SEVEN
Follow the MARYAM UMAR HAUSA NOVELS BOOKS LIBRARY 📚📚 channel on WhatsApp: ***
𝙈𝘼𝘽𝘼𝙉𝘽𝘼𝙉𝙏𝘼𝙉 𝙕𝙐𝙆𝘼𝙏𝘼❤️🩹❤️🔥
𝙎𝙏𝙊𝙍𝙔 & 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙏𝙀𝙉
𝙈.𝙎𝙏𝘼𝙍
𝘾𝙝𝙖𝙥𝙩𝙚𝙧 7
Kamar yanda Mommcy ta ce, driver ta tura bayan Ale Idi yayi ma shi kwatancen gidanshi, babu ɓata lokaci ya tafi ya kwaso mutanen gidan kusan su goma sha, tun ciki motar su ke baza ƙauyanci sunata sambatun kyawun motar da kuma girmanta.
Lokacin da suka isa asibitin kuwa, bakunansu a buɗe suka soma santin kyawun asibitin, sai de lokacin da suka yi tozali da fuskar Ale Idi suka ganshi a sanyaye, sai suka dawo hayyacinsu suka cigaba da jimanta lamarin.
Dukaninsu sai da suka sha kuka sosai ganin yanda kamar Najma ta sauya nan take, dan ma lokacin da suka zo barci ya ɗauketa, Mama Saudah ko sai da aka fidda ita waje dan kuka ta yi sosai, sama-sama Ale Idi ya basu labarin abin da ya faru, sosai suka yi addu'ar samun sauƙi ga Najma suka kuma nemi ya nuna musu waɗanda suka taumakesu, bai musa ba ya nufi haɗaɗɗen word ɗin da aka kwantar da Mahwish sai de du magiyar da sukasha ba'a barsu sun shiga ba, dan murɗa-murɗan securitys ne kusan guda biyar ke gadin ƙofar, hakanan suka koma suka ci gaba da tagumi.
Najma bata farka ba sai marice lis lokacin an maida ƴan gidansu, daga Inna Tabawa sai Mama Saudah shima Ale Idi ya tafi yaɗan huta dan zazzaɓi ne rau a jikinshi.
Mommcy ce ta shigo ɗakin hannunta ɗauke da wa ta madaidaiciyar jaka, nan suka gaisa da Mama Saudah suka kuma yi ma ta godiya sosai na irin taimakon da tai musu, amsasu tayi da babu komi sannan ta miƙawa Mama Saudah da take ganin kamar Najma kwance akan fuskarta, jakar kuɗin tare da yi mata bayani akan kuɗin jinyar yarinyarta ne me gidan Alhaji Muzaffar ya biya.
Har kuka sai da Mama Saudah ta yi ganin yawan kuɗaɗen bayan taimako da suka yi na ceti ran Najma suka kawota asibiti cikin lokaci.
Mommcy ta juya ta fice tana sake kallon jar fuskar Najma, tana fatan daina jin abin da ta ke ji akanta, tunda ƙaddara ce ta haɗa su kuma ita ce ta rabasu a yanzunan.
Sai de abin da bata saniba shine, wannan ƙaddarar me tsawo ce, hasalima yanzu za'afara ba'ayi komi ba, haka zalika bayan nan akwai wani wajen inda zata sake haɗasu, ba tare da su kansu sunyi tunani ba.
Kusan lokaci ɗaya Najma da Mahwish suka farka, sabanin ita data farka tana jinta garas saboda allurar kashe zugi bata sake ta ba, shi da matsanancin ciwo ya farko, kwararrun doctors ne zagaye da shi sunata faman aikinsu, yayinda Mommcy ta kwantar da kanta akan cinyar Papie ta shiga rero kuka kamar ƙaramar yarinya.
Likitocin sun yi iya yinsu akan shi amma sai a hankali, da kyar suka shawo kanshi matsalar, hakan ya saka bayan sun fito suka nemi ganin Papie.
Ko da ya je bayani suka yi ma shi akan yanda ciwon kullum yake ƙara gaba, zuciyarshi na ƙara raunana, ta yanda ba lallai ya iya sarrafa kanshi ba saboda raunin da ta yi, da buƙatar su samo wanda zai iya kula da shi, sam basu gane bayanin doctor na samo wanda zai kula da shi ba, dan haka sai Mommcy tayi karaf ta ce.
"Waye wanda zai kula da shi fiye da mu, muna bashi duk wata kulawa ta musamman hasalima a tare da shi muke barci a gado ɗaya."
Murmushi baturen likitan yayi sannan ya zare glass ɗin idonshi tare da duskantarsu da kyau sannan ya ce.
"A halin yanzu kulawar da kuke bashi sam ba ita yake buƙataba, yana buƙatae farin ciki da tarairaya, sannan yana buƙatar abin da zai dinga bashi ƙwarin guiwa, saboda rauninsa yayi yawa sosai."
Cikin lafiyayyen turanci Papie ya ce da doctor.
"Du abin da ka lissafo babu wanda muka rageshi da shi, muna yi mashi duk abin da ya dace, sai de idan wasu sharuɗɗan daban zaka bamu."
"Sorry freind, shin yanada mata ne ko budurwa?."
Tambayar ta zo musu a bazata, sai da suka kalli junanau sannan suka haɗa baki wajen faɗin.
"A'a babu."
"Good, to yana buƙatar mace arayuwarshi, amma macen jaruma mai taurin zuciya, wacce zata iya tafiyar da rauninshi ta bashi gwarin gwuiwa haɗi da kulawa."
Kalaman doctor sun haska wani abu a cikin kawunansu, su duka biyun hotonta ne ya gilma musu, amma sai suka maze suka ci gaba da sauraren doctor.
BAYAN KWANA BIYU.
Kwanan Najma biyu a asibiti aka sallameta bayan anyi mata du abin da ya dace, anbasu kayan dressing ingantatu akan du bayan sati ɗaya za'adinga wanke ciwon ana canza dressing.
Godiya da sanya alkairi Ale Idi yayi, sanan suka kwashi inasu-inasu sukai gida.
Har zuwa lokacin Najma bata nuna ta damu da ciwon da ke jikinta ba, hasalima tafi damuwa da damuwar Abdul da ke ƙara girma a zuciyarta, tana jin muddin zata haɗu da shi babu abin da zai hanata aiwatar da ƙudurinta, yanzu haka Allah-Allah ta ke ta warke ta koma aiki tasan acanne kawai zata dinga ganinshi.
Tattara kuɗaɗen da Mommcy ta basu suka yi suka aje gefe, basu taɓa ko sisina saboda shawarar da Inna ta bayar cewa a aje sai Najma ta samu sauƙi.
Yanzu du wannan hayaniyar ta ragu sosai, duda ba komi aka fasa ba, musamman habaice-habaice da ya riga yabi jikinsu, ana zama a zagaye Najama kowa na son yi mata fira dan ganin ta sake ta koma yanda ta ke a baya.
Yanznma Lawisa ce ke basu labarin wani saurayi da ta taɓa yi ya biyota kan hanya, shine dan taƙi kulashi kawai ya kama zaginta, harda jifarta da munanan maganganu, aiko ta kanainaye shi da dinga ɗirma ihu ta tara mashi mutane tace rasin ɗa'a yayi mata, nan matasa suka lakaɗa ma shi shegen duka suka barshi a wajen.
Buɗar bakin Najma sai cewa ta yi.
"Idan nice ke sai na fara ɗauke fuskarshi da zafafan maruka da zasu makanta ganinshi, sannan in laƙa ma shi shairin da babu wanda ya isa ya fitar sa shi, sai na tabbatar da na rabashi da du wani farin ciki na rayuwarshi sanan in kyaleshi."
Sai kowa yai tsuru ana kallon yanda ta ke magana a kausashe har tana taune busasun laɓanta.
Daga kuma wannan maganar bata sake magana ba har tsayin kwanaki biyu.
Mahwish.
Sai da ya shafe kwanaki huɗu baya huyyacinsa, a rana ta biyar ne ya farko, daga yanda yaga kwarin idanuwan Mommcy sun zurma can ciki, ya tabbatar da ya jima a kwace dan sosai yake ganin ramar da ta yi, duda a kimtse ta ke ciki wani arnen leshi me tsada a ido zaka fahimci kwayun da ta yi, amma shi kallon farko yaga rashin nutsuwa a tattare da ita.
A hankali ya ɗaga hannunsa sai tin inda ta ke tsaye bayan doctor kaɗan, da sauri ta matso kusa da shi tare da saka hannunshi cikin nata ta matse da ɗan ƙarfi hawaye na silalo daga gefen idanuwanta, sumbatar hannunshi ta yi tana jin yanda tsananin ƙaunarshi da tausayinshi ke zagaye jinin jikinta, da ace tana da dama, data cire ciwon daga jikinshi koda na kwana ɗaya ne, shima ya huta yayi sayuwa kamar kowa ba tare da ciwo ba.
Sake sumbatar hannunshi ta yi, tana jin yanda hannun yai lagai a cikin nata, sosai ta ke tsananin tausayin Mahwish musamman yanzu da take ganin rauni na sake baibaye rayuwarsa ba kamar baya ba, yanzu sam bashi da wani karsashi, tana son ganin tilon ɗanta ya watayawa kamar kowanne ɗa.
Bayan Doctor ya gama dube-dubensa ya ma fitar da magungun da za'a bashi a lokacin bayan ya saka wani abu a cikinsa, sai ya fice yana jinjina lamarin Mahwish ɗin, ba shi ba duka doctors da nurses da ke aiki a wannan asibitin sun san Mahwish da lalurarsa, muddin su na ƙasar ba'a rufe sati ɗaya ba tare da ankawoshi cikin halin ciwo ba, su kansu likitocin su na mamakin yanda har zuwa wannan lokacin ya ke a raye bayan irin baƙar wahalar da ya ke sha tun tasowarshi. (Sun manta da Allah ne me yin yanda ya so a kuma lokacin da ya so, babu me kashewa sai shi, kuma babu me rayawa sai shi, babu mai jah da al'amarinsa buwayi gagara misali Ubangijin hallitu baki ɗaya mai raha da jin ƙai.).
Mommcy ce ta taimaka ma shi yayi brush sannan ya yaɗansha tea shima ɗan kaɗan, sai ayaba da yaci kwaya ɗaya shikenan haka ta haɗa ma shi maganin, to fa anan ake yinta, dan sam Mahwish bai ƙaunar magani a rayuwarsa, duda kuwa ya zama abokin rayuwarshi dan ƙa'ida ne kullum sai ya sha su tun daga safe har dare, kullum sai anyi dambarwa da shi akan shan magani kamar wani ƙaramin yaro.
Yanzunma kauda kai gefe yayi tare da marairaicewa ya wani sake narke noƙaƙƙiyar muryarsa irinta marasa lafiya sannan ya ce.
"Please Mommy bana so."
"Sorry Love ni kuma ina so please."
Ta faɗa itama a marairaice kamar yanda ya yi.
sake shagwaɓewa ya yi sannan ya ce.
"Ni fa Mommy na ɓata da ke, yanzu sa Papie nike shiri dan haka ba kece za ki bani ba."
Yan da yai maganar ya sakata mirmusawa ba shiri sanna ta ce cikin mirmushi.
"Haba Love, sarai nasan halinka fa, shima Papie ɗin idan ya zo zaka ce kun ɓata ne, dan haka tun da mun ɓata maza amshi ka shanye ko in zane ka."
Ta yi maganae tana ɗaga hannunta ɗaya sama alamar zata kai suka, shi dariyama ta bashi, idan akwai abin yasan ba zata iya yi ba sam a rayuwarta, bai wuce dukanshi ba, matar da ko tsawa bata iya yi mishi bare kuma duka, ko kallon banza taga ana yi mishi sai inda power ta ta tsaya, saje taƙune fuska yayi tare da ɗora hannu ɗaya bisa kai kamar zai rusa ihu sai kuma ya ce.
"Shikenan tun da kin daina yi na, bani insha amma daga wannan ba zan sake shan wani ba."
Yanzu kam sosai tai dariya ganin yanda yayi zuba mashi kwayoyin ta yi a hannu tare da bashi ruwa, har lokaci da alamun dariya akan fuskarta.
Dariyar da ta sanyaya ran Mahwish har ya shanye magungunan ba tare da yaji antakurashi ba kamar kullum, kamar yanda ta ke a yanzu haka ya ke da burin ganin fara'arta a kullum, murmushinta na matuƙar sakashi farin ciki.
Duda sam baya jin daɗin jikinshi hakanan yai ta mazewa suka ci gaba da dira, ko Doctor da ya zo da takardar sallamarshi sosai yayi mamaki da ganin yanda Mahwish ɗin ya ware kamar ba shi, fatan samun sauƙi yayi mishi sannan ya sallamesu.
Sai da suka jira Alhaji Muzaffar ya zo sannan suka ɗunguma suka yi gida.
Akan hanya su na tafene kawai amma sam hankalinshi baya kansu, yana kan abin da tun da ya buɗe ido yake so ya ji wani bayani amma ya ji shiru, magana ce ta kubce daga bakinsa ba tare daya shirya ba.
"Wai Mommy ina wannan yarinyar Najwa ya jikinta ta farka kuwa."
Ɗif su dukansu suka yi tare da zubawa Mahwish ido, a daidai lokacinne motocin suka tsaya a kusa da sashensu, basu ce da shi komi ba illa sunkutarshi da Papie ya yi suka fice zuwa sashensu.
A saman luntsumemiyar sofa ya zaunar da shi, yayinda Mommcy ta danna oder da ke shedawa ma'aikatan kitchen ana nemansu da gaugawa, ma'aikata ne su biyu mata kowace hannuwanta riƙe da ƙaron tire, cike da girmamawa suka aje tare da jiran umarni, da hannu Mommcy ta sallame su, bayan ta tsiyayi ruwan tattaciyar kwakwa me sanyin ta miƙawa Papie, murmushi ya sakar ma ta sannan ya nufi bakin Mahwish da cup ɗin, shima tattausan marayan murmushi ya sakar musu su duka biyun sannan ya kirɓa a sanyaye yana jin yanda sanyin ya ratsa du wa ta gaɓa da ke aiki a jikinsa.....✍🏻
Taufa, ina team Mahwish ina Team Najma, shin mi kuke tunani game da waɗanan mutanen biyu masu mabanbanyan zukata.❓❓❓❓
YAUDAI IDAN BANGA COMMENT DAYAWA BA GOBE BABU UPDATE DAMA ZAN SHIGA BUSY.
NI CE TAURARUWARKU
MARYAM SYAR ⭐⭐