MABANBANTAN ZUKATA

NINE

by @maryamstar248


Chapter 9.

Haka kawai ta samu kanta da tsayawa cak, dalili wani sauti da ta ke tunanin iska ne ya ɗauko ma ta shi zuwa cikin kunnuwanta, amma mi ba iya sautin kaɗai ba, harda muryar Ale Idi ta ji yana ambatar cikakken sunanta.
   "Fatima tsaya manah."
  Shine abin da ta ji, sai kuma ta sake jin wannan tattausar muryar na tambayar Ale Idi ina zasuje, ji tayi da ace tana da dama da tuni ta saka remote ta tariye amsar da Ale Idi sai bayar, ta saka play daidai inda zai sake yin magana, aiko sai da Ale Idi ya bashi tun daga farkon labarin fitowarsu gida yau har zuwa yanzu, ta saki wa ta ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya ne a sa'ilin da ta jiyo muryar na faɗi.
   "To ku shigo mu ƙarasa nima zan je asibitinne zanga doctor."
  "Yah Allahu ya Rahaman ka kawo min ɗauki."
Najma ta furta a daidai lokacin da ta ke ɗaura hannunta me lafiya sitin zuciyarta da take jin wani abu na narkewa kamar yanda ƙanƙara ke narkewa, ba iya abinne kaɗai ya narke ba, ya narke ne tare da wani ɗaurin data kwashe satika tanajin zuciyarta ta yi, bama iya wannan ba, jinta ta ke fresh batada damuwar komi a rayuwarta, komi ya goge daga zuciyarta sanyin salama da nutsuwa ta soma sauko ma ta.
   Ji tayi koda sau ɗaya ne, tana so, tana so kawai ta ganshi koda a fizgenw, badan komi ba sai dan wani abu, wani abu wanda itama batasan ko minene ba.
   Saukar manyan dara-daran idanuwanta kalar madara a kan innocent pace ɗinshi, ya saka zuciyoyi biyu mabanbanta motsawa tare da soma harba jini ciki sauri da karsashi.
   Ita da ta ke nesa ita ya kamata ace ta karaso, amma sai ya ji bazai iya jure tsayuwa a inda ya ke ba, zai je ya isketa ya sake kallon tsakiyar cikin idanuwanta masu fizgar gami da ɗaukar hankalinshi.

  Abu na ƙarshe da bai zo tunaninta ba bayan zuwanshi gareta shine, kama hannuwanta duka buyun masu ɗumi da taushi da yayi a cikin nashi masu laushi da sanyi, sanyin daya haɗu da ɗumin hannunta suka bada wani abu na musamman, na musamman wanda ya soma aiki a mabanbantan zukata masu buƙatar samun kusanci na sosai.
   Hannayensa na cikin na ta ya soma takawa da baya-baya, dan bai jin zai iya sakinta saboda yanda yake jin sauyi na musamman na baibayeshi.

A karo na farko a rayuwar Najma data nemi inda taurin kanta da kafiya ya ke ta rasa, lokaci na farko data sallamawa wani namiji jikinta tana cikin hayyacinta, kuma lokaci ɗaya da ta ji zuciyarta ta buɗe, buɗewa irinta son shigar da wani abu me girma da muhimmanci a cikinta.
 Lokacin da suka isa gaban motar ne, ikon mallakar kai ya kwacewa Mahwish, yayinda kai tsaye yabi umarnin zuciyarshi, ba tare da jiran komi ba ya janyota da wani irin ƙarfi wanda a iya saninshi bai san yana da shi ba, yayinda ɗumin jikinta ya haɗu da nashi sai ya ji gamsashiyar nutsuwa irin wacce ya jima yana buƙata na baibaye shi.
   Lokacin da ta kwaci kanta gami da juya mashi baya tana sauke numfarfashi sai ya ji wani abu na matsewa tare da zuciyarshi.
   Ƙur ya ƙure bayanta da kallo, yana mamakin yanda rigar ta zauna ɗas a jikinta, duda bata kamata ba amma yana iya hango shape ɗin mazaunanta, haka kawai ya ji hannu sa na motsawa yana ƙoƙarin ɓallo mashi ruwa, sai de dawowar Ale Idi wanda ya amsa wayar Inna Sabuwa tun bayan tsayuwarsu wajen ya saka shi dawowa hayyacinsa.
  Cike da girmamawa irinta tsakanin talaka da mai kuɗi Ale Idi yaɗan rusuna yana neman afuwar ɓata mashi lokaci da yayi.

 A idon Mahwish kuwa babu komi sai tarin kunya data baibayeshi, kunya aba ce da bai cika jinta ba, hasalima zai iya ƙirga adadin sau nawa ya ji wata aba wai ita kunya a rayuwarsa, kuma koda zai ƙirga ɗin ba zata wuce cikin ƴan yatsun hannuwansa ba, amma ayau akuma yanzu sai ya ji wannan kunyar na baibayeshi, dan haka sai ya saka tausasan hannuwansa ya riƙi na Ale Idi tare da furta kalmar.
  "Papah, mu je ko."
Ba tare da ya saki hannun Ale Idi ba ya bada umarnin ɓuɗe gidan gaba kusa da driver sai da ya tabbatar ya shiga da kyau sannan ya rufe ma shi motar da kanshi, sai kuma ya dafa kafaɗun Najma da ke tsaye ta juya baya har a lokacin, bai jira komi ba ya juyo da iya gabanshi sannan ya kama nata hannuwan cikin nashi ya soma janta sanu a hankali har zuwa jikin motar.
   Tirjiya da kafewa abune da suka zama ɗabi'arta amma a yau kuma ayanzu ta  nemi kafiyar ta rasa, haka kawai ta ke jinshi kamar wani massarafinta.
   Koda ta zauna cikin motar kusa da shi a gidan baya, sai take jinta kamar a wa ta duniya ta daban, kuma kamar an sauya wani abu daga gareta, wanda bata taɓa tunani zai sauyu cikin sauƙi har haka ba, wato zuciyarta, zuciyarta data kasance mai taurin gaske, ta yanda take iya jin taurinta a cikin jikinta, amma a yanzu sai ta ji tayi laushi, laushi sosai irin wanda idan akace zata ti ita kanta zata ƙaryata hakan.
   Ale Idi na gidan gaba yana bawa Mama Saudah labarin wulaƙancin da ɗan sahu yai musu, yana kuma gama wayar sai suka hau fira da driver, do dama bakin drivern yayi tsami na rashin yin fira kullum zaman shiru, shima bahaushe ne amma irin samudawannan, dan haka sai suka ƙulle da Ale Idi suka ci gaba da fira.

  Mahwish ya so ya tsaida hannunshi daga ƙoƙarin kama nata  hannun da take wasa da shi, amma ikon mallakar kanshi ya kwace ma shi, dan sosai zuciyarsa ta shiga ingizashi har sai da ya damƙi hannun nata.
   Ɗan buɗe baki tayi da sauri tare da watsa ma shi wani kallo da dara-daran idanuwanta, kafaɗu ya daga irin i dont care, sannan yakai hannun ya sumbata tare da ƙanƙameshi a  ƙirjinshi.
    Sai kuma ya kalleta  da idanuwansa wanda take iya hango raunin a cikinsu sannan ya ce cikin lallausar muryarsa.
    "Ina son hannunki yana mini taushi sosai ina so please za ki bani."
  Idan ta ce ta fahimci abin da yake nufi to tabbas ta shutala zuƙeƙiyar ƙarya me wasilla, dan gaba ɗaya komi nata ya tsaya ne cak.

Ana cikin haka motocin suka ci burki a bakin ƙofar shiga cikin asibirin, kuma har lokacin bai saki hannuwanta ba, yana riƙe da su ahaka ya sauka tare da taimaka mata itama ta sauka.
  Kallon Ale Idi yayi tare da faɗin.
  "Papah zata iya tafiya ko in ɗauketa kawai."
 Baki washe Ale Idi ya ce.
  "Kai ɗannan wace ɗawainiya kuma ras ta ke iya tafita wallahi, Faɗima ce hwa, ai daga nan har birnin sin zata iya zuwa da ƙafafuwanta."
   Ware idanuwa da mamaki Mahwish yayi duda bai gama fahimtar maganganun Ale Idi ba amma sai ya ce.
   "Kai to tayaya take iya tafiya itada bata da lafiya sosai."
  Dariya Ale Idi ya kuma yi sanan ya ce.
   "Yo kai yaro indai gwagwarmaya ce ai babu wacce Faɗima taba saba da ita ba."
   
  "Papah, Mahwish, Mahwish sunana."

Dariya Ale Idi yayi kawai dan yaso ya kira sunan amma sai ya kasa, gudun kar ya kwafsa sai ya share kawai.
  
Najma bata ji ta gama shiga uku ba, sai da litita ya bata umarnin hawa gado, sannan ta buɗe raunikan.
  Ƙur ta ƙure Mahwish da ido tana jiran fitarsa amma sai taga ya sake gyara tsayuwa yana sakin murmushi.
  Ɗan taƙune fuska ta yi sannan tace da Doctor.
   "Kace mishi ya fita to."

Da dariya Doctor ya faɗawa Mahwish wai tace ya fita amma sai ya ƙi fitar illa zama da yayi a kujerarda Ale Idi ke zaune yana bawa Doctor bayanai jikinnata.
   Ko da ta yaye rigar zuwa sama sai da ta rintse idanuwanta duda akwai wando 3 kwata a ciki, amma irin me kama jiki sosai ɗinan ne.
Har doctor ya gama dube-dubensa da gwaje-gwaje Najma bata buɗe idanuwanta ba, har sai da aka gama komi, kuma kodata buɗe basu sauka a ko ina ba sai a kan innocent face ɗinsa, batasan yanda aka yi ba sai kawai ta samu kanta da gallara ma shi galelleyar harara gami da muguɗa baki gefe da gefe.
   Haƙuri ya bawa Ale Idi akan suɗan jirashi kaɗan zai amshi saƙo, saƙonda ya mance da saboda shi ya zo asibitin, sai da Doctor ɗin ya sake kiranshi akan koya fito ma shi da shi sai ya turo driver ya amsar ma shi, sai a lokacin ya tuna ya je ansa.
  Ko da ya je amsar a tsaitsaye suka gaisa a amsa tare da juyowa ya dawo, lokacin har an gama musu komi an sallamesu saboda babu wa ta damuwa.

A wannan karon gidan gaba Najma ta kankane driver na buɗewa Ale Idi tau wuf ta shige ta zauna, yayinda Ale Idi ya zauna kusa da Mahwish yana jinjina irin kyawun halin yaro na rashin wulaƙanci da kuma karamcinsa.

  Tun Ale Idi na labari da Mahwish har Mawish ɗin ya gaji, suka koma yi da driver, sai da aka jima ahanya basu isa ba, ahakama dan motocin lafiyayyu ne shiyasa suka isa da wuri.
   Kallon farko da Mahwish yayiwa gidan da yake mallakin Ale Idi sai da wani abu ya tsarga a zuciyarsa, ko a labari ba taɓa jin irin akwai ire-iren waɗanan gidajen ba, kuɗaɗen da shi kanshi bai san adadinsu ba ya bawa Ale Idi tare da faɗin.
   "Papa ga wannan please a nemo me gyara a sauya ƙofarnan kar a shigar muku gida ayi ɓarna."
  Ganin Ale Idi ya soma yin gardama ya saka shi kamo babbar rigar jikinshi ya saka jakar, dan a jininsu ya ke yawan kyauta, kyautarma irinta manyan kuɗaɗe masu nauyin gaske.
  Basu rabu ba sai da ya amshi number Najwa a wajen Ale Idi dan ita tuni tai shigewarta gida abinta.
DA DADDARE.

Kwance ta ke a ɗakin Inna Tabawa, babu abin da take yi sai juyi, tunani fal zuciyarta, tunanin mutumin da ya tsaya ma ta cak a rai, kafin Inna ta yi barci har saukowa ta yi daga kan gado ta nufi wajen Innar tana faɗin.
  "Inna riƙe hannuna kiji, kina jin wani abu ko."
  kama hannun nata Inna ta yi amma bata ji komi ba.
  "Fatsima wani abu ne ya sami hannun na ki nidai bana jin komi."
Maganar inna ta tabbatar ma ta da lallai ita kaɗai ta ke jin abin da ke a hannun na ta, ganin barci bazai ɗauketa ta sauƙi ya saka ta tashi ta ɗauki wayarta da ke cike da caji fal, ta kunna tare da lalibo indian film ta soma kallo, kira ne ya shigo wayar tata, mamako bayyane akan fuskarta ta ɗauki kiran bayan wancan ya yanke wani ya sake shigowa.



Mahwish
Da wa ta iriyar murna ya koma gida, tun akan matattakalar bene ya soma kiran iyayensa, yayin da suke a zaune su na shirin kiran wayar driver dan jin ko lafiya har yanzu basu dawo ba, sai suka cinkayo muryarsa cikin maɗaukakin farin ciki yana kiransu, mamaki damɓare akan fuskokinsu suka soma tambayarshi abin da ya faru.
 Da farko runguma ya  kai musu su duka biyun sannan ya daidaita zamansa akan cinyoyinsu kamar wani ɗan ƙaramin yaro, a wannan karon dariya yake kyalkyalawa sannan ya ce.
   "My Loves kun san wani abu, wallahi na ganta, bafa a mafarki ba a zahiri har kama hannunta na yi na matse a cikin nawa, Mommy kin ji wani da nike ji a nan."
 Ya faɗi yana ɗaura hannunta a saman zuciyarsa da yanzu take bugawa normal, sannan ya ɗaura da faɗin.
  "Ina jina cikin farin ciki sosai my Papie, ashe tana nan?."
  Fuskokinsu a sake suka tambayeshi.
Wai wacece wannan.
  Shiru ya gifta a tsakaninsu lokacin da ya basu amsa da Najma ce, nan take suka gane wacce yake nufi.
   A ƙasan ran Alhaji Muzaffar  sai da ya ji wani abu ya motsa, wani abu dabai wuce rashin jin daɗin yanda wa ta yarinya ta sake shigowa rayuwar ɗansu a karo na biyu ba, kamar wancan karon, wannan ma talaka ce, talaka marasa tausayi bare tsoron Allah, talakawan mutane masu tsananin son kansu. (Acewarshi amma ba ni ba.)
Alƙawari ya ɗaukarwa zuciyarshi akan ba zai bari ba, ba zai sake sakaci da rayuwar ɗanshi a karo na biyu ba, dole zai ɗauka tsatstsauran mataki, matakin rufe ƙofar du wani abu da zai sake kusanta ɗanshi da talakawan mutane, amma a zahiri sai ya ƙawata fuskarshi da murmushi gami da jerawa Mahwish tambayoyi a nutse.
  Kaf Mahwish ya basu labarin komi babu abin da ya rage a ciki hatta rungumar da yayiwa Najma, abinka da ɗan gayu sangartacce shalelen iyayensa, saima kallonsu da yayi tare da faɗin.
  "Wallahi har yanzu ina jin ɗumin tafin hannunta a nawa hannun." sai ya kai hannun saitin fuskarshi ya shafa, sai kuma ya janye tare da kaiwa akan fuskar Papie yana faɗin.
  "Ka ji ko Papie, har yanzu akwai." gyaɗa kai kawai Papie yayi dan shi bai ji komi ba illa sanyi da tafukan hannayen suka yi.

Shafama Mommy yayi, ita kam a maimaikon Papie sai jinjina kai tayi cikin.......

SAURA ƘIRIS MU GAMA FREE PAGE