08
~~
Aisha ta juya ta kalli Nana sanda ta bangajeta kafin ta danne duk wani abu dake taso mata tana fadawa kanta Nana bata cancanci ganin fushinta ba. Ta tunawa kanta da Maman Nana da kyautatawar ta a gareta. Maman Nanan da tana zaune a kitchen tana tattare kwanukan da tayi girki dasu da daddaren lokacinda Aishan ke shigowa Nana ta bangajeta. A idanuwanta komai ya faru kuma itama bayan ta kalli ledar dake hannun Aisha sai kawai taji a ranta taji dadin bangaje Aishar da Nanan tayi.
Ta juya sanda Aishar ke karasa shigowa cikin gidan tayi kaman bata san ma da ita ba tana cigaba da ayyukanta. Aishar ma kuma dama koh hanyar kitchen din bata kalla ba ta wuce dakin Inna inda Khausar ke kwance a kasa saman bargon da Inna ta shimfida mata ta dora pillow tana assignment dinta da fitilar wayar Aisha da ta bata dan dukda akwai fititlar Inna mai batur da aka kunna aka dora akan mirrorn dakin hakan baisa tana ganin layyukan rubutun work book din nata ba da kyau.
Inna kuma waya take da Uncle Muhammadu da ya kirata su gaisa. Yayinda Juwaira ke dinkewa Khausar aljihun wandonta na makaranta da zare da allura wanda tace ya yage dan kwanaki kudinta data saka a ciki faduwa sukai.
"Yaaya an kiraki"
Khausar ke fada bayan ta amsa sallamar da Aishar tayi. Aisha na jin haka zuciyarta tayi wannan kadawar dan yanxu mutane biyu ne kadai suke kiranta daga Mu'azzam sai shi. Ranar da tayi masa bacci a waya Allah kadai yasan iya kunyar dataji. Ya ilahi shigewa karkashin teburinta ne kadai batayi ba sanda ya shigo office din tareda Habeeb washe garin ranar dataje aiki. Da farko da taje tayi tsammanin yana ciki ne ta zauna tana lissafin yanda zata shiga cikin office din nasa bayan abun kunyar da tayi jiya tunda duk idan tazo sai ta shiga ta karanto masa schedule dinsa na ranar. Ta zauna tana ta lissafe lissafe, ita bata ma san yanda akayi bacci ya dauketa ba sai tashi kawai tayi taga ipad din a gabanta da wayarta yashe a katifar bayan ta zame daga hularta.
Kuma tana zaune a wajen ne ya shigo office din muryarsa mai taushi tana fita da maganar da yake fadawa Habeeb dinda ke biye dashi a baya. Taji zuciyarta ta nutse tana fadawa cikin cikinta gabaki daya sanda ya juyo ya kalleta kuma da kyar, da kyar ta samu muryarta ta fito tana musu barka da safiya sanda yace mata ta biyosu cikin office din.
Sam bai nuna mata wata alama ba da zata nuna cewa sunyi waya jiya ba har tayi mai bacci a wayar. Tayi briefing dinsa akan schedule dinsa kafin suka zauna suna tattaunawa akan wasu manyan mutanen da zasu zo kamfaninsu signing contract. Akwai meeting dinda za'ayi kuma tun a ranar suka soma shiryen shiryen sa kuma a yanda Aisha ta fahimta wannan contract din yanada matukar mahimmanci ga Yk Ventures shiyasa ta dage sosai kamar yanda taga dukansu sun dage akan shirye shiryen meeting din.
Wannan ne dalilin kiran da El Yakoub ya mata dan akwai rubutun da tayi da yace mata tayi editing wasu wajajen ta turo masa tasan kuma ya jita shiru shiyasa ya kirata. Ta karbi wayar daga hannun Khausar tana sauke ledar nama da Yogo fura dinda Mu'azzam ya bata tana duba wajen kiran. El Yakoub dinne ya kirata kuma mai makon taga missed call sai taga alamun an dauki kiran. Ta dago ta kalli Khausar dinda ke kallonta itama tana cin karshen biron dake hannunta.
"Khausar daukar kiran kikayi?"
Khausar ta hade labbanta biyu tana gyada kanta.
"Na shiga uku yarinyar nan kin kasheni" Aisha ta fada tana kaiwa zaune kan gadon Inna.
"Mey ya faru" Juwaira ke tambaya tana jan zaren alluran data soka.
"Kira na akayi yarinyar nan taje ta dauka toh me kika ce masa?" Aisha ta fada tana danna kiran dan taga dadewarsa.
"Au shiyasa dazu naganki kina noke noken kai ashe magana kike a wayar"
Juwaira ta fada tana kallon Khausar dinda tayi tsuru tana kallonsu.
"Kusan minti daya fa, Khausar me yace me kukace?"
Khausar da har idanuwanta sun fara kawo ruwa dan dama akwaita da saurin kuka tace
"Toh naga ana kiranki fa bakya nan shine na dauka nace bakya nan yace ina kikaje nace mai kin fita zance da Yaya Mu'azzam shine ya tambayeni idan na gane sa nace mai aa yace wai wannan Uncle dinnan ne da mukaje super market dashi"
Tsabar mamakin daya cika Aisha runtse idanuwa tayi kawai ta koma baya tana kwantawa kan gadon Inna. Inna lillahi Khausar ta kasheta. Ta fita zance kuma, ta fita zance Khausar tace masa????? Ya ilahi, ya rabbi Khausar ta gama tona mata asiri. Tana jin yadda Juwaira ke yiwa Khausar fadan karta sake daukar mata waya har zuwa sanda Inna ta gama wayar tana tambayar hayaniyar meye ne akeyi.
Ta mike zaune kawai ta turawa Juwaira ledar naman dan dukda yanda take son naman nan dan wani d'an kusa da anguwar su ne ana ce mai Sule yake naman sai taji ba zata iya cinsa yanxu ba. Ta share Khausar dake ce mata tayi hakuri ta bata wayar toh ta karasa assignment din. Ta dauko ipad dinta dake cikin jakarta dake rataye a cikin durowar su kafin ta zauna kan gadon tana kunnata. Ta fara aikin da ya turo mata tana saurarensu sanda Inna tace Juwaira ta dibi naman da furar ta kaiwa Maman Nana har tana cewa Mu'azzam dinnan akwai kyauta kafin daga baya kuma ta juye maganar zuwa yaro sai aukin zuwa bakin kofar gidansu da kiran wayar Aishar da kuma siyen abubuwan kwalama amma bazai turo iyayensa ba a tsaida magana.
Tana jin sanda Juwaaira ke ce mata ai tasan bai gama makaranta ba har yanxu. Inna tace mata toh tunda Aishar zaunawa zatayi tana jiransa sai su gani kafin ta fara lissafin yadda ita diya mace bata jiran saurayi sai dai saurayi ya jirata dan ita saurin tsufa takeyi shikuwa namiji baya tsufa da wuri itama jikar Hajiya Zulai Nabila dake nan makotansu ba haka akayi ba. Ta cigaba
"Shekara nawa tayi yaron nan Aminu na zuwa wajenta caa nake ba har wajen Mallam yake tsayawa su gaisa ba amma da yake yaron nan babu rabonsa sai gashi wani na zuwa koh wata uku ba'ayi ba akayi auren".
Juwaira dai sai jinjina kai takeyi
"Toh ai Inna kinsan kowa da tasa kaddarar yanxu zakiga ya gama karatun manya sun shigo maganar nan".
Inna ta tabe baki tana lalubo radionta
"Allah dai ya zaba muku abunda yafi zama alkhairi".
"Ameen Inna" Juwaira ta fada tana mikawa Khausar tata furar.
Aisha ta cigaba da aikinta har suka bar wannan zancen suka dakko wani. Tana gamawa kuwa ta tura masa kuma sabanin daa da duk idan ta tura mai aikin da yace tayi yana tura mata kalmar "Okay, good" koh ya turo mata wani gyaran da zatayi wannan karon baice komai ba har safe kuwa bayan ta tashi asuba ta sake duba wayar. Da asuban nan kuma rashin lafiyar Khausar ya tashi dan sanyi ne ya shiga jikinta da ya saka kafafuwanta ke mata ciwo sosai. Shiyasa makarantar ma sai hakura tayi bataje ba.
Aisha ta shirya cikin wani material fari mai fulawowi launin zuma. Sabo ne dan yana cikin wanda Inna ta saka Uncle Murtala ya turo kudi aka dinka mata sanda ta fara aikin nan. Tayi rolling da gyalen data siyamai shima launin zuma mai duhu kuma sosai kayan suka karbeta matuka da gaske. Ta fita bayan sunyi sallama da Mallam da ta samu wajen gidan yana magana da Sani d'an garuwansu dake kawo musu ruwa. Tana isa kamfanin straight sama ta nufa ta elevator. Kuma elevatorn tana kaiwa second floor ta tsaya kofofinta suka bude El Yakoub ya sako kansa a cikinta kamsin turarensa tsadadde ya cika iskar wajen tareda bugawar zuciyar Aisha a allon kirjinta.
"Good morning sir"
Ta furta mai bayan ya shigo dan kallo daya yayi mata ya dauke kansa. Yau jumu'a ta tunawa kanta tana kallon shigar kaftan dinda yayi yau launin brown dinda ya karbesa sosai yana hasko fatarsa mai kyawun kallo. Hular daya saka ma tana sake fitoda kwarjininsa da girmansa. Ba wani abu dake burge Aisha kuwa kamar jajayen hannayensa da suka sake wani kyau saboda wani bakin agogon da ya nada a tsintsiyar hannun ya rabbi Allah yayi halitta mai kyawu a nan.
"Morning" Ya amsa ta da muryar nan tasa mai taushi kafin shiru ya mamaye wajen kuma a cikin wannan shirun ne Aisha ta tuna kalaman Khausar data ce ta fada mai jiya. Ta dago ta kallesa ta kasan idanuwa tana tunanin yanxu yasan tanada saurayi kenan? Toh mey aciki? Take tambayar kanta bata kai tayi saurayin bane koh kuwa bai kamata tayi saurayi bane? Ta rasa gane dalilin tsarguwarta. Suna isowa third floor din kuwa elevatorn ta bude suka fito Ayo na gaishe sa dukda kuwa ya jima da zuwa.
Ya shige office dinsa ita kuma ta karasa table dinta ta tattaro takardunta taje office dinsa tana karanto mai schedule dinsa na ranar, bata kuma san wa ya tabasa ba ranar dan fuskar nan tasa a game take yau koh kallonta bayayi idan yana magana dukda dama can ba kallon nata yakeyi ba amma wani sa'in idan tana yimai wasu bayanan yana dagowa ya kalleta amma yau kam babu wannan duk kuwa da yawan kai kawon datayi a office din nasa.
Yanxu ma ta sake shigowa dan Ameer ( secretary din Habeeb ) ya shigo ya kawo mata wasu takardu dake bukatar saka hannunsa. Tana shigowa kuwa ta karasa tebur din nasa tana fada mai gasu kuma bata kai ga sauke su saman tebur dinsa ba yace da ita
"Karanto mun naji"
Dama ba yau El Yakoub ya saba sakowa Aisha maganar da sai daga baya take fahimtarta ba. Ba yau ne farko ba shiyasa bataji shayin cewa
"Na'am" ba sanda ya fadi maganar tasa.
"Ki karanto mun contract din ina jinki Aisha" ya fada yana cigaba da danne dannensa a keyboard manyan tafukan hannayensa na kusan rufe keyboard din gabaki daya.
Aisha ta kalli file dinda ke hannunta dan akalla pages din sun kai wajen bakwai kuma ba manyan rubutu bane. Yanxu duka wannan din zata karanto mai kenan? Wannan wani irin mutum ne shi? Ta koma gefe kafin ta bude file din ta fara karanta mai ahankali tunda ta gan aiki yake dan har shiru tayi ta dago ta kallesa bayan ta karanta layi na farko ta ga yana cigaba da danne dannensa kafin ta cigaba ahankali din dan gani take kamar ba jinta yakeyi ba. Kuma har ta gama karanta pagin farko kafin ta jiyo muryarsa
"Aisha"
Ta dago daga kallon takardun tana ware idanuwanta a kansa. Wani abu da ya saka El Yakoub lumshe nasa idanuwan a hankali ya bude dan yau gabaki daya wannan ne karo na farko da suka hada ido da ita.
"You're too slow sai ki sakani bacci ai"
Aisha ta hadiye wani abu da bata san da zamansa a makogwaronta ba sanda taji wannan furucin nasa kafin ta kalli computersa kuma watakila wannan kallon datayiwa computer tasa ne ya saka ya fahimce dalilin da ya saka take karatun ahankali sai kawai yace
"Karki damu ina jin komai da kike fada trust me" Ya karasa yana dauke idanuwansa daga kanta.
Sai kawai itama ta gyada kanta ta fara karanta mai kamar yanda ya umarceta din kuma sai da ta karance shafuka bakwai dinnan tasss tukunnna ya karbi takardun ya saka hannu a kai ya bata yace ta kaiwa Ayo. Kuma kawai sai gabaki daya ranar duk abunda ta kaimai in dai ya shafi takardu sai ta tsaya gaban teburinsa ta karanta mai shi tass komi yawansa kuwa. Wannan ne ya saka take ta shan ruwa ranar dan bakinta bushewa yakeyi idan tana mai karatun nan saboda yanda suke hada idanuwa wani sa'in idan ta daga ta kalleshi dan tabbatar da cewar yana saurarenta. Ta rasa meye dalilin wannan sabon salon tunda dai tunda ta fara mai aiki bai taba cewa ta karanta mai abu ba sai yau toh meyasa ? Wannan ai idan aka duba ta wani idon punishment ne wallahi.
Kuma abunda Aishar bata sani ba punishment dinne dagaske yake bata din. Dan jiya bayan ya tura mata file dinnan yaji shiru sai kawai ya yanke shawarar kiranta a waya da tunanin Allah sa batayi bacci ba kamar ranar dukda dare bai gota ba sosai saboda yana bukatar file dinnan gobe. Kuma yana kira Khausar ta dauka suka gaisa ya tambayeta ina Aisha tace mai ta fita zance. Zance? Hira kenan da "Yaya" kamar yanda Khausar ta kiraye shi wanda Aishar taje zancen wajensa.
Ya lumshe idanuwansa bayan sun sauke wayar yana hango Aisha da jan gyalen nan nata tsaye a gaban wani suna "zance" kamar yanda Khausar din ta fada yana sauraren muryarta wata kila hadda guzirin murmushin nan nata da takeyi idan Habeeb ya fadi wata maganar idan suna tattaunawa koh. Ya rabbi bai san meyasa ba amma kawai ji yayi ransa yana baci dan da kowace lumshewar idanuwan da zaiyi yana hango Aisha ne tareda wani suna zance.
Wato zancen ne ya hanata yimai aikin da ya sakata koh? Wannan bacin ran ne da tunanin ya haddasa mai baccin dole dan tashi kawai yayi ya rufe duka abubuwan amfaninsa kuma bayan yasha maganin ciwon kirjinsa sai kawai ya hada hadda wani maganin baccinsa da ya dade baiyi amfani dashi ba tun lokacinda yake wani ciwon kirjin dake hana shi bacci da daddare likitansa yayi mai prescribing dinsa daga baya kuma yazo ya daina amfani dashi amma ya ajiye just in case. Ashe kuwa ranar amfaninsa zatazo dan yana shansa ya kwanta sai bacci. Saidai bai yi mai maganin ainahin matsalar tasa ba dan yana tashi daga bacci abu na farko da ya tuna dashi shine maganar zancen nan ya kuma rasa meyasa abun yake zaune a ransa har da safen nan. Har da safen nan da ya hadu da ita a cikin elevatorn nan da yanda yaga tayi kyau cikin material dinda ke jikinta da ya haska fatarta mai walwali a safiyar nan.
Wata kila tafi haka kyau da taje zancen nan jiya koh? Tunanin yazo ransa batareda ya shirya ba sai kawai ya sake tamke fuska ya wuce office dinsa. Kuma haka kawai sanda ta shigo mai da takardun contract dinnan ya samu dabarar karatun da yace tamai. Ba dai zance taje jiyan ba tana hira yanxu zai bata wani abu da zatayi amfani da muryarta tayi dashi mai amfani ba wai wani zance ba da wani namiji can.
Can da yamma suna zaune su hudu a kujerun dake tsakiyar office dinsa. El Yakoub da Habeeb suna zaune a doguwar kujerar nan tasa sai ita da Ameer dake zaune akan kujeru guda biyu dake kallon doguwar kujerar sai center table dinda ke tsakiyar su dake cike da abubuwan amfaninsu na aiki.
Tattaunawa da tsare tsare sukeyi akan meeting dinnan yayinda kowa yake aikinsa ana kuma gyara wasu ababen. Akai akai kuma El Yakoub yake dago idanuwansa ga Ameer da Aisha dake zaune a gabansu. Ameer din yana nuna mata wani abu a cikin takardun dake hannunsa yana jan layi da biron dake hannunsa akan rubutun ita kuwa tana gyada kanta ahankali.
Ya sake tamke fuskarsa dan tun dazu Ameer din yake saka Aishar magana dan koh wani abu ta rubuta sai yace ta nuna mai yagani koh idan shi ya rubuta din zai wani duka yana nuna mata bai san kuma meyasa abun yake sake dulmiya mai mood dinshi ba na yau gabaki daya dan koh Habeeb ya lura cewa baya cikin mood din magana sosai.
"Toh Alhamdulillah" Habeeb ya fada yana sauke ajiyar zuciya bayan ya rufe laptop dinsa dake gabansa.
Aisha ta kalli lokaci akan agogon dake sanye a hannun Ameer dake nuna mata abu a takardunsa. Dama ta gayawa Inna yau bazata dawo da wuri ba saboda tunda aka fara maganar meeting dinnan ayyuka suka sake yin yawa wanda shi yasaka daga yau zuwa sanda za'ayi meeting dinnan karfe shida zasu ringa tashi daga wajen aiki. Inna nata mitar wahalar aikin nan dan taya za'ayi ace mutum yaje aiki wai daga karfe takwas zuwa karfe shida ai abun yayi yawa. Har Maman Nana na tayata kan cewa dama tun farko wai saida ta jiyewa Aisha wannan wahalar dan dai duk wanda yaji makudan kudaden da ake biyanta duk wata yasan cewa wannan aikin zaiyi wahala hadda karawa da wannan ai ba aikin mace bane aikin maza ne. Har wata magana tayi data bala'in tsayawa Aisha a rai kan cewa wai ita mace ai mutuncinta yafi daraja akan komai tana alakanta wannan maganar da aikin Aishar. Ita bata ma tsaya ta gama fahimtar maganar da kyau ba amma tabbas maganar ta tsaya mata a rai. Toh me maganar Maman Nanan take nufi kenan?
Ameer nagama nuna mata takardun nan shima ya fara hada kayakkinsa itama dama ta gama Allah Allah take ta tashi ta wuce dan dama tana so ta tsaya Pharmacy ta siyawa Khausar maganinta da inhaler ta data kusa karewa. Itama ta hada kayanta sukayiwa El Yakoub da Habeeb sallama suka fice.
Habeeb shima yayi sallama da El Yakoub ya fice. Sai kawai shima ya rufe Macbook dinsa yana tattare takardun ya ajiye sanda wayarsa da ya baro kan table ta fara ringing. Ya tashi daga kan kujerar ya karasa table din ya dauka suka gaisa da Mahmoud yana fara karanto mai wasu bayanai akan aikin da ya basa. Kuma acikin duk wannan bayanin na Mahmoud ne El Yakoub ya taka zuwa gaban manyan gilasan nan da aka zagaye ofishinsa dashi yana hango hadarin da ya taru a sama giragizai na harhaduwa. Ya kai dubansa kasa sanda idanuwansa suka sauka akan Ameer dake tafiya rikeda jakarsa ta aiki yana nufar parking lot din harabar kamfanin. Yagan sanda ya juyo yana magana da wani koh yace wata dan lokaci daya ganinsa ya dauko masa Aisha itama tana bin bayan Ameer din da y'ar jakarta data ratayo.
Yaga sanda Ameer din yayi wani murmushi kafin ya danna makullin motarsa fitillunta na haskawa alamar ta bude. Yagan sanda Aisha ta zagaye passenger's side tana kai hannunta zata bude motar ai kawai bai san sanda ya katse kiran da yakeyi da Mahmoud ba lokaci daya ya shiga calls yana neman numberta.
Kuma bai san cewa zuciyar dake bugawa a kirjinsa bugawa takeyi da tsananin karfi ba sai da yaji call dinnan yana ringing lokacinda Ameer ya tada motar bayan ta rufo kofar.
"Hello" ya jiyo sautin siririyar muryarta. Tana rufe bakinta kuwa yace
"Ki jirani a reception Aisha"
Ya cigaba da kallon motar Ameer sanda tayoyinta suka fara tafiya yana fita daga parking lot din.
"Na'am"
"Aisha, nace ki jirani a reception"
Kuma watakila Aisha taji wannan abun dake cikin muryarsa wanda ya saka ta fadin kalmar
"Okay sir" kafin ta kashe wayar kuma sakkanni uku kacal sanda motar Ameer din ta tsaya a tsakiyar harabar kamfanin Aisha ta bude motar tana fitowa. Baisan sanda ya sauke wata ajiyar zuciya ba kafin ya juya kawai zuwa cikin ofishin nasa sanda kiran Mahmoud ke sake shigowa. Sai kawai ya tura mai message yana ce mai ya tura mai komai ta email kafin ya tattaro kayakkinsa ya fito daga office din. Ya shiga elevator data kaisa kasa, kofofinta na budewa kuwa idanuwansa suka sauka kan Aisha dake tsaye a wajen counter din reception dinda ba kowa hannayenta duka biyu na rike da jakar dake rataye a kafadarta idanuwanta na kallon waje. Tana kallon hadarin dake cigaba da taruwa duhu na sake mamaye sarararin sama alamar dake nuna kowani lokaci ruwan zasu iya fara sauka. Ya karaso wajenta sanda ta juyo tana kallonsa bayan taji karar takun tafiyarsa. Yana karasowa kuwa yace mata
"Muje"
Kalmar data sake jefa Aisha cikin rudani. She's just so confused. Me yake nufi da suje? She thought wani aikin zai bata fa shiyasa yace ta dawo. Kuma ita Allah yagani dukda yanda taso cewa a'a da Ameer yace tazo ya sauketa saboda ruwan da ake kokarin yi kasawa tayi saboda tasan cewan taimakonta zaiyi dan yanxu ko kafin ta samu adaidaitan da zai dauketa daga nan aiki ne gashi kuma zata tsaya pharmacy kafin ta sake samun wani sai wani iko na ubangiji barinma idan ruwa ya fara shiyasa da kyar ta iya cewa Ameer yaje zatayi wani aikin ne da ta manta batayi masa ba ya tafi kawai. Kuma shine yanxu zaizo yace mata suje? Dama ba wani aikin zata mai ba? Sai kawai ta sauke ajiyar zuciya ta bisa din suna ficewa daga cikin kamfanin zuwa waje inda iska mai sanyi take kadawa. Taga ya nufi motar sa yana bude ta kafin ya nuna mata dayan gefen alamar ta shiga kenan. Ta zagaya din ta shiga sanda yake ajiye duka kayakkin da ya dakko a back seat kafin ya juyo yana tada motar ya jata suka bar harabar kamfanin yakai hannunsa ya seta temperataure din Acn motar.
Kowannensu yayi shiru yana kallon hanya kuma can har sun d'anyi nisa ya jiyo muryarta.
"Sir ba gida zanje ba fa"
El Yakoub ya juyo ya kalleta sanda itama ta juyon ta kallesa kuma ganin irin kallon da yayi mata ya saka Aishan cewa
"Zan tsaya wani waje"
"Ina kenan" ya tambayeta.
"Khaleel pharmacy" ta fada tana kamo gefen rigarta tsakanin yatsunta wani abu daya dauki idon El Yakoub. Mesa take yawan rike abu a yatsun ta idan tana magana. Ya lura koh a office ne idan ta kawo masa wani report koh file koh wani abu idan ba biro ne a yatsun nata ba toh takarda ce idan babu takarda toh gyalenta ne.
"Okay direct me" ya fada.
Ta gyada kanta kafin ta fara nuna mai hanyar pharmacy din har sanda suka iso. Suka fita kusan a tare daga motar yana rufeta da key iska mai sanyi na cigaba da kadawa. Suka shiga ciki ta fadi maganin da za'a bata mutumin ya dakko mata tareda inhaler da tace ya dakko kuma daidai sanda El Yakoub ke baiwa mutumin kudin da ya kirgo daga cikin wallet dinsa d'aya daga cikin wasu y'anmatan dake bayan Aishar ta furta wata magana
"Abida kalli couple dincan wallahi sun min kyau sosai"
Aisha taji zuciyarta tayi dumm dan koh rantsuwa bazatayi ba tasan cewa El Yakoub yaji maganar nan dan yanda tasan sa da kunne bazai yiwu ace bai ji yarinyar ba. Ta jiyo muryar Abidar da akayiwa magana tana amsawa
"Wallahi nima haka na so nayi magana kika rigani sun dace sosai"
Aisha bata san sanda ta sunkuyar da kanta ba cikin kunyar da Allah yagani koh sanda tayi bacci a wayar nan da sanda Khausar tace mai ta fita zance bata jita ba sai yanxu. Ya rabbi ya Allah. Ta karbi ledar maganin suka juya suka fita tana furta mai kalmar godiya. Ta kalli y'an matan nan dake maganarsu har suna hada ido da daya daga cikinsu dake mata murmushi. Kunya zata nutsar da ita dan bayan sun fito waje sai taji dama itama zata bi iskar dake kadawa kawai ta bace daga wajen.
Sai bayan sun fara tafiya tukunna El Yakoub yayi mata tambayar da tun dazu yake so yayi barinma sanda yagan inhaler dinnan.
"Dama bakida lafiya ne".
Aisha ta kalli ledar maganin dake hannunta kafn ta girgiza kanta
"A'a maganin Khausar ne"
"Subhanallah bata jin dadi ne" Ya furta sanda yake shan wata kwanar hannayensa na juya kan sitiyarin motar.
"Eh" Ta amsa sa.
"Allah ya bata lafiya"
"Ameen nagode sir" Ta sake fada.
"Aisha" Taji ya kira sunanta.
Ta dago ta kallesa taga ita yake kallo sai kawai ta dauke idanuwanta
"Sir" ta amsa sa
"Banason yawan godiya" ya furta bayan ya maida idanuwansa kan hanya.
Aisha ta gyada kanta kawai tana shakar iskar motar dake gauraye da turarensa mai sanyin kamshi kuma ba wanda ya sake cewa komai har sanda ruwa suka fara sauka suna kara karfi da kowace wucewar dakika. Suka iso gidan su Aishar inda ya paka daidai gaban gidan yanda tana bude kofarta zata shige cikin rumfar batareda ruwa ya jikata ba. Aisha tasake rataye jakarta a kafadarta tana rike da ledar maganin nan.
"Sir nago.." bata karasa ba saboda yanda ya juyo gabaki daya yana kallonta. Irin wannan kallon marar fassarar nan. Wannan kallon dake sakata jin kamar fatar jikinta zata narke yadda ake narkar da sugar.
Sai kawai tayi shiru bata karasa ba.
"Ki gaishe mun da Khausar" ya furta.
"In sha Allah" Ta fada kafin ta bude kofar motar tana rufo ta saukar ruwan saman jikin glass din motar yana disashe mai ita sanda take shigewa cikin gida.