....
***
𝙈𝘼𝘽𝘼𝙉𝘽𝘼𝙉𝙏𝘼𝙉 𝙕𝙐𝙆𝘼𝙏𝘼❤️🩹❤️🔥
𝙎𝙏𝙊𝙍𝙔 & 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙏
Chapter 4
Yana hango rauni baibaye da ita, kamar dai shi ɗin, shi daya kasance rauni gaba ɗaya rasuwarsa da komi nasa a raunane ya ke, haka ƙaddararsa ta zo.
Maganada Momcy ta yi ce ta farkar da Papie, haka shima ya miƙe tare da jero nashi tambayoyi yana yi yana dudduba jikin Mahwish ɗin, ƴar siririyar dariya Mahwish ya yi, ganin yanda Papie ke dudduba jikinshi kamar yana neman wani abu.
Jin saurin dariyarsa sai ya nutsar da zukatansu, suka ji farin ciki ya baibayesu, dan hakan na tabbatar musu da ya samu sauƙi.
Mommcy ce cikin muryar rarrashi ta ce da shi.
"Son zaka iya saka wani abu a cikinka in samar ma ka, du yaufa baka ci komi ba tun break fast."
Da disasshiyar muryarsa ya amsa ta da. "Hot chocolate tea."
Godiya ta yi masa sannan ta janyo landline da ke bisa bed side ta dannan wasu lambobi ta kira, ana ɗagawa ta sanar da abin da ta ke so ta ajiye wayar ta sake matsawa gabanshi.
Shi a yanda yake ganin sun saka shi tsakiya kamar wani baby abin dariya ya ke bashi, su kuma babu ruwansu sun dage sai fira me daɗi suke yi mishi du dan ya mance da du wata damuwa.
Ko da aka kawo Chocolate tea ɗin, da kansu suka soma bashi, bayan Papie ya wanke ma shi baki da wani irin brush na ƴan gayu.
Yaɗan sha sosai babu laifi, sannan ya kalli iyayen na shi tare da faɗin.
"Ina so zan yi wanka."
Dayake sun san abin da yake shirin yi har haɗa baki suke yi wajen furta.
"Ga bathroom anan ka shiga manah."
Ɗan kwaɓe fuska yayi cike da gajiyace ya ce.
"Please my lovely."
Amma sai suka kauda kawunansu gefe kamar dai yanda suka saba yi a kullum idan yana so su barshi ya tafi.
Badan ya so ba hakanan ya lallaɓa yayi a nan ɗin, amma bai koma kan bed ɗin ba, sai koma kan lallausar katifa ya kwanta, kyaleshi kawai suka yi amma su yanda zai motsa sai sun taso sun duba lafiyarshi, a haka har nannauyan barci yaci ƙarfinsu su duka.
Kiran Sallar da suka jiyo da lallausar sassanyar muryarsa ce ta farkar da su biyu, kallon juna kawai suka yi tare da murmushi, sannan suka tashi danngabatar da tasu sallar.
Tun da ya fice masallaci da asuba bai dawo ba, acan yai kwanciyarsa dan yana so ya dinga bawa mahaifan space, sosai ya sha barci bai farka ba sai ta ya ji hannu na tattaɓa shi, buɗe idon da zaiyi sai ya yi tozali da kamulalliyar fuskar Papie da ke shirin ɗaukarshi, kafin ya ce wani abu tuni Papie yayi sama da shi kamar wani yaro ya ɗaurashi a kafaɗa ya soma tafiya da shi cikin tafiyarshi ta izza.
Bai dire shi ako ina ba sai gaban wani sink, shima duƙar da fuskarshi papie yayi ya soma wanke ma shi da kanshi, sannan ya janyo brosh me caji ya wanke ma shi baki tas, ya kuma sake saɓarshi yai kan ƙayataccen dinning da shi, a kujerar tsakiya ya zaunar da shi sannan shima ya zauna kusa da shi, sai ya zama yana tsakiyar Mommcy da Papie.
Sauran mutanen gidan da sungama hallara tun ɗazu suka soma gaisar da shi one by one tare da tambayarshi ƙarfin jiki, cike da kulawa yake amsa musu, murmushi baiyane akan kyakkyawar fuskarshi.
Murmushin da ya dasa wani tsiro na tsananin tsana a zuciyar Muhasin da ke zaune wa je, gaba ɗaya ji ya ke kamar ya sanya bindiga ya harbe Mahwish kowama ya huta.
Zuciyarta tafarfasa haka ta tsaida ɗan sahu, murya a cunkushe ta sanar da shi inda zai kaita, Khadija ce ta tsayar da shi ganin yana ƙoƙarin wucewa da Najma, jaka da ledar abincinta ta ɗora ma ta akan ciyarta, sannan taja baya tana ɗaga musu hannu.
Adaidai ƙofar gida ya ajiyeta, naira dubu ta miƙa ma shi sannan ta shiga cikin gidan nasu da sallama can ƙasan maƙoshi.
Gidan Ale Idi kenan, yanzu ka taras ana tafka uban dambe kamar zasu kar juna, anjima kuma ka shigo ka taras anata nishaɗi.
Zazzaune suke akan shimfiɗa kwansu da kwarkwata harda mazan gidan kowa ya dawo gida, yayinda suka zagaye Mama Saudah da ke ta faman basu labari su na dariya, babu wanda Najma ta kallah ta tsallakesu ta shige ɗaki, aje jakarta ta yi sannan ta faɗa akan gado tana jin yanda zuciyarta ke tafarfasa kamar wuyan zafi akan wuta, ji take ina ma zataga Abdul yanzu da sai ta yi mashi abin da bai yi zato ba, wani sabon ƙunci ne ya kuma lullume zuciyartaw lokacin da ta kwanyarta ta hasko ma ta yanda ya Abdul ya riƙe hannunta, bayanan kuma ya riƙe fuskarta a harziƙe ta miƙe tsaye tare da kwalla wa ta iriyar ƙara me razanarwa, sannan ta sulale a wajen kamar gawa.
Su Mama Saudah ana zaune fira ta kai musu karo, sai ji ƙara me razanarwa suka yi ta cike kunnuwansu, da hanzari suka mimmiƙe tsaye su na salati suka nufi ɗakin Mama Saudah inda nan suka ji sautin, da mugun mamaki suke kallon Sauda yashe a ƙasa, kanta suka nufa da sauri Inna Laraba ta tallafota tana girgizata amma shiru, da sauri ta suri kofin ruwa ta shiga yayyafa ma ta a fuska amma shiru, zubewa Mama Saudah ta yi ƙasa tare da rushewa da matsanancin kuka tana kiran sunan Najma, kanta su Inna Lantana suka yi tare da soma rarrashinta cike da kulawa.
An kwashe mintuna talatin ba tare da Najma ta dawo hayyacinta ba, bayan sunyi sallar magrib suka yanke shawarar zuwa asibiti da ita, ana tsaka da shawarar sai ga Ale Idi ya shigo yana baza babbar riga, ganin Inna Lantana tsaye ya saka shi soma faɗin.
"Ke Lantana uban mi kike yi min cikin gida bana ce ki tafi gidank..."
"Yauwa dama kai muke jira ka zo akai Najma asibiti, bamusan shigowarta ba sai jin ƙararta kawai muka yi, muna shiga muka taras ta faɗi, gatacan har yanzu bata farko ba."
Bai gama jin bayanin Inna Laraba ba ya kwasa a guje yana salati ya nufi ɗakin Mama Saudah, kan Najma yayi yana salati ganinta kwance kamar gawa, kama hannunta yayi cikin na shi sannan ya ce.
"Faɗimatu ta shi kinji, babu abin da ya same ki."
Wani abin mamaki a hankali ta soma motsa hannuwanta, daga bisani ta shiga ƙoƙarin buɗe idonta, dishi-dishi ta ke ganin Ale Idi a gabanta, cikin disasshiyar murya ta ce.
"Baba zuciyata, zuciyata zata buga idan banganshi na sake jadadda ma shi cewar na tsane shi ba, ina jin zafi gami da zugi a zuciyata."
Ta yi maganar cikin sanyin murya.
"Ni da kaina zan raka ki ki faɗa ma shi hakan, yanzu dai ta so kiji ƴar babanta."
Ya yi maganar yana taso da ita zaune.
Ruwa Inna Tabawa ta miƙo ta ce.
"Ba ta ruwa ta sha, da alama itama ta yo gado, Allah dai ya kyauta." amsar ruwan Ale Idi ya yi tare da kafa ma ta a baki, sai de ruwan ya taru sosai a bakinta amma ta kasa haɗewa, du rarrashi da ban bakin da suka yi mata amma ruwan ya ƙi haɗuwa agareta, zubar da shi kawai ta yi sanna ta kwantar da kanta a kan kafaɗar Ale Idi gami da lumshe idonuwanta.
Inna Tabawa ce ta shigo ɗakin tare da zama a gaban Ale Idi, ta ƙurawa Najma ido tana ƙare ma ta kallo sannan ta nisa tare da faɗin.
"Iko sai Allah, wallahi itama ta gada, ta yo gado a wajen kakaninta, taurin zuciya ba."
Zuba ma ta ido Ale Idi yayi sannan a sanyaye ya ce.
"Taurin zuciya kuma Inna, tayaya hakan zata faru bayan su sun jima da barin duniyar."
Jujjuya kai Inna ta yi sanna ta ce.
"Kayya Idi, wa yace maka dan sun bar duniya shikenan an shafe babinsu, ka manta sun yaɗa zuriya, gakunan ku har yanzu, tabbas Faɗima ta gado kakanin kakaninta wajen taurin zuciya, ba zata sake samun salama ba a yanzu haka har sai ta aiwatar da abin da ta ƙudurta, abu ɗaya zan sanar da kai shine ka gaggauta samo wanda zai zama mahaɗin rayuwarta, ita nada da taurin zuciya, kuma tun da abin ya soma bayyana yanzu ya zama dole a nemo mutum me raunanniyar zuciya domin shine mahaɗin rayuwarta, masu irin zuciyarta rayuwarsu kan inganta ne idan aka haɗa MABANBANTAN ZUKATA a waje ɗaya, ita zafi da taurin zuciya, sai a samu sai rauni da sanyin zuciya, ahaɗata zama waje ɗaya ko kuma a ɗaura ma ta aure da shi domin inganta rayuwarta, naji matuƙar daɗi da hakan bata faru ba sai yanzu da takai munzalin aure, da ace abin ya bayyana tun a yarinta da ba ita kaɗai ba hatta mu iyayenta sai mun ji jiki, Allah ya jiƙan magaba masu wannan lalura ya haskaka makwancinsu, ita kuma Allah ya sassauta ma ta."
Tun daga kan ƴaƴa da matan gidan du jikunnansu sunyi sanyi ƙalau, su na da yawan rigima da hayaniya amma kawunansu a haɗe suke, kuma su na zama a tare su jajanta idan wani abu ya samu ɗaya daga cikinsu ko da kuwa ƙaramin yaro ne bare babbar budurwa irin Najma, wacce ita kaɗai ce ta fita zakka a cikin tarin ƴaƴan gida, bata faɗa haka kuma bata sa'insa da kowa, idan su na hayaniyarsu ko dambe takan kallesu ne kawai ta wuce wani lokacin kuma ta girgiza kai tace Allah ya kyauta, idan sun dame ta kenan.
Sai yanzu da Inna ta basu wannan taƙaitaccen labarin suka soma hasko yanda sam bata bada damar da ranta zai ɓaci, ko mi za'ayi ma ta kuwa, kodai ta wuce tabar wajen ko kuma ta share mutum har yayi ya gama.
Sharce zufar da ta ke to ma shi Ale Idi yayi, yayin da hankalinshi yai ƙololuwa wajen tashi, nan take labarin irin wahalhalun da kakaninsa masu irin lalurar suka sha ya haska a cikin kanshi, cikin rasa abin yi ya kalli Inna sannan ya ce.
"To Inna yanzu minene mafita?."
"Mafita ɗaya ce Idirisa dole sai de abin yanda na ce, ai kai nasan baka mance kakaninka da irin faman da suka yi ba, abin da zai fi shine kawai a dage da addu'a kafin a soma laluben mafita."
Jikin kowa a sanyaye haka suka fice daga ɗakin aka bar Najma ita da Ale Idi yana rarrashinta.
Mama Saudah ce ta ɗauko ledar abincin da Najma ta kawo ta aje gaban Inna Sabuwa tana sharce hawaye sannan ta zauna tare da dafe kai.
Abincin da ake rububi kanshi idan aka kawo sai gashi yau babu wanda abincin ya isa koda kallo, hatta ƴan matana gidan jikunansu a sanyaye ya ke haka sukaita rarraba ido jikunansu a sanyaye........✍🏻
MARYAM STAR⭐⭐