayuwar nan wanda ita bata kaisa ba.
"Wallahi mama kinji rantsuwar musulmi koh bazan zuba ido ina kallon Aisha ba na rantse sai nayi sanadiyar barinta aikin nan dan bazan yarda ba?"
Nana ta fada da wani irin kaushi tareda kudirin dake ranta. Wani abu da ya girgiza zuciyar uwarta yana dasa wani sabon tsoron Nanar a zuciyarta duk kuwa da yanda itama takeso Aishan ta rabu da aikin nan koh ta halin yaya ne kuwa.
~~
B…