MABANBANTAN ZUKATA

Chapter 1

by @maryamstar248

***
𝙈𝘼𝘽𝘼𝙉𝘽𝘼𝙉𝙏𝘼𝙉 𝙕𝙐𝙆𝘼𝙏𝘼❤️‍🩹❤️‍🔥

 𝙎𝙏𝙊𝙍𝙔 & 𝙒𝙍𝙄

Chapter 1-------------------

LEGOS NIGERIA

AJEGUNLE

Gidan Ale Idi, babban gida ne da ke ɗauke da mutane mabanbanta, tun daga kan mahaifiyar Ale Ido me suna Inna Tabawa, har kan matan Ale Idi da suka kasance su huɗu reras.
 Inna Lantana ita ce mace ta farko da Ale Idi ya soma aura tun auren saurayi da budurwa, yaranta shidda reras biyar maza ɗaya mace ita ce ƴar auta.
Sai Inna Balaraba mace ta biyu da ya aura bayan Inna Lantana, ita ma ta zazzaga na ta yaran guda takwas reras maza da mata (Nan gaba zaku ji sunan kowa kudai ku biyo ni.)
Sai Inna Sabuwa itama ce mace ta uku daya auro bayan matansa biyu itama da tata turigar ƴaƴan su shida, Maza biyu ma ta huɗu.
Sai Mama Saudah mace ta huɗu wacce daga kanta Ale Idi ya rufe ƙofa, kusan za'a iya cewa kaf cikin matayensa ya fi sonta, kasancewarta ba ƙabilar hausa ba, cikakkiyar buzuwa ce gaba da baya, Allah ne ya haɗa zukatansu waje ɗaya, sannan ya dasawa ko wannensu tsananin soyayyar ɗan uwansa.
Gidan Ale idi wani irin birkitaccen gida ne me cike da tarin mutane mabanbanta.

Zazzaume duka ilahirin matan gidan tun daga kan iyaye har zuwa ƴaƴa suke akan tamfal na buhu da aka ɗinka, gurzazzun farantai ne waɗanda du sunyi lamba alamar tsufa ciccike da lafiyayyar jolourp ɗin shinkafa wacce tai jazur da manja, Inna Tabawa kaɗai ce kwanonta daban, amma su duka a haɗe suke cin abinci.
  Fira ce ke tashi a bakunan su, su na yi su na buga loma kamar abin dole, sai tabga gardama suke kamar zasu tashi su dambata, amma hannuwansu na cikin kwanuka.
  Hankaɗo ƙofar langa-langar da aka yi ne ya dakatar da gardamar, inda kowace ta maida dubanta zuwa ga farar yarinyar da ta shigo bakinta ɗauke da sallama, a madadin su amsa sai   Inna Sabuwa tai karaf ta ce.
   "Yau ni naga zakama da baƙin hali, ke Najma ba ɗazu-ɗazunan na ji Ale ya gama kashe ma ki gargaɗi akan dawowa gida da ranaba, amma hine ɗan ɗibar albarka zaki tsallake kalamin ubanki ki kwaso jiki raɓai-raɓai ki dawo gida, to ai hikenan gaki ga gidannan ki ci uwar da muke ci, kuma dai hinkawa ta ƙare sai ƙanzo idan za ki karkara ki kai bakin salati."
  Tana aje maganar ta rarumo wawakekiyar loma ta wurga baki, sai faman zare idanuwa ta ke kamar shege a rabon gaɗo.
Mama Saudah ce ta zare hannunta daga tiren abinci farar fuskarta zagaye da annuri ta ce.
   "Ɗiyar arziƙi irin albarka har kin dawo sannunki da isowa ta shi muje ɗaka in baki abincinki kinji ko ƙyale mahassada da ƴan baƙin ciki."
  Ta yi maganar tana zuwa gaban matashiyar ta kamata, babu musu ta miƙe tsaye daga ɗosanon da ta yi a saman botiki ta bi bayan mahaifiyarta zuwa ɗaki.

   "Ahayye nanaye, ayidai mu gani idan tusa zata hura gani, ma ji ma gani ai."
   Cewar Inna Lantana da ta gama tsotse hannu tas, tare da sakin wa ta ƙatuwar gyatsa.
  "Yo ai wallahi ko babu abin da zamu ji mu gani sai takaici, indai Sauda ce da wannan jemamiyar ƴar tata sauran cuta haka zasu dawwama babu cas ba huss."
  Cewar Inna Laraba da ta ɗauki tire tana suɗewa.

Taɓe baki wa ta babbar buɗurwa ta yi tare da dire kofin hannunta wanda yai damal-damal da baƙin tukunya da manja, sannan ta ce.
  "Yasin Inna kun ishemu da ɗumi, ko narkewa baku bari abincin yayi a cikunanmu zaku dasa da gulma waccw bata ƙarewa, matsalar mutun ya wuni gidanan kenan yasin, ɗuminku du ya gajiyar da mutum ina dalili."
  A harzuƙe Inna Laraba ta yunƙuro har tana sakin zane ta ce.
   "Kam burar ubanan kayyasa, Sahura ni kike yiwa rahin kunya ɗan abun kazan tsohonki, yau ga lalatattar yarinyar barbaɗaɗɗiya sauran mazan titi, dan ubanki mu sa'aninki ne da za ki raina mana wayo, wallahi tsaf zan ɗage hammata in lakaɗa ma ki hegen duka uwa sakwara."
  Ta faɗi tana kumfar baki muryarta a sama kamar me yi da ƴan waje.

   Muryar Inna Tabawa ce ta karaɗe wajen cikin kuka irin nasu na tsofafi.
   "Yau ni Tabawa naga abin da ya ishi uwata, da mata da ƴaƴa duka ƴan banza, in banda ɗibar albarka ace da tsakar rana zaku gallabi al'umma kai Allah wadai da halinku ƴan bantan uba, ni da gidan ɗana an hana ni in wala, to wallahi gobe zan tattare tsumokaraina in koma ƙauye ina dalili."
  Abin mamaki sai duka matan hankalinsu ya tashi, jikunansu suka hau rawa, nan take suka soma bata haƙuri gami da rarrashinta.
  Inna Sabuwa ce ta ce.
  "Haba Inna tayaya za ki fara maganar barin gidanan, ya kike so mu yi da rayuwarsa, sannin kanki ne Idi sam bamu ne a gabanshi ba, hatta abin da zamu jefa a bakin salati sai ya gagare mu muddin kika barmu, gaskiya ko tahiya za ki yi sai dai ki tahi tare da mu, mu koma can ƙauyen baki ɗaya."
 Haka suka shiga rarrashinta gami da ban baki har suka samu ta haƙura, dama rayuwar da ake yi kenan a gidan, Idi yayi rantsewar muddin Inna tabar gidannan to ya gama cida ko wace mace, sun san halinshi kar shiyasa suke taka tsantsan da ɓatawa innar rai.

A ɗakin Mama Saudah, shimfiɗa ta yi wa Najma tabarma,  da zallar fara'a a fuska da muryarta ta ce.
   "Najma ƴar albarka ɗiyar Mamanta, zauna kici abinci ki more guminki, kina da ni babu ke babu kwamacalar gidanan bari in haɗa ma ki ruwan wanka kiyi ki koma kafin wancan jarababben Idin ya dawo ya hayyace ki da mita."
  Lumshe lumsassun idanuwanta Najma ta yi, kafin cikin taushi gami da sanyin murya ta ce.
  "Ina son ki Mamana, amma ki bari idan na gama cin abincin zan haɗa ruwan da kaina, nasan kin gaji da yawa."
  "A'ah wallahi ban gaji ba sam, ina ni ina gajiya da ɗawainiyar yarinyar kirki yar albarka, ai ni indai hidimar ki ce to gaba na bata ba baya ba, ki huta abinki ƴata ina zuwa."
  Cire mayafin kayanta Najma ta yi sannan ta tankwashe fararen ƙafafuwanta ta janyo kwanon abincinta ta soma ci tana lumshe idanuwa, dan Mama Saudah ba dai iya girki ba, sai da ta ci kusan rabi da kwata sannan ta ajiye cokalin hannunta ta ɗauki goran ruwan da Mama Saudah ta aje ma ta, sai da ta shanye ruwan tas sannan tai godiya ga Allah gami da janyo wayarta ta soma latsawa tana jiran Mama Sauda ta kammala haɗa ma ta ruwan wankan.
WANNAN KENAN.


VICTORIA ISLAND
Zazzaune suke a ƙayataccen falon wanda ya gama haɗuwa da tsadadun kaya na  zamani ƙirar ƙasashen turawa, gaba ɗaya mutanen da ke zaune a parloun farare tas ƴan gayu na gaban kwatance, zagaye suke da wani baturen matashi su na ta faman maimaita ma shi kalmar "Sorry", yayinda ya ke ta faman jujjuya kanshi gefe da gefe farar fuskarshi ta yi jazur.
   Wa ta farar mata ce tallabe da kansa a kan ciyarta tana ta share hawaye gami da ɗaura hannunta a saitin zuciyarshi inda ya riƙe gam da nashi hannun.
  "Mommcy anya ba za'a kira Papie ba, kar ciwon yai ƙamari mu kasa control ɗin shi, kin riga da kin san matsalar Broth."
  Wa ta farar ƴar gayun budurwa ta faɗa fuskarta a yamutse da damuwa.
   "Ko da mun kaishi hospital babu abin da zasu yi ma shi sai allura, kuma yanzu a gabanki ya sake jadadda roƙon kar a kaishi hospital, please kuci gaba da yi mishi addu'a." matar wacce aka kira da Mommcy ta daɗa cikin sanyin murya.
   Sake sanyaya jikunansu suka yi, nan suka zagaye shi kuma soma tofa ma shi addu'o'i idanuwansu na zubda kwallar tsananin tausayin matashin.

  Tun yana juye-juye cike da azaba har ya fara kafawa a hankali ya soma sauke ajiyar zuciya, amma still hannunsa na damƙe da saitin zuciyarshi, a hankali wahalallen barci ya yi awon gaba da shi.
 A tare suke sauke ajiyar zuciyoyi fuskokinsu na sauyawa daga damuwa zuwa farin ciki.
MUZAFFAR MAHMUD DOLLAR's FAMILY kenan, familyn da ke zagaye cikin farin ciki da walwala, basu da wa ta damuwa anan duniya kasancewarsu shahararun masu kuɗi da suka zo lamba ta ɗaya a Nigeria, ba iya Nigeria ba hatta da sauran ƙasashen turawa sun san da tarin dukiyar MUZAFFAR FAMILY, domin kuwa ana damawa da su sosai a harkokin business iri daban-daban, a fanni siyasama ba'a barsu a baya ba, dan sune siyasarma baki ɗaya, muddin suka ambaci sunanka, suka haɗa da ɗaga hannunka, shikenan cikin hukuncin ubangiji kai ka gama hayewa.
Sai de akwai wa ta gaba me ƙarfi tsakaninsu da talaka, a cewarsu talaka sam bashi da alƙawari, talaka butulu maci amana.
(Domin jin yanda zamu warware wannan asalin cakwakiyar ku biyo ni)
Su na taimaka talakawa sosai da gumi da kuma aljihunsu, amma su na bayar da tazara me yawa a tsakaninsu dan sam basu yarda da raɓar talaka ba, bawai dan wulaƙanci ba, A,ah a kwai babban dalilinsu na aikata hakan.

Mahwish Shine babban ɗa a cikin tarin ƴaƴan da ke akwai a MUZAFFAR FAMILY, ana matuƙar ji da shi sosai da sosai, shine hasken idanuwansu kasancewarshi gwarzon jarumi da ke  da kyakkyawar alaƙa da kowa, kaf hali da ɗabi'unsa sak irinna Alhaji Muzaffar ne wato mahaifinsa.
   Kamar yanda ya zamo ɗan lele a familyn haka kuma ya zamo rauninsu, musamman da Allah ya jabarce shi da matsalar zuciya, ba daga baya ciwon ya same shi ba da shi aka haifeshi, sai de ciwon ya sake tsananta ne bayan ya girma ya shiga shekarun samartaka, inda wani lamari daya girgiza duniyarsa ya faru da shi (Ku biyoni sannu a hankali a sannu zaku ji komi dalla-dalla.) lamarin da ya zaftare rabi da kwata na farin cikin rayuwarsa, sannan kuma ya ƙara tsananta ciwo a gareshi, har sai da takai baya cika sati ɗaya ƙwaƙwara ba tare da ya kwanta gadon asibiti jinya me tsanani ba......✍🏻

Anan zan dasa aya ku kasance tare da Alƙalamin MARYAM STAR dan jin wanda zamu warware zaren da ke dabaibaye da wannan labari.

MABANBANTAN ZUKATA littafin kuɗi ne, a halin yanzu muna free pages ne

KIYI JOINING SABON CHANNEL ƊINA DOMIN SAMUN DAMAR YIN KARATU CIKIN SAUƘI.


M.STAR⭐ WRITER...✍🏻