MABANBANTAN ZUKATA

.....

by @maryamstar248

***

𝙈𝘼𝘽𝘼𝙉𝘽𝘼𝙉𝙏𝘼𝙉 𝙕𝙐𝙆𝘼𝙏𝘼❤️‍🩹❤️‍🔥

 𝙎𝙏𝙊𝙍𝙔 & 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙏𝙀𝙉
𝙈.𝙎𝙏𝘼𝙍⭐⭐⭐

💪𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉 💪

𝗧𝗛𝗘 𝗦𝗛𝗜𝗗𝗢𝗥𝗜𝗔 𝗪𝗥𝗜𝗧𝗘𝗥'𝘀 𝗧𝗘𝗔𝗠💪✍🏻
Chapter 12
Daga ƙasar da suke ya bayar da umarni ta waya akan cewa yana so a tayar da duka mutanen da ke unguwar AJEGUNLE gaba ɗayansu cikin kwana ɗaya jal, maƙuden kuɗaɗe ya ɓarnatar akan a bawa kowane gida, sannan au tashi cikin hanzari.
  
A safiyar ranar Asabar ne saƙon tayar da unguwar ya riski iyalan Ale Idi, nan kowa ya shiga safa da marwa bayan gama jajanta lamarin,  mama Saudah ce ya ce.
  "A ganina tunda ance kowa ya tashi cikin mutunci ya kamata ace mu soma haɗe kayanmu mu jirayi tsammani, ance su na biyan kuɗaɗe masu kauri, idan kuma aka saka musu taurin kai sai su bazar da gidan gara kawai mu haɗe kan kayanmu mu zama ready idan Allah yasa babu mu cikin waɗanda za'atayar falillahil hamdu."
  Cike da gamsuwa da zancen Mama Sauda aka shiga harhaɗe kan ilahirin shirgin gidan, sun jima su na aiki tuƙuru, basu suka gama ba sai wajajen azahar, lokacin jikunnansu du a sanyaye, su na zaman hutawa ne Ale Idi ya shigo gidan, bai ce da kowa komi ba ya dire jakar kuɗaɗe a gabanshi sai ya tallafe goshinshi yai shiru, Inna Lantana ce tai ƙarfin faɗin.

   "Lafiya dai ko?."
 A nan ma bai ce komi ba sai jakar da mayar gefen Mama Saudah sannan ya ce.
  "Sauda idan baki komi dan Allah ki ƙirga kuɗaɗenan, kuɗin gidannan ne aka bani yanzu dana dawo zan shiga gida, sun ce kar mu wuce gobe bamu tashi ba, wai rusau zasu yi."

"Oh ni Laraba yau muna ganin jalala, ita kuma wannan gwamnatin haka zata yi da mu?."
  Ta yi maganar tana jinjina kai.
   "A,a Laraba wannan aikin bana gwamnati bane, a majiya me ƙarfi na ji wai wannan shahararen me kuɗin ne yake son unguwar zai gina babban kamfani, aikin ya taso cikin gaugawa shine aka bama kowa kwana ɗaya ya tashi, sauƙi-sauƙinma dai suna biya me kwari naji ance."

Wani abu ne me kama da mashi ya soki zuciyar Najma da ke ɗakin Inna tana harhaɗa sauran kayanta, cak ta tsaya da komi jin yanda kanta ya shiga sarawa, zuciyarta ta soma tafarfasa tana hayaƙi, a  hasale ta soma taka ƙafafuwanta da niyyar ta fito waje, ta yi nasarar fitowa amma bata idasa isa wajensu ba jiri ya kwashe ta, tai taga-taga ta faɗi ta baya.
A kuje suka yo kanta amma sai da Inna Laraba ta ɗauki jakar kuɗin ta  jefa ƙofar Mama Saudah.
    Ruwa Inna kw shafa ma ta a fuska amma shiru babu wa ta alamar da ke nuna tana numfashi, du wani abu da zasuyi ma ta, sun yi amma shiru babu wani ci gaba, shawarar zuwa asibiti Inna ta bada ganin an kwashe awa ɗaya babu wani ci gaba, haka suka rankaya aka tafi zuwa asibiti kowa da irin fargabar da ya ke, a canma likitoci suka duƙufa akan Najwa sun yi ƙoƙarin daidaita numfashin ta hanyar saka ma ta abin shaƙa, amma bata farko ba, har dare babu wani bayani, hakan ya saka Ale Idi komawa gida yayi shawara da Inna akan ko dai su haƙura da zaman Legos su koma gida hakanan sai a nema ma ta na gargajiya, dan abin ya soma bashi tsrono, Inna ma  tayi na'am da hakan badan komi ba sai dan dama ita ta jima da gajiya da zaman Legos tana son zama cikin ƴan uwanta da sauran abokan arziƙi.
   Lokacin da aka zauna cin abincin dare ne ya sanar da sauran matanshi batun barinsu Legos gobe, dukansu jikunnan su sunyi sanyi dan basu son komawa ƙauye, sun saba da zaman birni, hakanan ba don san ransu ba suka amsa shi, ganin sun amsa ya saka inna ce.
   "Barin Legos ba shi ke nuna zako koma ƙauye da zamaba, Idi zai yi magana da abokinsa da ke dillacin gidaje a  Katsina sai ya sama sa shi gida acan sai ku koma, amma nidai zan tafi ƙauye cikin dangina in zauna."
  Sosai suka yi farin ciki da hakan, suka zauna jiran tsammani.
   
Bayan Ale Idi ya yiwa Mama Saudah bayani, sai ya nemi sallama a wajen likita, dama ƙaramar asibiti ce babu wani ƙarin bayani aka basu sallama suka rankaya gida da Najma wacce take kwance kamar gawa.


MATAKI NA FARKO.
 Matakin farko daya fara gida bagon ƙadarrar da ya gifta atsakanin MABANBANTAN ZUKATA, waɗanda suka cure a waje ɗaya shine barin Ale Idi da iyalansa a washe gari suka kama hanyar barin Legos da sanyin safiya.
   Yayinda jirgin Alhaji Muzaffar da iyalansa yaiwa garin Legos tsinke a safiyar ranar, ranshi fes da tunanin ya raba alaƙar ɗansa da talakawa, rabuwa ta har abada, tun da gaba ɗaya unguwar ya siye ya saka a mayar da ita flate, mataki na biyu kuma dayabi wajen sake ruguza ƙaƙƙarfar alaƙar da ubangiji ya haɗa shine saka gidan layi lalata wata lamba wacce Mahwish ke waya da iya, ba tashi lambar aka lalata ba, wancan layi dai na ƴar talakawan ya saka aka lalata shi ta yanda baza'a sake kiran waya ya shiga ba.

Yana cikin farin cikin dawowa da Mahwish gida cikin ƙoshin lafiya, shi kuma Mawish yana cike da ɗokin san yi tozali da wacce ta zama bugun zuciyarshi gaba ɗaya, yana ji ajikinsa yana da gwarin guiwar tunkarar gidansu, gidansu da hotonshi ke zane a kwanyarshi, bana iga gidanba, du wa ta hanya da ake bi wajen zuwa unguwar ta su tana zane ne a kwanyarshi, yana jin yanzu ne lokaci mafi dacewa da zai tunkareta ya bayyana ma ta kalmar da zata wanzar da ɗorarriyar alaƙa a tsakaninta da shi, sannan zai sanar da ita rauninsa, yana buƙatar ta bashi ƙwarin gwuiwa a yayinda ya gaza, zai buɗe ma ta sirrin zuciyarshi da kuma sirrin rayuwarshi gaba ɗaya, tun da suka sauka a jirgi aka zo ɗaukarsu ya ke ƙawata fuskarshi da murmushi me kyau, ya kuma zaɓi yin tafiya da ƙafafuwanshi tun daga sauka akan matattakalar bene har zuwa wajen mota, a maimakon shiga mota ɗaya da iyayensa sai ya zaɓi wa ta motar daban ya shiga yana ɗaga musu hannu da murmushi akan fuskarshi.
  A madadin murmushin fuskar Mahwish ya burge Alhaji Muzaffar sai tsintar kanshi ya yi cikin wani yanayi me kama da fargaba, amma sai ya dake shima ya ɗaga ma shi nashi hannu ya shiga mota shi da Mommcy suka jera akan layi su na barin airpot ɗin.
Ko da suka isa gida cike da farin cikin ganinsu mutanen da ke rayuwa a gidan suka tarbesu, abin mamaki shine yansa Muhasin ke nan-nan da Mahwish, mutumin da kowa na gidan ya kwana da sanin rashin jituwar da ketsakaninsu, amma sai gashi ya taryesu da annuri akan fuskarshi yanayin da ya sosa ran Mahwish ganin yau ɗan uwansa ya yarbeshi da sakin fuska.

Bayan ya tashi daga barcin huce gajiya, duda jikinshi babu kwari sosai hasalima ƙarfin hali kawai ya ke yi, sai ya hau shiryawa cikin shiga ta musamman, babbar shaddace yar  ubansu blue kala, wacce ta ji lafiyayyen tsadadden ɗinki irina hausawa, ba ƙaramin kyau shaddar ta yi mashi ba, ya ɗauki tsadaddiyar hula ya kafa asaman lallausan ɗan kaɗan ɗin gashin kansa wanda bai da cika sai tsayi, agogo wacce sam bai damu da sakawa ba ya ɗauka ya saka a tsintsiyar hannunsa, ba ƙaramin kyau me daskarar da zuciya ya yi ba, ko da ya kalli wawakeken mirron da ke kafe a ɗakin sai da ya saki ƴar ƙaramar dariya, a zuciyarshi ya shiga hasaso yanda Najma zata kalle shi da waɗannan jaruman idanuwanta masu tafiya da nutsiwarshi.

Sosai Iyayenshi suka shagala da kallonshi lokacin da ya fito, zaka rantse ba shi bane ya kwanta tsawon sakita jinya asibiti kamar bazai rayuba, bayan ya zauna a tsakiyarsu a taɓare ya kallesu su duka biyun sannan ya ce.
   "Ku yi min addu'a zan je in buɗewa wa ta zuciyata."
  Idan na ce faɗuwa na rage ƙarfin abin da gaban Alhaji Muzaffar ba ya yi, kwankwatsewa gaban shi ya yi da tsananin ƙarfi har bai san lokacin da ya ce da sauri.
  "Wcece wannan, miyasa kaza yi haka, ka manta bakada lafiya ne?."
 
Babu tunani komi Mahwish ya ce.
  "Najma ce tauraruwar zuciyata, zan je in sameta in sanar da ita ina tsanani ƙaunarta dama jinyar ai ta kewarta ce."
   Wata irin zuface ta shiga tsatstsafowa Alhaji Muzaffar, kafin yasan abin cewa Mahwish ya bisu da sumbata, sannan a gaggauce ya fice.

Zuciyarshi ta soma sauya bugu ne daga lokacin da bahaushe driver ɗinsa ke sanar da shi ai antashi unguwar da ya sanar zasu je, gardama ko musi sam ba halinsa bane, amma haka ya sake jadadda akaishi can cikin kaushin murya, tiryan-tiryan ya ke ƙarewa hanyar kallo, yana nazarin wasu abubuwa, zuciyarshi cike fal da farin ciki.
A daidai lokacin da suka shiga kwar ne idanuwansa suka soma hasko ma shi filayen gidajen da aka barbaje, a kuma daidai lokacinne motar rusau ta tinkarin gidansu Najma, tare da bi takanshi nan take ya faɗi rugu-rugu a ƙasa, wa ta iriyar zaburarriyar ƙara Mahwish ya saki daga cikin motar, hakan yayi daidai da taka birki da sauran drivers waɗanda ke tuƙa security suka yi.
  Ta ɓalle mota da fitarshi akan ƙafafuwan da suke lankwashewa duka ya faru ne cikin abin da bai gaza second biyarba, kafin ƙafafuwansa su idasa kaiwa wajen da ya ke iya hangen ƙurar ƙasar gidan Ale Idi tuni motar ta gama tushe gidan tabi takan na kusa da shi.
Wa ta razananniyar ƙarar ya sake saki, tare da durƙushewa akan sagaggun gwuiwoyinsa ya dafe kanshi dake barazanar ɓallewa saboda ciwon daya dirar ma shi nan take,   a cikin kunnuwansa ya ke jin ƙarar bashewar glashin zuciyarshi, kamar yanda yake ganin yanda aka ruguje gidansu Najma, nan take a wajen ya yankewa kanshi hukuncin haƙura da rayuwa na har abada, domin kuwa idan har ya sake yai gangancin cigaba da rayuwa ba shakka sai ya gwammaci mutuwa, Najma ta zama rayuwarshi gaba ɗaya rasa ta tamkar rasa tashi rayuwarne, nan take bayan ya gama yankewa kanshi hukunci ya ɓingire a wajen.
   Hakan yayi daidai da isowar Alhaji Muzaffar harma da matarshi Mommcy wajen hankulansu a mugun tashe, domin kasa jurewa ya yi bayan fitowar Mahwish ya labarta ma ta abin da ya faru, ko kafin ya gama bata labari tuni tayi waje babu ko mayafi tana kiran sunan ɗanta, sai dai kuma lokacin har motocinsa sun gama ficewa, a yaune rana ta farko da bata tsaya sauraren jawabi daga bakinsa ba kai tsaye ta wuce shi da sauri ta bada umarnin a ɗauko motoci cikin gaugawa, koda aha jere motocin idanuwanta a rufe ta shiga ta zauna tana bada umarnin a tafi, sam bata san da shigowar Alhaji Muzaffar motar ba sai da aka tayar sannan ta tsinkayi muryarsa, karo na garko da taji sautin muryarsa kamar ƙarar injin ɗin markaɗe a kunnuwanta, bata jira komi ba ta toshe kunnuwanta gami da sakin kuka me ƙara, har suka isa wajen kuka ta ke, akan idanuwanta ɗan ta ya yanke hukuncin haƙura da duniya baki ɗaya, a kan idanuwanta ya kwanta a saman ƙasar unguwar bayin Allah talakawa waɗanda aka tayar da su saboda son zuciyar mijinta da bayada tawassali a rayuwa, koda ta tarbi Mahwish a cikin hannuwanta sadaƙarwa gami da juriyar  haƙurin rasashi ya sakawa zuciyarta, yayinda ta tallabi gawarsa da kanta ta kinkime shi ba tare da jin nauyin komi ba kamar yanda ta ke saɓa shi a kafaɗa lokacin yarintarsa, da kanta ta buɗe mota ta saka gawarsa a ciki, idanuwanta na bushewa ƙamas ta nemi ruwan hawaye ta rasa, sai wani zugi da raɗaɗin azaba da ziciyarta ke yi.....✍🏻



Uhummm haka rayuwa ta ke dama, a lokacin da Allah ya haɗa ƙaddarar wani da wani, addu'ar fatan alkairi ce ta dace kawai a yi, shi dama son zuciya ai ɓacinta ne.

Shi wannan talakan da me kuɗi ke rainawa, shi ke gina rayuwarsa, da ace babu talakawa da rayuwa ba zata yi sauƙi sam ga masi kuɗi ba, da ace babu talakawa da me kiɗu bazai mori kuɗinsa ta daɗi ba, saboda babu wanza zai yi mashi hidima ya biya shi, babu wanda zai saka aiki ko wani abu.

Alhaji Muzaffar na son kawo ƙarshen rayuwar ɗansa da kansa saboda son zuciya, shin ba'a kuskure ne a rayuwa❓bai dace ace yayiwa Talakawa kuɗin goro ba saboda laifin da wasu suka aikata a gare shi, laifin wani baya taɓa shafar wani ko a wajen Allah.

ALHAMDULILLAH ANAN NA KAWO ƘARSHE LITTAFIN MABANBANTAN ZUKATA BOOK ONE, KUMA A YAU NE NA GAMA FREE PAGES.

Ga me buƙatar ci gaba da karatu zai biya 500 only domin ci gaba da samun damar karanta wannan labari.

9136291920
MARYAM UMAR
OPAY

Shaidar biya ta wannan layin.

0912636748.

NAGODE SOSAI NI CE TAKU 
   MARYAM
      STAR ⭐⭐