GIDAN YAWA

Episode 2

by @zahraroyal

GIDAN YAWA

By

Zahra Royal Star

Episode 2

House no 13 Bayan ETC Katsina State Nigeria

Saurin tashi tayi hango Baba dauke da kaya a bak’ar leda tana murmushi da gudu ta tafi tarbosa tana k’ara fad’ad’a murmushinta.

“Baba sannu da dawowa”

“Yawwa Mamana ya gidan?”

“Lafiya lau Baba”

Ta fad’a tana murmushi sosai.

Hango ta tsaye gefe guda tana ta bak’in rai yasa Baba idasowa inda take yana zama akan tabarmar dake shinfid’e barandar.

“A’a Bahijja minene aketa bakin rai haka?”

“ba komai”

Cewar Bahijja tana faman b’ata fuska kamar zatai kuka.

Umma ce ta fito tana cewa.

“Kai ma dai Mlm ai kasan ba abunda za’ai mata iskanci ne kawai irin na Bahijja haka nan ma kawai saita fara fushi kamar mai Aljanu”

Sauke ajiyar zuciya Baba yayi yana girgiza kai kawai Umma ta kai ta zauna kusa dashi.

“Kuzo nan kaya na gani a hanya shine na sayo maku”

Baba ya fad’a yana fito da wasu kaya dogayan riguna ne masu Kyan gaske ya fara fitar da wata mai kalar ruwan k’asa yaba Zahra dake zaune kusa dashi da wani kalar murna ta rungume Baba cikin jin dad’i tana masa godiya kamar bakinta zai tsage.

Bahijja ma ya d’akko ruwan k’asa ya mik’a mata tana b’ata fuska ta amsa idonta na kan rigar da aka bawa Zahra.

“Ke wato kinfi k’arfin Kiyi godiya ko?”

Cewar Umma tana jefa mata harara.

Da sauri ta ce.

“Baba an gode”

Murmushi kawai yayi yana duban Mama itama ta mik’a mata tata rigar, da murmushi akan fuskarta ta ce.

“Ah Ah au Mlm harda ni a ciki?”

“Gashi kuwa Mmn yara”

“Kai amma mun gode fa Ubangiji ya k’aro bud’i”

Cike da jin dad’i ya amsa.

Can sukaji muryar Bahijja na cewa.

“Ni gaskiya wannan kalar nafi so”

Tana aje tata ta d’auki ta Zahra tana turo baki gaba.

“Kee kinsan Allah zan b’ata miki rai Bahijja, miye haka kike yi ne wai?, wanne irin bak’in hali kika d’akko ma kanki ne?”

“Ya isa haka Mmn Yara”

“Haba Mlm ace Kamar Bahijja da bata wuce shakaru 15 ba amma tasan irin wannan bak’in halin tun yanzu kenan?”

“Umma ta d’auka kawai ba komai nasaka tatan”

Cewar Zahra tana murmushi kad’an.

Jinjina kai kawai Umma tayi tana wurgama Bahijja wani kallon da yasa ta barin wajan d’auke da rigar Zahra data aje tata.

Itama Zahra d’in tata ta d’auka tana shigewa d’aki.

“Wallahi Mlm ina jin tsoron wannan halin ja Bahijja harga Allah”

“Amma dai kin san yarinya ce zata daina nan gaba kad’an”

“Haka kullum kake fad’a fa Mlm amma ni ina hango wani abun ne daban su duka suna da mugun banbancin halaye”

Baba zai magana saiga Safiyanu ya shigo jikinsa duk zufa yana zama kusa da Baba.

“ah ah Babana yaya dai?”

“Hmm Baba na gaji da wannan aikin ne wlhy”

Wani kallo Umma tayi ma Safiyanu tana cewa.

“To wai kai idan baka tashi Ka nema ba arzik’in kana zaune zaizo ya iskeka ne Safiyanu?, kai da kake da son rayuwar jin dad’i sosai ta k’arya”

“To ni Umma wannan aikin na gidan Biredi baifa dace dani ba kwata-kwata sabo……..

“Kai gafara can Ka rufe min baki, to kai d’in waye wai da har kake cewa wani wai kafi k’arfin aikin gidan biredi. Ai kaida Bahijja ban san wadda yafi wani bak’in hali ba wallahi”

“Babana ai shi samun halal da wahala yake kaji, amma yau da gobe ta wuce wasa zakaga kamar bakai ba insha Allah. Yanzu tashi kaje ciki Ka watsa ruwa”

Tashi yayi yana wuce wa d’akinsa Umma tabisa da kallo tana girgiza kai.

“Mlm……”

“Minene kuma Mmn yara?”

“Uhm Mlm Akan yaran nan ne mn kaga Safiyanu da Bahijja walla…..

Baba ya katse Umma da cewa.

“Addu’a kawai ya kamata kina masu yanzu ba magana kullum ba”

“Addu’a ai kullum sai anyita amma ya kamata kaima kana masu fad’a amma sai nake ganin duk sanyi kake masu fa Mlm”

“Ai shi fad’a ga yaro baya gyarashi Badiya kawai nasiha da addu’a shine kawai”

Ya idasa maganar yana mikewa ya d’auki buta ya barta nan da binsa da kallo itama ta kasa gane Mlm abunda yake nufi duk da tasan abunda ya fad’a gaskiya ne, amma dole wani abun sai ana tsawartarwa yaro akansa ita kam indai sukai saita masu fad’a danta tsani wannan halin nasu sosai wallahi…………