SIX
Chapter 5&6 Ɗazu nayi mistake zan saka 4 sai na saka 5, zanyi wannan a matsayin 5&6
Ale Idi wanda jikinshi ke rawar tashin hankali ya shiga motar jikinashi na rawa, gidan baya Mahwish ya nufa da Najma yayinda idonshi ke ƙur a kanta yana ganin yanda ta kafeshi da nata idanuwan waɗanda suka yi jazur kamar gauta, du lokacin da idanuwan na ta suka shanye kamar zasu lumshe sai ita kuma ta ware su sosai tare da sakin ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya, wani abu ne ke sake buɗewa a ƙirjin Mahwish.
"Mommynah, kin san mi."
Ya faɗa ba tare da ya janye idonshi daga kan Najma ba.
Mommcy da ta riga ta ruɗe ganin yanda jini ke kwarara daga jikin Najma ta kalli ɗanta da a yanzu ta ke gani wani abu a tattare da shi, wani abu wanda kullum shine fatanta akanshi, wani abu mai muhinmanci a rayuwarshi wanda baya da, wato kwarin gwuiwa.
"A,a son ban sani ba minene faɗamin, da sauri please."
"Ina jin sauyi sosai a zuciyata idan ina kallon idonta, a,a ba idonta ba Mommy cikin idonta akwai wani abu kina iya ganinshi."
Da jin abin da ta faɗa sai Mommy ta zauɗo kanta sai tin fuskar Najma, iya ganinta bata ga komi ba, sai de ta jinjina tsananin jarumta irinta yarinya.
"Banga komi ba son, bana ganin komi sai tarin jarumtaka a tattare da ita."
A kuma daidai lokacinne motocin suka tsaya a harabar hamshakin asibitin( LAGOON HOSPITAL VICTORIA ISLAND).
Da sauri nosis suka iso da gadon ɗaukar marar lafiya aka ɗaura Najwa da Mahwish ya ɗauko a hannuwansa cikin jini, ko da ana tura ta akan gadon hannunsa na cikin nata su na tafiya a tare, lokacin da aka nufi ƙofar emergency da ita, anan ne aka zage hannunsa daga cikin na ta, sai de mi zare hannunta daga cikin na shi keda wuya ya ji wani irin jiri na ɗaukarshi, ba shiri ya duƙa a wajen yana haki gami da maida numfarfashi, cikin alamun soma galabaita ya ce da Mommcy.
"Ruwa."
Ko bayan da ya sha ruwan bai dawo daidai ba, sai ma soma rikice da jikinsa yayi nan take aka bashi gado.
Ale Idi kuwa nan bakin ƙofar emergency ya zauna tare da rafka takumi, nan take wani imani da tsoron Allah ya shige shi, ganin yanda lokaci ɗaya komi ya faru, daga wayewar garin yau zuwa fitowarsu gida da afkuwar lamarin kwata-kwata ba a wuce awanni huɗu zuwa biyar ba, sai ya dinga hango Najma a jiya daya taras ta dawo gida, da yanda ya bita a guje yana zaginta har bakin titi, sai kawai kuka ya sake kwace ma shi, a fili ya dinga furta.
"Faɗima ki yafe min, nasan na gaza wa rayuwarku ta wajaje da dama amma da yardar Allah daga yau na canza, na canza ta sanadiyar ƙaddarar data same ki Faɗima".
Wasu ma'aikata maza ne biyu suka zo inda ya ke zaune cikin tausasa harshe suka soma rarrashin shi da kalamai masu tausasa zuciya, da ya ke aikinsu ne nan da nan suka samar ma shi da ƴar nutsuwa, abin ka da asibitin masu kuɗi, harda sassanya ruwa da abin motsa baki suka aje ma shi, sai de bai iya taɓa komi ba illa ruwa me sanyi, shine ya shanye ruba ɗaya har da rabi, yana ganin kira na shigowa wayarsa da numbobin ƴaƴansa data Mama Saudah amma ya kasa ɗauka, dan bai san yanda zai soma yi musu bayani ba.
Mama Saudah.
"Bai daga ba ko Lawisa, ni dama nasan ba lafiya ba, jikina yana bani ku barshi kawai mu gani zuwa anjima a sake kira ƙila aci sa'a ya ɗauka."
Jiki a sanyaye Lawisa ta ce.
"Gaskiya ko ni na fara zargin da wani abu, idan ba haka ba tayaya za'ayita kiran kayin Baba amma baya ɗauka, Baban da a kira na farko yake ɗaukar waya koda kuwa flashing ne, to kodai inbi bayansu asibitin in gani."
"Eh wallahi Lawisa da gaskiyarki garadai a bi baya aga ko lahiya, bari in ɗauko babur ɗina sai mu je mu gani."
Sauran matan gidan ma du sunyi na'am da Lawal da Lawisa su je su duba amma sai Mama Saudah ta ce.
"A'a Lawal ni ina ganin zaifi kawai a haƙura mu jira dawowarsu, kasan dai halin Babanku idan da matsala ai da tuni ka ganshi nan ya dawo ko ya kira waya mu barwa anjima mu gani."
"A'a Mama bara dai mu je ɗin ko hankalinki ya kwanta kema, bamuso kina wannan kukan wallahi."
Cewar Lawisa tana gyala mayafi suka wuce ita da Lawal, da fatan alkairi kowa ya bisu sannan suka dawo su na tattaunawa akan lalurar Najma, da kuma yanda za'a samo mafita cikin sauƙi.
Aƙalla Lawal da Lawisa sun je ƙananun asibiti kusan biyar amma sam basu samu ganin Ale Idi ba, haka sukayita zagaye haɗi da tambaya ko wani ya gansu, amma ba wani labari, har ma'aikatar sa Najma ke aiki sai da suka je, amma aka hanasu shiga, du magiyar da suka yi ba'a barsu ba hakanan suka juya gida jiki a sanyaye, yayinda suke ta sake kiran number Ale Idi amma sam bata shiga kwata-kwata, yanzu wayar a kashe ta ke.
LAGOON HOSPITAL VICTORIA ISLND
Likitoci kusan su uku ne suka fito su na sharce gumi, daidai lokacin da Alhaji MUZAFFAR da Mommcy suka ƙaraso wajen, yayinda shima Ale Idi ya taso cikin rawar jiki yana tambayar.
"Doctor ta mutu ko, nasan ta mutu ai.!
Sai ya soma share hawaye, amma mi sai Doctor ɗin ya dafa shi tare da faɗin cikin harshe nasara.
"Na taya ka murna abokina, tana a raye bata mutu, mun gama yi mata ɗinki ta samu raunuka masu girma sosai, yanzu haka idanuwanta biyu munyi ma ta allurar barci amma bata amshi jininta ba, zata iya kai awanni biyu jafin ta fara aiki a jikinta, zaku iya ganinta amma banda hayaniya da surutu."
Ale Idi tare da Mommcy suka sauke ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya, da sauri ta damƙi hannu Alhaji Muzaffar suka rufawa Ale Idi baya.
Kwance ta ke saman gadon asibitin, cikinta da cinya harma da kafaɗunta nannaɗe da bandeji, fuskarta ta sake jin jazur idanuwanta ma haka, ta kafe waje ɗaya da ido tana kallo babu ko ƙiftawa.
Alhaji Muzaffar mutum ne me damuwa da dauwar nash kawai, baya sanya damuwar wasu a kanshi, a karo na farko a rayuwarsa da ya ji zuciyarsa ta cike, irin cinkewar da ta ke idan yaga Mahwish a cikin yanayin ciwo, al'ajabi gami da mamaki lulluɓe a saman kamilalliyar fuskarsa, fuskarsa wacce a waje babu wanda yasan damuwa ko farin cikinshi, iya iyalanshi kawai, su kaɗai ne suke gani damuwa akanta amma banda bare.
Ciki de izza ya soma takawa zuwa wajen Najma data tsare Ale Idi da ido tana yi mishi magana amma sautinta bai fita.
Karo na farko da yaji bakinshi ya ambaci sunan wa ta bare da kalmomin "Ƴata." ba iya shi da furucin ya daki kunnenshi a bazata ba, hatta Mommcy sai da ta ware idanuwanta a kanshi, kiran sunan bai ishe shi sai da ya ƙarasa wajenta ya ɗan ranƙwafa tare da shafa kanta da aka zame hular saboda wawakekiyar yarkar da aka yi ma ta.
Tsigar jikinshi ce ta soma tashi ganin yanda ƴar ƙaramar alhaki ta iya jure waɗanan manyan raunukan da ya ke gani, farko da Mommcy ke sanar da shi zuwanta asibiti da abin da ya faru bai kawo komi ba, amma yanzu da yaga yarinyar da hannayensa suka soma ƙirgen iya adadin shekarunda ba zata wuce ba, sai ya ji wani abu ya harbi dakakkiyar zuciyarsa, da kuma ya kirata da sunan ƳATA sai wani fata ya lullube zuciyarshi, fatan da shi kanshi bai san na minene ba, yanzu kuma da ta saka idanuwanta a cikin na shi, sai da zuciyarshi ta yi rawa, jarumta, juriya gami da ƙarfin hali ya ke gani kwance a cikinsu, abin da kullum ya ke buri da mafarkin gani a cikin idon na shi ɗan.
Dafa kafaɗarshi Mommcy ta yi ganin yanda ya kafe yarinyar da kallo.
"Kaima kana ganin abin da Mahwish ya ce min ya gani a tattare da ita ko."
Ba tare da ya ɗauke idonshi daga kant ba ya ce.
"Tabbas na gani."
Wayar da Ale Idi ya soma yi ne ta sa suka ɗago su duka suna kallonsa.
Waya ya ke da Inna Tabawa yana sanar da ita su na asibiti sun yi hatsari ne a hanya, kuka ta fashe da shi tare da tambayarshi wace asibitice suke gatanan zuwa.
Dawo da kallonsa yayi wajen su Mommcy sai ya tambayesu cike da girmamawa.
"Ranku ya daɗe nace ya sunan asibitin nan iyalaina na nan tafe zuwa dubiya."
Mommcy ce ta faɗa ma shi sunan sannan ta ƙara da tambayarshi miye sunan unguwar ta su sai ta aiki driver ya je ya ɗauko su.
Wani yanayi ne ya gifta akan fuskar Alhaji Muzzafar, ba tare da ya ce komi ba ya soma takawa cike da izza ya fice.
Jiki a sanyaye Mommcy ta bi bayanshi, ɗakin da aka kwantar da Mahwish ta nufa, tana buɗe ƙofar ta iske Papie zaune akan kujera ya tsurawa Mahwish wanda na'urori ke aiki ta ko ina a jikinsa ido, zama ta yi itama tare da kafe Mahwishi da ido, tsintar muryar Alhaji Muzzafar ta yi yana faɗin.
"Ki basu iya adadin kuɗaɗen da zasu ishesu jinya, amma karki kuskura ki sake kusantarsu, suɗin talakawa ne, bana son wa ta alaƙa ta kusa kota nesa ta sake haɗaku."
Cike da girmamawa ta gyaɗa kai, a can ƙasan ranta ta na jin wani iri, ta sani bama ita kaɗai ba du wani wanda ya ke cikin MUZZAFAR FAMILY basa hulɗa da talakawa, saboda wani lamari daya auku a can baya, haka kawai sai ta ke jin kamar zasu rasa wani abu wanda suka jima su na nemane a tattare da waɗannan talakawan, kamar zasu aikata kuskure idan suka nisance su......✍🏻
TAKU HAR KULLUM
MARYAM STAR.