Episode 3
by @zahraroyal
GIDAN YAWA
By
Zahra Royal Star.
Episode 3
Unguwar Yammawa, Rimaye Kankia Local Government Katsina state Nigeria
Zama yayi yana bak’in rai, Mama ta dube shi tana girgiza kanta ta sauke ajiyar zuciya.
Zatai magana kenan aka zuk’e da wani irin ruwa kamar da bakin kwarya. Hankali a tashe Mama ta dafa bango ta mike da kyar, dan har d’akin nasu ya fara zubar ruwa daga sama.
“Mama ki zauna daga can gefe ni zansa roba na rinka kwalfe ruwan”
Sakin ajiyar zuciya ta sake yi tana zama can k’arshen d’akin inda baya zubar. Mita tuna kuma saita mik’e tana lalubar wata jaka, canta fiddo wata bak’ar leda a ciki, ajiyar zuciya ta sauke, jin K’anzon data tuno dashi yana nan Allah baisa sun cinye ba, danta manta dashi ne Sai yau Allah yayi ta tuno.
“Kaga Babawo zo maza ga wani sauran k’anzo nan ka jik’asa koda magi ne kaci haka nan, zama da yinwar bashi da dad’i”
Tahowa yayi da sauri bayan ya zubar da ruwan daya taru ya sake tara rubar har lokacin ruwa ake sosai.
Amsa yayi yaje ya juye a wani kwano ya tarbo ruwa ya jik’a da fitarsa yaga Mama bata tarba ruwa ba yasa shi tsayawa ya tara masu abun ruwansu.
Yana shiga yaga ta taso ya ce.
“Ina zaki kuma Mama ana ruwan nan?”
“Zan lek’a barandar nan ne na tarba mana ruwan sha kasan na manta ne, dama kuma bamu da ruwan bare kud’in saya, gara Allah ya kawo saimu tarba”
“Kiyi zamanki kawai ai na tara mana ruwan”
Zama tayi tana murmushi tana saka masa albarka. Koda shi ta tsira wannan yaron a duniya aita gode ma Allah, abu d’aya ne dake b’ata ranta game da Babawon shine baya jin magana baya kuma d’aukar wulak’anci a wajan koma waye daga cikin gidan, shi yasa da yawan mutanan gidan ke ce masa d’an wake kafi ubanka mai bak’ar zuciya, abun na cima rai, tayi-tayi domin ya aje wannan d’abi’ar ta rashin hakuri amma ina kullum dai addu’a take masa Akan Allah ya rage masa zafin zuciyar nan.
Haka nan ya fara cin k’anzon ba magi ba mai, sai tuttusawa yake dan ance baki shi yasan dad’i.
Tasowa yayi kusa da Mama dake kallonsa da tausayi ya ce.
“Mama kema ki ci to”
“A’a Babawo kaci kai Ka k’oshi”
“Mama muci tare dai dan Allah”
Tana murmushi zata saka hannu ya girgiza mata kai ya fara d’ebowa yana bata da kansa, wani irin jin k’ai da son d’an nata ya k’ara shiga ranta.
Haka suka ci badan wai sun k’oshi ba amma a rage yinwa. D’akin duk ruwa ya b’ata ciki danma Babawon na fitar da robar da suka tara inda ruwan ke zuba yana zubarwa a waje ya sake tarawa.
Sai cikin d’are wajan sha d’aya sana Abba ya dawo jikinsa duk ruwa sai atishawa yake.
“Cikin ruwan nan kuka dawo Abban Babawo?”
“Wallahi kuwa kin dai gani neman halal ne da wahala”
“Sannu to Allah dai yasa wannan karon a dace samun aikin?”
Saida ya tsane jikinsa ya zauna yana sauke lumfashi ya ce.
“Ina yaron nan?”
“Wai Babawo ai ya tafi d’akinsu, wata kila yanzu yayi bacci ma”
“Kunci abinci kuwa?”
“Eh to na samar mana wani k’anzo munci”
Girgiza kai yayi yana sake cewa.
“Yanzu duk girman gidan nan ba wadda zai baku abinci?, na tabbatar sun dafa dan duk sunfi ni k’arfi ni ba wata cikakkiyar sana’a”
“Kamar baka san yanayin gidan nan ba Abban Babawo?”
“Na sani Amma abun na cimini rai, ace uwa daya Uba daya muke dasu Gasu nan wajan mu biyar a cikin gidan nan Hindatu ce kawai babu tana gidan mijinta, Amma ga Yaya Bature ga Yaya Basiru ga Sama’ila ga Zubairu Amma ace cikin matansu a rasa wacce zata dafa wani abu ta baku?”
“Idan da sabo ai an saba kai kam”
Jinjina kai yayi Cike da tak’aici ya ce.
“Idan har Allah yasa na samu aikin nan dole mubar garin nan baki d’aya domin bazan iya zama a cikinsu ba”
“To Abban Babawo ina zamu koma?, wadda kasan cewa Ku duka haka kuka taso a gida d’aya, wadda kasan ko mutum
Ya samu bud’i Sai dai ya gyara b’angaransa amma ba maganar tashi?”
“To daga kaina za’a fara”
Ya fad’i maganar babu wasa ko wata fargaba, danya rantse muddun dai ya samu bud’i ya gama zama a garin bama cikinsu ba.
“Yanzu yaya an samu aikin?, sana kaci abinci kaima?”
Sauke wani lumfashi yayi mai zafi kamin ya ce.
“To sun dai amshi takardun namu sunce zasu nememu amma babu rana sai dai munji kira kawai. Abinci kuma mun tsaya nida abokina Shamsu ya sai mana munci, dan ni idan banda shi ko
Kudin Motar ma ina na gansu bare na abinci?”
“To Allah dai yasa a dace a nan kusa”
Ya amsa da amin yana mik’ewa tsaye yana sake duban d’akin nasu dake naso ko ina rabin d’akin a jik’e danma suminti ne a shafe a k’asan, saukin ruwan zuwa lokacin ya d’an lafa sai d’an yayyafi da akeyi a garin……..