MATAR MAZA

Chapter 8

by @reza12

MATAR MAZA 8
  (Life story)

Sai kuma gabanta ya faɗi ta kamo hannun Sadiya Kamar zata yi kuka ta ce "Waiyoo Allah na, wallahi kinsa na fara tsoro, yanzu meye abun yi?" "Kawai yadda yace haka zakiyi, kawai ki kirƙiro wani abun da zai raba ku da mijin naki shine kawai mafita". Azima tayi shiru tana tunani. Har bayan kwana uku da yin maganar nan bata samu matsaya ba, ta rasa ma ta yaya zata iya rabuwa da Kamal, har mafarkai take yi akan wannan matsalar. Bangaren Kamal kuwa tun da ya tafi bai kirata ba, kusan sati biyu kenan ba text message ba kira, har ga Allah abun na bata mamaki yadda bashi da wani lokaci sosai. Washegari ta tashi da shirin zuwa school, domin wannan shekarar ce zata kammala, tana shirin tana tuno lokacin da Alhajinta ya kaita makarantar a lokacin da bata da ikon zuwa. Tana fitowa harabar gidan taci karo da motar Kamal. Maimakon tayi murna sai ta haɗe rai, sam zuwan nasa bai wani burgeta ba, ba sanarwa kamar wanda yake zargin ta. Koda ya fito daga cikin motar sai taga ba shi ɗaya bane, tare yake da wasu samari guda biyu masu yanayi da shi kamar an tsaga kara. Haka ta ɗan saki rai tana musu maraba da zuwa, sannan ta fasa zuwa school ɗin suka koma ciki. Bayan ta kawo musu ruwa sun sha suka gaidata suna ɗan tsokanar ta da ta ƙwace musu ɗan uwa sai lokacin da taso ake ganinsa. A lokacin yake sanar da ita cewar ƙannensa ne, haka kawai suka ce suna son ganinta shine fa ya kawo su. Ta ji daɗin yadda suke ta girmama ta ga fara'a, sannan suna ta yabon kyawunta kaman dai yadda ta saba ji a bakin mutane. A daren ranar take masa korafin rashin kiranta da baya yi idan ya tafi, sannan mai yasa da zai zo bai faɗa mata ba. Ya bata haƙuri yace yanayin aiki ne, amma tayi hakuri zai gyara. Kwanansu biyu a gidan, izuwa lokacin ta saba dasu, kullum idan suna hira babu abun da suke sai yabon kyawunta da dogon hancinta. Bayan sun tafi ne kuma ta sake dawowa cikin lamarin alhajinta. Ganin lokacin da ya bata ya kusa cika ne yasa ta kira shi. Bayan ya daga ta ce "Dan Allah wata alfarma nake nema a gurinka idan zan samu?" Yace "Babu wata alfarma da ta rage, daga gobe idan har baki fito daga gidan nan ba wallahi sai kin fito ta dole na faɗa miki, zaki koma yin kwana biyu a nan gida na, sannan kiyi kwana biyu a gidan sa, na faɗa miki". Ta ce "A'a ba ma za'ayi haka b, dama ina so ne kara min lokaci yadda zan kirkiro matsalar da zata sa ya sake ni da kansa ba tare da mutane sun san cewa laifina bane pls?" Ta faɗa Kamar zata yi kuka. Ya ce "Kamar wani adadi kike so?" "Wata ɗaya dan Allah?" Ta faɗa da sigar roƙo duk tayi sanyi. "Ba damuwa na baki wata ɗaya, amma idan har ta wuce baki fito ba". Ya kashe wayar. Ta sauke ajiyar zuciya tana kama ƙugu hadi da sakin murmushi a lokaci ɗaya. A fili tace "Zakaci gidanku ne tsohon banza kawai, da Azima kake wasan, ai kai shiga tarko na nima.

Wannan karan ma sati Uku kenan da tafiyar Kamal amma babu waya, sosai abun ya ɓata mata rai, ta kira bai ɗaga ba, ta whasop ma baya ko budewa. Duk da cewar tana neman hanyar da zasu rabu, amma bata kawo abun zai zo mata ta haka ba. Komai akwai amma bashi da lokacin ta, kuma ita sam ba zata iya ba, koda ace wanda take so ne bata jin zata juri haka bare wanda bata so. Abun da bata sani ba shine, tuni Salma ta dinga haɗa hotunanta dana samari tana turawa Kamal da wata number, hakan yasa shima ransa ya ɓaci, kullum sai an turo masa sabon hoto, sannan ta bashi labarin alhajin da ya ɗauki nauyin karatun ta, wai ita karuwarsa ce, har yanzu bai bar bibiyan ta ba, wai har gida yake samunta. Wannan dalilin yasa ya shirya zuwa Nigeria domin tabbatar da komai, duk da kuwa baya bukatar wani abu ga komai nan. Duk da a cikin fushi take amma tana ganin yanayinsa sai da ta tsorata. Amma ta nuna kamar bata ganshi ba ta ce "Gaskiya na gaji da irin wannan zaman na rashin lokaci, yau ko dai akuya ka ajiye dole ka dinga bibiya bare mutum kuma mata, to wallahi na gaji, dole a sake". Ta faɗa cikin fushi. Ya ce "Kin gaji ko? Ai dama dole ki gaji saboda ba zaki iya zaman aure ba, kin saba yawon banza a gari, duk da kinyi auran ma baki tuba ba, Allah ya wadaran ki wallahi". 

Mamaki da kuma tsoro ne ya kamata, ba kuma saboda komai ba sai yadda har ya iya tsayawa a gabata yana faɗa mata irin wannan kalaman, ina ita Azima ai wallahi batayi wannan lalacewar da har Namiji zai zageta, kuma ya zarge ta amma ta tsaya tana kwallonsa ba, wallahi karya ne, ba'ayi ba kuma ba ma za'ayi ba. Sosai sukayi faɗa a daren, Karshe ma da abun yayi zafi saboda har yunkurin dukanta yayi, saboda ba karamin zagi itama tai masa ba. Sai dai kuma wani abun mamaki da ya faru wanda ita kanta bata zaton zai faru ba, domin ya girgiza ta tabbas, domin tana rufe baki ya danƙara mata saki hadi da baƙaƙen maganganu, ya nuna mata cewar yanzu haka mata huɗu gareshi, abun da yasa ma bashi da lokacin ta kenan, shi bai ɗauki mace a komai ba, yana iya aurar Mace kawai domin ya ɗandani romonta ne". Sosai tsoro ya kamata da ta tuno da Hajiya, yanzu sai tace mata auranta ya sake mutuwa, ta kalleshi ta sake kallonsa, har ga Allah ba wai sakin nata ne ya ɓata mata rai ba, a'a yadda zata kwashe da Hajiya ne. Shiru tayi tana jin tashin hankali na ziyartarta. Sai kuma ta tuno da alhajinta ta, a fili tace "Wallahi kai ma ba zan aureka ba dan uwarka.

Washegari da safe ta fito Palo ta sameshi yayi shirin komawa abunsa. Kamar tayi masa magana sai dai tayi shiru har ya bar gidan gaba ɗaya. Zama tayi apalo tana tunanin meye abun yi. Take zuciyoyi suke ta kawo mata shawarwari barkatai. Sai da ta gama sauraronsu kafin tayi na'am da shawara ɗaya akan kar ta bari Hajiya da sauran ƴan uwanta susan auranta ya mutu, tunda dama mijin ba zama yake ba, kuma ba dan gari bane, domin ko ita kanta bata san kowa nasa ba idan ban da yara biyun nan da suka zo tare kwanakin baya. Sosai tayi na'am da wannan shawarar idan yaso shi alhajin nata tana gama ida ta aure shi ko na sati ɗaya ne tunda yana da kuɗi ta ci kuɗin ɗan iska. Sati ɗaya da yin sakin sai ga sako ta whasop Kamal ya turo mata akan yana so zai dawo da ita. Tayi wani murmushin ta kira shi video call. Bayan ya daga ta fara sanar da shi kar ma ya kuskura ya fara wannan gangancin domin ta gama zama da shi domin bata maimaita aji. Duk yadda yaso da ita haka taki yarda, a lokacin ne ma ta samu damar gaya masa magana kamar yadda ya faɗa mata. Kuma har wata guda ya cika babu wanda yasan da anyi sakin. Izuwa yanzu ta mai da hankali akan karatunta domin sun fara jarabwa. A wannan tsakanin ne kuma alhajinta lokacin da ya bata ya ciki. Ai kuwa ko kwana ɗaya bai ƙara ba sai gashi a gidanta, wannan karon har cikin palon gidan ya shiga zauna yana sauraronta. Sosai ta shirya ci masa mutunci domin ta tsaya tayi tunanin auransa ba mafita bace, gara kawai su rabu da uwaka ubanka, tasan dai ba abun da ya isa ya iya mata. Ya ce "Ina jinki, kun rabu da shi ɗin ne ko kuma auran za'a ƙara?" Ya faɗa yana ajiye kufin ruwan da ya sha. Azima ta dake ta ce "Ina son mijina shima yana sona, ba zan iya rabuwa da shi haka kawai ba dalili ba". Ta faɗa kanta tsaye tana kuma kwallon cikin idonsa. Ya danyi murmushi ya ce "Mai kike ce?" Ya faɗa har lokacin yana murmushin nan nasa na mugunta a gurin ta. Ita ma ta maimaita abun da tace. Sai ya fara tafa hannu har ya miƙe tsaye. Ya nuna ta da sandar kusa da shi ya ce "Ina alfahari dake ƴata, tabbas har yanzu ke ɗin Azimar da na sani ce. Ya ƙaraso har gabanta ya ce "A lokacin da na fara ganinki, nayi kwaɗayin auranki da gaske, sai dai kuma a lokacin kika tabbatar min da cewar baki sona, duk abun da nai miki ban miki shi da nufin zan aure ke ba, na miki ne da nufin na taimake ki, sai dai nayi mamakin da kikayi aure ban sani ba, ko ba Komai na zamar miki uban da idan zakiyi abu zan sani, hakan ma duk bai dameni ba, sai da nazo na ga wanda kika aura. Kin san waye shi a gurina?" Azima ta miƙe tsaye tana zare ido kamar taga abun tsoro, idanun nan ƙur a kansa kamar warkewar makanta. Ya ce "Yaro nane, na gwada ki ne domin na tabbatar kina sonsa ne ko kuma saboda kuɗin sa kika aure shi, kuma gashi kin tabbatar min da cewa kina sonsa, dan haka daga yau ba zaki sake ganina a rayuwarki ba, kuma ga wannan ki ƙara a kasuwancinki, ki riƙe mijinki yana da kirki". Ya faɗa ya ajiye mata daurin dubu guda goma ya ƙara gaba. 

Har taji tashin motocin su bata sani ba, sai kusan minti talatin kafin ta kalli kuɗin tana kallon Ƙofar da suka fita. A fili ta furta. "Na shiga uku ni Azima, mafarki ko dai gaske. Number Sadiya ta kira tace tazo gida yanzu ta sameta. Ai kuwa bayan awa ɗaya har lokacin tana dai palo bata tashi ba. Tana zama ta fara bata labarin alhajinta da kuma alakarsu da Kamal. Sadiya ta ce "A haf, ni ai na faɗa, nace wannan mutumin wallahi ba don ya aureki yake miki wannan hidimar ba, kuma gashi, kai Allah ya saka masa da alkairi ya biya masa bukata, kuma sannan sai ki riƙe auran naki daya faɗa miki ko dan mutuncinsa". "Wani aure da yau wata ɗaya harda wani abun da ya mutu". Ta faɗa tana taɓe baki. "Sadiya ta ce "Mutuwa fa, kina nufin baki da aure yanzu haka?" "Tabbas kuwa, mun rabu". "To saboda me?" "Bana sonsa, Kuma bashi da lokaci na". Ta faɗa tana hararar ta. Sadiya ta ce "Gaskiya Anty Azima baki kyuta ba, kuma idan Hajiya ta san da wannan maganar kin san ciwonta, dan Allah ki gyara auran kafin ma labari ya kai mata". Azima ta ce "Kece kenan zaki faɗa mata ko?" Sadiya tayi shiru. Ta ce "Kalli nan, ta faɗa tana nuna mata kuɗin da ya kawo mata. Sadiya dai bata sake cewa komai ba. Sai can anjima ta ce "To yanzu yaushe zaki fadawa Hajiya?" "Babu rana ba zata taɓa sani ba". "To idan zakiyi wani auran fa?" "Ba zanyi wani aure ba sai na gama karatu, daga lokacin ne kuma zan duba na darje nayi auran tsakani da Allah auran zama auran da zan zauna har abada, idan kuma ban samu irin namijin ba, to dama kin san ba auren na ke so ba sai na haƙura. 

Bayan sun kammala izam sakamakon su yayi kyau, anan ta sake haɗuwa da wata ƙawa mai suna Namra. Wanda a lokacin ita Namra ɗin ta samu aiki mai kyau ita kuma Azima ta cigaba da kasuwanci. Har lokacin babu wanda yasan da batun mutuwar auran, daga ita sai Sadiya, gashi ta gama idda. Sosai kasuwanci ya sake zama akanta, yanzu a sati sai ta shiga Maroco sau biyu, yanzu har Masar da Chana Dubai duk tana shiga sari. Tsakaninta da Kamal sai mutunci, har yanzu kuma shi yake biyan kudin gidan da suke ciki daga kuɗin wuta zuwa na ruwa. Har lokacin yana son mayar da ita amma ta nuna bata so. A wannan yanayin ta shekara cir a gida ba tare da ansan bata da aure ba, abotarsu da Namra kullum shaƙuwa suke yi, duk da cewar iya yanzu bata zama daga nan sai nan. Aduk lokacin da zata yi tafiya kuwa wani irin kwalliya takeyi wanda kai idan ma baka isa da kanka ba ba zaka iya mata magana ba. A cikin wannan shekarar tayi samari sama da guda hamsin manyan mutane wanda suke sonta da aure amma taki yarda. Yanzu dai akwai wani babban mutum ɗan sarauta ne shima a filin jirgi suka haɗu, ɗan Bauchi mai suna Bilal, shine take ɗan saurara. Bayan shi akwai Alhaji Sule, wanda shine ma yanzu take da nufin aura domin yana da kuɗi kuma yana da sanyin hali ga haƙuri sai dai yana da Mata mai mutukar masifa. Bayan shi akwai Mansur wanda ɗan uwa ne a gurinta, shine yake son kawo mata matsala domin bata san a ina yasan bata da aure ba, dan ranar har gida yazo a gaban Hajiya yaso ya tona mata asiri hajiyar ce da kanta ta faɗa masa cewar tana da aure mijin ne ba mai zama ba. Shi dai Mansur bai yarda ba, domin babu macen da zata dinga wannan irin yawon da aure, kuma ya sha kamata tana hira da zawarawa, hakan yasa yake zargin bata da aure. Fadila kuwa tuni ta koma gidan babanta.

Sosai Mansur yake taƙura mata har ta faɗawa Namra shine take son ta bata shawarar yadda zatayi da shi. Hakan yasa har gida tazo suka tattauna. Suna cikin wayar Alhaji Sule ya kirata. Ta ɗaga tana saka wayar a amsako domin ta nunawa Namra yadda yake ji da ita. "Dan kutumar ubanki mai ya kawo number ki wayar mijina, to kiranki nayi da babbar murya, Azima karuwa mai yawan karuwanci ƙasa-ƙasa da sunan kasuwanci ko, to ni nan ina daidai da uwar ki ba ke ba, kuma mijina yafi karfin ki wallahi, dan haka ina mai faɗa miki kiyi baya da shi ko kuma rayuwarki ta lalace". Ta na faɗa ta kashe wayar. Namra ta ce "Tofa! Yar balaja'u a cikin gidan aure". Azima ta ce "Tashi muje". "Muje ina?" Ta tambaya a rikice. "Gidan mana naji wa take kira da karuwa, kan bala'i, har ni zata yiwa wannan zagin, na rantse da Allah sai na je har gidan na nuna mata ni ba sa'ar ta bane, wato dama ana faɗa min cewar ita bata da hankali ashe da gaske ne". Suna cikin haka aka sake kira. Ta ɗaga kafin ayi magana ta ce "Idan kin cika yar iska zan zo gidan ki yanzu ki jira Ni". Ta faɗa a haukace. Sai ta tsinkayayo muryarsa mai sanyi yana faɗin "Haba Azima Kema biye mata zakiyi kenan ko?". Ta ce "Baka ji irin zagin da tamin ba ko, harda ce min karuwa, to wallahi sai ta maimaita wannan kalmar". Daga haka ta kashe wayar. Ta shiga zaga dakin. Lokaci ɗaya ta ce "To wallahi sai na aure Alhaji Sule ko dan wannan matar, zan nuna mata asalin karuwancin da take faɗa". Da sauri Namra ta ce "Ina ke in haɗa miji da wannan mahaukaciyar keda kike da Bilal ɗan sarauta". Ta ce "Kin san Allah, wallahi sai na aure shi ko dan na nuna mata tayi kaɗan". Tana faɗa ta shige ciki tabar Namra da mamaki.

Tana zaune a palo ta fito da kin Mota. Ta ce "Wai me kike shirin yi ne, ta yaya zaki aure shi bayan Hajiya bata san baki da aure ba". Ta ce "Ni nasan abun yi, ke dai zuba ido kiyi kallo". A haka suka iso gidan su, ta sauko daga Mota taga Sadiya da Mansur saurayin ta suna hira. Duk yadda ta kai da ɓacin rai sai da ta saki fuska suka gaisa da shi domin tana ganin mutuncin man ɗin, ba zata taɓa mantawa da abun da yayi masu ba. Tana shiga taga Mansur nata a cikin palon Hajiya. Sai da gabanta ya faɗi, ta harare shi kawai ta samu guri ta zauna. Ganin yana gurin ta fasa faɗin a bin da tayi niyya. 

Washegari tana da tafiya amma haka ta fasa suka haɗu da shi. Bayan sun zauna a gurin da suke haduwa cikin wani bar. Anan suka shirya cewar zasuyi aure harda sa lokaci, kuma ya ce mata karta bari matar tasa tasani domin sau uku tana rushe masa aure. Itama tace bata so Hajiya ta sani, domin ita bazawara ce tana da ikon aurar da kanta. Haka suka tsayar da magana. Washegari kuwa sai ga kira da sabuwar number. Tana ɗagawa taji matar Alhaji Sule ce. Nan ta cigaba da mata gargadi akan idan ta sake ta aura mata miji wallahi sai ta mutu, duk yadda Azima take da kishi da kuma bata son auran mai mata, amma ji tayi wallahi sai ta auri wannan mutumin domin ta koyawa wannan shegiyar hankali. Hakan yasa ta ce "To bari na faɗa miki sati na sama juma'a iwar haka na zama matar Sule, ki rubuta ki ajiye kuma wallahi sai kin bar gidan a tsiyace wallahi". Matar ta ce "Aure ko, to ayi mugani dan uwarki, wallahi mijina yafi karfin karuwa irinki, kuma muddin ina raye wallahi baki isa ki aure mijina ba, har gaba da abada". Itama Azima taci wannan alwashin suka rabu da zage-zage. Sosai ta sake jin kwaɗayin auran koda na kwana ɗaya ne ta tarwatsa matar sai ta fito...📝

Kar ku manta wannan labari ne na gaske, shi yasa zaku ga salon a haka, dan haka kuci gaba da bin S-Reza, ayi mana like da shering, kuma ku dinga faɗin ra'ayin ku a comments section.