SARƘAƘIYAFree

ArewaPen original

General fictionFreeOngoing

SARƘAƘIYA

  • 1views
  • 6chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

ongoing

No synopsis yet.

Sample · Chapter 1

SARƘAƘIYAH Mallakar Umaimah Ado Gaya (Ummu Ahmad) Sadaukarwa Ga Auntyna mai daraja Amina Haruna Hassan New Edition 2026 *** Tsokaci     Wannan shi ne littafina na farko da na fara fitarwa. Saboda haka ina roƙon masu karatu da su yi haƙuri da duk wani kuskure da za su iya gani a cikinsa.    Bayan kun kammala karantawa, ku bar tsokacinku, ku yi like da share domin ƙarfafa mana gwiwa.    Haka kuma ina roƙonku da ku sanya Auntyna Amina Haruna Hassan cikin addu'o'inku. Allah Ya ba ta zuri'a ta gari mai albarka. Chapter 1 Page 1 Gabatarwa     Fujeerat Muhammad Isma'il kyakkyawar yarinya ce mai kamala da nutsuwa. Allah Ya hore mata kyau gwargwadon iko. Sunanta na asali Hafsat, sai dai iyayenta da na kusa da ita suna kiranta da Fujeerat.    Tana da fata mai launin chocolate, doguwa ce amma ba sosai ba, sannan tana da cikakkiyar sura irin ta "number 8". Allah Ya azurta ta da yalwar gashi, na kai da na gira, tare da dogayen gashin ido masu ƙara mata kwarjini.            Idanuwanta  farare ne masu sheƙi, yayin da ƙwayar idanunta ke da launin ruwan maroon mai haske.     Mahaifinta, Malam Muhammad haifaffen Jihar Adamawa ne, yayin da mahaifiyarta 'yar asalin Kano ce. Sana'ar mahaifinta ta sayar da kayan miya ce, kuma Allah Ya hore masa ɗan abin hannu da yake ba shi damar kula da iyalinsa cikin rufin asiri.    Fujeerat ita ce kaɗai ƴarsu, don haka tana samun kulawa da ƙauna ta musamman daga iyayenta. Suna rayuwa ne a cikin birnin Kano cikin kwanciyar hankali da fahimtar juna. ******     Wata rana bayan an tashi daga makarantar Islamiyya, Fujeerat da ƙawayenta suka kama hanyar gida cikin nutsuwa. Kowacce daga cikinsu tana tafiya cikin kamala da nutsuwa, suna ɗan tattaunawa cikin raha da annashuwa.   Da suka isa layinsu, kowacce ta kama hanyar gidansu. Fujeerat kuwa kai tsaye ta shiga gidan da suke haya mai ɗauke da ɗakuna biyar da bayi guda biyu. Lokacin sallar Magariba ne, don haka tsakar gidan babu kowa. Ta wuce ɗakinsu ta tarar da Umminta tana sallah. Cikin sauri ta cire kayan makaranta, ta sauya zuwa kayan gida sannan ta yi alwala ta shiga don yin sallah.Bayan ta idar, ta gaida Ummin cikin ladabi. "Fujeerat, yau kuma ina kuka tsaya har aka kira sallah ba ku dawo ba?" Ummi ta tambaya. Cikin girmamawa Fujeerat ta amsa, "Wallahi Ummi, mun je gaisuwa ne. Mahaifiyar wata ƴar ajinmu ce ta rasu." "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Allah Ya jiƙanta da rahama," cewar Ummi. "Amin Ummi," ta amsa cikin tausayi. Ummi ta miƙe tana naɗe sallayarta. "Ga abincinki can, ki ci kafin ya huce." Ta nuna mata inda aka ajiye abincin, yayin da Fujeerat ta miƙe domin cin abincin cikin biyayya.    Fujeerat ...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters6
premium0

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play