MABANBANTAN ZUKATA

TEN.

by @maryamstar248



 𝙎𝙏𝙊𝙍𝙔 & 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙏𝙀𝙉
𝙈.𝙎𝙏𝘼𝙍⭐⭐⭐

💪𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉 💪

𝗧𝗛𝗘 𝗦𝗛𝗜𝗗𝗢𝗥𝗜𝗔 𝗪𝗥𝗜𝗧𝗘𝗥'𝘀 𝗧𝗘𝗔𝗠💪✍🏻

Chapter 10.

Na sadaukarda wannan page gaba ɗaya ga fans ɗita wato LATEEFA MUHAMED HASSANA, wacce aka fi sani da Last born, wato a gaskiya ina matuƙar jin daɗin comment na ki sister, ita ce the first a du lokacin da nai update da take fara comment and like, gashi jiya har nick name ta bami RYAM STAR, ina matuƙar godiya sosai siste, Allah yabar tare ina yinki over three billion dollars💞🌹.



Cikin biyewa shirmenshi ta ce. "Aiko dai son ga ɗumi nan gwanin daɗi."
  Dariya mai cike da nishaɗi ya yi sannan yakai ma ta sumbata  a goshi cike da farin ciki.

A daren ranar su na kwance akan makeken lafiyayen gadonsu, babu abin da ke tashi sai sassanyar muryar Mahwish yana basu labari, ba akan komi ya ke basu kabarin ba illa akan Najma, yarinyar da ta tafi ta kaso me tsoka na zuciyarshi ba tare shi da ita sun saniba, hannayenshi na cikin na mahaifanshi kamar kullum suna yin hakanne dan gudun kar su farka suga babu shi, saboda sun san akoda wane lokaci ciwonsa na iya tashi.
    Wani abu ne ya me kama da fata ya lulluɓe zuciyar Mommy, sai ta ke jin inama ace abin zai tabbata, badan komi ba sai dan farin cikin ɗanta, tillon ɗanta da zata iya sadaukar da komi nata akan farin cikinshi, sai de tasan hakan ba mai yuyuwa ba ne duk kuwa da irin son da Alhaji Mizaffar ke yiwa Mahwish ɗin, ta jima da sanin cewa babu wa ta dangantaka ta kusa ko ta nesa da ke shiga tsakaninshi da talakawa, tun bayan faruwar abubuwanda suka sauya komi, ciki harda rayuwar ɗansu da take a rikice da tarin ƙalubalen ciwo, ciwon da dashi ya zo duniya amma faruwar wani lamari ya ƙarawa wutar ciwon fetir, fatanta ɗaya Allah ya shiga lamarin ya nuna ƙarfin ikonsa akan zuciyar mijinta me tsananin tauri gami da riƙo, tana fatan samun sauyi a wannan rayuwar tasu, su koma kamar yanda suke a baya, walwala da dawwamar farin ciki ya sake lulluɓe su.

Tambayar da Mahwish ya jefawa Papie ce ta dawo da ita duniyar zahiri.
  Tambayar inda aka aje ma shi wayoyinsa da sai su ɗauki tsayin lokaci bai yi amfani da su ba ya jefawa Papie.
   "Wayoyinka su na wajena my son a ɗauko ne."
  Da alamar ƙaguwa ya amsa ta, tare da sake matsewa Papie yana yi ma shi raɗa a kunne, wacce ta saka  Alhaji Muzaffar murmusawa, har fararen haƙoranshi suka fito, sai ya kama ɗayan hannun bayan Mommcy ta tashi dan ɗauko ma sa wayoyinsa, a hankali ya shafa kan Mahwish ɗin tare da faɗin.
   "Farin cikinka shi ne nawa, kayi abin da kake so my lovely one and only son."
Sumbata ya mannawa hannun Papie tare da maida ma shi amsar  shima yana ƙaunarsa.
   Ko da Mommcy ta miƙo ma shi wayoyin  saboda sangarta sai ya umarceta ta kunna, bayan ta kunna ya amsa bayan ya bata sumbata sannan ya bawa Alhaji Muzaffar, Jerarrun lambobin wayarta daya jima da hardacewa tun lokacin da ya amsa a wajen Ale Idi ya shiga  karantawa Papie a nutse, shi kuma ya shiga saka number yana jin wani abu na ƙoƙarin taso ma shi, amma yana ƙoƙari wajen dannewa, ɗansa ne fa, ɗansa da yake fafutikar yawon ƙasashen duniya dan kawai ya nemo ma shi abin da zai saka shi farin ciki, dolene ya daure zuciyarsa na ɗan wani lokaci kafin ya aiwatar da abin da yake ganin shine daidai a lissafinsa.
  Kiran farko ba'a ɗauka ba sai da aka sake kira sannan aka ɗauka, kafin Mahwish ya ce wani abu sai da ya ja dogon numfashi sannan ya sakeshi tare da.
   "Assalamu alaiki warahamatullah."
  A yanda sallamar ta shi ta dira a ƙunnuwan Najma bata san sanda zuciyarta tai wani tsalle ba, saura kaɗan ta ɓalle allon ƙirjinta ta fito waje.
   Sai da ta saita muryarta sannan ta amsa da tata lallausar muryar.
 
  "Wa'alaika salam."

A tare Mommcy da Papie suka kai dubansu ga Mahwish da ya wani lumshe ido yana sake ƙanƙame hannayensu a ƙirjinsa saboda tsabar yanda muryarta ta saita ma shi nutsuwa, tare da dirar ma shi da wani abu a cikin jinin jikinshi.
  (Oh Allah kana gani, dan tsabar shegantaka irinta ƴaƴan gata a tsakiyar gadon iyayensa zai yi waya, uhumm ma ji ma gani ai muje zuwa 🥺😁🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️)

Bayan sallamar ya ɗauki lokaci ba tare da yace komi ba, ba kuma dan ya rasa abin faɗar ba, sai dan yanayin da ke sake lulluɓe shi a duk sanda sautin fitar numfashinta ya daki dodon kunnensa duda wayar na riƙe a hannun Papie amma du wani motsinta yana iya jiyo shi.

   Kamar yanda ya yi shiru baice komi ba haka itama ta zaɓi yin shirun tana sauraren bugun zuciyarta a cikin kunnuwanta tare da motsinshi.

   "Ya jikin ki?." 
Ita ce tambayar da ta daki dodon kunnenta a bazata.

A zuciyarta ta same maimaita tambayar, sai ta ɗora ta a wani mizani na daban, a zaronta yana iya ganin  yanda jiki da zuciyarta ke tsalle a sanadiyar kusancinta da shi a wayar, sake danƙar zanin jikin gadon ta yi a cikin tafukan hannayenta da suka sake yin ɗumi, kafin a hankali bakinta ya furta.
    
   "Alhamdulillah."

Sa'ilin da muryarta ta sake dira masa a kunne sai kawai ya zare hannayensa tare da dira ƙasa yai tsalle haɗi da juyi, gaba ɗaya farin ciki ya baibaye shi, ga wani ƙarfi da yake ji na mamaye mataciyar zuciyarsa, datse kiran Papie ya yi ganin abin da Mahwish ke yi kamar wani ƙaramin yaro, ba tare da ya shirya ba ƴar siririyar dariya ta kubce ma shi, sai kawai ya girgiza kai tare da tashi zaune.
   Sosai Mommcy ke ƙyaƙyatawa da ganin abin da Mahwish yayi, haka kawai sai ta ji ta samu sukuni, wannan tsoron gami da fargabar du sun kama gabansu.

A rana ta farko tun bayan shuɗewar wasu sheƙaru da afkuwar lamari, Mahwish ya kwana cikin matsanancin farin ciki, farin cikin da tarin dukiyar Alhaji Muzaffar ya gagara siya ma shi tsayin shekaru.


    Da amsa kuwar amon sassanyar muryar Mahwish Najma tai barci, waɗanna gajerun kalaman na sa taƙaitattu sun saka nutsuwa a hargitsatsiyar zuciyarta ta samu nutsuwa fiye da zaton mai zato, a washe garin ranar sai da ta makara sallar asubahi, dama gidan ba kowa ke tashi sallar asuba ba, sai randa aka yi katari wani ya farka da wuri, daga ita sai Inna ke yin sallar asuba cikin jam'in akan lokacinta, amma har Ale Idi sai garin Allah ya waye ya ke fitowa ayi layin shiga kewaye tare da shi, saura ƴaƴan gidan kuwa wasu har takwas na safe su na sallah saboda shagala.
    Hayaniya da kacaniyar gidan ta dawo, dama abin da ya faru da Najma ne ya shafi walwalarsu ganin yanzu ta ji sauƙi sai aka koma gidan jiya, hayaniya da iface-iface tun a farkon layi ana jiyo su, ɓangaren Ale Idi an samu cigaba dan yanzu na rage abubuwa da dama, ba kamar yawan faɗa da zagi, duda yana ɗan taɓawa saboda abin ya bi jikinsa, yanzu kuma ciwon daya dameshi bai wuce na zaunawa yaita yabon wannan matashin me suna Mahwish ba tare da bawa ƴan gida labarinsa da irin kyawun halinsa, yayi shawara da Inna Tabawa akan tulin kuɗaɗen da Mahwish ya bashi a gyara ƙyauren gida, sai ce mashi ta yi ya dakata da batun ƙuɗaɗen nan gaba zasuyi amfani, andai ɗauki ɗauri biyu ciki waɗanda Alhaji Muzaffar ya bayar aka yi amfani da su wajennjinyar Najma amma daga nan ba'a sake taɓa kudaɗenba, to dama Ale Idi ido ga naira bare hasu yana gani tuluguji, ai sai hankalinshi ya sake kwanciya.
  Da lokacin kari ya yi haka kowa na gidan aka hallara kwai da kwarkwata, Najma ce ƙarshe fitowa saboda barcin da ya ɗauketa, sai da ta bi du wani babba ta gaisar sannan ta zauna fuskarta washe da annuri, nan aka shiga tambayarta yanayin jikinta, da annuri akan fuskarta ta soma bawa kowa amsa da jiki ya warware, haka aka zauna ana karyawa ana raha, yau dai harda Najma a cikin masu kwasar dariya, akwai kyakkyawar alaƙa me tsafta a cikin iyalan Ale Idi, matsalarsu ɗaya yawan faɗa da kuma ruwan ashariyar da suke yayyafawa kamar ɗiyan maguzawa, idan aka cire wannan ahaline masu haɗin kai sosai  gami da ƙaunar junansu, su na ware lukuta dan su zauna da ɗiyanzu ayi fira ayi raha, abin gwanin burgewa.

 Sai wajajen ƙarfe goma kowa ya watse aka shiga sabgogin da aka saba, masu nema suka bazama, masu aikin gida suma aka saka haramar yi.




ABUJA NIGERIA.

ASOKORO
Zaune ta ke akan sofa, yayin da hannayenta ke tallabe da kumatunka ta yi nisa sosai a duniyar tunani har batasan zuwan matar da ke tsaye a kanta ba tana ƙare ma ta kallo cike da takaici.
   Girgizar da ta yiwa kafaɗarta ce ta dawo da ita duniyar zahiri, a ɗan firgice ta ke kallonta tana murtsuke ido, a sanyaye ta ce.
   "Sorry Mamaah ban san da zuwanki ba wallahi." ta faɗa tana share guntuwar ƙwallar data silalo akan idonta.
  "Wai ke Najwa yaushe za ki daina tunani akan wancan matacen wanda ya jima da mutuwa, a kullum kina ƙara ƙona raina idan na ganki a irin wannan halin, ko ki so ko ki ƙi, wannan yaron ya mutu, ya jima da mutuwa Najwa."
  Kallon matar ta yi idanuwanta na sake cika taf da zazzafar kwalla murya a hasale ta ce.

  "Ya mutu, tabbas ya mutu a idanuwanki amma banda nawa idon, ni nasan bai mutu ba, Mahwish bai mutu ba Mamaah, na sani kin sani shi ɗin yana da rauni, munyi amfani da rauninsa muka cutar da shi amma tabbas ni nasan yana raye, cuta ba mutuwa bace bare kuma dama can ya jima da ɗanɗara zafin ciwo, kina tunanin dan na yaudaresa shikenan zai mutu, a'a zai rayu, ni nasan zai rayu da ace zai mutu da tuni ya mutu Mamaah, tun kafin in shiga rayuwarsa, kin san raɗaɗi da azabar da nike fuskanta kuwa, kin san iri ɗacin da zuciyata ke yi, ba Mahwish muka cuta ba Mamaah kaina muka cuta, bai aikata komi bai da zunubin kowa, amma mufa, ga dukiya nan mun tara amma ta gagara ciyuwa a garemu, indai kuɗi ne mun samu a wajensa amma tsoron cin su nike, nasani ni da shi muna da MABANBANTAN ZUKATA, ni tawa zuciyar baƙa ce ƙirin saɓanin tashi da take fara ƙal mai nufin kowa da alkairi, Allah sarki Mahwish bawan Allah, bawanda ya ke kwanciya yana tashi da ɗumbin gafarar Ubangiji akan jinyar da ya jarabeshi da ita."
.......✍🏻
  Taufa masu karatu kun ji mun buɗo wani shafin kuma, ku biyoni sannu a hankali dan jin yanda zata kaya.

LAST BORN wannan shafin naki ne baki ɗayansa alkairin Allah ya kai miki sister💞

CIKIN IKON ALLAH MUN TAHO GANGARA, DAMA TUN A FARKO NA FAƊA MUKU BOOK ONE FREE NE AMMA BOOK TWO PAID NE, GA MASU BUƘATAR KARATUN LITTAFIN MABANBANTAN ZUKATA BOOK TWO DA ZARAR MUN GAMA BOOK ONE ZAKU IYA NEMAWA A  WANNAN LAYIN.

0912636748

NAGODE MASOYA, ALLAH YA HAƊA MU DA ALKAIRI AMIN

NI CE TAKU 
   MARYAM STAR ƳAR BAIWA (RAYAM STAR⭐)