RAYUWAR SAMHAD

.....

by @maryamstar248

chat.***
PAGE 1️⃣8️⃣



بسم الله الرحمن الرحيم.


Girgiza kawai kawai Malam Umar ya yi tare da ficewa daga gidan zuciyarsa na ƙuncin halin da Mamam Nabila ta jefa Beelah, shi kanshi yasani sam baiyi dacen mace ta gari ba, sai yanzu ya ke danasanin ƙin bin shawarar abokinsa na ƙaro aure ko Maman Nabilar ta yi hankali.





Mubeen ya riga Samha tashi, ganin barci ta ke haiƙan ya sanya ya lallaɓa ya zare jikinsa tare da nufar toiket yai wanka, agaggauce ya shirya ya fice gidan zuwa restourance dan siyo musu abinda za su ci.

Bayan fitarshi ba jimawa Samha ta tashi, ganin bayanan ya sanya ta lallaɓa ta shiga toilet ta sake gasa jikinta sannan  ta fito ta zauna gaban mirro, haka kawai yau take son yin kwalliya, dan haka babu ɓata lokaci ta zauna gaban mirron ta shafe jikinta da lallausan mai mai ƙamshi sannan taɗanyi ƴan shafe-shafe a fuskarta, powder ta shafa da kwalli sai lip stick kalar jah, aiko bakinta yai bala'in kyau kasancewar lips ɗinta pink ne.

Gaban sip ɗin kaya ta nufa ta buɗe tare da ƙurawa kayan ciki ido, yau atamfa ta ke ra'ayin sakawa hakan ya sanya ta koma gefen sabbin kayan da suka yo shopping wanda harda ɗinkakkiyar atamfa Mubeen ya gani ya ɗauko ma ta kala uku.

Atamfar kalar jah ce mai ratsin fari da baƙi, ɗinkin riga da skert ne wanda akaiwa ado da stones sai walwali suke da ɗaukar ido.
Ɗas kayan suka zauna a jikinta lokacin da ta sanya, kayan sun sake fiddo da shape ɗinta mai ɗaukar hankali, tare da fito da zallar kyawunta.

Lokacin da ta gama ɗaura ɗankwalin atamfar ita kanta sai da ta tsaya ƙarewa kanta kallo a jikin madubin, idan tai rantsuwa akan tunda ta mallaki hankalin kanta ba ta taɓa yin kwalliya tai kyauba kamar haka to ba za tai kaffara ba, tabbas yau ta gasgata irin kyawun da ƙawayenta na makaranta ke faɗin ta na da shi.

Juyi ta yi ta kuma juyawa ta na sakin killer smile dan sosai ta tsinci kanta cikin farin ciki a yauɗin.


Cikin kula da taka tsantsan ta gyara bed room ɗin sama-sama dan babu wani datti, cikin tafiya ahankali kamar ƙaramar yarinya mai koyon tafiya ta fara takawa har ta isa farlo, kallo ta kunna dan ragewa kanta kaɗaici tunda babu kowa.

Ba ta jima da fara kallon ba ta ji horn ɗin mota, haka kawai ta raya a zuciyarta ƙila Mubeen ne   ya dawo duk da ba daga part ɗinsu ta ji horn ɗinba daga babban get ne, ilai kuwa  Mubeen ɗinne dan ba'ayi minti biyar da jiyo horn ɗinsa ba ta ji muryarsa ya na waya, samun kanta tai da miƙewa tsaye ta je bakin kofar parloun ta tsaya tare da riƙe handle ɗin ƙofar, duk da gabanta na faɗuwa amma haka ta daure ta tsaya.
Sallama Mubeen yai da wanda yake wayar sannan ya juyo da niyar shiga parloun, lumshe manyan idanuwansa yai tare da ƙara buɗe ƙofofin  hancinsa yana shaƙar ƙamshin turaren da yai mishi wellcome.
Yawo ya fara yi da da hannunsa da yakai da niyyar buɗe ƙofar,  caraf Samha ta damƙe hannun nasa da baiyi masauki ako ina ba sai akan ƙirjinta da suka fito ta saman rigar atamfar kasancewarta mai buɗaɗɗen wuya.

A hankali ya fara buɗe idanuwansa jin saukar lallausan tafin hannu akan nashi hannun.
Tar Mubeen ya buɗe idanuwansa akan Samha wacce ta caake cikin kwalliya wacce ta nemi tsayar da lumfashin Mubeen.




DA GA ALKALAMIN..✍️
MARYAM STAR⭐⭐⭐🌹RAYUWAR SAMHAD🌹(Abar tausayi ce😭)

WRITTING BY.....✍️✍️

MARYAM STAR ⭐⭐⭐