MABANBANTAN ZUKATA

....

by @maryamstar248


Chapter 11.

Zama Mamaah ta yi kusa da Najwa sannan ta dafa kafaɗarta tare da faɗin.
   "Daga yau kuma yanzu anan ina umartarki da ki cire Mahwish da tunaninsa akan ki kwata-kwata, ban yafe maki ba idan har kika sake bari tunaninsa yayi galaba akan ki, babu ke babu shi, sannan ki sake sabon shiri domin kuwa nayi maki wani sabon kamu, ina so ki nutsu da kyau dan mu fara shiri."
  Har zuciyarta tana tsananin danasanin irin baƙar rayuwar da suka zaɓawa kamsu ita da mahaifiyarta, amma bata da yanda zata yi, dolene ta ƙarasa abin da ta ɗauko, domin kuwa ita ta wayar wa Mamaah ido ta hanyar damfarar samari su samu manyan kuɗaɗe masu nauyi, sai kuma gashi mahaifiyar taata ta zarceta a yanzu, a yanzu da ita ta tsani harkar tsana me yawa, saboda manyan dalilai guda biyu.

Ta shi ta yi daga wajen ta shige wani ɗaki tana ɗauke kwallar idonta, kai tsaye toilet ta shige bata jima ba ta fito jikinta na ɗigar ruwa da alama wanka ta yi, a ɗan gaggauce ta shirya cikin riga da wando waɗanda suka kame jikinta kam, sai wani yalolon vail data yane kanta da shi, babu laifi kyakkyawa ce, sai dai ba iya kyawunta ne yake haskata ba, harya irin wayewar da ta yi ya sake fitar da kyawun nata.
   "Mamaah ina so zan ce hospital dan a duba ni, har yanzu ƙirjina yana yi min nauyi sosai, har nakan kasa yin numfashi da kyau, idan na dawo zamu ƙarasa maganar."
Tana gama faɗin hakan ta juya a gaggauce ta fice ba tare data jira cewar Mamaah ba, dan kuwa a ƙage ta ke ta bar gidan ko ta samu sauƙin abin da ta ke ji.  (To ke Najwa ta ina zaki samu sauƙi alhalin kin cuci ɗan mutane, ai haƙƙi bazai barki ba kema.)




LEGOS NIGERIA.

A cikin ƙasa da wata ɗaya, ƙaƙƙarfar alaƙa me ƙarfi da gifta a tsakanin mitane biyu masu MABANBANTAN ZUCIYOYI.
  Mahwish ya kamu da soyayyar Najma me tsananin gaske, sai dai ya kasa bayyana ma ta, kamar yanda itama sannu a hankali tsananin ƙaunarshi ta dabaibaye zuciyarta, duda tana gayawa kanta shiɗin ba ajinta bane, musamman ranar da suka ji labarai ita da Inna aka dinga lissafo manyan kamfanoni guda biyu da Alhaji Muzaffar ya kyautar, kuma ba wani nashi yayiwa kyautar ba wani babban ɗan siyasa ne wanda ke tsimakon talaka bakin gaskiyarshi, lokacin da Inna ke bata labarin ai shine ya bayar da maƙuden kuɗaɗe lokacin da ta kwanta jinya sosai kanta ya ɗaure, da kuma Ale Idi ya shigo aka dasa firar da shi sai yake bawa Inna labari ai Mahwish ɗan Alhaji Muzaffar ne, daganan bata sake sauraren firarsu ba, ta nutsa a kogin tunanin ta yanda aka yi ta ke waya da babban mutum ɗan manyan masu arziƙin Nigeria wato Mahwish, kanta bai idasa kullewa ba sai da ta kwantar da haƙarƙarinta a kan gado tana jiran kiran wayarshi, magana ta farko da tayi bayan sallama ita ce.
   "Da gaske kai ɗa ne ga shahararen mai kuɗinan wanda sunanshi ke yawo a mujallu wato Alhaji Muzaffar?."
  Amsar da Mahwish ya bata kai tsaye ita ce ta tsiyaye man kanta tas.
   "Ih Najma, ni ɗanshi ne, ya aka yi ne."
Ya amsata da iya gaskiyarshi da ta karanta a maganarshi.
    "Tayaya haka?."
Bai gane abin da ta ke faɗi ba dan haka sai ya idasa daskarar da kwanyarta ta hanyar faɗin.
   "Ai baki saniba kullum gabanshi shi da Mommcy muke wayafa, yanzu haka wayar na hannun Papie bara ku gaisa."
  Bata jira ya isada faɗi ba tai wani irin tsalle ta diro daga kan kagon ƙarfe inna tana ƙoƙarin datse kiran, sai de kuma kafin ta yanke ɗin ta tsinkayi cikakkiyar muryarsa me cike da zallar izza na yi ma ta sallama, 'Yah Allahi yah Rahaman.' shine kalmar da ta faɗi a zuciyarta, a fili kuma ta amsa sallamar tare da soma gaisar da shi a mutunce, bayan gaisuwar kuma sai ya ta sake tsinkayo lallausar muryarsa na faɗin.
   "Ga Mommcy itama ku gaisa."
   Itama da girmamawa ta gaisar da ita, tsananin mamaki na kassara tunaninta.
  Daga wannan ranar ta zaɓi janye jikinta daga Mahwish, saboda nesa ba kusa ba shi ɗin ba ajinta ba ne, babu wani abu da zata tsinta idan taci gaba da alaƙa da shi, saima cutar da kanta da zata yi.
   Daga ranar da ta fara ƙauracewa kiran wayar Mahwish ta gagara samun sukuni da walwala, wunin ranar a ƙuntace ta yi shi, hakama da tazo kwanciya juye-juye tai ta yi sautin muryarshi da yanda ya ke magana na yi mata gizo, da kyar ta samu barci ya ɗauketa, daga ranar bata sake yarda ta kunna wayarta ba, sai ma sake ma ta wajen ajiya da tayi, ta kuma tattaro litattafan karatun addini ta samu Ale Idi da maganar tana son komawa makarantar islamiyya, ya so tambayarta batun komawa aiki amma sai ya share, da kanshi ya kaita wa ta sabuwa da aka buɗe, tun a wajen gwaji da aka yi mata malamin ya ce ai ita ta zarce a koyar da ita, sai de su ɗauketa ta koya kasancewar suna fuskantar ƙarancin malamai, aji uku aka kaita a  matsayin malama, dan sosai malaman suka yabawa ƙoƙari da gazaƙarta, a cikin farin ciki ta koyar da su karatun Ƙur'ani, tana tunano faɗar Manzon Allah a wani hadisi inda ya ke cewa.  "MAFI ALKAIRIN CIKINKU SHINE WANDA YASAN ALƘUR'ANI KUMA YA KOYAR DA SHI".
 Ko gida bayan ta dawo ana firar dare bata saka musu baki ba sai bitar karatukanta da ta ɗauke mata hankali taci gaba da yi, duda irin busy da take saka kanta, sam tunaninshi bai bar kwanyarta ta huta kona second ba, ko bayan da ta gama komi ta nufi wajen barcinta, hakanan ta kwanta tana ta juyi kewarshi na addabar zuciyarta, tana jin Inna na mitar yanda ta ke juyi har tana faɗin idan bata da lafiya ta tashi ta nemi magani amma tai biris da ita, da kyar da haka barci ya ɗauketa bayan ta raba darw tana juyi, a cikin barcin ma sam bata huta ba, dan mafarki tayi akan shi.

Da kyar ta sabawa kanta rayuwa ita kaɗai kamar yanda ta ke yi a baya, tana zuwa  makaranta ta koyar idan ta dawo ta tattara yaran gidansu suna ta koyar da su, duda ba ƙaramin ciwon kai suke bata ba amma ahaka take jurewa, dan bata so su taso babu ilimin addini a tare da su, to dama gashi ba wargi take ɗauka ba hakan ya saka suke jin shakarta, idan tayi ƙari kowa ƙoƙari ya ke ya iya, idan ko mutum bai iyaba sai ta dake shi ko a gaban babarshi ne.

Haka rayuwa taita haurawa har aka kwashe satika uku kwarara ba tare da wa ta magana ta sake shiga tsakaninta da Mawish ba.



A ɓangaren Mahwish kuwa kwana biyu sam baya jin daidai ga matsalar rashin samun Najma a waya da yake, haka zai tasa iyayenshi a gaba yana musu mitar yana son zuwa dubata amma sai Alhaji Muzaffar ya dinga kawar da tunaninshi akanta, ga ciwo da ke ta cinsa a tsaitsaye, a kwana na uku ne ciwo yaci ƙarfinsa, ko tashi baya iya ci numfashima a hankaki yake yinsa, babu shiri aka kaishi asibiti, kafin su isa tuni ya shiga mawuyacin hali, likitoci sun jima akanshi kafin suyi nasarar daidaita numfashinsa, bai farka ba sai da ya kwashe kwanaki biyu cur, kuma koda ya farka ɗin baya iya cewa komi, zai buɗe idonshi na ƴan mintoci sannan ya sakw kulle su, sai da ya kwashe sati guda babu wani ci gaba, ganin hakan ya saka Alhaji Muzaffar shirya musu tafiya, zuwa ƙasar turawa, kusan ƙasashe uku su na zuwa ganin manyan likitocin zuciya, amma sam babu wani ci gaba sai magana ɗaya da ake maimaita musu, maganar da ke sake hargitsa tunanin Alhaji Muzaffar, du inda suka je ganin likita za'ace da su.
  "Yaronku na da matsalar zuciya, ba lallaine ya rayu kamar kowa ba saboda raunin da yake da shi, zai rayu ne kawai idan ya samu wanda zai taya shi ɗaukar abin da zuciyarsa bata iya ɗauka ita kaɗai "
 Idan aka yi wannan maganar babu abin da ke zuwa kan Mommcy da Papie irin hoton fuskar Najma, musamman a ranar da aka kwantar da ita gadon asibiti da tarin raunika a jikinta, bama wannan ba, wani abu na musamman suke hangowa a tattare da ita, wanda a ganin su na farko da ita suka lura da hakan, tsanani  jarumtaka da taurin zuciya suka gani a kwayar idanuwanta a lokacin, sannan yanayin da Mahwish ke waya da ita, da irin dakiyar da ke ciki tata siririyar murya ya sake haska wani abu game da ita a kawunansu, sai de akwai abu ɗaya daya gina babbar katanga a tsakaninsu da ita, ba komi bane wannan abun face kasancewarta talaka, ita ɗin ƴar talakawa.

 Ko bayan da Mahwish ya farfaɗo ya samu kanshi, tambayarshi ta farko ita ce ina Najma, yarinyar da ko a yanayin jinyar daya tsinci kanshi yana jin yanda raunananniyar zuciyarsa ke dokawa da tsananin ƙaunarta,  ƙaunar da yake jin zata iya zama ajalinsa muddin ya rasa ta, ya rasa hope a karonshi na farko daya faɗa soyayya a wannan karon yana fatan mallakar abin da zuciyarshi ke so, ko zai samu rangwame daga azaba biyu, azabar raɗaɗɗin ciwo da kuma azabar azababbiyar ƙauna, wacce ta ƙulle da ruhinsa a zare ɗaya.

Wani tunani ne ya ɗarsu a zuciyar Alhaji Muzaffar, a tunaninsa hakan zai zama kaifin datse du wata alaƙa da zata sake haɗa ɗanshi Mahwish da talakawan mutane, sai de ba tare da saninshi ba tabka ƙaton kuskure, kuskuren da zai iya shafar sauran ƙanfin daya ragewa tilon ɗansa, da ace yasan abubuwan da zasu faru marasa daɗi idan ya aikata abin da zai aikata ɗin, da tun a matakin farko da zuciyarsa ta bashi shawarar yayi fatali da ita, bayan hakan ya kulle zuciyar yasa me ya hanata sake tunani na tsawon lokaci dan kar ta sake maimaita ma shi abin da ta maimaita, sai de kash alƙalamin kaddara ya riga da yayi rubutu akan faruwar lamarin.....✍🏻
KU KASANCE DA AKƘALAMIN RYAM STAR DOMIN SAMUN CIGABAN WANNAN DADDAƊAN LABARIN.


SAURA ƘIRIS MU IDASA BOOK ONE MA'ANA FREE, ASALIN ZALLAR CAKWAKIYA NA NAN GABA.

KU KASANCE TARE DA NI.

***
Only whatsapp