MABANBANTAN ZUKATA

Chater 2

by @maryamstar248

***

𝙘𝙝𝙖𝙥𝙩𝙚𝙧 2
Mahwish matashi ne kyakkyawan gaske, ga kyau ga tsari, sannan iya yuwa ka maƙuɗen kudaɗe baibaye da shi gaba da baya, yana gudanar da rayuwarshi cikin tsari kasancewarshi me rauni, akullem yana ƙare lokacinsa ne wajen samarwa kanshi farin ciki, badan komi ba sai dan sanyaya raunananniyar zuciyar, ya sani shi me rauni me, amma baya bari raunin yayi yasiri a kanshi, yana haƙurewa kanshi abubuwa da dama dan gudun tashin ciwonshi, ko yaya yaga abin da zai ɗaga hankalinshi babu makawa sai ya kwanta jinya, jinyar da akullum yake bawa kanshi mutu a kurkusa saboda tsananin a zabar da yake sha.
 
   Jiniyar lafiyayyun jibga-jibgan motoci ƙirar M.B.W ta karaɗe tun daga farkon main get na MUZAFFAR mansion, jere ajere suke tafiya cikin tsari da burgewa, basu tsaya a ko ina ba sai a gaban tangamemen diamond get wanda samanshi ke fitar da rubutu da mabanbantan kaloli an rubuta.  
WELLCOME TO MUZAFFAR HOUSE 001, da kanshi get ɗin ya soma buɗewa bayan na'ura ta tabbatar da wanda suka iso, harba motocin kwararun drivers ɗin suka yi har zuwa wawakeken ƙeraren gidan wanda ya gaji da haɗewa, a gari guda ɗin ƙayataccen parking lot suka jere motocin, kafin daga bisani securitys suka shiga firfito kowa na ɗana ƙunamar bingidar hanunsa jiran ko ta kwana, sai da suka tabbatar da komi daidai sannan wani sangameme ya isa jikin motar da tafi kowace ɗaukar ido ya buɗe gidan baya tare da ƙamewa a gefe.
  Haɗaɗen tsadadden coven takalmi ɗan zamani ne irin na manyan attajiran duniya ya zuro zuwa ƙasan da aka lailaye da tattausan grass carpet, anɗauki mintuna uku sannan gaggar jikin ta idasa bayyana gaba ɗaya.
  Dakakken babban mutum ne me cike da haiba gami da kwarjini na musamman ya fito, cike da izza irinta gogagun attajiran masu kuɗi ya soma takawa ahankali kamar me tausayin ƙasa, du inda ya gifta sai ma'aikata sun ɗurƙusa tare da kwasar gaisuwa, ko kallo basu isheshi ba haka ya ke giftasu ya wuce a binshi.
 A daidai sanda ya dira ƙafarsa cikin kyakkyawan parlon nan take gabanshi yai mummunar dokawa, da ɗan sauri ya idasa shigowa tare da yin siririyar sallama wacce babu wanda ya ji shi, bai tsaya a ko ina sai a gaban Mommcy da ke wurga ma shi wani irin kallo me cike da rauni gami da gazawa.
   Lafiyayyun nahhayensa ya saka gami da tallafar Mahwish daga jikinta zuwa na shi, nan take ya saki ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya.
  One by one mutanen parloun suka shiga darewa kowa na komawa muhalinsa.
  A hankali Mommcy ta kwantar da kanta akan kafaɗar me girma MUZAFFAR  a tausashe ta saki wani sassanyan kuwa me tsuma zuciya.  (Kunsan ƴan gayu komi nasu dabanne🤩😁), Lumshe fararen idanuwanshi da suka soma sauya launi yayi sannan ya kwantar da Mahwish akan cinyoyinsa ita kuma ya janyota zuwa jikinshi tare da soma shafa bayanta sannu a hankali.
  A ƙasan ranshi yana jin yanda kukanta ke nuƙurƙusar zaman lafiyarshi, sannan kuma ciwon Mahwish na tayar da hankalinshi fiye da kima.
  Cikin muryar ƙuƙa Mommcy ta ce.
  "Papie!!😭 bazan iya jurewa ba, nima zuciyata ta kusa daina aiki, ina tausayawa ɗana."
  Ta yi maganar tana ƙanƙame hannun Alhaji Muzaffar kamar ance wani zai ƙwace ma ta shi.
  "Shshshhhh, ki daina wannan maganar in sha Allah Mahwish zai samu lafiya kamar kowa, ki ɗauki lalurarsa a matsayin jarabawa daga Allah, kiyi ƙoƙari mu cinye jarabawarmu, sannan shi kuma ki ci gaba da tarairayarsa gami da nuna mashi ƙaunar, ki daina nuna damuwa akan abin da Allah ya riga da ya rubuta a lauhil mahfuz, bamu da tsumi bamu da dabara sai a wajen Allah."
  Papie ya faɗa da muryarsa wacce da zurfi cike da izza.
  Sun ɗauki tsawon lokaci a haka, zirawa kyakkyawar fuskar Mahwish idanuwa suka yi su na tazbihin yanda Ubanjigi buwayi gagara misali ya bawa Mahwish baiwar kyawu, du lokacin da zai motsa yana motsawa ne da nutsuwarsu, domin kuwa Mommcy na jin yanda gabanta ke kakkaryewa yana faɗuwa cike da tsoro, ba komi ta ke tsoro ba sai irin halin da Mahwish ɗin zai iya farkawa a ciki, addu'arta ɗaya ya farka cikin sabun sauƙi da salama, idan kuwa akasin hakan ta faru tana da tabbacin itama sai ta kwana a gadon asibiti.
Mahwish bai farka ba har lokacin sallah ya shiga, hakan ya saka Papie ya sureshi cike da taka tsantsan ya kama hannun Mommcy ya wuce da shi ɗakin barcinsu, ɗakin da ya kasance sirri a garesu kafin samuwar Mahwish babu mahaluƙin da ke shiga, amma a yanzu sun mayar da ɗakinsu su uku, idan dai ba tare da Mahwish zasu kwanta ba to ba shakka ba zasu  runtsa ba a ranar.
   A kan lafiyayyen gadon alfarma Papie ya aje Mahwish cike da kulawa da taka tsantsan, bayan ya kwantar da shi a hankali ya shafa fuskarahi tare da sumbatar goshinshi da saman dogon hancinshi da yai jazur.
  Ita ma Mommcy sumbatar shi ta yi tare da fatan samun lafiya, sannan suka shiga bathroom suka ɗauro alwala a tare suka fito, a nan ɗakin Papie ya ja su sallah, bayan sun idar suka shiga nemawa ɗansu lafiya a wajen me bayarwa kuwa me hamawa Ubangijin dukanin hallita (Allah).




AJEGUNLE
  "A ƙalla  Najma ta kwashi mintuna arba'in da ɗoriya a cikin bayin tana ƙalƙale farar fatarta, tana jin yanda Yaya Saddi ke ɗuɗɗura ma ta guma-guman ashariya lokacin da ya shigo gidan a harziƙe zai shiga bayi yaga towel ɗinta a kan kyaure, biris ta yi da shi kamar bata san yana yi ba, idan da sabo ta saba da irin banzar rayuwar da ake gudanarwa a gidan na su, tana jin shi ya gama buyagin na shi ya fice, su Inna Labara na sake zugashi su na tayashi kwashe ma ta albarka.
  Aiko dai bata yi asarar wanka ba, domin kuwa wani irin sheƙi da ɗaukar ido jar fatarta ta soma yi lokacinda ta fito ta tsugunna cikin hasken rana tana alwalar sallar la'asar data gabato.
  "Ke ko wannan yarinya anyi ƴar kwal uba, jarabarki ta gallabi kowa a gidannan, ina ce ko shi kanshi Ale Idi me gidan idan ya shiga bayi ya daɗe yai mintuna goma, amma dan kan bura uba ke idan kika ahiga sai kin kwashe awanni kamar me sauya fata, a haka za ki dawwama ai." 
  Cewar Inna lantana da ke zaune akan kujera ƴar tsuguno tana tankaɗen garin tuwo, sam Najma bata kulata ba sai ma juyawa da ta yi cikin takunta me kawa da tafiyar hawainiya ta shige ɗakin Mama Saudah.
  "Yo ke Lantana in banda iyayi irin na ki miyayi ruwanki da wannan ƙallemar yarinyar marar tarbiya, a kule dai kinsan ba kulaki zata yi ba saboda babu albarka a tare da it...."
 Bata ƙarashe ba sai ganin Mama Saudah ta yi tsaye akanta ƙerere ta riƙe ƙugu fuskarnan a ɗaure ta ke faɗin.
  "To munafukan Allah ta'ala, masu barci da ido ɗaya, kunbi kun takura rayuwar baiwar Allah ita da gidan ubanta kun hanata sakewa, ku ubanwa ya sakawa naku watsatsun yaran idon akan lamuransu, wato sai ita kuka me daɗin hawa ko, to wallahi tallahi zan rufe ido in zabgagawa ma ta rashin mutunci muddin ta sake shiga harkar ƴa ta."
  Aifa dama kamae jira ake nan waje ya kacame aka ci gaba da hayaniya anata kace na ce, sai ɗuɗɗuran guma-guman manyan ashariya ake, daga ƙarshe dai harda taƙa dambe gida ya rikice, tuni aka hankaɗar da garin da Inna Lantana ke tanƙaɗewa ƙasa, aka tattake shi ya shige cikin jar ƙasar wajen wacce ta haɗu da danshin ruwa.

  Guntun tsaki Najma ta saki gami da girgiza kai, a fili ta furta, "Allah kyauta halin gidanan". ta ci gaba da shirinta anutse, tsaf ta fito cikin ɗinkin riga da sket mix and match pich colour, yanayin ɗinkin ya bi jikinta ɗas gwanin kyau, duda ba kamata kayan suka yi ba, wadataccen mayafi wanda yai matching da kayan ta gyala irin na manyan ma ta, sosai ta yi kyau kamae ka sace ta ka gudu, fuskarta babu wa  ta ƙwalliya face kwali data zizarawa manyan fararen idanuwanta, sai kuma lips glow data shafa shima ɗan kaɗan akan siraran lips ɗinta, amma karku so kuga bala'in kyan da ta yi, kamar me shirin zuwa bikin president.
  Lokacin da ta fito hatsaniyar ta lafa dan baka jin muryar kowa sai ta Inna wacce ta raba faɗan tana ta mita gami da kwashe musu albarka tana zaginsu ta uwa ta uba tana kiran sam ɗanta baiyi dace da mata na kwarai ba.
  Ina fitowa Ale Idi na shigowa gidan shima yana kwasa kala-kalar ashariya bakinsa har kumfa ya ke dan masifar faɗa.
   Karaf idanuwansa suka hasko ma shi Najma take saka tarkacenta a cikin jaka, ashar ya kutuntumo tarw da nufar inda ta ke, da mugun ƙarfi Mama Saudah ta furta.
  "Najma ruga da Abbankinan."
  A zabure ta kwasa da gudu kamar zata kifa ta fice tana salati, duda haka sai da Ale Idi ya samu nasarar ɗirma ma ta  dundu a baya, bayan ya rakata har ƙarshen layi.
  A rumfar wani shago ta tsaya tare da maida numfashi, sai ta da saisaita kanta sannan ta tashi bayan ta ƙama sun glasiss a idanuwanta.....✍

KU KASANCE TARE DA ALƘALAMIN.

MARYAM
          STAR ⭐⭐⭐
                    WRITER

Domin morewa karatun zafafan litattan hausa.

Karku manta wannan littafin na kuɗi ne iya book one ne kawai free amma book two paid ne.