RAYUWAR SAMHAD

.....

by @maryamstar248

BOOK TWO PAGE 2⃣6⃣

Idan damuwa sa kaɗaici sukaimin yawa photon Ummana nike ɗaukowa ina kallo ina kuka, ina faɗa ma ta dukkan abinda akaimin.


BAYAN SHEKARA BIYAR.

Bayan na tsallake tarin ƙalubale na rayuwa, yanzu na girma na daɗa yin wayo da hankali, nasan daidai da ba daidai ba, nasan maisona kuma nasan mai ƙi na.
Abinda na fuskanta yanzu da shekaruna suka kai na girma shine rashin samun kulawa ta jiki da lafiya, su Anty Zee duk sun girma yanzu kusan shekara Anty Zeey ashirin, kuma ta kammala karatun secondary daƙyar dan ba garatun ne a gabanta ba, sau biyu ta na maimaita jarabar qualifyn. tun da ta samu ta zana waec da neco shikenan da jingine maganar karatu gefe, batada aiki saina yawace-yawace zuwa gidan ƙawaye da kuma fita da samari, tun Abbu bai fahimta ba har mutanen unguwa suka ankarar da shi, da yaje da niyar ɗaukar mataki nan take Hajiya Adama ta dakatar da shi ta nuna bai isa ya takurawa ƴarta ba.


Anty Fauzy kuma ta na shekara sha takwas a lokacin, amma halayyarta ba irin ta Zee ba ce, ita bata kula samari amma akwaita da ƙarya da kai kanta inda Allah bai kaita ba, sannan ta na so idan ta na waje kowa yasan da zuwanta, ko a gida babu ruwanta da ni bata shiga harkata ko kashe ni Anty Zee zatai a gabanta ba za ta kula ni ba, idan kaga ta lulani to aikena zatai ko wani aiki zanyi ma ta, wanda nikuma cikin rawar jiki nike yin duk abinda ta sakani saboda har zuciyata ina sonta.


Haka rayuwa taita gurgurawamin yau da daɗi gobe babu, yanzukan na fidda kowa a raina sai Ummana da Umma Suwaiba, duk da dai Umma Suwaiba ba ganinta nike akai-akaiba, amma nasan ta na sona sosai, dan itace keyimin dinkuna da sayomin ƴan mayuka na shafawa da sauran tarkacen abin buƙata.


Hakanan naci gaba da rayuwa aduk yanda na sameta, ba ruwana da ƙawa ko saurayi harkar gabana kawai nike, duk da ƙarancin shekaruna bai hana idan na fita samari su biyo ni da zancen soyayyaba, akan hakan ba ƙaramin worning Hajiya Adama ta shata min ba, ni kuma dama ko bata hanani kulasu ba bazan kulasunba tunda basune a gabana ba.