Chapter 3
***
𝙈𝘼𝘽𝘼𝙉𝘽𝘼𝙉𝙏𝘼𝙉 𝙕𝙐𝙆𝘼𝙏𝘼❤️🩹❤️🔥
𝙎𝙏𝙊𝙍𝙔 & 𝙒𝙍
Chapter 3
A nitse ta soma tafiya a hanya tana tsallake caɓali da kwatocin da suka baibaye unguwar tasu har ta isa bakin hanya, cikin sa'a ta samu abin hawa nan ta tsaida tare da sanar da shi inda zai kaita, suka yi ciniki ta hau suka ɗauki hanya.
A zahiri idanuwanta na kallon manyan gine-ginen kamfanonin da ke wajen, amma a baɗini ta yi nisa ne a duniyar tunanin irin rayuwar da ake gudanarwa a gidansu, wa ta rayuwa da sam babu tsari a cikinta, tana tsananin son ahalinta son da ya zarce gaban kwatance, amma tana tsananin jin haushin irin rayuwar da ake gudanarwa a cikin ahalinnata, daga ka karyo kwanar layin gidansu zaka fara jin ɗure-ɗuren ashariya iri da kala na tashi, ko kuma ka ji ƙarar doke-doken faɗa, ba daga yaranba ba daga iyayenba.
A daidai makeken babbar ma'aikatar aka sauke ta, inda ta zaro kuɗinshi ta bashi sannan ta soma yakawa cikin sassanyan taku me birgewa da jan hankali.
Wani baƙin ƙaƙƙarfan namiji ne ya sha gabanta, fuskarshi murtuke babu ɗigon fara'a ya tambayeta ina ID card ɗinta, cikin harshen turanci.
"Oh god." ta faɗa tare da kai siririn farin hannunta ta shafa saman goshinta sannan ta zuge zif ɗin jikkarta ta ɗauki Id card ɗin ta sarƙafa tare da bashi haƙuri, janyewa yai daga gabanya tare da bata hanya ta wuce.
Tun da ta shi ta ke ta faman cin karo da mutane mabanbanta, wasu ta tsaya su gaisa wasu kuma ta wuce su ba tare da ta ko kallesu ba, da haka har ta sadu da ainahin inda ta ke aikinta.
Tulin wanke-wanke ne na kwanikan da aka yi amfani da su a ma'aikatar jinge, a yanda idanuwanta suka hango ma ta, na yau kamar sun doke na kullum yawa, haka ta shiga wani ɗan ƙaramin ɗaki ta ɗauro wa ta rigar unifor a saman kayanta sannan ta dawo, har abokan aikinta su biyu sun ƙaraso dama ita suke jira, nan suka hai aikinsu babu ɓata lokaci suna yi su na fira jifa-jifa, a madadin sauran lokuta da ita ce ƙarfin hirar, sau sam bata jin daɗin firar musamman da ya kasance yau zuciyarta a cunkushe ta ke.
"Kutumar uba, uban waye yai min asarar gari haka a ƙasa, wacce me bakin uwarce a cikinku?."
Ale Idi ya yi maganar yana hura ƙofofin hancinansa cike da bala'i.
"Yo wacece ta isa tai wannan ɗanyen aikin in banda matar so, ita ce ta zubar da shi dan baƙin ciki, saboda tasan ƴarta na can na rabawa mazan kan titi jikinta ana fakewa da sunan aiki tana kawo ma ta kuɗaɗe su na cin me kyau ai dole ta zubar mana da gari."
Inna Lantana ta faɗi tana hura hanci gami da harare-harare.
"Ke Lantana ki iya bakinki wallahi, ƴa ta aiko ta ke zuwa ba wani wajeba, kuma nine nan na samo ma ta aikin da kaina munafukar banza kawai wacce batasan hallaci ba."
A masife Inna Laraba ta harzuƙo tare da faɗin.
"Wallahi da gaskiyarta, idan ba karuwanci ba uban mi take fita ta yi, kullum yarinya na fita kwaskwas da ita tana yauƙi sannan ace aiki ta ke zuwa, idan aikinne miyasa baka samowa namu ƴaƴanba, sai ita na faɗa na ƙara yawon tazubar take zuwa ba aiki ba."
Wa ta ashariya me gunna Ale Idi ya lailayo ya watsawa Inna Laraba sannan ya ɗora da faɗin.
"Uban wa ya hana kuyiwa ƴaƴan naku tarbiya ta kwarai, ƴaƴa du sun lalace sun zama tambaɗaɗɗu, yawon ɗaukar magana kwararo-kwararo sun iya shi, na rantse da Allah, du shegiyar matar da ta sake yin mummunar magana akan Najma sai na bata mamaki, munafukan mata kawai."
Wa ni saurayine ya shigo gidan ya na tafe yana layi ya sha yayi tatul ya kalli saitin da Ale Idi ya ke ya ce.
"Ahucu hakanan Dagus, Allah wallahi sai da kai, wato Dagus ka gane ko eh yane waɗancan matan naka ƴan wahala ne, basu da aiki sai halin karnuka du sun cika manah kayi, a huce Dagus a huce, yane ɗan sinno min naira hamsin inɗan busa hayaƙi manah."
Yai maganar yana rangaji irinna ƴan ƙwaya.
"Mtswwwwww Allah ya sawaƙe biyar ɗina ta zo hannunka lalatacen yaro marar amfani kawai."
Cewar Ale Idi yana baza cukuikuyayyar babbar rigarshi ya wuce ƙofar ɗakin Mama Saudah.
Da Murmushi Mama Saudah ta taryi Ale Idi cike da kulawa gami da lankwashe murya kamar ba ita ta gama banbamin masifa ba yanzu ta bi bayanshi ta na faɗin.
"Sannu da dawowa Babansu, ka dawo lafiya ya gajiya da kuma rana, bara in ɗauko maka ruwa ka jiƙa maƙogaronka da shi, dan nasan ka gaji."
Cewar Mama Sauda bayan ta miƙe ta nufi wajen da ta aje kular da ta ke saka ruwa.
"Allah sarki Saudah nah, shiyasa nike tsananin ƙaunarki wallahi Allah, saboda kinfi kaf matan gidannan hankali."
Ya faɗi bayan ya amshi ruwan ya kafa a baki.
Sassanyan murmushi ta dinga jifanshi da shi harda wani shafa kafaɗunshi tana zayyano ma shi yanda ta ke bala'in ƙaunarshi a ranta.
Haka ya dinga washe bakinshi du miyan goro yana murmushi, amma ka rantse da Allah yaƙen kuka ya ke, Saboda Ale Idi yana daga cikin maza marasa kyawun fuska, sam murmushi baya kyau da fuskarshi ko dariya, idan yayi ko yanda kasan an tattaro duka muninshi ne.
Karkacewa gefe yayi tare da zaro damen kuɗaɗe ya ɗora bisa cinyar Mama Saudah sannan ya ce.
"Matar so yau fa kasuwa ta yi kyau, tas na saida kayan miyar yanzu ku ware min kuɗin siyen wasu kayan sai mu ƙirga ribar.
Sam Ale Idi bai iya lissafi ba, duda irin mugun son kuɗinda yake da shi, du cikin matanshi yafi yarda da Mama Saudah ita ce ta iya takunta bata nuna zalamarta ƙiri-ƙiri kamar sauran, hakan ya saka take yi mashi wayau wajen lissafi, kuma idan taga kuɗi bata kawo mashi wa ta buƙata a lokacin, saɓanin sauran matan dasun kyalla ido sunga kuɗi shikenan ba saura ba kingi sai su fara lissafo buƙatunsu kai tsaye, har da marasa amfani, shi kuma daya ji haka sai ya danƙe bakin aljihunshi yai gaba abinshi.
Yanzumma haka ce ta faru, Inna Lantana na ganin ya shiga ɗakin Mama Saudah ta salalaɓo ta laɓe wajen taga tana hangen du abin da suke yi, sai faman cizon yatsa ta ke tana karkaɗa kai, ta na ganin Ale idi ya warci wasu kuɗi ya bawa Mama Saudah da sunan nata ne ladar kwalliya da ruwan da ta nashi, aiko tai wuf ta faɗa ɗakin, bata dira ko ina ba sai gaban Mama Saudah ta miƙa hannu zata warci kuɗin, da hanzari Mama Saudah ta janye hannunta tare da hankaɗe Inna lantana har sai da ta faɗi ƙasa, a kausashe Ale Idi da ranshi ya gama ɓaci ya ce.
"Wallahi kin yi asara Lantana, kinji kunya sannan ki zubda girmanki, ki tattara kayanki ki lalubi hanyar ƙauyenku yau ba sai gobe ba kar in sake ganinki cikin gidannan har sai idan ni na dawo da ke."
Ya na gama faɗin hakan ya miƙe a fisace tare da kaɗa babbar rigarshi ya fice yana banbami.
"Wayyo Allah na higa uku, Allah ya tsine miki Sauda yau gashi ta sanadiyar ki kinja min bala'i, Allah ya isa baƙar munafuka me baƙar aniya."
A maimakon Mama Saudah ta ji haushi sai tashi ta yi tare da soma jujjuyawa Inna Lantana bazazzun mazaunanta tana waƙa cikin yaren buzanci, kamin ka ce mi tuni ƙofar ɗakin Mama Sauda ta cika da ƴan kallo, tun daga kan matan gidan har zuwa ƴaƴayensu da basu samu tarbiyya ta kwarai ba, ita ko, ko a jikinta bata ji komi ba haka Mama Sauda ta tiƙi rawa tana baza canjin hannunta ranta fes.
Inna Lantana na kuka harda fyace hanci ta fito tsakar gida tare da zazzago manyan ashariya ta dinga makawa tana kiran babu inda zata je wallahi, yayinda ƴaƴanta da saura matan gidan suka shiga turata akan karta yarda ta tafi ta, suna kuma jifar Mama Sauda da habaice-habaice.
Najma ba ita ta tashi daga wajen aiki ba sai marice liƙis, lokacin waɗanda zasu yi night sun iso.
Wajen da aka tanada domin bayar da abinci suka nufa ita da sauran abokan aikinsu, su na zuwa suka iske an gama harhaɗa musu abincin da kullum ranar ta duniya ake basu idan sun gama aiki, karɓa suka yi kamar kullum sannan suka fice suna ɗan taɓa hira.
Yauma kamar kullum a daidai lokacin da suka isa bakin makeken get ɗin shiga ko fita daga company, anan ta iske motarshi a fake, ya buɗe murfin gaba, yana ganin sun kusanto waje yai saurin fitowa tare da soma ƙawata kyakkyawar fusarshi da kyakkyawan murmushi.
Tun kafin ya idasa ƙarasowa wajensu Najma ta ɗauke kanta bayan ta tsayar da murmushin da take yi, a daidai saitin ta ya ci burki, ta yanda ta ke iya jin kusancin su da yayi yawa, ba tare da ta ɗago kai ta kalleshi ba ta yi ƙoƙarin kaucewa, amma mi sai ya dinga ɗaga takunsa yana binta du inda ta yi, a gajiye ta ɗaga kyakkyawar fuskarta tare da watsa ma shi wanni kallo irinna ka ƙureni fa, amma mi sai ya sakar ma ta lallausan murmushi kamar kullum.
Wani abu ne ya tokare girjinta, ida akwai abinda ta tsani gani bai wuce fuskar mayenta Abdul ba, sake ɗaure fuska ta yi tamau sannan a tsiwace ta buɗe bakinta tare da faɗin.
"Miye hakan?."
Bata aje ƙarshen kalmar ba ya amsa ta.
"So da ƙaunar ki ne hakan kyakkyawar flower."
"Na rasa acikin mayu wane suna zan kira ka da shi, nace bana yinka ka barni mana."
"Ai ni ina yinki, nawa ma ya ishe mu."
"Bana da lokacinka Abdul please ka rabu da ni."
"Nayi alƙawri akan bazan taɓa rabuwa da ke ba har gaban abada, ke ɗin tawace ni kaɗai, babu wanda ya isa ya raɓe ki da kalmar so, zuciyarki tawa ce."
"Ƙarya kake Abdul baka isa kaja da ikon Allah ba, zuciyata tawa ce, sam baka da gurbi a cikinta, kuma ba zaka taɓa samu ba har gaban abada."
"Ƙarya kike Najma ke tawa ce, sannan zuciyarki ma tawa ce koki so ni koma karki so ni babu ruwana abu ɗaya zan sake jadadda maki shine, babu wani matsuguni a zuciyarki da soyayyar wani mahaluƙi bayan Abdul zata tsaya, zuciyarki tawa ce."
Wani irin ɗumi ne ya lulluɓe cikin tafukan hannayenta, yayinta tsananin ɓacin rai ya turniƙe kafaffiyar zuciyarta, bata san mi ta aikata ba sai da takai dubanta kan hannunta da ya soma rawa.
A razane ƙawar aikinta Khadija ta ja da baya gami da dafe baki ganin yanda Najma ta ɗaga hannu ta wanke fuskar Abdul da lafiyayyen mari wanda ƙararsa ya karaɗe wajen.
Cikin kausashiyar murya ta soma faɗin.
"Akwai banbanci tsakanin zuciyarka da tawa, sam bamu dace da juna ba, bana sonka kuma bazan soka ba har gaban abada."
Caraf Abdul ya damƙi hannayenta duka biyu wani abu da bata san ko mineneba na narkewa a fuskarshi, idanuwanshi ya saka a cikin nata da yake iya hangen ƙiyayyarshi kwance a ciki, sannan ya furta.
"Kin yi kuskure, kin yi kuskure da har kika yarda akaro na farko hannunki ya sauka akan tsadaddiyar fuskata sa sunan mari, wannan marin da kika yi min shine matakin farko da zai ɗorar da ƙaƙƙarfar alaƙa a tsakanina da ke dole ki so ni, dole ki zama mallakina dole inzama linzami da akalar sarrafa zuciyarki."
Sai kuma ya saki hannayenta ya kama fuskarta cikin tafukan hannayensa sannan ya ce.
"Ki shirya tarbata a matsayin masoyinki, domin a koda yaushe zan iya mamayar rayuwarki da zazzafar soyayata."
Yana gama faɗin hakan ya cire idanunsa daga cikin nata da ke faɗar ma shi da gaba, domin ƙiri-ƙiri yake kallon tsanarshi a cikinsu.
Ƙwace fuskanta ta yi tare da zubar da yawu a ƙas sannan da kakkausar murya ta furta.
"Baka isa kayi komi ba Abdul, baka isa ba wallahi, kuma mu zuba ni da kai mu gani, ɗan halak ka fasa, a yau a kuma wannan wajen na yi maka alƙawarin baka kunya, saina saka ka ka ƙaryata kanka da kanka."
Tana gama faɗin hakan ta bangaji gefen jikinshi ta wuce a zafafe tana jin yanda taurarriyar zuciyarta ke tunzurata, amma sai ta yi galaba akan zuciyarta ta hanyar ambaton Allah akan harshenta.
"Ka....ka...kayi haƙuri dan Allah." Ƙawarta Khadija ta faɗa jikinta na rawa, sannan ta giftashi itama ta wuce da sassarfa tana kiran Najma.
VICTORIA ISLAND.
A hankali ya soma buɗe raunanin idanuwansa, amma mi, a maimakon yaga haske sai ya ga duhu me gauraye da hasken dum light da suke kunna kansu da kansu idan dare yayi, a hankali ya soma motsa yatsun hannuwansa yana fatan Allah yasa ba abin da ya ke zargi ba ne ya faru, sai de jin yatsun hannuwan nashi cikin tausasan hannuwa a rumtse ya tabbatar masa da zarginsa, wani ɗan guntun murmushi ya saki tare da juya kanshi a hankali ya kalli saitin Papie da ke barci rungume da hannuwansa a ƙirji, sai ya dawo da kanshi a saitin Mommcy da ita abin nata ya girmi na Papie domin duka hannayenta ta saka ta matse nashi a cikin, ahaka barci ya ɗauke ta, wani sashe ne na raunanniyar zuciyarshi ya motsa da tsananin tausayawa iyayenshi da suka sadaukar da farin cikin rayuwarsu akan shi, shiɗin dai daya kasance gawa ta ƙi rami, shiɗin da yake jiran zuwan mutuwarshi a kullum, yana ji inama ace Allah zai ɗauki ranshi kowa ma ya huta, su su huta da zullumi shi kuma ya huta da wahalar ciwo, kamar ya manta da Allah ne keyin yanda ya so a kuma lokacin da ya so, ya manta da Allah na rayar da matacce cikin rayaye, haka kuma ya rayar da matacce cikin rayayye.
A hankali cikin rashin kuzari ya soma ƙoƙarin zare hannayensa daga nasu hannuwan, a can ƙasan ranshi yana sa rai da abin da baya da tabbacin faruwarsa, hasalima yana gudun du wani abu da zai kawo ayi maganar bare a danganta shi da shi, zuciyarshi na hango ma shi yin aure ne kaɗai zai hutar da iyayensa akan gaganiyar da suka shafe shekaru suna yi da shi, sai de kuma idan ya tuna wani abu, yana hanzarin kawar da tunani nan take.
"Son ka farka ne ya jikin naka fatan babu wani abu, a kira doctor ko mu tafi hospital."
Mommcy da cikin barci ya ji yanda ake son rabata da hannun Mahwish ta yi hanzarin miƙewa, ganin idanuwanshi a buɗe ya sakata soma jero ma shi tambayoyi fuskarta da alamun damuwa gami da tsananin tausayinsa, tausayin da ke zaune akan fuskarta tsawon shekarunshi, tausayi da dam u wa sune suka za ma ado akan kyakkyawar, ko yaya zata caɓa ado yana hango hakan....✍🏻
KUYI FOLLOWING SABON CHANNEL ƊINA DAN SAMUN ZAFAFFAN LITATTAN HAUSA 👇👇👇👇👇👇👇👇👇
***
NI CE TAKU MARYAM STAR ⭐⭐