MURADIN ZUCI

Muradin zuci

by @bintuuu

Ta bude kofan amma sanin hali irin nata yasa ko shi Papan baya shiga sabgarta in ba dole ba duk da kuwa suna kwana kuma su tashi a daki daya. Every morning in sun tashi zai tambayi yanayin jikinta koda bazata amsa ba wani lokacin, sannan kuma yana lura da duk motsinta dalilin haihuwanta na nan tafe ko yau ko gobe. Wani zubin ma in yaga tana takawa da kyar shida kansa zai riqe ta ya tallafa mata wajen zuwa toilet da sauransu amma har sannan bata kulasa sosai. Ga yaranta ma hakan take saboda sun san halin mahaifiyar tasu a duk lokacin da take cikin irin wannan halin sai suke kaffa kaffa da ita. Banda Jidda da take zama a gurinta su twins zuwa suke gaisheta sannan su koma dakinsu, barin ma Imam da daman maganar bakinsa aiki ta zame masa. A tarin lokuta suma kansu iyayen suna mamakin hali irin na yaron nasu da ya kasance mai nutsuwar da ta kere sa'anninsa, wani irin haiba da nutsuwa Allah ya saka masa mai ban mamaki. Abun qarin burgewa game da lamarinsa shine yanda he's always attentive akan komai. Duk abunda yakeyi indai za'a yi masa magana nan zai maida dukkan hankalinsa yana sauraro kamar wani babba, dadin qarawa ta yanda ya dauki lamarin Fadwa da girma shi ya qara baiwa Papa mamaki game dashi, yayin da gadon sa ya zamo gurin baccin Fadwa a tarin lokuta, ko da Habiba ta tafi yin hidimar Momma shi yakan zamo mai kulawa da Fadwan har ta gama abunda take wanda bazaka taba ganin Imran yana yin hakan ba saboda yanda ya daukaki bacci da muhimmanci a rayuwar sa fiye da komai. A wannan lokutan da Fadwa take yawan yin bacci akan gadon Imam din haka zai tisata a gaba yana zanata a white sheets dinsa kuma ba wanda yake nunawa ko da wasa sai Imran kadai da ya sani kuma bai maida hankali akai ba dalilin sabon da yayi da ire iren zanen da Imam din keyi, dan harshi ma yana zanashi.  in kuma Fadwa ta tashi Imam dinne zai kaita gurin Habiba ta bata duk kulawan da take buqata amma kuma yanayin hakan duk bada sanin mahaifiyar tashi ba. 
Dan wani irin zaman daki Momma ta koma yi kamar wadda ake kora daga gidanta, bata dai yin wannan mugun fushin amma kuma duk wani fara'anta da ake gani a gidan ta dauke daga fuskarta, kuma duk da hakan Papa bai fasa siyo mata duk abunda yasan tanason din ba, bai fasa kulawa da lamuranta ba, bai fasa zama da yaransa suyi hira ba, bai fasa cin abinci tare da iyalinsa ba, bai kuma fasa kula da Fadwa ba dan itama ya dauketa kamar 'yar cikinsa da kulawanta solely yake qarqashinsa yanzu. Duk wani abunda yasan Baby na buqata yana siyo mata shi harda maji gaba sannan bai fasa rainonta ba, akasarin lokuta Idan ya dawo daga gurin aiki zai dauketa a hannunsa su zauna anan falon suyita hira shida yaran nasa suna kallon wild life a TV, dan Papa mutum ne mai son kallon abunda ya shafi rayuwar dabbobin jeji sosai.
Hakan da sukeyi shima sai ya zamto abunda yake qara tunzura Momma ganin 'ya'yan nata mazan ma basu damu da zuwa gurinta suyi hira ba wanda kuma itace sanadin hakan, mace ce da Idan tana cikin yanayi na bacin rai ko nukra sai ya shafi har 'ya'yan cikinta, abu kadan ta kai bugu, abu kadan tayi hantara ko zagi wanda duk yana daga cikin abunda yasa 'ya'yan nata suke janye jikinsu daga gareta in tana cikin wannan halin...They know better than to go near her.
Bata sake zuwa inda Fadwa take ba tun incident dinda ya farun, ta danne komai aranta tana rayuwarta batareda ta waiwayi inda jinjirar take ba ko sau daya. Bata kuma damu tasan halin da mijin nata suke ciki akan kula da yarinyar ba wanda hakan ke qara ba Papa mamaki akan miskilancinta, amma sai ya danne komai arai shima ya cigaba da sauqe nauyin yarinyar da ya rataya a wuyansa batareda yabi ta kan matar tasa ba.

Bayan sati biyu a wani yammaci Papa ya dawo gidan daga gurin aiki, a gajiye ya shigo falon sai ya samu Momman da yaran nasu duka a falo suna zaune ranan, Habiba na zaune a qasan Momma dake zaune akan kujera tana yanke mata farcen kafafunta, bayan Jidda ta taro shi da murnan ta sai suka qarasa ciki ya zauna a kujeran dake facing din matar tasa, twin suka masa sannu Habiba ma tana qoqarin miqewa tace "Barka da dawowa ranka shi dade" ya amsa da Yauwa sannan ya kalli Momman yace "How are you feeling?" cikin qanqanuwar murya ta amsa "Lafiya" sai ya sake kallon su Imran dake zaune a gefenta yana cin popcorn while Imam na riqe da nashi a hannu, yace dasu "Yau baku dauko qanwar taku ba ne?" dan tun da ya shigo ya lura da dukansu ne zaune a falon banda Fadwa, Imam baice komai ba amma dai Papan ya lura ba cin popcorn din yake ba yana zaune agurin ne kawai, kallon Habiba yayi data kawo masa drinks da bottle water yace "Yau tayi baccin yamma ne?" tace "Yanzu zan qara dubota ranka shi dade" Imran yayi saurin cewa "Batayi bacci ba Papa" sai kuma ya kalli Maman tasu da har sannan bata dago kanta daga gyaran farcen hannunta da takeyi ba, kallonta Papan ya tsaya yi yana ayyanawa aransa yau ma ta hana a kula da yarinyar kenan, sai ya dan girgiza kai tareda miqewa ya nufi dakin da Fadwan take Imam ya bisa da kallo. Bai dade ba ya fito falon hannunsa riqe da Fadwan sannan Habiba na biye dashi a baya cike da sanyin jiki, sai da ya iso gurin Momman ya juya yana kallon yaran nasa yace "Go upstairs" suka miqe Imam ya kama hannun Jidda suka nufi saman, saida ya jira suka shiga dakinsu sannan ya sake kallon Matar tasa da taqi kallonsa, a nutse ya budi baki yace "Fatima, kinsan Allah zai iya miki hisabi da wannan yarinyar?" ta dago kai tana hade fuska tace "Wane irin hisabi? Menene hadina da ita? Ko ka taba ganina a kusa da ita balle wani abun ya hadoni da ita?" bai bar kallonta ba yace "Why are you so cruel ne nikam? She's just a baby, a few weeks baby. Me ta sani a duniyar nan da har zaki rinqa mata irin wannan hukuncin?" rai abace Momma tace "Wai me na mata dan Allah?" Yace "Kin fini sanin me kikayi Fatima, yanzu ki duba fa kiganta, kashi ne a jikinta tun na safe yana wari, sannan ko madaranta baki bari an bata ba, bata samu na mahaifiyarta ba sannan wannan din ma sai an mata katanga dashi?" ya qasara maganar zuciyarsa na karyewa yana qara riqe Fadwan a jikinsa wadda har sannan idonta biyu kuma batayi kuka ba, sai Momman ta fara kokarin miqewa tace "Yaushe na hana a bata madaran?" ta kalli Habiba dake bayansa "Ni na hanaki bata madaranta?" Habiba ta girgiza kai da sauri tana qara sunkuyar da kanta, sai Papan ya sauqe numfashi yace "Fatima, duk wani fushinki da zakiyi ya qare a iya kaina, in kina qaunar Allah da manzonsa ki daina uzzzurawa yarinyar nan, babu ita acikin lamarin nan dan bata zabi hakan ba itama, in laifi ne naji. Ni na miki laifi amma ki cire ta aciki" sai lokacin Momma tayi wani qaramin murmushi tace "Au kasan kamin laifi kenan?" cikin gajiyawa yace "Face me, but don't drag this innocent child into this please" tace "Ka maida ita inda ka daukota, na fada kuma zan qara fada bazan riqeta ba Abdulaziz. Tun ba'a je ko Ina ba ni da yarana ka fara nuna mana banbanci akanta. Tun ba'a je ko Ina ba ka fara fifita ta akanmu" Papa baisan lokacin da ya zauna a kujeran gurin ba yana kallonta, ta cigaba da kallonsa tana fadin "Bazan lamunci ganin bare tana zama abun fifiko a zuciyarka fiye da jininka ba" ba shi kadai ba har Habiba ta girgiza da furucin bakin Momma, amma kafin ya amsa mata ta juya da saurinta ta nufi dakinta tare da bude kofan da karfi sannan ta shiga ta banko kofar duk suna kallonta shida Habiba dake tsaye a gefe har sannan. Sauqe nauyayyen numfashi yayi sannan ya miqa Fadwan ga Habiba yace "Ki mata wankan, amma ki fara bata madaran nata tukunna" ta qaraso ta karbi yarinyar itama zuciyarta na karyewa ganin yanda Fadwan ta fara koyan hakuri ala dole, sai taji ya sake cewa "Please ki rinqa iya kokarinki na ganin kin bata duk abunda take buqata, kuma ki rinqa fahimtar da uwar dakin taki akan gaskiya ko da a fakaice ne, yarinyar nan itada maraya banbancinsu kadan ne. Kema zaki iya fuskantar naki hukuncin a gurin Allah in har kika tauye mata hakkin kulawanta da na rataya miki" a sanyaye tace "Ka gafarceni ranka shi dade, da yardar Allah zan gyara" ya gyada kai kawai tareda daukan ruwan dake kan table din ya fara sha, da haka kuma ya miqe ya nufi dakinsa da ke upstairs dan yanda mai dakin tasa ta banko kofarta yasan ta datse harda makulli kuma.
Amma ga mamakinsa da dare bayan ya gama putting yaran nasu to bed ya dawo dakin nata sai yaji a bude ta cire makullin, kan gado ya hangota ta kwanta as usual ta juya masa baya tana kallon ginin dakin, sai da ya kwanta tareda jan duvet ya juya bayansa shima sannan yaji muryanta qasa qasa tace "Ladan ne ya baka shawaran daukanta?" ya juyo amma bai amsa ba, sai ta miqe zaune itama ta juyo tana kallonsa ta sake cewa "Ladan ne ya saka ka daukota ko?" yace "Meyesa Ladan zai sani yin abu kamar wanda yayi owning dina?" tace "In bashi ba nasan ba ta yanda za'ayi nace maka banason abu kuma kaje ga abun nan, bamu taba haka da kai ba Baban jidda, meyasa zamu fara yanzu?" nan ya miqe zaune shima yace "Tun farkon ganina da yarinyar nan naji tausayinta kuma naji Inason kulawa da ita, da kika nuna bakyaso sai na fara tunanin in bada itan tunda baki aminta da mu riqetan ba, amma sai kikayi defying maganata Fatima. Kika nunamin kinada ikon kiyi abu a karin kanki bada izinina ba" tana share hawaye tace "Wallahi zuciyata bata aminta da yarinyar bane, yara irinsu akasari zakaga ba ta hanya me kyau aka samesu ba, d'an bature ba abun riqewa bane" sai yayi saurin cewa "D'a na kowa ne sannan Fadwa ba baturiya bace, abayyane yake tana da hadin jini da balaraben mutum, ko yau kika fara ganin jinjirin bature ne? And again D'a na kowa ne Fatima, muma bamusan..." tayi saurin katseshi da "Banason kana dangantamin yarana da irin maganganun nan" sai yace "Babu wanda yasan gobe Fatima, kar kiga muna cikin arziqi da daular mulki gaba da baya...Babu wanda yasan gobe" a dan fusace tace "Toh ni kodai 'yarka ce ne yarinyar nan?" ya ware Idanu da kyau yana kallonta yace "What??" ta sake cewa "Ka bani amsa in yarka ce Abdulaziz" sai kawai ya tsaya kallonta kamar wadda kai na biyu ya tsiro mata a wuya, bata bar kallonsa ba tace "Abdulaziz" a nutse ya amsa da " Fatima, are you insane?....kaf zuri'armu kin taba ganin me irin idon yarinyar nan?" tace "Probably ta biyo na uwarta wadda kayi tarayya da ita mana" nan kuma hakurinsa yakai geji, rai a bace ya daga murya yana cewa "Da mutuncina?. Da kimata?. Na fito daga tsatson mutunci irinna gidanmu sannan ki zargeni da bin wasu matan a waje har a haifamin dan gaba da fatiha...Fatima you're insane!" kawai ya miqe daga gadon dan zamansa a dakin zai iya sawa ya fada mata abunda ze iya regretting, ganin haka ta sake hasala itama tace "Toh in ba 'yarka ba ace ka dage lallai sai ka kula da ita, baka damu da mutuncin naka ba balle kimarka" yana tsayen yace "Kinsan me?...kiyi tunanin komai ma, ki yarda da duk abunda zuciyarki zata kitsa miki akanta, ga ki ga yarinyar ki kasheta. Ni kuma zan nuna miki nine ubanta a yanzu dan sai nayi shari'a dake wallahi, Fadwa mazaunin 'yar cikina take yanzu kamar yanda hakkin kulawan Jidda ya rataya a wuyana haka itama" da haka ya juya da sassarfa ya fice daga dakin tana kallonsa with shock.

Free page 

Bintu Musa ✍️