FIVE
***
💗💗💗💗💗💗
𝙈𝘼𝘽𝘼𝙉𝘽𝘼𝙉𝙏𝘼𝙉 𝙕𝙐𝙆𝘼𝙏𝘼❤️🩹❤️🔥
𝙎𝙏𝙊𝙍𝙔 & 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙏𝙀𝙉
𝙈.𝙎𝙏𝘼𝙍⭐⭐⭐
💪𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉 💪
𝗧𝗛𝗘 𝗦𝗛𝗜𝗗𝗢𝗥𝗜𝗔 𝗪𝗥𝗜𝗧𝗘𝗥'𝘀 𝗧𝗘𝗔𝗠💪✍🏻
Chapter 5
Har aka yi isha'i su na a wannan yanayin, a ranar ko firar dare basuyi ba haka kowa ya je ya kwanta tun da wuri.
A safiyar ranar litinin, motoci ne su biyu akan haryar da sam bata da kyau sai ramuka da kwazazzabai, gudu kawai suke sharara kowa na ƙoƙari wajen ganin ya wuce ɗan uwashi, abin da ya basu mamaki bai wuce yanda suke sake dosar hanga ɗaya ba, a daidai wajen wa ta ƴar ƙaramar bukka da ke can cikin surniƙin daji suka ci birki, ko wannensu ya fito da sassarfa tare da nufar bukar gadan-gadan, kafaɗunsu na gogar na juna suka shiga bayan sun karanto wasu kalmomin surkulle.
Ƙaton baƙi ƙirin ɗin mutum ne me mummunar hallita zaune akan iska idanuwansa a waje, wa ta murya ce marar daɗin amo ta karaɗe wajen tare da faɗin.
"Mi ke tafe da ku."
Waige-waige suka soma yi amma basuga kowa ba, kuma wannan mutumin na gabansu babu alamun shine yayi maganar dan yana a yanda suka iske shi.
"Hhhhhhhhh ba zaka tu taɓa ganin me magana ba ƴan samari, ku faɗi buƙatunku kai tsaye kunzo inda za'a biya muku su."
Abdul ne ya soma magana.
"Sunanta Najma zuciyarta nike so a mallake min sai yanda na yi da ita, ina so ta kamu da matsananciyar soyayyata wacce zata zautar da ita."
Shima Muhasin a daburce ya furta.
"Mahwishi, so nike a idasa bugar da bugaggiyar zuciyarsa, ina so yaci gaba da jinya har tsayin rayuwarshi, sannan a janye hankalin iyayenshi daga gare shi, ina so inzama ɗan gaban goshi a MUZAFFAR FAMILY, ina so in zama ɗaya daga cikin masu faɗa a ji."
Shima ya karanto buƙatarshi kamar yanda Abdul ya karanto.
A maimakon waccan muryar yanzu sai suka ji tashin muryoyin mutane biyu mace da namiji su na faɗi.
"Buƙatarku zata biya, kusa a ranku anyi wannan angama, muddin kuka cika sharriɗai babu makawa komi zai faru cikin ƴan kwanaki, amma muddin aka saɓa sharaɗi koda guda ɗaya ne, la shakka aiki zai baci sanan a kwai bi baya."
Kallon junansu suka yi duda basu san juna ba sai suka saki murmushi a tare sannan suka ce.
"Mun amince."
Rufewar bakinsu ke da wuya suka hangi wannan mutumin ya motsa gami da buɗe idanuwansa, ruɗewa suka yi gaba ɗayansu, ganin wuta na fita daga idanuwanshi, bakinshi kuma ya buɗe lokaci ɗaya wasu ƙulluka suka bayanna akan dogon harshensa me rassa biyu, ko wane reshe ya aiko da maganin wajen mutum ɗaya.
"Ku ɗauki wannan maganin ku tabbatar kun bawa waɗanda kuke son halakawa da mallaka a cikin naman fararen tantabaru, ku basu suci har na tsawon kwanaki bakwai, sannan karku kuskura ku sake haɗuwa da junanku, idan hakan ta faru komi zai lalace, lalacewar komi kuma na nufin ladama marar amfani, ku tashi ku je, idan buƙata ta biya zamu zo da kanmu mu amshi ladar aiki.
Jikunansu na rawa suka ɗauki magungunan sannan suka fice, a gaban motocinsu suka tsaya su na kallon junansu, sai kuma ko wanensu ya juya ya shiga mota suka sake yin tsere a hanya.
Sun tafi ne kowa da ƙudurin aiwatar da aikinsa, ba tare da sun san wa ta ƙaddarar ta riga da ta gifta a tsakanina ba, wa ta ƙaddara da basu yi zaton zuwanta a yanzu ba da wataƙila basu je wajen boka mushiriki ba.
Najma.
Yau tun farar safiya Ale Idi ya rarrasheta akan ta samu ta ci wani abu, amma ko bakinta bata iya buɗewa bare ta amsa shi, sai idanuwanta da suka kaɗa sukai jazur babu wannan haske me burgewa a cikinsu, da taimakon Mama Saudah aka canza ma ta kaya, suka nufi asibiti, da fatan alkairi duka mutanen gidan suka bi su, wasunsu na sharce wahaye, da suka isa daidai bakin hanya inda zasu tari abin hawa, sai Najma ta kwace hannunta daga na Ale Idi ta soma takawa cikin sassarfa, Ale Idi har ya tsaida abin hawa si yaga ta tafi, ba shiri ya sallami me abin hawan ya biyo bayanta yana tambayarta, ba tare da yasan suna taka wani tsani bane daga shi har iya wanda ƙaddara ta zartar a kansu a wanan ranar, jerawa yayi shi da ita su na tafiya akan ƴafafuwansu har suka yi nisa sosai suka bar unguwar, ta layin da ke shaƙe da ma'aikatu suka gibta, a daidai nan ne suka cimma ƙaddararsu.
Najma na bayan Ale Idi suka zo giftawa ta gaban wani Company sai suka iske anata tafka rigima, mutane sai guduwa suke yi, yayin da a daidai lokacinne Najma ta ɓacewa Ale Idi wanda hankalinshi yai masifar ta shi, juye-juye ya ke yana kwalla kiran sunanta cikin dandazon mutanen da ke gudu, amma ba tare da saninsa ba ya ke komawa baya, yayin da ita kuma ta yu gaba bisa ga umarnin zuciyarta.
Mahwish
Bayan antafka mahawara shi da Mommcy da ya ce mata zai fita ya zaga gari ya ɗansha iska, tuburewa ta yi akan babu inda zai je, amma ya nace ma ta, daga ƙarshe dai ya samu ta amince amma da sharaɗin tare zasu fita, cikin ƴan mintuna ta sa aka shiya musu motoci na alfarma tare da securitys kusan motoci goma, cike da farin ciki suka fito hannunshi cikin nata su na tafiya su na ɗan tafa hira, haka ma'aikata sukaita zubewa miƙa gaisuwa gami da addu'ar samun kafiya ga Mahwish.
Lokacin da lafiyayyun motocinsu suka fice daga gidan suka haura kan kwalta, wani abu ne ya shiga warwarewa daga can cikin zuciyar mahwish, yana ji wani abu me muhimmanci na gab da kusantarshi, sai ya ji ya ƙagu su ƙarasa wajen da abin ya ke, haka yai ta danna alamar sanarwa ta cikin motae yana bada oder a canza hanya, a daidai lokacin da suka kusanto wajen, ji yayi raunanniyar zuciyarahi ta ƙara sauri wajen dokawa, alamar sanarwar akwai matsala nan gaba kaɗan securitys suka dannan amma sai ya basu alamar ci gaba da tafiya ba tare da shi kanshi yasan abin da yake yi ba, daidai lokacin da ya zuge glashin tare da danna alamar tsayawa idonshi ya tsallake tarin mutanen da ke guje-guje a wajen ya sauka akanta ita kaɗai, ita kaɗai ɗin da tarin mamakin da aljabin ganin yanda hankalinta ke a kwance ya kusa sumar da shi, sai de komi ya tsaya ne a sa'ikinta ya hangi wa ta kakkaifar wuƙa daga gani sabuwa ce dal tai masauki a gefen cikinta, ƙyas idonshi ya ɗauki hoton yanda ta rintse ido tare da dakatawa da tafiyar, da dannan alamar umarnin fitowar Securitys da zagayeta da mutanen wajen sukai da hakalin Mommcy daya kai wajen da taga ɗanta ya maida hankalinshi bayan taga tsananin ruɗu gami da tashin hankali akan fuskarshi, ƙara itama ta saki ganin yanda mazaje biyu suka soki matashiyar budurwa a wajaje mabanbanta da wuƙaƙen hannunsu, atare ida, Mahwish da gurds suka isa wajen a gigice.
Bayan guadrs sun yi nasarar watse matasan ta hanyar harbin iska da bindugunsu, da sauri Mahwish ya isa wajen, saƙala hannunta Najma wacce jiri ke ɗiba ta yi a na wani matashi wanda ta kira da balarabe tayi, sannan gwuiwoyinta suka sake, ta ɗurƙushe a wajen, a lokacin ba ita ke da iko da gangar jikinta ba, zuciyarta ce ke riƙe da ita, shine dalilin da ya hanata kaiwa ƙas tuntuni.
Jajayen idanuwanta ta saka a cikin nashi a saman ballanta da ke makyarkyata ta furta.
"Abbana, ka nemo min shi tare muke."
Yasan shi me rauni ne, zuciyarshi bata da ƙarfi sam amma sai yaji wani ƙarfi nan take na tsaga ƙirjinshi yana dira akan zuciyarshi, da hannuwansa ya ɗauke ta cak jininta malala a ƙasa, yana ƙoƙarin juyawa da sauri Ale Idi ya riƙe kafaɗushi idanuwansa na soma zubar da kwalla ya furta kalmar.
"Ta mutu ko, ƴa ta ce ita."
A lokaci ɗaya bayan faruwar abubuwan da suka faru a baya, Mommcy ta ji wani abu me nauyi na kwaranyewa daga zuciyarta yana bin isa, tsanar talaka shine wannan abu, kallon yanayin rauni da sadaƙarwa a karon farko daga fuskar Ale Idi ya sanyata jin ta yi nasara tayi nasarar ganin rauni akan fuskar talakawan mutane masu tsananin son kansu, masu ganin sun fu kowa wayo.
Bata san ya akai ba sai cintar muryarta ta yi na faɗin.
"A'ah bata mutu ba she is still a life, muje hospital."
Ta faɗa a tausashe tana kallo yanda hawaye ke gudu akan fuskar Ale Idi.
Idan kunyi comment yanda ya dace zan sa muku page 6 zuwa dare idan kuma naga sai a hankali zan barku da halinku🤓😠
NI CE TAKU
MARYAM STAR ⭐⭐