SARƘAƘIYA

Chapter 03

by @umaimahadogaya905

 Chapter3 Page 5

       Cikin sati daya M.d yayi iyakar bakin kokarin sa gurin ganin ya koya wa Fukhaihat yadda ake yin cikakkiyar alwala kamar yadda ya zo cikin littafan da suka nuna yadda manzon Allah salallahu alaihi wa sallama yake yi. Sannan ya koya  mata yadda za ta yi Salla daidai da fahimtarta da matakin ilimin da take da shi. Zuwa lokacin kuma ta iya suratul Fatiha da kuma Nasi da kyar. Saboda karatun babba wanda ya girma yana da wahalar dauka ba kamar lokacin kuruciya ba. Kuma da su take amfani gurin yin karatun Sallah Kamar yadda yake wajibi Sallah ba ta ingantuwa sai da Fatihatul kitabi. Kuma Yana da buri da kudurin ganin ya zage dantse iyakar bakin kokarin sa ya koya mata dukkan abin da ya dace a matsayinta na Mace musulma, irin su wankan tsarki da abin da ya kamata ta kauracewa a lokacin da ba ta cikin tsarki. Idan kuma har ya ga lokacin aikinsa zai danne nata,to zai yi cikiyar malamin da zai rika zuwa har gida yana koya mata idan har zai samu. A cikin kankanin lokaci Fukhee ta canza ta dawo nutsattsiyar mace kamar dai cikakkiyar musulma mai tarbiyya. Ta daina shigar banza da shashamci da shiririta. A yanzu ba ta shigar da ta wuce Abayas masu kyau da tsada. Haka nan ba ta da burin da ya wuce ta samu ilimin addini mai yawa har ta Kai matakin Malama wadda za ta rika koyarwa. A inda ta samu matsala gurin kwayoyinta ne kawai, domin ta zama addicted da su ba ta taba iya rayuwa ba tare da ta sha ba. Dole ya sanya M.d ya nemi rehabilitation center ya Kai ta.

  MASARAUTAR AGADAS

   DAKIN FULANI MAIRAMA

Zaune suke su uku a can cikin kuryar dakin Fulani Mairama kamar yadda suka saba a duk lokacin da suke tattaunawar sirri. Fulani  Mairama ta zabga tagumi Kamar yar da aka sanarwa da mutuwar iyayenta. Hajiya Lubba da Hajja Asime sai rattabo mata bayani suke Yi. Fulanni Mairama ta girgiza kai tana cire tagumin da tayi cike da sanyin murya take fadin "Gaskiya ni dai ba zan iya aikata wannan mummunan abu ba Lubba. Zuwa yanzu ni kam ma na fara saduda da sha'anin mulkin nan. Ki ga dukan wani kokari da  muke yi,Amma kullum da an doshe wannan ƙofar sai wata ƙofar ta sake bullowa." Hajja Asime ta maka mata harara tana fadin "ni fa dama na fuskanci kwana biyun nan gabadaya so kike ki canza. To dama wa ya gaya Miki sarauta ta ragwaye ce? Malama idan za ki saki ranki ki nemi mulki ko ta halin kaka ne ki tashi ki nema don rayuwar yanzu sai kana da madafun iko ake damawa a sha da Kai."

   Fulani Mairama ta girgiza kai "Gaskiya ba zan iya aikata wannan abun ba. Na baya ma da nayi yanzu damu na suke yi, wannan ma kenan da ban salwantar da rai ba kenan,ina kuma ga yanzu da kuke maganar kawar da Iqbal? Kuma ma ni wallahi yaron tausayinsa nake ji. Haka nan nake jin wani irin sonsa da kaunarsa a kahon raina tun Yana jaririnsa."

   Hajiya Lubba ta tabe baki tana fadin "Anya ko Asime ba asiri wannan shu'umar tsohuwar ta Yi wa Mairama ta daina sha'awar mulkin nan ba? Idan ba haka ba,ta ya muna tsaka da Shan gwagwarmayar da har yanzu ba mu fara fanshe walahar da muka sha ba,za ta saduda?

   Asime ta amshe zancen da cewa "kuma fa haka ne Lubba,kema kin ce wani abu. Ai ko wallahi ko da tsiya ko da tsiya-tsiya sai mun kwato hakkinmu a gurin annamimiyar tsohuwar nan. Haba! A ce ke mace kin zama handumbana kenan? Ki ci zamaninki ki ci da Yaya da jikoki? Allahu ya dauki ranta uban kowa ma ya huta." "Amin" Lubba tayi saurin amsa addu'ar.

   Fulani Mairama ta sauke ajiyar zuciya "wallahi ba wani asiri da Gimbiya Hadiza tayi mini,kawai ina jin zunubanmu sun yi yawa ne. Gashi kuma yanzu kuna maganar salwantar da rayuwa."

   Asime ta yi murmushi "Mairama kenan. Ai ranar biyan buƙata rai ba a bakin komai yake ba. Ban da abin ki da ki kwashi zunubanki ba tare da cikar buri ba,ai gara ki cika burinki idan ya so daga baya sai ki tuba gabaɗaya.Kinga ga biyan buƙata ga kuma gafarar Ubangiji." Haka Lubba da Asime suka saka ta a gaba suka cigaba da yi mata fanfo har sai da ta amince da abin da suka zo mata da shi.

***ABUJA***

Duk in da ran Daddyn Fukhee ya kai to a masifar tashe yake. Yanzu haka kaiwa da kawowa yake yi,yana tunanin mafitar da za ta fi masa sauƙi gurin cimma ƙudurinsa.  Tunaninsa gabaɗaya ya kulle bai taɓa tunanin aikin da ya taya Matarsa zai iya juye wa ya haɗe guri ɗaya da nashi ba sai da hakan ta faru. Gashi a yanzu sun yi wa juna nisa,nisa mai tarin yawa. Amma zai nemi surƙulu ya sanar da shi halin da ake ciki ya tabbatar saƙo zai isar mata kuma dukkanninsu za su samu mafitar matsalar su a gurinsa.  Ya juya ya nufi sif ɗinsa da niyyar ɗauko kayan aikinsa da za su sada shi da surƙulu, a daidai lokacin kuma Mommy ta samu nasarar buɗe ƙofar ta shigo ɗakin bakinta ɗauke da sallama. Daddyn Fukhee ya juyo a fusace yana mata wani irin duba. "Wai har sau nawa zan sanar dake ki daina shigo mini ɗakina kai tsaye?" Mommy ta rausayar da kai fuska cike da alhini take faɗin "Kayi haƙuri Alhaji, na jika shiru ne gashi tun ɗazu na kammala abin kari. Wai ma lafiyarka ko kwana biyu? Na ga gabaɗaya ka canza ba ka walwala sam." Daddy ya nuna ta da yatsansa manuniya cike da fusata kamar wadda tayi masa gagarumin laifi yake faɗin "Ban sani ba. Nace ban sani ba. Wai ma ba na sanar miki ki daina shiga sabga ta idan har ban saka da ke ba? Ko da yake, ina tunanin kin fara gajiya da zaman auren ne. Wallahi idan har ba ki fita a sabga ta ba ina daf da tsinke igiyar da take tsakanin na da ke. Oya fitar mini daga ɗaki." Mommy ta juya ta fita ciki a sanyaye kamar tayar da aka sacewa iska. Hawaye suna bin kuncinta ta nufi ɗakinta ko gani sosai ba ta yi. Zuwa yanzu ta fara gajiyawa da halayen Daddyn Fukhee, dama can haƙuri take yi da shi saboda ta san iyayenta babu abin da suka tsana kamar su wayi gari su ganta a cikin gidansu da sunan yaji bare kuma mutuwar auren gabaɗaya. Daddyn Fukhee kam dogon tsaki ya ja mata sannan ya ƙarasa bakin ƙofar ɗakin ya murza mata mukulli sannan ya koma kan abin da yayi niyyar yi.

  BAYAN SHEKARA ƊAYA

***KANO***

    Da gudu Fujeerat ta shigo cikin gidan tana gunjin kuka mai tsuma rai. Ummi dake gyaran sif ta yi watsi da kayan da suke hannunta ta nufo ƙofar ɗakin don jin kukan na Fujeerat. Kafin ta ƙarasa bakin ƙofar Fujeerat ta bankaɗo labulen ɗakin ta shigo ciki kamar wadda aka jefo. Kai tsaye Ummi ta nufa ta ruƙunƙume ta tana rufzar kuka kamar yau ne aka sanar mata da Abbanta ya mutu. Ummi ta ƙanƙame ta a jikinta tana shafa bayanta hawaye na ciko idanunta saboda yadda take jin kukan Fujeerat ɗin har ƙahon zuciyarta. Sai da Fujeerat ta sha kukanta ta ƙoshi sannan ta saki Ummi wanda itama hawayenta suka kasa daina zuba. Cikin muryar kuka Fujeerat take faɗin "Ummi,dan Allah ki sanar mini gaskiyar wace ce ni. Na gaji da jin habaici da tozarcin da mutane suke mini akan Abbana ba shine ainihin mahaifina ba,kuma hakan shine dalilin da ya sanya har yanzu danginsa ba su ne meni ba tun bayan mutuwar sa."  Ummi ta tsira mata idanunta masu kaifi a gare ta ba tare da tace da ita kanzil ba. "Ki yi haƙuri Ummi,amma ya kamata a ce zuwa yanzu kin daina ɓoye mini abin da ya kamata ace na sani. Ummi don Allah wane ne mahaifina? Ki sanar mini gaskiya ko hakan zai sanya na samu sassauci a raina. Ki sanar mini gaskiya ko da  ko ni ɗin ba ta hanyar aure aka haife...." Ƙaƙƙarfan marin da Ummi ta yanka mata a fuskarta ya sanya ta datse ƙarashen kalamant. Cikim kakkausar murya wadda ba ta taɓa jin Ummi tayi amfani da ita ba ta ji ta ambaci sunanta na ainihi "Hafsat!" Ba ta bata zarafin amsawa ba ta cigaba da faɗin "Har yaushe kika yi girman da za ki iya kallon cikin idanuwana kina jifana da irin munanan kalaman nan? Nace har yaushe kika yi wannan girman?"  Ummi ta faɗa cikin tsawa. Fujeerat ta fashe da kuka mai tsuma rai muryarta na kakkarwa alamun kukan da take yi yana fitowa ne tun daga ƙasan ranta tace "ki yi haƙuri Ummi,ban faɗi wata magana don na ɓata miki rai ba. Sai dan ki san cewar zuwa yanzu ya kamata a ce na san komai game da rayuwata. Ki tuna Ummi a wannan zamanin kiwon mutum ake ba na dabbba ba. Yanzu fitar da nayi gurin Shamsu zuwa yai ya sanar da ni iyayensa sun ce ba zai aure ni ba,saboda har yanzu babu wanda ya san ainihin mahaifina. Ki gaya mini Ummi har zuwa yaushe ne za ki cigaba da ɓoye mini abin da tuni mutane sun fara bayyana mini wani sashen nasa."

   Ummi tayi shiru ta kasa cewa komai. Ba ta san bayyana wannan sirrin da babu wanda ya sanshi   sai ɗaiɗaikun mutane. Ba ta son bayyana wannan sirrin saboda bayyanarsa wani ƙalubalen ne mai zaman kansa a gare ta da ita kanta Fujeerat ɗin. A daidai wannan lokacin kuma Malan Musa da matarsa Fauziyya suka yaye labulen ɗakin suka shigo. Tun daga  bakin ƙofar Malam Musa ya fara magana "Tabbas Fujeerat tayi gaskiya Samira,ya kamata ace zuwa yanzu kin sanar damu gaskiya game da samuwar Fujeerat a rayuwar ki. A wancan lokacin mun yi shiru mun rabu da ke ne ba tare da mun tilasta ki akan maganar ba,ba kuma wai don mun yarda da abin da kika faɗa ba ne,sai don mun fahimci yadda ba kya son yarinyar ta bar rayuwar ki. Samira, masu iya magana sun ce ranar wanka ba a ɓoyan cibi don haka ya kamata ki buɗe sirrin da kika binne shekara da shekaru saboda lokaci yayi da ya kamata mu san gaskiya,ta yadda za mu sanar da duk wanda ya zo neman aurenta ba tare da mutane sun ɓata zancen kamar yadda suke yi a yanzu ba.

  Ummi ta mayar da dubanta kan Malan Musa da matarsa Fauziyya har suka zauna daga  gefe. Banda hawaye babu abin da yake sintiri a dandamalin kumatunta. Ta share hawayenta sannan ta haɗiye wani malolo da ya tokare mata maƙoshi sannan cikin rarrauniyar murya ta fara magana.

  SHEKARU ASHIRIN BAYA

  Gudu drivern taxi ɗin da na ɗauko shata daga tashar kano zuwa Zariya in da nake karatu,kasancewar yau Abbana da Yayana ba sa gida ni kaɗai nake koma wa makarantar a karo na farko tun da na fara karatu a A.B.U Zariya. Wayata ce a hannuna ina duba saƙwannin abokan karatuna da suka turo mini a daidai lokacin da direban yaja wani wawan birki sannan na jiyo sautinsa yana salati da ƙarfi. Ko da na ɗago kaina daga kallon wayar da zummar tambayarsa abin da yake faruwa tuni ya ɓalle murfin motar ya fice daga ciki motar,hakan ya sanya nima na ajiye wayata a cikin jakata sannan nima na bude motar na fito domin na baiwa kwarkwatar idanuna abincinta. Sai dai tsananin tashin hankali ya bayyana a fuskata a daidai lokacin da maganaina suka yi tozali da wata mace da tsohon ciki kwance a ƙasa hannunta guda dafe da cikinta yayin da jini yake fita daga jikinta. Gabaɗaya direban ya rikice ya gigice ban da salati da tasbihi ba abin da yake yi,wanda cikin rikicewa ma baya sanin lokacin da yake ɗauko salati ya dire a tasbihi ko kuma ya janyo wata surar. Duk da yadda ni kaina na firgita musamman da ganin gurin ba hanyar tafiya a ƙafa ba ce kuma daji ne babu gida a gaba balle baya, amma haka na ƙwararawa zuciyata sannan na ƙarasa ga matar. Da taimakon direban muka cicciɓe ta muka sanya a mota sannan muka cigaba da falfala gudu domin mu yi hanzarin sa da ta da asibiti. Sai dai sanin cewar ko da mun je asibitin ba za mu samu likitan da zai duba ta ba tare da Police ba hakan ya sanya tun kafin mu ƙarasa cikin garin na nemi lambar ofishin ƴan sanda na kira na sanar da su halin da ake ciki,kafin mu ƙarasa tuni ƴan sandan sun ƙarasa asibitin da suka sanar da ni shine mafi kusa daga in da nake.

   Likitoci sun taru a kan matar da har yau ban san sunanta ba. Kuma sun yi nasarar ceto rayuwarta. Sai dai sun sanar da ni  cewar akwai buƙatar a yi mata aiki cikin gaggawa domin ceto rayuwar abin da yake cikinta wanda yake da watanni bakwai amma yana cikin barazanar rasa rayuwar sa. Ba tare da zaɓi na biyu ba na sanya hannu tare da biyan kuɗin aikin da kuɗin da ya kasance na makarantana da Abba  ya ba ni nayi ɗawainiyar makaranta da shi.  A wancan lokacin ban yi tunanin makomar karatuna da kuma abin da zan sanar da gida ba idan na neni wani kuɗin fatana kawai shi ne a yi aikin a gama lafiya kuma a yi nasarar ceto rayuwar uwar da abin da yake cikinta.
  Kuma  Alhamdulillahi,an yi nasara an ceto rayuwar jaririyar kamar yadda aka yi nasarar ceto rayuwar mahaifiyarta. Ina cikin jinyar mahaifiyar kasancewar yarinyar tana Nursery a cikin kwalba,Yaya ya turo mini da kuɗi ba tare da na kira shi na tambaye shi ba. A cewar sa ya ji a jikinsa zan buƙace su. Nayi murna sosai hakan ya  sanya na je makaranta na ƙarasa abin da ban yi ba. Bayan na dawo daga asibitin ne na tarar da mummunan labarin ɓatan matar nan wadda har zuwa lokacin ban san sunan ta ba. Na yi kuka na yi baƙinciki kafin na haƙura na fawwala wa Allah komai. A kullum ina zuwa na duba jaririyar da na yi wa huɗuba da Hafsat sannan nake yi mata inkiya da Fujeerat sannan na koma makaranta har zuwa lokacin da aka cire ta a kwalba. Kasancewar tun bayan ɓatan mahaifiyarta na sha maganin da yake kawo ruwan nono ni na cigaba da shayar da ita. Bayan na koma makaranta da ita ne hukumar makaranta ta bincike ni akan yarinyar kasancewar kundina ya nuna ni budurwa ce,ni kuma na kafe kai da fata cewar yarinyar ƴata ce. Haka hukumar makaranta suka kira iyayena kuma suka tabbatar da ban da aure hasalima su ba su san da zaman yarinyar ba. Ina ji ina gani hukumar makaranta suka kore ni,amma ban ji ko ɗar ba don nayi alƙawarin zamarwa Fujeerat uwa har ƙarshen rayuwata.
    Ko da na dawo gida aka tuhume ni akan yarinyar suma kamar yadda na sanar a makaranta haka na sanar musu ƴata ce. Tun daga wannan lokacin babu wanda ya ƙara ɗaga maganar ni kuma na haƙura da kowacce makaranta na rungumui ƴata ba tare da na biyewa cin mutunci da ɓatancin da mutane suke mini ba,har lokacin da muka haɗu da Muhammad wanda ya amince da ni, kuma ya ƙi rabuwa da ni duk yadda mutane suke kai masa sukana,wanda hakan ya janyo mini baƙin jini sosai a danginsa har suka haramta masa amfani da dukiyarsu, shi kuma yace ya ji ya amince zai ciyar da ni da guminsa. Sai bayan aurenmu da ya same ni a budurwa na sanar da shi komai game da Fujeerat,shi kuma ya ɗaukar mini alƙawarin riƙe ta a matsayin mahaifi har ƙarshen rayuwarsa." Ummi ta ƙarasa labarin tana fashewa da matsanancin kuka. Ba ta son tuna ba ita ce ta haifi Fujeerat ba, ba ta son tuna cin zarafi da ƙagen da mutane suka sha yi mata a lokutan baya. Ɗakin yayi tsit ba ka jin komai sai shassheƙar kukan Ummi da Fujeerat. Fujeerat ta rungume Ummi cikin kuka take faɗin "Duk duniya Ummi ba ni da wata uwa bayan ke,ke ce sanyin idaniyata farincikin raina. Na miki alƙawari daga wannan ranar ba zan sake tada wannan maganar ba,kuma ba zan sanar da kowa ba ke ce kika haife ni ba,sannan ba zan taɓa bari maganar mutane ta ɗaga mini hankali ba. Zan jira lokacin da wani mai irin zuciyar Abbana zai zo ya amince da ni ya aure ba gori ba kyara kamar yadda Abbana yayi miki." Ummi ta sake ruƙunƙume Fujeerat tana jin sonta na ƙara huda jini da tsokarta. Malan Musa da matarsa suka miƙe jiki a  sanyaye suka bar ɗakin cikin ransu suna jinjinawa Samira akan sadaukarwar da ta yi wa Fujeerat......

Chapter 3 Page 6

***MEXICO***

    Zuwa yanzu Fukhaihat ta canza    gabaɗaya,ta koma nutsatssiya mai kamala. Ba ta gajiya wa gurin bincike da neman ilimin addini. Zuwa yanzu ta hadda ce izufi biyar cif da kuma ƙananan litattafan addini irin su fiqhu,hadisi da tauhid. M.d ya tsaya a kanta tsayin daka kama daga kan lafiyarta,cimarta dama iliminta. A duk lokacin da yake gida kuma  yake free ba tare da wani aiki ba to za ka same shi ne yana biyawa Fukhaihat karatu. A duk lokacin da ya kalle ta ya ga tarin cigaban da ta samu ta dalilinsa,sai yaji wani  irin farinciki da alfaharin ceto rayuwarta    daga duhu zuwa haske da yayi. Haka nan yana jin gamsuwa a karan kansa ko ba komai yana ƙoƙarin cika ayar da Allah maɗaukakin sarki yake cewa (Yaa ayyuhallazina amanu quuu andusakum,wa ahleekum narah. Waro ya ku waɗanda kuka yi imani ku tseratar da kanku da iyalanku daga wuta).

    Kamar kullum idan yana gida,yana kwance akan kujera doguwa three sitters. Hannunsa ɗaya akan ƙirjinsa yayin da ɗayan ya ɗora kansa a kai. Fukhaihat ta fito daga kitchen hannunta ɗauke da tray mai ɗauke da butar shayi da ƙananan kofunanta. Fuskarta ɗauke da murmushi take kallon M.d a lokacin da take takowa cikin falon. Idanunsa da suke    lumshe    ta zubawa idanu tana kallon yadda zarazaran gashin idanunsa suka kwanta luf akan fatar Fuskarsa. Ta ja stool ta ajiye trayn sannan ta zauna a gefen sa tana kallonsa tana sakin murmushi. Sosai take tsintar kanta da farinciki idan tana duban Fuskarsa,sai dai ba ta samun damar kallonsa a lokacin da yake farke sai dai lokacin da yake barci kamar dai yanzu. Ta sanya hannunta ta shafa gefen Fuskarsa a hankali tana jin yadda wani abu yake janta gare sa. Duk da cewar M.d yana kulawa da ita,yana zama yayi hira da ita har ma su kan zagaya a wasu lokutan domin yawan buɗe ido amma wani abu mai alaƙa da soyayya ko aure bai taɓa shiga tsakaninsu ba.

"Wataƙila har zuwa yanzu ba ya jin soyayyata a ransa,tausayina kawai yake ji." Ta faɗa a hankali kamar mai raɗa yayin da hawaye suka fito daga idanunta suka sauka a gefen Fuskarsa. M.d da duk abin da take yi yana sauraren ta yayi saurin buɗe idanunsa yana kallonta wanda hakan yayi daidai da sake ɗigowar hawaye daga idanunta. Sai dai a yanzu saɓanin Fuskarsa a cikin tsakiyar idanunsa hawayen suka ɗigo. Ya lumshe idanunsa hawayen suka ziraro ta gefen idanunsa sannan ya sake buɗe su a karo na biyu yana duban Fukhee da sam ba ta san da buɗe idanunsa ba. A hankali kamar mai shakkar taɓa ta ya ɗa hannunsa ya riƙo fuskarta,wanda hakan ya ankarar da ita farkawarsa tayi saurin ɗago hannunta da zummar share hawayen amma M.d ya hana ta hakan ta hanyar riƙe hannun da ɗayan hannun nasa da ya cire kansa daga kai sannan ya sake ranƙwafo da kanta zuwa daidai fuskarsa. Har hancinsu na gugar juna. Yana duban ƙwayar idanunta yake faɗin "Mai yasa kike kuka? Ko kina son nima nayi ne?" Cikin lallausar murya yayi maganar wadda tun da take da shi ba ta taɓa jin sa da ita ba. Hakan ya sanya ta shiru tana duban cikin idanun nasa a karo na farko a rayuwarta. Wani irin magnet ta ji yana fitowa daga idanunsa suna mannewa da nata. Haka nan take ganin wani yanayi a cikin idanun wanda ba ta gane me suke nufi ba. Asaad yayi amfani da harshensa gurim goge mata hawayen fuskarta sannan ya cigaba da kallon idanunta yana magana "kin san yadda nake jin damuwarki a cikin raina kuwa?" Ya riƙo hannunta guda sannan ya ɗora a saitin zuciyarsa wadda take harbawa da wani irin yanayi a lokacin. Yayi  gajeren murmushi sannan yace "Fukhee before you i had dreams,but after you,i found a reason to fight for them. My F before you i had a heart,but after you,i discovered what it truly meant to love. My Dear, you are the smile behind my happiness,the peace behind my silence,and the strength behind my determination. If i could live my life a hundred times, i would search every corner of the earth just to find you again and make you my wife. Fukhaihat i love you beyond words,beyond distance,beyond time itself."

    Fukhaihat ta  fashe     da  kuka    tare    da  faɗawa jikinsa tana jin wani irin daɗi yana ratsa zuciyarta da jiki da tsokarta. Cikin muryar kuka take faɗin " Yaya,every day i thank Allah for bringing you into my life. You are not just the love of my life;you are the reason my life feels completed. Na gode Yaya,Thank you for choosing me and loving me."  M.d ya lakace mata hanci "Iyye! Dama haka matar tawa ta iya kalamai ban sani ba? Ko da yake ai ba a taɓa mini ba! Ya ƙarasa maganar yana langwaɓar da kai gefe tare da turo leɓe gaba. Fukhaihat ta fashe da dariya sai kuma ta yi saurin ɗaga shi tana rufe fuskarta alamun kunya. M.d ya miƙe da sauri ya riƙe ta sannan ya cire hannun daga fuskarta ya ɗage gira ɗaya yace "really? Wai kunya ta kika ji? Cab ashe ko da sake. A haka za mu yi angoncin kina jin kunya ta? Aikam Fukhaihat ta sanya ƙarfi ta fincike jikinta ta falfala bedroom da gudu."

VILLA CAPTAL STATE ABUJA

  Mr. President ya zauna a kusa da matarsa Mrs. Khaujud wadda ta kasance uwar gida a gare sa kuma first lady,fuskarsa na bayyanar da damuwar da take ransa ganin yadda ta zabga tagumi hawaye na bin kumatunta. Ya san wannan damuwar,wannan hawayen da wannan tagumin akan abu ɗaya ne, abun kuma da tun a shekarun baya ya kasa yi mata maganinsa. Jiki a sanyaye ya sanya hannunsa ya kamo nata hannun da ta rafka tagumi da shi ya rintse a cikin nasa. Muryarsa mai cike da kwarjini da haiba ta ratsa da rauni da damuwar  halin da ya ga matarsa mafi soyuwa a ransa a lokacin da ya fara mata magana "Masoyiyata Khaujud, har sai zuwa yaushe zan daina ganin zafafan hawayen nan naki masu ƙona mini zuciyata tamkar saukar ruwan dalma a cikinta? Sau nawa zan sanar dake kuka ko damuwa ba su ne za su dawo mana da Fakiha ba?" Ya dakata kaɗan yana kallon yadda hawayenta suka ƙara gudu a dandamalin kumatunta kamar an buɗe fanfo. Sosai har cikin ransa yake jin ciwon halin da Khaujud take shiga, saboda yadda yake jin ta a cikin ɓargo da jijiyarsa. Ya cigaba da magana kamar haka "Shin Khaujud ta manta da cewa Allah ne mai bayar wa kuma mai karɓewa a duk lokacin da ya so? Mai yasa kike so ki bar sheɗan yayi galaba a kanki ta hanyar wasa da imaninki? Kin fa karanta kin kuma sani, manzon Allah salallahu alaihi wa sallam yace (Mankana yu'uminu billahi wal'yaumil akhiri, fal yu'uminu bil ƙadri khairan au sharran) amma mai yasa ke kika kasa imani da wannan ƙaddarar taki? Kin manta da duk kwakwarmayar da muka yi a baya ne? Kin manta tulin ƙaddarori da ƙalubalen da muka fuskanta a shekarun baya da suka shuɗe. Ina mun fafata da ƙaddarar da tafi wannan kuma mun jure,amma mai yasa kika kasa jure wannan ƙaddarar Khaujud ? Ina tsoron rashin yadda da wannan ƙaddarar taki ya zoɓe dukkanin ladan ƙaddarorin da kika yadda da su."  Mrs. Khaujud ta girgiza kai "ba zaka gane bane your Highness. Akwai ƙuna ace kasha wahalar laulayi na tsawon lokaci sannan kasha azabar naƙuda,kuma kana cikin yanayi na jinyar wannan ciwo a samu wani mara imanin da ya ɗauke maka abin da ka haifa ko ganin farko baka mishi ba. Akwai ciwo ka rayu tsayin shekaru kana tsammanin da babu tabbas a cikin sa. Akwai ciwo ka riƙa raba tunanin ka akan wani makusancinka ko yana raye ko ya mutu ? Idan yana raye  a ina yake? Ya ci abinci? Ya sha ruwa?  Yana da makwanci ko kuma a titi yake kwana? Babban abin takaicin shine ban san addinin da yarinyar nan take ciki ba. Musulunci ne ko kirista?  Allah kaɗai ya sani." Mr. President yayi shiru yana ba daɗi a ransa, sai dai sanin rauni a gurin sa kamar ƙara wa Khaujud nauyi ne ya sanya   ƙarfafa  kansa sannan ya sake damƙe hannun Khaujud cikin nasa sannan yace "wannan ita ce ƙaddararta. Ki sani Ubangiji ya fi mu sanin halin da za  ta iya shiga ciki. Amma ya zaɓi ya nisantata da mu,hakan yana nufin shine alkhairi a gare ta da gare mu baki ɗaya. Don haka addu'a kawai ya dace mu cigaba mata Allah ya sa tana hannu na gari,idan da rabon kuma mu gana da ita Allah ya kawo mana mafi sauƙi da za ta sada mu da ita"